Sashe 10
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na wanka Saboda zuwa makaranta Domin dokar da Mama ta kwafanin kafin bakwai na Safe na gama komai kada ta fito bata iske abinci a saman dining ba,ko kuma taji kafafunta na taka Datti acikin Falonta Shiyasa ina yin abun kari wani Lokacin ina Share sharen dakuna hatta Dakin Jamal ni nake gyaramai in suka tafi makaramta Saukin ta ma shi bai cika mgana ba barshi da waya a Hannunsa irin su ba kasafai ake gane inda suka dosa ba. Ya ishaq kuma baya gida sai an yi Hutu yake zuwa yana ABU Zaria inda yake Masters di'nsa nima abakin Anty Binta naji sunan karatun nasa har na iya rikewa,Hatta da kayan Jamal da na Badariya da na Mama ni nake wankewa ammh Baba bai sani ba Saboda yasan duk wata baya fashin bada kudin mai wanki da guga Tunda Mama ta sameni take soke yan kud'ade'nta,in wankin ya taru tun safe in naje baya na fara sai yammah watarana ma bana ko samin zuwa islamiya,Washegari kuma Baba na fita zan dasa guga har sai bayana ya kage ba ci ba sha sai na gama in kuma nace zan tashi ko sallah in yi sai Mama ta kai min duka tana Fadin"Me kika sani a karatun sallar..?Ni fa jin baban su kawai nake in yana Fadin kina da ilimin addini ke da kike Bebiya gaki ba kyau ba fasalin y'a mace ai bautar da ta dace da irin ku kenan.." In ta fadi haka bana damuwa sai naga gaskiya ta fada domin na fahimci in baka da kyau ko Asali da gata ko kana da wani nakasun Hallita baka da wani amfani Domin wad'anda suka fi kusanci dakai sune suka fi kowa kyamatarka to inaga na waje wad'anda basu san ka ba, mu'alama ce zata hadaku..? Ina tuna Lokacin muna Malumfashi Iyayena sun san ina da Lalura ammh ko sau daya basu taba nuna gazawar su ba sun min dukkan gata a malumfashi makarantan da aka kaini ina gane karatu tunda ana yimin yadda zan gane sannan bamai kyamatata Saboda ina da gata alokacin ammh daga Lokacin da gata na ya kare sai nima nake fama da guilt din shiga cikin Mutane ina ganin ban kai ko wani matsayi ba sannan na aminta da mganar Mama iri iren mata irina Bautace ta Dace damu.. Shiyasa duk wahalan da nike sha bana Damuwa ina ganin ahakan ma ni kila nafi wasu ma ire irena,Baba duk baya sanin wasu abubuwan tun da in ya fita tun Safe sai Dare,in kuma ya Dawo yayi sallah yaci abinci zai kirani falo yayi ta kokarin na bayyana mai abunda nake bukata ko nake so ammh bana iya mgana Saboda Mama ina bala'in jin tsoronta kamar wata mala'ikar Mutuwa. Baban katsina irin mazan nan ne marasa Bibiyan al'umuran gidansu shiyasa Mama ta samu dama tana Damawarta,Komai na Cefane Mama yake bamawa,Duk watan Duniya ita kuma sai ta samu nata aciki Mama tasan kan kasuwanci,Tana saida dikkakun kayan mata da maza anan ake dinka mata tana aika ma yan'uwanta dake yamai suna Siyar mata kuma har anan tana samun ciniki sosai tana harka da manyan mata bayan dikakku har Tamfofi da Lesuna tana saidawa da takalma Shiyasa take da tarin kawaye da Mutanen arziki da ke shiga suna Fita agidan,Shiyasa ko Sutura ita Baba ke bama kudin ko na Mutanen karofi ne kuma baya Bibiya,Shiyasa sai wanda taga dama ta bawa,ba kuma wanda ya isa yayi mgana duk sallah har da su Yaya Asiya Baban katsina ke yi ma Dinki adadin yadda yayi ma Badariya dani ammh ni ko Sabo daya Mama bata bani na saka sai tace Mace irina da kwance ta dace ni kuma sai mganarta ta zaunamin kayan alfarma masu kyau sai ajikin kyawawan mata wad'anda basu da wani nakasu Mata kuma irina da kwance muka Dace yawancin kayan yaran kawayen Mama nake sakawa Domin na badariya bazai min ba Na girmeta sosai alokacin,Su Yaya Asiya kuwa Kala dai'dai take jifan su dashi Yaya mariya bata da matsala ita da Hafsatu Goggo macece mai Tsayawa akanta ita da iyalanta Yaya Asiya kuma tace duk mugunta Hajiyar Dala tana barinta da Suturu Saboda ita yar gayu ce sannan mijinta Soja ne ya'yanta fes suke itama haka saboda haka Itama Yaya Asiya badai a ganta da kama mara kyau ba. Ni dai ko da yaushe cikin Tsumma da Ragga In Baba ya gani yayi mgana Mama ta lawayance zance ni kuma bana iya karyatata agabansa,bazan taba mantawa da wata sallah ba,Sallah da na fara yinta a gidan Baban katsina Lokacin na kwashe wajen wata Tara a katsina,kuma tunda nazo ko Karofi kafata bata kara takawa ba Ga Hajiya na raina in Baba zai tafi gaisheta sai naji kamar na bisa,tunda duk karshen wata yake zuwa wani Lokacin shi da Mama suke zuwa wani lokacin shi kadai da Direba ko shi da Jamal. Hajiya na rai na ita da su Yaya Asiya musamman Hasfatu kewar Tamadina kuwa har na cire sa araina tunda ba samun ganinta zan yi ba Tun