← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 175

Sashe 31

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jiri tsaye kawai nake ina tafe da Lalura ban sani ba. Satin da muka shiga a Daddafe nayi sa saboda ciwon kan ya matsa min ga jiri da zazzabi,sai dai ban kwanta ba Saboda yara,in suka fita makaranta sai na Dad'e ina kwance ina fama da kaina tun ina Daurewa har sai da ciwon ya kwantar dani Daran jumma'a,Cikin Dare na tashi na shiga Bayi na Dauro alwala kawai jiri ya kwasheni na koma na kwanta Tun daga Lokacin jikina ya rikice,sama sama nake jin komai kaina kamar zai Tsage gida biyu ga zazzabi na jin jikina,ina so na tashi ammh na kasa tashi ina jin su Amir suka shigo suna kirana "Umma.."Umma.." Ammh na kasa amsawa Ahmad ma ya gama Budurina ajikina yana ta Dukana yana kiran sunana da gwarancinsa ammh na kasa tashi,ganin Halin da nake ciki yaran suna Tare dani barin ma Amir dake da wayau ya fahimci bani da lafiya su Anum nata damuna da surutu yace su daina Umma bata da lafiya Anum yar rigima sai ta saka kuka ganin haka Musty ya kama Amir ya Lallashe su. Ina jin Amir na taba kafata yana fadin"Umma..Umma ana buga get" Dakyar na iya bude baki nace"je ka bu d'e Amirr.." Tare suka fita da Anum da Musty yana kai wa daman wajen sakatar tsakiya ne ya bud'e ashe Haruna ne yana ganin su basu shirya ba yace"Au yau ba zuwa makaranta ne Kabiru..? Amir ya karkace kai kafin ma ya samu mgana da Sauri Anum tace"To ba Umman mu bata da lafiya ba ne" Haruna yace"Subhanallah..Allah ya bata lafiya" Aransa daman yayi tunanin haka Tunda bakwai da rabi bai taba fashi basu shirya ba,har zai wuce Anum ta saka kuka tana kiran Umman su,Haruna ya kalli Amir yana fadin"Jikin nata yayi zafi ne..? Amir ya gyada mai kai yana fadin"eh bata iya tashi ma" Cikin alhini yace"Bari nayi ma mai dak'i na mgana sai ta shigo ta duba ta..Allah ya bata lafiya" Cikin Hanzari ko ya shiga gidansa ya samu matarsa Sa'adatu na sharan Tsakar gida tana ganin mijinta cikin mamaki tace"Ah baka tafi ba ne Megida..? Cikin wani yanayi yace"Wlh ke dai bari naji shuru ne yaran basu fito ba na buga gidan sai ga su sun bude gwanin ban tausayi suna ta kukan wai Umman su ba lafiya" Sa'adatu tayi salati kafin tace"Wayyo..Allah ya bata lafiya" Ya amsa da Ameen kafin yace"Sako mayafin ki ki shiga gidan ki ga Halin data ke ciki" Bata yi musu ba ta ijiye tsintsiyan Hannunta ta shiga D'aki ta sako Hijabi tace bari taje ta gani,a kofar gidan ma taga su Amir taja su zuwa cikin gidan Halin data ganni a ciki yasa Hankalinta ya tashi da Sauri ta fita ta koma gida ta fadama mijinta ga Halin da ake ciki. Cikin wani yanayi yace"Jikin nata yayi zafi kenan..?. Sa'adatu tace"Gaskiya ya kamata a tafi asibiti" Ya jinjina kai yana fadin yana da lambar Ishaq bari ya kirasa sai dai yayi ta kira har sau uku bai daga ba sai kawai yace Sa'adatu ta shiga makotansu gidan wata Habiba ta mata mgana sai a kai yaran gidanta su kuma su tafi dani asibiti tunda ba'a samu Ishaq a waya ba. Haka ko akayi ta shiga tayi mata mgana Habiba duk da bana Huld'a da ita bata ki ba tace