Sashe 125
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gabanta nake kira yaki Dagawa so yake yayi amfani da yarana ya sake Cutar dani tana bashi ko mganarsa ban jira ba na fara fadi'n"Kada kace zaka yi amfani da yarana domin ka sake Kuntatama rayuwata Ishaq.." Kada mu yi haka dakai. Ka bar su, su zauna in da ya zame musu Dole. Naji Labarin kana shirin kwaso su ka kawomin su nasan manufarka wlh karka fara na riga nayi rantsuwan Wallahi Tallahi NAGAMA aure dakai. ya rage naka ka kyalesu ko kazo da su, ka kara Rikita su yadda kaima din zasu Gagareka" Ina gama fad'in haka na yanke kiran ina Huci duk da Abba bai Fito Fili ya fad'amin ba ammh na Fahimci zama Abba ya Shiryamana kamar yadda yaso yayi tun farko na tuna mganar mu da Nana Fatima jiya har ce min tayi in Abba yazo yana tambayata kada naji nauyin gayamasa komai Abba zai kwatar min yancina to sai yanzu na Fahimci mganar ta gefen gado na zauna gabana na Faduwa ni bazan taba iya mgana ba. sai in har Ishaq ya warware mafarin komai da bakinsa. Washegari ma yadda Goggo ta tashi da Shirye shirye na tabbatar da Zargina sannan da Safe mun yi mgana da Hafsah tace Har da Ammi da Yaya Abdul'Ahad a babbar Jeep din Abba zasu taho,Kuma naji Goggo na waya da Yaya mariya ita zatayi girkin bakin,Tunda Tafi kusa akan Anty Nasara ina Daki sai na Lafe wanka kawai nayi na koma na kwanta Ina Tunanin yadda komai zai gudana yau sai dai na samu mutuwar jiki da Faduwar gaba Ishaq da Mama suka Fara isowa tunda su tafiyar Jirgi ce,Ina Daki naji muryoyinsu suna gaisawa da su Goggo,naki Fitowa nima kuma ban ji an yi mganata ba Duk da Raunin jina nima na Koyi na kasa raunanun kunnuwana ina Jiyo mgana daga Falon Goggo. Su Abba sai wajen sha Biyu suka iso,zuwan su yasa na fito bazan ji zuwan Abba da su Inno naki Fitowa ba,sanda na fito su Abba na kofar gida sai su Inno na duka na gaishesu Inno tace"Yar nan haka kika sha jinya..?jiki sai kashi..? Baba Ati tace"Daman ai duk sauran sun fita kumari sannan ga rashin Lafiya kuma" Sai mamakin Ramata suke yi wajen Mama na isa tana Falo na gaisheta sai naga bata son kallona kanta na kasa ni dai ban bi ta kanta ba. araina nace yaji barazana kenan bai Daukomin yaran ba wajen Ammi naje muka gaisa ita kan sai da ta taba wuyana Tana Fadin"Na shige su ni Aziza..Fa"i kin ji kasusuwa..?bari Baban Nana yazo tafiya dake zan yi na cike miki wannan kasusuwa da ba su da kyan gani" Inno tace"ke ana shirin Daidaita komai tabi megidanta kina wata mgana" Sai Ammi tayi shuru batayi mgana ba,Abba basu shigo gidan ba sai bayan azahar yaje duba ginin gida sai da kuma suka Tsaya suka yi sallar azahar sannan suka shigo nan ma cikin gida su Ammi sun yi salla sun ci abinci Inno da Baba Ati da Goggo sun kule sai Tattaunawa suke ni ko muna tare da Ammi tana ta ja na da Hirarta na barkwanci,su dai sun ci abimci ammh Su Abba ko da suka shigo akace ga abinci yace sai an gama zaman muna Daki ni da Ammi ya kirata yace tazo dani. Ina jin haka sai na Rude ganin haka yasa Ammi ta mike ta Dafa kafad'ana tana Fadin"Kada kii damu Fa'i ba wanda zai miki Dole. sai dai kada ki yi shuru ki Cutar da kanki ki yi mgana domin nema miki yancinki aure Ibadan Allah ne ba Cutarwa ko bautan Mutum ba ne, kin ji ko? Sai na gyada mata Kai Lokaci d'aya ina maimaita sunan Allah a raina yadda zan samu natsuwa Hijabi na saka ta riko Hannuna har Falon Goggo kaina na kasa har gaban Abba. Ina zama na dago kaina karaf ana Yaya Ishaq ya rame yayi baki yana Sanye da shadda navy blue daga bangaran Hagun Abba ni kuma ina Bangaran Dama mun saka shi a Tsakiya, sai na dauke idona ina zagayen mutanen falon da kallo. Dukkamu muna saman Cafet ne Inno da Baba Ati ne suke kan kujera,Naga Mallam mijin goggo sai Ammi sai Mama sai ni sai Abba, sai Uban gayyar Ina jin Yaya Abdul'Ahad yana waje shi da su Yaya isa. Kaina na maida kasa ina kokarin Daidaita kaina. domin sai naji kamar bazan iya mgana a yanayin da na samu kaina a gaban Abba ba. *Janafty* [7/25, 8:30 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3004* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* Abba ne ya