Sashe 36
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bautar ubangiji. Na kuna riga na sakama raina ba sai na samu soyayyar miji ba,sannan ba kima sai na zama wata aba mai Daraja ba ni dai ya kasan ce watarana zan zama bango ga ya'yana shikenan Burina ya cika bani da wata Damuwa Ban matsa ma kaina sai su Mama sun so ni Dole ba domin akwai mutanen da ko Naman jikinka ka ke yankawa ka na basu suna Dafawa baza su taba sonka ba sai na sakama raina haka,Sannan nasan ba ni da abunda zasu kaunace ballatana na saka watarana komai zai zama Tarihi. Ban san ma ba'ayi suna ba ashe an kara Sati d'aya kafin taron suna ana gobe sunan Badariya ta zo take fadamin Sakom Mama akan na shirya su Amir da kayansu na kwana Biyu zata tafi da su,Baban su yace a taho da su ban yi musu ba na tashi na Shirya musu kayan su masu kyau Amir da Musty da Anum Ahmad kuma ya cika Rigima daman su ukun Mama tace za'a tafi dasu sai da ta jira suka Dawo daga makaranta jin zasu Abuja wajen Daada Anum da Musty suka fara Tsalle Amir ne ya kalleni yana kwabe Fuska Lokaci daya yana fadin"Umma ni bana son zuwa a bar ni a gida" Sai na kallesa Badariya Hankalinta yayi gaba kan wayarta sai bata ji sa ba na jawosa jikina ina Fadin"Haba Baban katsina wajen Daadan ku zaku je da Anty ku fa..?ba kwa so kaga Sabon kanin ku da Anty ta Haifa muku..? Sai ya gyad'a min kai alamun yana so kumatunsa na shafa ina Fadin"To kada ka kara cewa bakason zuwa..Kai ma zaka je ka ga Sabon kanin ku ko Amir di na..? Sai yayi dariyan su na yara kafin yace"Umma ke bazaki je ba..? Kai na girgiza kafin nace"Zan zo ammh Daga baya kaji ko..? Sai ya jinjina min kai,mganar da nayi mai yasa ya shiga cikin kannensa suna Murna sai da suka yi sallar mangariba suka ci Faten Ramar da nayi ina da Tsakin tun wanda Goggo ta kawomin ne yayi saura Gidan Sa'adatu na shiga na samu Rama dayake suna da Fili tayi shukeshuke har da su Zogale yanzu na fahimci mutane sune Rahma ina shiga makota na bayan kwana Biyu mu gaisa nima Sa'adatu da Habiba sukan lekoni Lokaci bayan Lokaci sai hakan yake min Dad'i ko da ba na ganin wani nawa a kusa dani Su din da nake gani sai suka Debemin kaso mai yawa na kewar da nayi shekaru yana Damuna. Sai da su Amir suka tafi naji gidan yayi min shuru Kuka sosai Ahmad ya yi da yaga yan'uwan zasu tafi sai da na Shige da shi daki sannan suka samu Tafiya,Dakyar na samu yayi barci ballatana daman Ahmad akwai rigima irin goyon da nayi Anum ne itama akwai Rigima kuma har yanzu bata Daina ba tana tabawa wani Lokacin don ma ina had'a mata da Nasiha sai take rage rigiman wani Lokacin. Sunan zai kama ranar jumma'a da Safe misalin karfe goma na Safe na gama wankin kayan yara kenan ina Daki ina shirya Ahmad da nayi mai wanka,kwata kwata ban ji sallama ba Saboda lalurata sai da naji Mganar ta kamar daga kofar Dakin da nake ciki,Ina juyowa muka hada ido Hudu da Yaya asiya Sabe da Jaririnta da karamar jakar matafiya a Hannunta. Na saki baki fararan hakora na suka bayyana cikin yanayina da murnar