bayan dawowata Ko mutum daya Daga karofi bai leko mu ba na dai ga Hajiyar Dala da suka taba zuwa Bikin Dangin mijinta ta sauka anan kawaye ne ita da Mama sai muguntar su tazo daya sai dai ita tafi mama ji da kai da nuna ita din watace. Sallar azumi ne Dama da azumi duk na Rame na kara lalacewa,Ni bansan gayu ba, bansan komai mai kyau ba ni na dauka abu mai kyau a wajen mata masu kyau ake samun sa,Wani Riga da Sikat na saka cikin kwancen kayan ya'yan kawayen Da mama ke bani ne wuyan zamemin yake haka ma Sikat din yayi min yawa sai da na saka Tsumma na Taresa ajikina Hijabi ne kadai Sabo Shima Anty Mahma ce ta dinkamin domin jiya gidanta na wuni na tayata soyan Nama da aikin cinci Sai Dare ita da mijinta suka maidoni gida ita ta na da kyauta in nayi mata wahala tana min alheri takalmin kafata na Roba ne shima din Na jamal ne da ya daina amfani da shi na Dauka Da farko Mama bata so aje dani Sallar idi ba,Sai Baba yace dani za'a tafi Ya Ishaq ya dawo agida yayi azuminsa Shi na lura kamar baya ma san kallo na shiyasa ban cika giftawa ta gabansa ba. Lokacin da na fito Kofar gida Baba ya ganni sai da yaji kwallah ta cikamai ido,Ya kalli Badariya ta kure adaka ita da Mama,Jamal da Ya ishaq sun ci Fararan Shaddodi sai Faman sheke suke ni kuma bazar bazar kamar mahaukaciya wata yar aikin ma tafini kyan gani ni kuwa bakina kamar zai Tsage Saboda murna zan fita masallaci naga jama'a Tun kafin Baba yayi mgana Mama ta rigasa da fadin"Ke Fa'iza meyasa kika saka wadanan kayan..? Ina naki irin na Badariya..? Sai na kasa mgana Saboda ni dai bansan da wani kaya ba,ba'a bani ba ganin Baba ya saussauto yana kallonta yasa ta kara karya murya tana Fadim"Bansan meke damun Yarinyar nan ba Abban Ishaq ko da yaushe bata da aiki sai saka Tsumman kaya nama ce ta hada su in zaka Karofi ka tafi da su arabama mabukata" Ban yi mamakin kalaman Mama ba Domin tun zuwana gidan ba Dadewa,Ta daina Fada da Baba akaina sai ta koma aiki da Kissa shima shawaran wata kanwartace daga Yamai hure ita tace mata in tana so taci Ribar Rayuwa to ta daina tada Hankali ta yi amfani da kiss,kuma Tabbas kissanta tana Tasiri wajen Baba don nan take ya kalleni kafin yace"Haba Fa'iza ya zaki saka wadanan kaya..? Baki ga sauran yan'uwanki ba ne.?maza je ki sauya kaya mu tafi kada mu makara'" Da Sauri Mama tace"Zamu bata Lokaci Alhaji muje in mun dawo sai ta sauya" Sanin Halinsa na rashin bincike kan al'umura yasa tace haka,Haka muka tafi su kamar zara cikin wata ni kuma kamar yar aikin su Shikenan ko da muka Dawo Baba yayi baki yana falon waje har Dare bai kara bi ta kaina ba,Sai da Washegarin Sallah da kwana Biyu mukaje Karofi ranar dai Mama ta bani Sabon kaya na saka ta kuma ja kunnena in taji wata mgana sai na Raina kaina ni ko araina nace wazan gayamawa.?bata san ina da zurfin ciki ba ba tun yau ba,bakomai ake jinsa bakina ba. Duk da Sabon kayane ammh da na sanya kamar wata Dussa komai ba Tsari ni kaina nasan ba kyakyawa bace ban mallaki komai na mata masu sa'a da gata ba,Kusan daman Hausawa kan ce in kana da kyau ka kara da wanka to ni bani da kyau din sannan ban iya wankan ba ballatana na kara dashi,Wani Lokacin sai Dare nake samun Damar yin wankan Tunda Dakin da nake ciki akwai karamin Tiolet to iya wankan ne ko shi ba don kyau nake yi ba Komai bazar bazar ne bansan iyakarsa ba. Da mukaje karofi na hadu da su Ya Asiya har sai da sukace har baki na kara na rame sun yi tambayan Duniyan nan kan wani irin rayuwa nake yi agidan Baban katsina naki ce musu komai sai dai in kallesu ina mirmishi naji dadin ganinsu haka barin ma Hafsatu da ta zama kamar ba ita ba ta kara wayau da girma. Ina jin su a tsakaninsu suna tattauna yadda Rayuwa ta jefa su a inda suke ni dai bana ce musu komai nadai san na Tambayesu tamadina suka fadamin tana Lafiya Yaya mariya na zuwa Dubata ita da Goggon Karofi sukace In Baba ya barni gobe sai muje na ganta. Ganin Goggon Korofi yasa Mama batayi mgana ba,Baba kuma ya amince washegari chan muka wuni sai yammah muka dawo ita kanta Tamadina ta na cikin wahala gida cike da yara,wahalar tayi mata yawa sai dai ba yadda zatayi ne kwanan mu biyu muka koma Katsina,Na koma da Tausayin Hajiyar Karofi ganin jikinta duk ya kara rikicewa yanzu ma dayan barin shima ya Daina aiki Goggon Karofi da ya'yanta suna matukar kokari kan Hajiya. Haka rayuwata ta cigaba da tafiya a gidan Baban katsina duk da irin azaban da nike sha achan ban taba jin na gaza ba sai ma nake ganin Sun yi min komai tunda zan ci na sha na kuma samu wajen barci Baba na jin Takaicin rashin Karatu na