fara bude taron da addu'a sannan ya gyara zama ya yi gyaran murya kafin ya fara da fad'in"Alhamdulillah dukkanmu nan mun san abunda ya taramu Magana ce akan ya'yan mu Fa'iza da Ishaq," Ya na gama fad'in haka sai ya karkato ya kalleni kaina na kasa ya kira sunana na amsa bakina na rawa na Dago ina kallonsa,Sai ya karkata kansa zuwa ga Uban gayyar shima ya kira sunansa abun mamaki da kwarin gwiwa ya amsa har yana wani gyara zama. Abba ya sauke numfashi yana Fadin"Zaman nan naku ne. Tun tuni ya kamata mu yi sa sai bamu yi ba. Saboda Rashin Lafiyan Fa'iza da wasu uzurirrikan da suka sha kan mu, ammh yanzu Alhandulillah ga shi lokaci ya bamu dama mun zauna ke Fa'iza dake zan fara mganata" Ina jin haka naji na fara rasa karfin gwiwana bai damu ba ya kalleni ya kara kiran sunana Idanuwana cike da kwallah na Dago ina fadin"Na'am Abba" Cikin kaushinsa yace"Mijin ki ya rasa aikinsa a baya kin zauna da shi acikin Halin babu kuma da bakinsa ya fad'a min kin Tallafa masa da sana'o'in ki,bamu taba jin kan ku ba,Sannan Daga Baya Allah ya wankesa aka dawo masa da aikinsa da karin girma. kowa yasan Dake aka yi shirin komawa Lagos sai kuma Daga baya zence ya sha bambam,ina so ki bud'e baki ki Fad'amana me ya faru kika bin mijin ki Sabon Muhallinsa? sannan meyasa kike neman Saki a wajensa..? Yana Dire mganarsa nima na Dire kukana saboda yana mgana zuciyata na bud'ewa da wani kunci sai na kasa mgana gabad'aya suka zubamin ido suna kallona. Ammi dake gefe ta kalleni ta kalli Ishaq taga sai kifta ido yake yi alamun rashin gaskiya karaf ta taso tazo gabana ta rike min hannu tana Fadin"Yanzu ba Lokacin kuka ba ne Fa'iza. bude baki ki fad'i Abunda ke faruwa dukkan mu nan mun zauna me domin yi ma kowanni bangare adalci" Wani irin kallo Abba ya watsa mata da ban taba ganin yayi mata irin shi ba. Da Sauri ta sakeni tun kafin yayi mgana ta koma wajen zamanta tana Fadin"Kayi hakuri Baban Nana" Kai ya jinjina cikin bacin rai yace"Baki da Hurumi a kan wannan mganar ki yi shuru da bakin ki" Jin haka yasa ta hade rai ta kama bakinta,Abba ya dawo da kalllonsa kaina yana Fadin"Umh muna jin ki Fa'iza ki juya ki ga wad'anda ke zaune gabadaya iyayen ki ne da kakaninki, zaki iya fad'amana duk abunda ke Faruwa Domin neman masalaha" Hannayena na saka na kare bakina ina kuka,kamar a wani Lokacin kalamansa suke min duka acikin raina Dakyar na iya bude Idanuwana cike Taf da hawaye na sauke kan na Ishaq na wani Lokaci ina kallonsa ina kallo ya sunkuyar da kai yana zufa ni kuma kai tsaye cikin muryata da kuka Ya taimaka wajen Dasashe su nace"Ku tambayesa shi ke da duka amshoshin tambayoyin ku Abba. Ammh ni bazan iya cewa komai ba matukar bai yi mgana ba" Na fad'a ina kuka na da Sauri ya Dago yana kallona gabansa na fad'i bai Dauka zan iya Dawo da wannan mganar ba Tunda nace na yafe masa cikin rawan baki yace"Haba Fa'iza na dauka mun gama da wannan mganar Tunda na roke ki gafara,kuma kika yafemin" Ina Sharan hawayena da bayan Hannuna nace"Da gaske nake yi na Yafe maka yaya ishaq duniya da Lahira,sai dai ka sani ba hurumina ba ne Tun a wata Hudun Farko addini ya bani Damar haka. Mganar nan kuma Wlh kamar yadda nayi alkwarin baza'a ji ta daga bakina ba. Ka sahale min auran ka,kamar yadda na Bukata sai mganar nan ta mutu har Gaban Abada ba wanda zai jita" Sai ya Rude kamar zai ta shi Daga inda yake Abba da suka zama yan kallo yace ya koma ya zauna ammh ya kasa zama Daidai Cikin sigar Lallashi yace"Bazan iya ba. ai na fada miki bazan iya sakin ki ba Fa'iza Baba yana kabarinsa wlh zai yi fushi dani Sannan me zan fad'ama su Anum da suke jiran na dawo musu da Umman su..?Sannan Zainab na fad'amin bazata zauna ba indai bakya gidan don Allah ki yi Hakuri Fa'iza ki janye wannan mganar ki had'a kayanki mu tafi" Yadda yake mgana zaki san bai da gaskiya duk ya rasa natsuwa sai kowa ya koma yana kallonsa ni kuma Sai naji duk wani Fargaba na fita daga rainaa. Naga kamar yama raina min wayau yana so na koma saboda ya'yansa da Muradin matarsa ba domin muradin kansa ba. sai na samu kaina da yin Wata karamar Dariyar da babu Nishad'i ko kadan