zasu zauna a wajenta har mu dawo tare da Fatan sauki a gareni. Sa'adatu ta sakamin Hijabi dakyar ta iya fito dani na shiga adaidaita sai general Hospital muna zuwa ganin Halin da nake ciki yasa suka karb'eni suka shiga dani bayan Dube Dube da gwaje gwaje suka bani gado bayan sun Dauramin Drip ana bukatar kudi mganguna,sannan Likitan ya fad'ama wad'anda suka kawo jini na ne ya yi sama sannan ga Zazzabi a jikina sosai. Na galabaita da sai sun rikeni anan na kwana Biyu,Allah sarki ni ban san inda kaina yake ba ammh ina kwance ne Hankalina na wajen ya'yana sai da yammah na farka da su na Bude bakina Sa'adatu ce a wajena tun Safe girki kawai ta koma gida tayi,ita ke fadamin su Amir na gidan makociyarta Habiba cikin koshin Lafiya ta tambayeni ko ina da Lambar wanda za'a kira a sanar da su nace babu Saboda Lambar goggo kad'ai na Haddace kuma bana so a kirata a tada mata hankali. Sai Dare Haruna ya biyo bayan ya Taso daga aikinsa ya Dubani ina ta musu godiya,ya kalleni kafin yace"Na yi ta kiran megidan ki bai Daga ba..Ko kina da lambar yan"uwan ki na nan sai ki bada na kira su na shaida musu"? Kafin ma nayi mgana Sa'adatu ta bashi da amsa da nace babu. Sai ya kara fadin"To ko gidan kakanin yaran nan zan je na shaida musu..?. Sai na kasaa mai gaddama na D'aga mai kai kawai nan na kwana Sa'adatu ta kwana dani nayi nayi ta tafi gida tace bakomai su Amir kuma ta kira Habiban ta mata bayani tace bakomai zasu kwana a wajenta. Washegari da Safe ta koma gida ta yi wanka ta yi abinci da Haruna yazo da Safe yace daganan gidan Mama zai je ya fadamata saboda yasan gida yana kai su Amir watarana in ya Dauko su daga makaranta. Abun mamaki har Dare ba wanda yazo kuma daya dawo yace yaje ya sanu Maman da kanta ya fadamata,ammh kuma ba wanda ya lekoni sai Habibar ne tazo da yammah ita da su Amir suna ganina suka Nufeni suna kiran sunana na Rumgumesu ina jin Tausayin kaina,basu jima ba ta tafi da su ina ta mata godiya ganin su Amir sun yi tsaf dasu,tace bakomai ai d'a na kowa ne sai Dare sa'adatu ta dawo min da abinci da kayan da zan sauya na rasa da kalmar da zan gode musu su yi min gatan da su mama suka kasa yimin. Sai da na kwana uku a asibiti sannan Sai ga Mama da anty binta sunzo dubani Lokacin ma naji sauki sosai basu iske sa'adatu ba ta koma gida ina gadon asibiti ma ban tsira wajen Mama ba, sai fad'a take min wai da gangan na kirkiri ciwo saboda ishaq ya dawo gabana ya Lalace to ban isa ba kaina na kasa ina kokarin maida hawayen dake cikin idona Anty Binta ne ta kalleni tana fadin"To meke damun ki..? Wata mata dake jinyar na kusa da gadona Saboda general ward ne na mata tace"Haba baiwar Allah kya yi mata hankali baki ga bata da lafiya ba ne..?kun sameta ma yau da Sauki Sauki da kun ganta sanda aka kawota sai kun Tausaya mata Hawan jini yanzu ya zama ruwan Dare baga yara ba, ba ga manya ba" Anty Binta da Mama suka kalli juna kafin Mama tace"Hawan jini..? Anty Binta tace"Ba dole ta samu hawan jini ba ta sakama ranta bala'i ..Ishaq dai kike ma wannan kwanciyar shima mara lafiyan garesa achan tunda muna nan basai yazo