← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 175

Sashe 173

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwaya da saida su. Nan take ma yace akwai abokinsa dake aiki da Kotun musulunci a kano Lauya ne zai sa ya gayyacesa ya yi masa nasiha da barazana ko za'a dace. Ta hannun Anty Binta aka samu lambar wayarsa aka turama Lauyan shi kuma yace in sha Allahu zasu zauna da shi. Kwana Biyu tsakanin Lokacin muna shirin tafiya Edo washegari tunda yace tare zamu koma ya Kira Engr ya fad'amasa ya nemesa sun zauna ya Fahimci rashin sana'a ne da kuma rashin gata yasa ya fad'a wannan harkan sai kuma Tarayya da abokan banza,ammh ya yi masa alkawarin in yau ya samu wanda zai tsaya masa zai bar wannan sana'ar daman sha ba kullim yake afata ba,zai koma makaranta sannan zai zama nagari Engr na jin haka yace tafiyarmu sai Jibi washegarin jirgi yabi zuwa kano sai Dare ya dawo yace min kamar ya yi ma mijin Halisa kuka ga namiji har namiji ammh zuciya ta mutu,yace ya bashi Miliyan daya zai fara kasuwanci sannan zai koma makaranta Tunda yana da Diploma kuma ya yi masa alkwarin zai zama nagari in dai zai Tsaya masa shi kuma yace zai Tsaya masa har abada, ya bashi lambarsa yace in yana bukatan wani abu,Har kuma gidan yaje yaga Halisa yana Fad'amin ko abinci basu da shi ga gidan Haya an yi yawa. sai ya ce masa ya samu wani gidan da zasu kama su kad'ai zai biya kudin to sun rabu akan sai an samu zai kirasa. Idanuwana suka ciko da hawaye Allah Sarki rayuwa na rumgumesa ina masa Godiya sai ya rikeni sosai yana Fadin"ko kashi ne indai dan'uwanki ne abun Darajawa na ne Faa'izaa" Ban ji wani bakinciki domin ya taimaki Halisa ba yar'uwata ce har Abada ban isa in raba wannan jinin ba,ballatana abuda ya faru a baya ya Dade da wucewa ni din ne kuma na rabu da Ishaq na auri wani wanda yasan Darajata da mutumci,ban taba rikonsa araina ba ina yin komai Saboda Zumunci ne. Sai ga Anty Binta na kuka tana min godiya ita da Mama tsakani na ko da Halisa kamar uwarta haka ta Dauke ni. kira akai akai Anty Fa'iza kaza Anty Fa'iza tun balle da suka samu gida karami Flat,Engr ya biya musu kudin haya na shekara Biyu,sun koma sannan Rayuwa ta fara zama daidai bata iya yin komai sai da shawarana. Sai da muka koma Edo sannan na Tura mata 50k nace itama ta fara sana'an cikin gida sai ta nuna min tunda ta iya su Cake,donut bari ta gwada sai nace hakan yayi ta kuma tallata cewa tana aikin su Sai a biyata,bansan irin addu'an da muka sha Daga ita har mijin nata ba, Ni da Engr ne madubin su yanzu a baya Hajiya Dala suke ganin zata iya musu komai sai ga shi yanzu an ce tsakanin su ba Mutumci Hajiyar Dala da kanta ta Kirani Duniya mai ya yi tunda yanzu ina auren mai kudi nima kuma ina da abun hannuna na wuce reni. Da bakinta take fad'amin fadan su da Anty Binta daga karshe tace"Chan sanda Halisar ta hadu da shi nama sani ya yi musu barin kudi lokacin ana samun dillar kwayoyi na kai masa,kuma koda suke ganin dan'uwan megida na ne. yace fa Zaman makota ne na iyayensa da kakkanin yaro ammh basu hada komai da shi ba. ammh daga karshe Binta da Saudatu na ganin laifina ai ni kiri kiri na fad'a musu cewa hakkin ki ne ke bibiyan su suke ta ganin haka daga Halisan har Badariyan'" Mamaki bai barni nayi mgana ba ina Tunanin ita duniya daman haka ta gada tunda har yau Hajiyar Dala ke kirana tana sukan Mama da ya'yanta komai daman ka gina shi da amana,ba ma ita ba kaf ya'yanta suna kirana da masu auren da yanmatan alhalin a baya ba wanda ma yasan da zamana ba.. Autan ta ma Futuha,ta kirani tazo Abuja bikin kawarta ko ina nan nace mata ina Edo ammh sai na had'a ta da su Kafaya ta kwana Biyu a gidan su Paapa kuma suka karammata da zata koma Ta jirgi paapa ya siya mata Tiket bayan abun arzikin data koma da shi sai ga shi ta koma tana labarin iyayen mijin Anty fa'iza suna da kirki kadan kadan sai na zama abun so a family kowa yana nema na, har da wanda ban taba zato ba in na zauna ina Tuna matakin Rayuwata tun daga farko har zuwa yanzu hannuwana kadai nake Dagawa sama na godema Allah Tunda Duka Ni'imarsa da ta mamaye rayuwata sanadinsa ne yau ga shi Fa'izar da ake gudunta sai ga shi na zama abun son kowa da kowa Allah kenan. Muna Edo kafin mu koma Abuja,Zainab ta kirani tace yara sun samu Hutu ammh bata ji Yaya Ishaq na mganar zuwan su wajena ba,ina jin haka sai naji na kosa suzo sai na gayama Engr shi kuma ya Kira Ishaq ya kara rokonsa sai ya cika masa ido yace zasu zo yana jiran jamal ne tunda