da ta cikani nace"Yaya Asiya.." Dariya tayi Lokaci daya tana karisa shigowa Dakin tana fadin"Na'am Yar Fa'i"Daman ta kan kirani da hakan in tana so ta zolaye ni.. Sai nayi Dariya,na bar Ahmad kan gado bayan na gama sakamai kaya na karbi jakar hannunta na sauke a gefe sannan na karbi Muhammad Auwal dake hannunta ita kuma ta Dauki Ahmad ta daga shi sama tana fadin"Kai Ahmadu naga ka kara girma ne daga ganinka Yaya Ishaq ka Dauko Tsawon kafa zaka yi" Dukkanmu gefen gadon muka zauna na kamkame Muhammad Auwal da ya zama Lukuti da shi Dagani yana samun kulawa da kuma Nono mai kyau. Cikin nuna farincikina na shiga gaisheta ta amsa itama cikin Fara'a kafin tace"Nace ni dai bari nazo na gani ko Fa'ina na lafiya ko bata san na Haihu ba ne? shuru baki ba wayarki sannan ina ta kiran ki a kashe kwata kwata bana samun ki kin gani Karofi zani nace bari na fara sauka naga Lafiyarki" Tana fad'a tana karemin kallo Lokaci daya da nazarina sai na sunkuyar da kaina ina wasa da showel din dake jikin Muhammad Auwal,Naji kunya sosai shi yasa na kasa mgana na kuma san ko zan mutu Ya Ishaq bazai barni naje kano ba ko da ma nasan Haihuwarta ballatana ban sani ba sai zuwan da su Goggo suka yi,bayan sun baro kano alokacin. Ganin na ki mgana yasa ta kyaleni ta Fahimci abun sai bata matsa min ba,Cikin Nazarin Dakin tace"Naji gidan shuru su Amir suna makaranta kenan..? Kai tsaye nace mata"Suna chan wajen Babansu jiya mama ta aiko Badariya ta tafi da su baban su yace a taho da su" Yaya Asiya tace"An yi haka jiya naje gida na iske su Hajiya nata shiri ni ban ma sani ba sai ajiyan ake cemin Amaryan Yaya Ishaq ne ta haihu aiki akayi mata gobe taron suna..har ma ake fadin Ishaq din ya yi ma mahaifin ita zainab din kara sunan babanta ya saka Lawal ammh zasu rika kiransa Farhan" Kai tsaye nace"Allah ya raya sa" Ta amsa da Ameen tana fadin"Ke ba'a je da ke ba kenan..? Sai da na dago na kalleta sannan nace"eh bai ce a zo da ni ba" Ta gyada kai tana fadin"Bakomai bayan an kwana biyu sai kije ki yi mata barka in kuma tazo shikenan" Ban amsa mata ba na daga Auwal a Hannuna ina Fadin"Kai Yaya Asiya naga ya girma ne kun yi wata uku ne..? Dariya tayi kafin tace"Watan sa biyu ne fa da kwanaki yana da girman jiki ne irin Goyon Husain ne zan yi" Na mike ina Sab'asa a baya na kafin nace"Eh ai suna ma kama da Husain din" Tace"haka kowa ke cewa" Tsab na goyesa a bayana na Saka zani ya lafe Ahmad kuma dama n da yaji Ruwan zafi sai barci kan gado Yaya Asiya ta kwantar da shi muka fito Falo muna Hira ni dai ina ta Fargaba kada ta sako mganar abunda ya faru Tsakanin Ya Ishaq da Yaya mariya sai naji batamin ba. Ita tayi mana girki Shinkafa da wake da mai da yaji,Ita tazo min da yaji da kori a robobin su tunda Sana'arta kenan na Dauka ina shinshina kamshin Korin cikin jin dad'i nace"Yaya Asiya korin nan nada kamshi nima ina so na iya had'awa ko shi na fara saidawa in za'a siya" Yaya Asiya tace"Indai za'a siya koyan sa ba shi da walaha Fa'iza..Sai na koya miki ke da ma na sanki