Sashe 72
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gwiwa ya shigeni Duk daman masu sari ta wajena basu hakura ba sun ce duk inda nake zasu biyo ni su siya Saboda inganci zobo na da kunin Aya na. Su Anum sun koma makaranta ba nisa da safe ko Yaya ishaq ya rakasu su tsallaka titi ko Jamal,watarana har Amir ko Hafsah,Amir ne kadai ke gida shi da zai fara Junior section ga ba kudi ammh ina iya bakin kokarina ina so ya fara zuwa da wuri kafin wannan zangon karatu na farkon ya kare. Muna da Sati Biyu da dawowa Sabon Muhallin mu na cigaba da sana'ata Ranar tare da su Hafsah da Badariya suka taimakamin muka hada zobon da kunin Aya,ta waya na kira masu sara,bayan yayi sanyi chan da yammah suka zo suka Dauka Mama sau daya ta leko komai batace ba ta tabe baki ta koma ciki Sannu Sannu sai ga shi an fara ganeni ana zuwa Siya,ballatana anguwan akwai Dandali na matasa sosai tunda suka gane shikenan da yammah haka nake Ciniki sosai,Daga Mama har Uban gayyar basu taba ce min ba nima ban ce musu ba ina kokarin kiyaye abunda zai saka a tozartani. Jamal zai koma makaranta,ga kudin mota ga pocket money da kudin kayan abinci ga kudin makaranta Haka ma Badariya,Anty Binta tazo ranar sun dade a daki suna tattaunawa dukkansu sai dai har kwana Biyu ba wani mafita,Na lura shi kan shi Hankalinsa duk ya tashi a ranar suma su Anum aka basu takardan tunasarwan Biyan kudin makaranta Saboda damuwa abinci daren sa ma yadda na kai masa haka na koma na dauke sa bai ci ba,Da safe ma ruwan buni kadai ya sha ya fita ashe gidan Anty Binta yaje itama duk bata da wani kudi duk da su ta kwashe aka rufa asiri,Ammh tace ta ma mijinta mgana zai biya ma Badariya nata kudin makaranta sai dai a nemo na jamal ita zatayi kokarin nema mai na abinci kafin Lokacin tafiyarsa. Haka naji yana Mama bayani da Daddare da ya dawo ni kuma na shiga kai mata abinci.Mama tayi tagumi duk ta shiga damuwa kawayen nata da take takama da su,Duk sun janye daga gareta daman sai kana da shi ake yi da kai,Sannan itama babu jarin yin kasuwancin komai ya tsaya ita kanta duk ta rame ta Fige alamun ba natsuwa ba kwanciyar Hankali. Sai da yadawo bangarena na zubo mai abinci naga ya kasa ci yayi Tagumi sai naji ya bani Tausayi Namiji har namiji ammh lokaci kadan ya nemi ya susuce,batare da Tunanin komai ba ko shawara da wani ba,ina da kudi a banki na sun kai dubu dari da Hamsin daman shawaran Yaya Isa nabi da ya ce na tara wani abu ko Fili na siya kaddara ne saboda watarana,Washegari da Safe na bama Hafsah Atm dina zata tafi makaranta nace ta ciro kudin dake ciki Duka ita kanta tayi mamaki sai dai bata tanka ba. A hanyar dawowarta ta tsaya ta ciro kudin Dubu Dari da ashirin ta bani na adana su sai da Daddare da ya dawo Futu futu daman ya Dauki Takardunsa ya fita,Ko da ya dawo ya gaji salla ma acikin gida yayi ta ya kasa fita tun safe bai ci komai ba,Ruwan Citta da kunfari na Dafamai yasha cikinsa ya warware sannan ya Dora da abinci. Inda na fahimci damuwa ta masa yawa su Anum tana kiriniya bai bi ta kansu ba sai na saka Hafsah ta tarka su zuwa Dakin su nace su Dauko Littafan su,kafin su kwanta Sai da suka bar Falon sannan na shiga Daki na fito mai da kudin hannuna na basa da farko kin karb'a ya yi sai da nace ya karba sannan ya karba cikin mamaki yana fadin"Wannan kudin fa Fa'iza.? Ina zama nesa da shi nace"ka biya ma Jamal kudin makaranta shi da Yaran nan, zaman haka bazai yuyu ba tunda an fara sai a karisa" Sakin baki yayi yana kallona Lokaci daya yana kuma kallon kud'in bakinsa na rawa yace"Duka wannan kudin Fa'iza na waye..? Kai tsaye nace"Nawa ne dubu dari da ashirin ne Allah yasa zasu isa" Kai tsaye ya maidomin da kudin a gabana yana fadin"Bazan karb'a ba" Nima sai na turamai ina fadin"Kayi hakuri ka karba dukkanmu bamu da zabi ne" Sai yayi shuru ya kasa mgana,cikin wannan shurun ne wayarsa dake gefensa ta dau kara ina gani ya Duba yaja tsaki ya kashe haskenta ya mike daga zaune ya koma kan kujera yana fadin"Fa'iza duk ina kika samu kudad'e haka? Cikin mamakin Tambayarsa nace"Ina sana'a ai ka sani" Yana kallona yace"wata sana'a kike yi haka da ta ke kawo miki kudad'e haka..? Ina yar dariya nace"Kunin Aya da zobon da kake sha kullum,to shine abunda nake saidawa" Ido ya zaro kamar bai sani ba ahalin nasan ya basar ne ban bari ya kara mgana ba,na tashi da kudin na karisa gabansa na sauke mai saman cinyarsa ina fadin"Don Allah ka karb'a" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya Dauki kudin yana fadin"Zan karba ammh