bazai sako su su kadai ba. Jin haka yasa Engr ya karbi Lambar Jamal din suka yi mgana shi kuma ya Siyama duka yaran ticket yace su biyo Jirgi in zasu taho mu hadu a Abuja. Duk yadda naso na boye murnata na kasa sai da na bayyana Engr nata min Tsiyan nace na bar masa ashe zence ne namu na mata kunya naji ganin har Zalamata ta fito Sarari. In da ta ni za'a bi har Islam azo min da ita Zainab tace bata yayeta ba in bari sai in ta isa yaye zata kawomin na yayeta da kaina,ammh duka yaran su Shidda zasu mana Hutu suma Zainab tace suna ta murna zasu wajen Umma. A satin muka dawo Abuja mukaje muka yi shooping saboda Engr yace bayaso su nemi wani abu su rasa,kamar Yadda Babansu yace Jamal ya taho da su ni da Engr mukaje Filin jirgi muka Daukosu haka yara nan suka kamkameni suna Ihun kiran sunana Umma Umma har da Anum babban banza Amir dai yana gefe shi Babba bai cika harkan yara ba. Sai ga Jamal a gidana bai kuma san haka saukin kan Engr yake ba, sai da suka zauna suna ta hira ni kuma ni da yaran muna cikin gida,Amir daki guda na sauke shida Musty ,Dayan dakin kuma su Ahmad,Anum kuma nace ta zauna adakina. Duk inda na saka kafa nan suke sakawa komai suka gani sai sun yi mgana Labarai ko haka nake shan su gidan sai ya karade da hayaniyar yara daman nayi abinci kafin su iso ai sai kowa yace ga abunda zai ci wannan yace Shayi wannan indomie ammh ban damu ba haka na shiga kitchen ina yi musu ra'ayinsu zuciyata Fes kamar an yi min albishir da gidan Aljannah. Jamal jirgin yammah ya sake bi zuwa kano,ya yi ta godiya karramansa da Engr ya yi har yace ma ya kawo C.V Dinsa tunda acikin Hiran su ya fadamasa Software Engering ya karanta,Zuwan yaran yasa walwalata ya karu ranar dai tare da su Engr ya barni na kwana Amir ne kadai ya kwana shi kadai da Musty ammh har Ahmad a dakina suka kwana Engr mutum ne mai kawaici da kauda kai ya kyaleni naci Lokacina ni da ya'yana ba Takura ba shiga Hakki. Ni da kaina da na gano zakewata sai na rage rawan kafa shima cikin su yake shigewa ayi ta wasa har da Chinness yake biyo musu suna yi shi da su Ahmad Amir kuma in kaga suna mgana kace Amir wani babba ne,Ballatana Anum iyayin karanbana fadi kuma ba'a tambayeta. Yadda muka saba tun a baya zuwan su ma haka muke yi karatu tare da cin abinci tare,Sannan Anum na zage mata da koya mata girke girke zamani Tunda chan bayi suke ba ita kanta Zainab din tana neman mai koyamata. Mun fiffita yawo da su na kaisu gidan su Papa suka yi musu ma kwana uku,Maa ke son yara kamar kada su dawo,sannan mun je parks da su Engr ya kaimu suka yi wasa suka sha Hotuna,yaso ya koma ammh yace sai ya maida su har Lagos yadda gobe za'a ji dadin barin su Sati uku daman akace su yi saboda makaranta. Naso su kara Engr yace a'a gwara su koma akan Lokaci,Farhan da Fadil na kai su gidan kakkanin su ni da Engr muka je sai ga Dr.Laawal kamar ya kwantamin Hajiya Halima daman ban taba samun matsala da ita ba. naga kanwar Zainab zuzu ta dawo daga kasar waje ita kanta da ta ganni tayi mamaki sai ga shi itace da sakin jiki muna mgana har tana karban lambar wayata nan na barsu suka kwana Biyu Zuzu ta kirani tace suna ta kiran yan'uwan su, sun ki zama ita ta dawo da su,To ranar ma bana jin dadi kasala ga zazzabi ga dacin abinci ga shi mun Tsara tare zamu maida su lagos. Ciwo fa rigis ya kwantar dani Tsaraban yaran ma su Kafaya Engr ya bamawa suka je suka yi musu shopping ni kuma ya kwasheni muka je asibiti gwajin Farko aka gani ina da Shigar ciki wata uku,Murna gurin Engr kamar zai shid'e nasha Rumguma tun a gaban likita tun kuma muna asibitin ya labartama su paapa ina da ciki suma kamar shi haka suke ta murnan. Dole Saboda Laulayi wajen Maa na koma shi kuma yaje ya kai yaran aranar suna da sati uku da kwana Hudu ne,achan ya kwana da Safe ya Biyo Jirgi zuwa Edo suna da Meeting dalilinsa da yasa ma bai dawo Abuja ba sai dai waya fa akai akai muke yi ko su Abba shi ya fasa mganar cikin a wajensu ni kunya ma nake ji in naga yadda ake rawan jiki a kaina Motsi kadan Maa tace menene..! Motsi kadan granny tace ina lafiya..? Haka su kafaya ashe haka ake renon ciki ni na saba nawa cikin har nayi sa na haifesa ba wanda yasan zafina sai ga shi na zo inda kamar a lasheni tun kafin abun cikin ya fito duniya. Bansan ya akayi ba kowa sai da yaji Labarin cikin na ba Dangina ba ga nasa Danginsa ba. kunya nake ji wlh gani nayi mu ba yara ba miye na yamad'di. Zainab ma tace Badariya ta fad'amata ta kirani
Chapter 173 · 0% Book details