da Sauri Dauke abu cikin Lokaci zaki gane komai sai ki rika zuwa kasuwa kina Siyo kayan had'in kina hadawa da kanki kuma wlh akwai samu in dai kika Samu masu siya sosai" Tun da naji ta ambaci kasuwa jikina yayi sanyi sanin ko sama da kasa zata Hade Ya ishaq bazai bar ni na rika fita kasuwa ba sai na share zencen ban kara mata mganar ba. Sai bayan mun yi sallar azahar mun zauna muna cin abinci ta dago tana kallona kafin tace"in na kwana anan Gobe da Safe zan yi sammako na biya ta Dutsemah na gaida Tamadina na kwanan mata Daya daganan na karisa Karofi na sauke gajiya achan sati yace nayi kafin na koma" Kai na jinjina kafin nace"Tamadina ta na lafiya..? Kai tsaye tace min"Lafiya ke shuru Fa'iza muna saka ran haka kwanki da ina jego mun yi waya da Megidanta da Abokiyar zamanta sun tabbatar min tana lafiya,ban ce a bata ba ne kinsan ko tayi mgana awaya bazan gane komai shiyasa na bari sai nazo naje na ganta" Na kasa mgana kunya nake ji ni da nake kusa ammh mahaifiyata na Raye sai ta shekara bata ganni ba Idanuwana suka ciko da kwallah Yaya Asiya ta gani ta kalleni sannan ta Girgizamin kai kafin tace"Kada ki dami Fa'iza nasan yanayin da kike ciki..Ki zauna ki yi ma aure Biyayya In sha Allahu zaki Rabauta ranar gobe kiyama a wajen Ubangiji..Sai dai duk Lokacin da kika samu dama ki rika zuwa kina Dubata bayan mu bata da kowa Fa'iza ita kadaice ta rage mana sauran gatan mu anan duniyan" Jinjina mai kai nayi ban ce komai ba ina Tunanin to yaushe nake samun Daman. ?Ko karofi sai na jima ban je ba,in kuma naje sai mutuwa ko Biki suna ma ba na kowa ba sai wanda Mama ta amince min naje nake zuwa. Zuwan Yaya Asiya ya D'ebemin kewa sosai,Sannan na Fahimci ko Rashin Lafiya na bata sani ba sannan ban ji tamin mganar ba sai nima nayi mata shuru ban gayamata ba. Da yammah na rakata makota na ta gaida su Sa'adatu da Habiba ina jin Dad'i Lokacin da na nuna ta nace yayata ce itace Babba ad'akin mu Sa'adatu ta kalleta tace"Ba kwa kama Maman Amir" Dariya nayi ban yi mgana ba Yaya Asiya ce tace"Ai mu mun fi kama da Babanmu..Ita yanzu da ace kin taba ganin Mahaifiyarmu sai ki iya cewa yaya da kanwa ce saboda Tsabar kamar da suke da juna" Haka ma Habiba tace itama kamar yadda ta fad'ama Sa'adatu haka ta fadamata,Da muka Dawo gida Yaya Asiya tace"Ko kefa Fa'i ki rika shiga Mutane don.Allah..Yafi ki yi ta zama agida ke kad'ai kamar mayya..Mutane Rahma ne sannan Makoci yafi dan'uwaka tunda sai wani abu ya sameka kafin wani naka yazo ya kawo maka Dauki makocinka yazo ya taimake ka" Cike da gansuwa da mganarta nace"Hakane" Domin ya faru akaran kaina kuma nagani,Tare muka kwana agado daya yaran mu na tsakiyar mu mun dad'e bamu yi barci ba Duk Mganar Yaya Asiya na Hakuri ne da kuma hakuri da yadda zamantakewar aure tazo min kafin mu kwanta sai da tace min"Fa'iza gaskiya ya kamata ki fara wata sana'ar ai zama haka bazai haifar miki da komai ba sai takaici Daman mun yi mgana da Mariya zamu tarfa miki jari tunda kina sha'awar Korin ko shi zaki jaraba ki