Sashe 11
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko da yaushe naje gaishe shi da Safe sai ya kalleni yace min"Fa'iza kin k'i makaranta ko..? Baki san ilimin zamani ginshiki ne ga rayuwar ya'mace ba..? Ni kuma bana iya mgana sai dai na Dukar da kaina cikin Tausasawarsa yake cigaba da Fadin"Da kin Daure Fa'iza ai kina jin mgana zaki gane komai sannan zan yi ma malaman ku bayani kamar yadda nayi ma malamanki na islamiya bayanin Laluran ki" Ina Dagowa muka Hada ido da Mama ta Sakar min harara sai jikina ya fara rawa cikin yanayin mgana ta nace"Baba shi na addinin ba Ilimi ba ne..? Sannan shi ba Ginshiki ba ne ga rayuwar mu ba..? Baba ya jinjina mganata kafin yace"Ginshiki ne Fa'iza babban ginshiki ba kuwa..Sai dai ka hada duka fufukan guda biyu sai ka samu na zaman duniya da Lahira" Alokacin sai nace ma Baba"Baba ka barni haka..na islamiyan kadai ya isheni" Zai matsamin sai Mama ta taresa tana nuna mai Tunda ban so to ya kyaleni,Shi kuma bai da Zafi sai ya Rabu dani ammh ko da yaushe kalamansa akaina na alheri ne har ya bar duniya ko kallona yayi sai yace"Fa'iza Allah yayi miki albarka In sha Allahi bazaki Taggyara ba..Ina ji ajikina kina da wata baiwar da Sanadinta zaki Daukaka watarana" In naji haka sai nayi Dariya araina Domin bana hango ma kaina hakan Na amince Baban Katsina ya karbo ni Hannun Goggo karofi ne domin ya inganta Rayuwa ta,sai dai bashi da Mafita ne Mama ta fi karfinsa ammh har yau bazan manta kokarinsa akaina ba. Shi ya fadama malaman islamiyan da nake zuwa yanayina suke bani kyakyawan horo ko an gama karatu gabadaya sai an kara min bita ni kadai,Bani da wata kawa shiyasa ni kadai nake zama iyakata da kowa Mirmishi ko Sannu nasan ana mgamata ammh da yake bana ma ji Sosai ban cika Damuwa da su ba. A farkon zuwa na gidan Mama cikin kasuwar katsina take zuwa siyayyarta ammh sai Kawarta Hajiya Barira irin masu son kudin nan ne ita ta bata shawaran ta rika zuwa kano kwantin kwari tana saro kaya alokacin Mama sai tace"Kai Barira ya yi nisa ni kinsan ban san wahala" Hajiya barira ta rika nuna mata yanayin komai tare da fadin nachan sun fi sauki sannan zata hadata da yan kasuwar chan tunda itama tana siyayya achan har sai da Maama ta amince bazan manta ba na zo kawo ma Hajiya Barira abinci na juya naji tana ce ma Mama"ko wannan bakar yarinyar kika tara sai kuje tare ta rika Daukan miki kaya" Mama ta kalleta kafin tace"Ko Hajiya barira"? Tace to zauna Daman meye amfanin irin su in ba aikin wahala ba. Da wannan shawaran Mama ta zauna tana fadama Baba ya amince tunda shi ba mutum ne mai Takura ga iyalansa ba.kuma da tace dani zata bai yi gaddama ba domin nuna mai tayi ina kokari zata nuna min komai Domin tana Tunanin nan gaba ko ban yi karatu ba zan yi kasuwanci to ai Daman haka take fadamai ko na wahalan da nake yi ne,Girki ma Baba yace nayi kankanta Mama tayi Karaf tace gwara na koya Saboda gaba gidan wani zani Daganan Baba bai kara mgana ba. Daman tun anan ni nake kaimata Dinki chan batagwara kusa da gidan Anty