ba kyauta ba,bashi.In na samu aiki na warware zan biya ki kudin ki" Sai nace mai shikenan na amince nan ya zauna yana lissafin kudaden ya Dago yana cemin"Zai iya isa na biya ma su Anum kudin makaranta ammh Amir fa? Nazari nayi kafin nace'Shi ka kyalesa gaba sai a saka shi in an samu"sai ya jinjina kai yana fadin"Nagode Fa'iza" In yayi min godiya har mamakin sa nake yi tun ina mamaki har na daina adaran yaje ya fada'ma Mama kuma har aka bama jamal kudin ya koma makaranta ko mganar batamin ba nima don Allah nayi ban damu ba,daman bana jiranta. Bansan cewa zaman Hafsah a gidan nan na damun Mama ba, sai da ta kirani a gaban Yaya Ishaq tace yanzu ba da ba ne nasan ba shi da shi ammh na kara kawo mai Dawainiya ina ganin suma suna fama da kansu,Ni dai har tagama mganar ta ban ce komai ba ina mamakin me zaman Hafsah ya tare ma Mama..?ban da abinci bata cin komai agidan nan,kudin mota da duka Dawainiyarta da Sana'ata nake yi mata Yaya ishaq ne ya tare mganar yasa Mama ta kyaleni sai abun ya dameni a cikin raina kamar Goggo ta sani tace Ko Hafsah zata nemi Dakin makaranta ne ta koma, ni ko naga ina garin kamar bai dace ba da ma ace bana nan ne,shine ammh Tunda ina nan ta zauna a wajena ai nima ina moranta ta bangaran sana'ata. Sai kuma korafi na biyu ne,mama ta fito da Tsirfan Masu zuwa a bani kunin Aya da zobo sun fara damunta ballatana da taga ina samun ciniki da yake akwai makarantar secondaryn Gwamnati ta mata dake kusa damu, tunda suka gane ni, shikenan arana sai na Dafa zobo fin sau biyu kunin Aya da yawa nake yi,Masu sari in basu zo da wuri ba sai dai su samu kad'an sai ta fara fadan ana damunta da Hayaniya sai na Fahimci bakincinta da na d'anta take so na zauna ya kasheni ni ko nace araina, bazan miki Rashin kunya ba ammh kuma baki isa ki hanani sana'ata ba. Amir ne ke taimakamin tunda yana gida sai Hafsah in tana gida Badariya ma ba'a barta a baya ba, Kuma Maman tana sha kuma in tayi baki ina basu,ammh bata gani ba tamin mgana ban ce mata komai ba shima ta same shi ta mai mgana inaga shi ya kashe mgana bata kara tara ta da mganar ba. Ni dai na toshe kunnuwana na cigaba da sana'ata ganin wannan abun da tayi bai sa na dakata ba ko kuma shi Wanda take gani bai taka min Burki ba, sai ta fara fadin ina barinta da yunwa ina chan ina sana'ata sai rana ta take nake dafa abinci har da kwanciya ciwo sai da aka kai ta Chemist,ulcer ta kamata saboda zama da yunwa Anty Binta ta zo ta kirani dakin Mama ta na ta masifa Yaya Ishaq na jinta bai ce komai ba nima har ga Allah ban yi niyar mgana ba Saboda ni dai nasan ina dafa abinci akan Lokaci tunda na safe kafin tafiyar yara makaranta ne na rana kuma shi nake fara dorawa in na Dafa Zobon Farko na Dare kuma duk latti na bayan isha'i na gama abinci na kai mata ammh ban tsira ba. Sai da naji Anty Binta tace zan daina sana'ar da nake yi tunda Saboda ita zan kashe musu uwa da yunwa sai alokacin na dago na kalleta ban ji tsoro ba nace"Gaskiya Anty Binta ki yi hakuri ammh bazan daina sana'a ta ba.Domin banga ta inda hakan ya zama Takura ba" Sai ta saki baki tana kallona kafin ta kallesa tana fadin"Kana jinta dai ko..? Rashin kunya zata min a gabanka baka ce komai ba..? Sai ya muskuta kafin yace"Anty Binta mu bi komai a sannu in zaki ce mata ta gyara sai ki yi mata fada ammh babu Adalci mu hanata sana'arta" Mama na kwance ta daga kai tana fadin'"Ki yi shuru Binta ta siye shi da kud'i tunda yaga ta fara nuna tausayawa garesa shikenan bai iya tsawarta mata" Cikin mamaki ya kalli Mama kafin yace"Mama wannan wata irin mgana ce..? Mama ta zabura ta mike kamar daman chan lafiyarta kalau tana fadin"ai gaskiya na fad'a kada dai ta manta kafin tayi maka uban ka ya fara yi mata gata, sannan ya rufa mata asiri, kaima kazo ka rufa mata,ka zama gatan ta, in adalci kuma zatayi ai jarin ba Ita ta ginama kanta ba kai ka gina ma ta shi" Da sauri yace"Aa wlh bani da hannun akan sana'arta ban san komai akai ba" Anty Binta ta koma ta zauna tana fadin"Shiyasa naso na dauke Mama ka hana ashe zaka bari matarka ta gana mata azaba ne ban sani ba..? Yaya Ishaq yace"Anty Binta ki bar wannan mganar matukar ina raye Hakkin kula da mama da su Jamal yana wuya na ne sai dai in ciwo ko mutuwa sun kwantar dani" Ina zaune ina jinsu so nayi na tashi na fita ammh kada suce na raina su,yasa na zauna kaina na kasa ina tsintar wasu mganganun su. Mama da ranta ya gama baci tayi Kyafci kafin tace"Ta gama da shi ne Binta shiyasa kiri kiri yaje ya Duba Zainab yaki zuwa itama ai tana