Sashe 76
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
anguwan su Hajiya kusa da jami'ar alkalam. Nasameta a gida da tana shirin fita ne ma sai gani,sai ta fasa bayan mun gaisa tamin bayanin komai zan had'a Turaren rushi da na Humra sai kwallacha sai zan yi ma Amaryan gyaran jiki,duka zasu bani dubu dari biyu,Naji kudi sai na rude cikin Firgici nace"Hajiya duka nawa..? Hajiya na dariya tace"Eh kudin aikin ki da ladan ki ba' Sai na hau mata Godiya sai ta bata rai tana fadin bata so na koma na zauna araina ina Hamdala,Nan take ta bani dubu dari a hannuna sauran tace zata Turamin ta banki ta karishe da fadin"Sati mai shiga amaryan zata zo nan zaki zo ki yi mata ko sai dai ta biyo ki gida..? Cikin Ladabina nace"Hajiya sai dai gida kinga ga yara sannan ga Mama bazai yuyu na rika Dadewa a waje ba" Hajiya tace"Eh hakane shiyasa da suka yi mganar girki nace su dauki wata kawai zuwan ki kaduna da wahala" Na jinjina mata kai sai tace ba Damuwa fita zatayi duk abunda ake ciki sai mun yi waya,tare muka fita da ita bayan ta bani kyautar atamfa da Mayafi,sai turare da lotion mai kyau,tare muka taho Direban ta ya Daukoni sai da suka saukeni a gida sannan ya wuce da ita in da zataje. Bakina kamar gonar auduga haka na shiga gidan cikin murna naja Hafsah Daki na zayyana mata komai na nuna mata kudin cikin Farinciki tace"yaya Fa'iza Hajiya tana da kirki tana son ki da arziki" Ina jinjina kudin hannuna nace"Bari Hafsatu Allah dai ya biya ta kawai" Aranar bamu je kasuwa ba sai washegari mukaje da Hafsah ta tayani na sissiyo abunda zan bukata ina Dawowa na Dukufa na fara aikin Hada Turaruka,araina ina jin duka matsalolina zan kauda su in na samu wannan riban aikin,Aikin zobo sai ya koma sau daya a rana kunin Aya ma sai da yammah Lokaci na bada kacokan kan hada Turarukan nan ban rufe kwana hudu ba, na gama su duka,Kwallachan ne ma ta bani wahala ita sai da nayi kwanaki ban gama ba,inagamawa na kira Hajiya sai tace na ijiye komai a Hannuna in su Laila sun gama gyaran jiki in zasu tafi sai su tafi dashi. Haka ko akayi satin bikin Amaryan Laila mai kyau da ita yar gayu ga ilimi ga nasaba ga kudi,ma'aikaciyar banki ne a kaduna suke Raliya ta dinga rakota kullumn da yammah muke farawa sai shida,A tsakar gida nake bazamana Tabarmana a rumfar nan Ishaq na Daki baya fitowa ga Hafsah wani Lokacin harda Badariya sai abun ya kara armashi,Laila ba ruwanta ga sakin fuska Anty Fa'iza kasa da sama take kirana kamar yadda Raliya ke Kirana,Sannan jininta ya shaku ita da Anun ta dinga rokona in bar ta su Tafi Bikin ta kaduna da ita Amana Hajiya zasu dawo da ita ban yi mgana ba sanin Halin Babansu da Mama ba lalle su bari ba. Sati daya nayi ina mata sai ga shi ta fito shar da ita abunka ga farar fata,ga jiki lawai lawai sai tashin kamshi take yi,Da naga ta matsa da mganar Tafiya da Anum sai nayi ma Yaya Ishaq mgana da kaina nayi mamaki da ya barta ammh yace kada ta Dad'e a dawo masa da yarsa. ranar Litini Laila taji Dadi tana ta Godiya Direba yazo ya kwashe su ranar karshe da kayan su aranar kuma Hajiya ta Turomin sauran kudina, na daka tsalle ina murna nayi sujuda na gode ma Allah. Batare da sanin Yaya Ishaq ba,naje na yi ma Amir komai har Uniform an basa na Biya musu kudin Tahfeez sannan na shiga kasuwa na siyo mai takalmin makaranta da jaka da littafai,yanzu nima sana'a ta Budemin ido nasan sirrin shiga kasuwa lungu da sako. *INGANTACCEN ZANCE*. *Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*. *Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin* *Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.* *Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*. *SAIWOWIN itatuwane da basu da illah* *Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.* *Kawai ki tuntu'bi Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani* *08032773332.*