binta,in ba'a gama ba sai na zauna an gama Wani Lokaci anan nake wuni buhu ne shake da kaya zam Dauko akai zuwa bakin Titi na samu Daidaita sannan in na Dawo na Hau ware ma masu kayan nasu,wad'anda za'a tafi da su yamai kuma duk ni ke shirya su Mama na gefe tana lissafin komai ban isa nace nagaji ba. Ranar da muka fara zuwa kano sai da na raina kaina Wuni guda acikin kasuwa kuma bata Dauki dan dako ba ni ke daukan mata kaya akai kamar mahaukaciya ga yunwa ga kishi Takalmi a Hannu hijabi a hannu Wlh ko abinci bata siyamin ba Da muka Dawo sai da nayi rashin Lafiya Saboda na Jigata matuka alokacin Mama fada ta Dinga min akan na fara zama mai son jiki to in zam mike tun wuri gwara na mike Bani da wani amfani in ba Bauta ba. Ni ba kyau ba,Ba ilimi ba,Ba ji ba,ba komai na inganci rayuwa ba,bai kamata na rika nuna gazawata ba tabbas gaskiya ta fada ba ni da wani gata a Duniya Bautar dai da ta Fada shine ya fi dacewa da mata marasa galihu ire irena zuwa Lokacin da na shafe shekaru Shidda Cif a wajen Baban katsina bazan iya fadin irin bautar da nayi ba abu daya na sani ni Fa'iza ban sauya ba Sai dai na kara girma ammh ba Domin na sauya Daga yadda nake ba Ina nan a mai raunannan ji,Mara gata baka Mummuna mara sa'an rayuwa in ji ya Ishaq in ya ganni yakan ce Bai taba ganin mace mara sa'a ba irina komai Total zero ne a bangarena ba wani abun so ko sha'awa tare dani nima nasan haka ko badariya dake tasowa mai kyau ce sannan yar gayu kuma yar gata ni kuwa ban ma san me ake kira da gayun ba,Ni dai kawai nayi wanka na suturta jikina mganar gyaran jiki da Tsaftan jiki ban san shi ba Ba kuma wanda ya ke zaunar dani ya koyamin Ko kitso sai ni nagaji da kaina na tsefe shi kitso kuma sai in Mama taga dama zata bani kudi naje,ayi min. Zuwa Lokacin rayuwa ta Daga,Sosai ba kamar baya ba,kawayen Mama da suka sani tun abaya in suka gani sai like sai suka rika ce ma Mama Daman wannan mummunar dangin mijin naki na nan baki aurar da ita ba.? Mama kan basu amsa da cewa wazai kwashi Baki da muni da bebanci sannan uwa uba ba ilimi sai su yi ta Dariya suna cema Mama shikenan ta samu yar aiki to ai daman ba marabata da mai aiki maraban mu daya in da Daukoni akayi da sunan aiki za'a rika biyana albashi,Shine kawai bambamcina da mai aiki acikin wannan gidan. Su Yaya Asiya duk sun yi aure ita da Yaya Mariya Ya Asiya acikin garin kano tayi aure wani malamin makaranta ne yana da mata da yara,Mai karamin karfi ita kuma Yaya Mariya A karofi tayi aurenta wani dan kasuwa ta aura mai rufin asiri. Kusan tare akayi Bikin su sai dai na Ya Asiya aka fara yi ,Duka naje bikin su ammh na Ya Asiya sai da Goggon Karofi ta kira Baba ta mai mgana domin tasan Halin Mama munje kano mun yi kwanaki Tunda Bikin tare da manyan ya'yan Hajiyar Dala babansu ya Hada, da Asiya harta duka kudin siyayyan kayan Daki tare ya bada ammh Mama ta zuga Hajiyar Dala akan su ya'yanta suna da gata Asiya kuma ayi mata na Daidai da ita Daga karshe ma ita taci kudin domin duka Dawaniyar Yaya Asiya Baban katsina yayi