Sashe 133
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da yammah har da na Turanci in nagani Dariya nake yi na goge a raina nakan ce ya manta Fa'iza ba Turanci ne Sulhu yake nema ni ko Har Abada Ishaq ya fita raina sannan yayi sanadiyar da Sauran maza suma suka fita a raina. Rayuwata nake yi cikin Farinciki bani da matsalan komai ina sana'ata ban nemi komai na rasa ba, duk wata Abba na sakamin kudi bayan riban da nake samu,yan'uwana dukkansu yanzu Tallalina suke yi kamar kwai Goggo da mallam sai abunda nace duk kuma abunda bana so wlh suma sun bar shi kenan. Ni da kaina na kira Hajiya na fadamata Mutuwar aurena Hajiya bataji Dadi ba ammh sai tamin Fatan alheri da kuma Fatan kada na bar sana'a ta shi zai taimakeni sannan a Satin har karofi tazo mun jima tana mgana dani shawarwarim da uwa zata bama yarta shi ta bani ta nemi na koma makaranta nace mata bani da Ra'ayi sai ta kyaleni ta kawo min kayan kwalliya sannan ta kawo ma Goggo atamfa,ni dai duk kyautar da su nayi ga su Anty Nasara har da Hafsah da Khadija na ijiyemawa,sun yi mganar har sun gaji sun san ba ruwana da kwalliya balle ina cikin iddata. Sa'adatu ma da na fad'amata Har Karofi tazo ta jajantamin sai yammah tatafi bayan ta fadamin Haruna ya samu aikin Bijilanti,nayi mata Murna da na Rakota zaure zata tafi sai ta kalleni kafin tace"Kai Maman Amir kinga yadda kika yi kiba kika sauya kuwa..? Ina Dariya ban yi mgana ba sai tace"Allah ya kawo bazawari nagari" Da Sauri na Tareta ina Fadin"A'a ni yanzu namiji baya bani sha'awa kasuwancina zan bunkasa domin goben ya'yana" Kai tsaye tace"An ya..?da kuruciyarki fa wadanda suka fiki ma ai sun yi aure" Dariya nayi kafin nace"Bani da Ra'ayi kwata kwata kuma ina kuruciya anan Shekarata 34 fa" Sa'adatu tace"Uhm ko dai da Baban Amir din za'a daidaita? Mganarta yasa sai da gabana ya fadi araina nace ba Ameen ba Daganan na Sauya mganar sai itama ta barta. Dubu Biyar na bata tana ta godiya sannan na bata garin Danwake da yawa na kuma bata na ce ta kaima Habiba sun yi min abunda bazan manta da su ba. Ina gida bana fita ko'ina ina kuma lissafin iddata ko alama ban taba mgana da wani nace masa Ishaq na damuna da kira da sako ba,gogewa ma nake yi saboda kada wani ya gani Ranar wata Jumma'a da Daddare aranar ina da kwana talatin da Hudu da Iddata,misalin karfe takwas da wani abu na Dare naga Ishaq nata kirana ban Dauka ba,Kiran ne naga yayi yawa yasa na daga sai naki mgana maimakon naji muryansa sai naji Karadin Anum tana fadin"Umma Umma" Da Sauri nace"Na'am Anum din Umma" Cikin zumudi tace"Umma Yaya Amir ya yi na 1st postion a makaranta. yau aka bamu Hutu an basa kyauta Umma" Farinciki ya rufeni Cikin Dariya nacr"kai masha Allah..Amir din Umma yayi kokari ke fa nawa kika yi..? Da zumudi tace"Umma na 8th nayi fa kinsan bamu jima da fara zuwa ba aka fara Exams" Cikin nuna jinjinata nace"Dakyau Anun din Umma Ahmad da Musty fa..? nan ta rika zayyanomin abunda sukaci ina saka albarka Amir bai karbi wayar ba sai Musty daga shi Sai Farhan,yana ta min hiran an bama Yaya Amir kyauta nace dakyau ina tambayan Fadil suka bashi yana min Hira da gauranci ina Dariya wayar tsakanin yaran ta fara zagayawa wani har sau biyu ma irin su Ahmad da Farhan da basa gajiya daga karshe Anum ta kwace wayar sai nake tambayata ina Amir..?tace yana Daki ta kai masa ne sai nace ta kyalesa Antynsu na tambaya tace min Tana Daki ko da yaushe daman in na Tambayeta zasu ce tana ciki na Fahimci zainab bata son yara kwata kwata. Mamakin jimawar mu muna mgana nayi yasa nace ma Anum"Waya baki waya haka Anum..? Kai tsaye tace"Ta Daada ce fa shiya ce bari ya kiraki mu fad'a miki" Ba'a sirri da yaro ina ji ana mgana ban dai jin me ake fadi naji Anum tace"Me kace Daada..? Sai araina nasan wata mganar zai ce ta fadamin kamar ina wajen sai ji nayi tace"Umma Daada yace yaushe zaki zo..? Ban bata amsa ba na fara Hamman karya ina fadin"Oya sai da Safe barci nake ji"Ba ason ranta ba na katse wayar a fili na yi mirmishi ina mamakin Rashin kunya a wajen Ishaq sai yanzu yasan ya'yana suna da Rana. Nasan kunya ce ta hanasa zuwa garin nan ammh a juri zuwa rafi tunda bai da