ba" Mama ta karb'e da cewa"Ai na gayamasa yayi zamansa kawai ya kula da Zainab" Ina jinsu kaina na kasa ban ce musu komai ba suka gama cimin mutumci suka tafi ko tsinke basu zo min dashi ba,ba tambaya waya kawoni asibiti ina yarana..?ba abunda ya Dame su bayan tafiyar su haka na koma na kwanta ina ta kuka Matar dake kusa tace"Ki daina kuka kada ki kara ma kanki Lalura..Wad'anan dai ko suwaye basu da kirki kina gadon asibitin ma baki tsira ba..? Ni dai na kasa mgana Likita yazo yayi zagaye da yazo wajena na tashi zaune idanuwana sun kumbura ya duba Fayel d'ina yana kallona kafin yace"Fa'iza Ishaq kin san abunda ke Damun ki..? Na girgiza kai na alamun a'a cikin Sanin aikinsa yaja farar kujeran dake gefen gadon da nike kwance ya zauna yana fadin"Hawan jini..Jinin ki ne ya d'aga Sosai sannan kina da maleria" Na dago ina kallonsa duk da naJi matar d'azu ta fad'a sai da nayi mamaki cikin yanayina nace"Hawan jini Likita..? Sai ya d'agamin kai ya cigaba da fadin"Ki daina yawan Tunani in kina so ki Tsira da lafiyarki..Damuwa ita ta Haifar miki da matsalan da kike ciki..Sannan daga yau ki rika kwana cikin gidan Sauro saboda rigakafin Cizon Sauri Maleria na tada Hawan jini..Shima Hawan jinin yana Tada maleria in suka Had'e ma Mutun kuma bama son haka kiyi kokarin cin abinci sosai ki kuma kiyaye dokokin mu" Na jinjina kaina kafin nace"Nagode likita..ina so ka sallame ni na koma gida" Ya kalleni kai Tsaye kafin yace"Mijin ki ne zai dawo..?Domin wanda ya kawoki ya ce shi makocin ku ne mijinki kuma yana wajen aikinsa" Cikin yanayin mganata nace"Ya'ya na..Likita na bar yarana ba su da kowa sai ni don Allah ka Sallameni" Mirmishi yayi kafin ya mike yana Fadin"kada ki damu zuwa gobe da Safe zaki koma gida" Na gyada mai kai daga haka ya wuce gado na gaba ni kuma na koma na kwanta ina Tunanin yadda rayuwata ta kare ace ina kwance bani da lafiya ammh ba wanda ya damu dani nasan da Goggo taji bazata zauna ba ni kuma bana son Damuwarta,Yau in da ace mutuwa nayi babu wanda zai san na mutu shi kawai ke sakani kuka. Da yammah Sa'adatu tazo na tambayeta su Amir tace yau sun je makaranta,har acikin raina naji Dadi idona ya cika da Hawaye na kalleta ina Fadin"Nagode sosai..Allah ya saka da Alheri" Ta amsa min da Amin a raina na Guduri niyyar in naji sauki na koma gida zan gyara mu'amalata da duka mokota na Domin na Lura sune Dangina dake kusa dani,Washegari da Safe aka bani sallama sai dai bamu tafi ba ba'a biya kudin gado da Sauran kashe kashe ba,Sai da Haruna ya koma gidan Mama ya fad'amata tace zata zo sai da muka kusa yini a asibiti sannan Anty Binta tazo tana ta wani yamutsan fuska ita ta biya duka kud'in da ake bukata sannan ta siya mgangunar da aka rubuta bata tsaya ba ta kara gaba Sa'adatu ta kamani ta Daukan mana Sauran kaya muka yi sallama da yan daki muka fice. Har cikin Dakina Sa'adatu ta kaini ta zaunar dani ina ta mata godiya matar nan bata tafi ba,Sai da ta share Dakunan ta gyara ta Dora girki Saboda yara ita ta Dinga fad'ama makotanmu bani da Lafiya duk da bana shiga ammh suna ta
Chapter 31 · 0% Book details