mata shi,Duk ciki ita kadai ta auri mai karamin karfi gidan falo daya ne sai Dakuma nata da na uwargidan Ba Shakka Baba yayi mata kokari sosai,Bangaran Yaya mariya Goggo da Mijinta sukayi komai ita gidanta ita kadai wannan bikin ne har Tamadina tazo,na Yaya Asiya ne bata je ba, in naga yadda Rayuwar Mahaifiyarmu ta koma sai na kara tabbatarwa lalle bamu da gata gatanmu ya fadi tun Lokacin Rasuwar Baba. Da ace Hajiyar Karofi na Da lafiyanta da kila abubuwa sun sauya ammh kuma tana kwance sai dai a kwantar a tayar bama wanda ya zata kai haka araye,ana zuwa gida ana Dubata har yau tana nan jiya iyau bata ko mgana Sai wanda ya kara kunnensa yake ji me take fadi in naje Hajiya ta rika kallona kenan na rike hannunta ina Fadin"Allah zai baki lafiya Hajiya" Sai dai kaga Hawaye na Bin gefen fuskarta Hajiya na bani Tausayi sosai shekaru kusan bakwai tana jinya tana kwance waje daya,Gidan su na karofi Babban Yaron Goggo Yaya Isa ya gyara da yayi aure yake zaune da matarsa kada abar gidan ba kowa ya mutu Baba ya matsa sai ya zauna da Farko Goggon Karofi bata so hakan ba gudun Rigiman zumunci. Ya Ishaq ya dawo gida ya gama karatu har ya samu aiki a Hukumar Tattara Haraji na kasa reshen jahar katsina,Shekaru uku da suka gabata,Sai dai baya zaman gidan in ya fita tun safe sai dare in kuma ya Dawo yana Dakinsa na fada muku tun a baya shi baima son ganina shiyasa bamu cika Haduwa ba, bana zama inda nasan zai ganni Saboda yafi kowa iya kallon wulakanci da kaskanci. Akwai watarana tana cikin cikin Ranakun da bazan manta da su ba acikin kaddarorina ba,Muna gabda Riskan kaddaran auren mu ni da Ya Ishaq al'amarin ya faru watarana ya kira Mama a waya yace yana son abincin Mutum hudu abokansa zasu zo su yi Dinner anan biki sukayi na wani abokin aikinsu. Nan da nan Mama ta tasoni na shiga Kirchen daman na fada muku a bangaran girki ni Fa'iza bani da makusa,Harta Mama yanzu in ba girki na ba bata iya cin abinci,Shi ko Baba kullum Mama yake godemawa yana ganin ita ta tallafamin na iya girken girken zamani zuwa kuma Lokacin na rage wasu walwahalun,Saboda Mama ta daina aike na ta samu yaron aike bangaran kasuwancinta kuma komai ta waya ne sai dai a saka mata a mota a aiko mata dashi,sannan ta dauki masu wanki da guga da kuma mai wanke wanke na koma gyaran gida da girki. Jin baki ya ishaq zai zo da su na Zage nayi musu girki mai rai da lafiya fatan pototo,da Hanta sai white rice da Miyar kifi,Sai nayi musu lemun Abarba Sai na hada musu da na Gwangwani kafin ya kariso Mama ta sani na je na shirya komai afalon Baba,na koma kitchen na Dora abincin dare na gida har bakin suka zo ni bansani ba Na gama girkin Dare doya da Miya Mama tace ayi naje nayi sallar mangariba ina zaune saman sallaya Jamal ya shigo Dakin da nake mai karamar katifa sai tarkace yace min Ya Ishaq na kirana afalon Baba sai da gabana ya fadi ban cire Hijabin jikina ba yamin yawa yana neman gadani na nufi Falon Baba Ina shiga da sallama gabadaya zaratan mazan dake falon suka Dago suna kallona ni ban