kunya zai iya zuwa. Kwana Biyu Tsakani Zainab ta Haihu aiki akayi mata An cire mata yarta mace kyakyawa nima Anty Fadila ta fadamin Tunda ita Ishaq ya taso cikin Dare sai tace ya kawota asibitin datake aiki a bakinta nake jin zainab din ta wahala karfinta ne ya kare sannan yarinyar ta karkace acikinta shiyasa akayi mata aiki. Dole Mama ta koma Lagos itama Zainab din daga Adamawa yayar Hajiyar Halima aka tura mata ta kula da ita,aikin yayi kwana biyar suka sallameta suka koma gida,na kirata nayi mata barka tace tana jirana sai nazo barka ina Dariya nace zan bata mamaki kuwa. Ba suna suka yi ba tunda ga nisa ga kuma kashe kudi,Sai dai Dr.Lawal da Hajiya Halima sun je sun ga yarsu da jikarsu sai kanwarta zuzu da ta gama karatu ta je aka barta achan sai Anty Fadila da yaranta,yarinya taci sunan FA'IZA. Da Anty Fadila ta fad'amin sunan yarinyar sai da Dariya ya kamani shima yayi ta kirana ban Dauka ba. Zainab ta kirani tace sun yi min takwara in dawo ko saboda little Fa'iza,yara kuma suna ta murna an haifa musu bby,Anty Fadila tayi bajinta kamar ni ce na Haihu, kayan alfarma tayi ma Zainab da Little Fa'iza har Abba da yaji sunan Bby sai da yayi Dariya Tausayin Ishaq kad'an ya tsirga masa. Sai dai kuma ina! bakin alkalami ya riga da ya bushe. *Janafty* [7/27, 7:24 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3007* *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Zainab tayi tayi dani nazo naga Little Fa'iza naki ce mata zan zo,Har da yaran suka had'a baki suna ta kirana suna magiyan Umma kizo don Allah. Zuwa Lokacin Anum da Amir sun Fahimci yanzu Umma da Daada basa tare Anty ce kadai ko da ba'ayi musu bayani ba. Nii kadai na kudura araina zan bada Sako a kai ma Zainab da yaran sai na kira Badariya nace yaushe zataje..?sai tace min da tare da Anty Binta da Anty mahma zasu bi jirgi ammh daga baya su zasu rigata tafiya zata tsaya sai ta gama karban takardunta gabadaya tunda ta kamallah bautar kasarta in tatafi bazata dawo ba,har ina mata tsiyan ta zauna a kanon ta kawai wajen Hajiyar Dala. Kai tsaye tace min Allah ya kyauta zaman hakuri da ba yadda zatayi ne yasa ta zauna a baya. Gwara ta koma inda tafi wayau,mun rabu cikin Raha nace kafin tatafi ta biyo ta Karofi na bata Sako Tunda tace min doguwar Mota zata bi tana da kaya da yawa. Ko Goggo ban yi shawara da ita ba sai dai taga ina ta shiri Zainab Less na siya mata ita kuma takwara kayan kanti masu kyau da Huluna da Dan kunne da abun hannu har da lalle mai kyau,sai takalma na yara masu kyau da yarari. Sai na siya shadda Mai ruwan kasa na bama Yaya isa ya kai dinki aka dinka ma duka mazan har da su Farhan Anun kuma na mata dinkin Atamfa da less,sai hijabai kala Uku,sannan na fansar musu kananun Qur'anai sai azkar dukkan su kowa Daya Daya Amir kuma sai na karamai da karamar Mp na saka aka cikata da Complete Qur'an kyautar na yin na D'aya da yayi,na kuma zage nayi musu Dambun nama kaza,daman na iya bana yi ne to yanzu kuma ina so na Dawo da shi na rika karban aikin ana Biyana sannan daman na Dawo da sana'ar Turaren wuta dilka ce ban fara ba Tukunnah A na gobe Badariya tazo ta kirani ta fadamin ranar jummala na bar ma Hada zobo da kunin aya na Dukufa Hada Tururika sai da na cika Dan Botiki da na icce,sai wani gora da kwallacha na ruwa ne ban yi ba,kwallacha kuma nayi ma Anum nata ita da Amir sun girma suna Bukatar kamshi suma Goggo taga na kasa zama ta tambayeni sai na Fada mata rike baki tayi kafin tace"Duk wannan kayan na mutanen ikkon ne..?ko dai ko dai fa'i..? Nagane nufinta yasa nayi Saurin Dagowa ina Fadin"Haba Goggo..Ko ba komai ai tana rikon ya'yana sannan akwai kauna Tsakanina da Zainab wlh ba domin Ishaq ba, domin kaunar da ta nuna min ni da ya'yana tun farkon auran su da Ishaq" Zan iyi ma zainab komai in dai bai gagareni ba" Goggo ta jinjina kai kafin tace"Na Fahimta nima zolayarki nake yi" Sai nayi Dariya ban kara mgana ba sai da naga har Dinkin nasu An karbo na hada kayan waje daya kowa kuma na saka sunan shi jikin nasa gudun rigima. Washegari karfe Tara da wani na Safe tayi ma Badariya a karofi Daki muka kulle muna ta Hira,Daman kuma tace tana son ganina