← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 175

Sashe 6

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiga cikin Dakinsa minti kad'an ya fito Hannunsa Dauke da wani Hoto ya zauna Lokaci Daya yana mika min Hoton na sa ka Hannu biyu na karb'a Fuskata da mamaki da neman karin bayani. Ya Dora kafa d'aya kan D'aya kafin ya kalleni yana Fadin"Duba ta da kyau ki gani Fa'iza.." Sannan ki Fadamin ya kika ganta..? Fa'iza tabi Hoton Dake hannunta da kallo Wata kyakyawan Hallita nagani kamar ita tayi kanta wajen kyau Doguwa mai Dogon Fuska da Hanci har Baka Farace tss mai ja ja ja,Sannan tana da lobawar Kumatu,Wato Dimple Gashinta Har gadon bayanta yake,ga Diri na Cikar ya mace duk da Abaya ne ajkinta Shape dinta ya bayyana sannan tana da Wushirya hakoranta data Bude sun bayyana Farare masu Tsari ga Kunshinta ja ne ya fito akan Fararan Hannayenta masu kyau da sheki Fa'iza tana ganin Ya Ishaq mai kyau ne sai dai dataga wannan sai taga ai shi bamai kyau bane. Ganin yadda ta bada Zuciyarta wajen kallon Hoton yasa ya Karbe Hoton batare data shirya ba na Dago ina kallonsa ya Daga Hoton yana Fadin"Ya kika ganta..? Fa'iza cikin yanayin mganarta tace"Tana da kyau..!" Ishaq yace"Eh ban ji me kikace ba..? Fa'iza tace"Tana..tana da kyau sosai.." Ishaq yayi wani irin Dariya kafin yace"Bayan kyau fa..? Baki Fahimci ta mallaki komai na Kyau da Zatin ya' mace ba..? Fa'iza tayi shuru batayi mgana ba Ishaq ya kalli Hoton na wani Lokaci kafin yace"Kinsan wacece wannan..? Fa'iza ta girgiza kai kafin Ishaq ya Cigaba da Fadin"Matar da zan aura ce..Zabi na ce Fa'iza Zainab lawal Bako kenan..Mace ce mai kyau Kamar yadda kika ganni Mai tarin ilimin Zamani Tana da Degree Biyu sannan tana Shirin komawa Phd dinta,Iyayanta masu Kudi ne da Nasaba ta mallaki Duka Burina na nan duniya nan da Sati uku zata zama matata zata cika min gurbin mafarkina da kika Tarwartsa Fa'iza. Shiyasa na yanke shawaran zaki Dakatar da Haihuwa hakanan ki bar mai wuri tazo ta fara Haifamin kyawawan ya'yan da nike Mafarki.Yanzu ne zan san ni Ishaq nayi aure,abaya ina jin kunyar nuna ki a matsayin Matata ammh ayanzu banda Haufin Duniya taga Zeey a matsayin Matata ina Rokon ki Fa'iza nayi miki komai a Rayuwar ki yi Free d'ina ki barni naji D'adin Rayuwata ni da Matar data dace dani." Ya karishe fada ya na kallon Fa'iza da kanta ke kasa ta kasa gane ina mganganunsa ya Dosa Cikin wani yanayi na Dago ina Fadin"Bangane ba..? Kai Tsaye yace"Zamu jingine AURAN mu ne Fa'iza..Wlh in nace ashekara Takwas din da mukayi da aure ban cutu da auranki ba nayi karya kiyi ma kanki adalci kiyi min adalci nima" Gaskiya ya Fada Tabbas gaskiya ya Fada Fa'iza ta fada acikin aranta. Cikin wani karfin gwiwa na kallesa kafin nace"Jingina kamar ya..? Kai Tsaye yace"Jingina ina nufin ba Saduwar aure tsskanimu a matsayin miji da mata ba wata mu'alama ta aure ba Raba kwana Tsakaninki da Zeey..Sai dai zan cigaba da kula Dake saboda Darajan ya'yan dake tsakanin mu Kada ki manta ba Mu'alaman miji da mata Tsakanina Dake..Kawai zan kula Dake ne Saboda ya'yana kawai" Har ya gama mganansa kallonsa nake yi Hawaye sun gama wanke min Fuskata ga mamakinsa sai kawai yaga nayi Mirmishi,mirmishin da zai iya rantsuwa bai taba ganin Fa'iza tayi irin sa ba. Cikin wata irin muryan da baisan ina da ita ba yaji nace "Na Amince.." Farinciki ya kamasa ya kalleni yana Fadin"Nagode Fa'iza ko bakomai kin yi sakayyah ga Alherin Baba agareki." Ko kara Sauraransa ban yi ba na mike Zan fice ya Kira sunana na waigo Cikin Kaushinsa yace"I ya ni da ke..Ban yarda wani yaji wannan mganar ba kina jina..? Kai na gyadamai ina sharan Hawaye, muryata na rawa nace"Insha Allahu ba wanda zai ji sai indan kai kaso hakan" Daga haka na fice da Sauri Saura kadan Rigar jikina ta Hardeni na Fadi bai Damu ba Murna yake zai samu Salama Shekara Takwas yana cikin kurkuku sai yanzu yaji sa kamar yana Shakan iskar yanci. Har na karisa Dakina kuka nakeyi bana ko ganin gabana sosai,kan gadona na Fad'a gefen Ahmad ina wani gunjin kuka Dake fitowa Daga kasan Raina Hasbunallahu wani'imal wakeel shin ni na Tsara ma kaina Rayuwata a haka..? Allah ne yayi ni baka mummuna Allah ne ya so ya ganni afasalin daya ijiyeni meyasa ya Ishaq bazai gane haka ba..? Yau ni Ya Ishaq ke mganar zai jingine auranmu Saboda wata.? Na tabbata ba Domin mganar Baba ba da tuni aurane da Ishaq ya kare to ai yanzu ma ba Maraba..? Zai jingine ne kawai saboda mganar Baba ba Domin Ra'ayinsa ba,sai kuma domin kuma ya'yansa Ba laifi na bane domin na fito a mummuna ba, kuma ba Laifina bane domin na fito daga jikin Bebiya ba, ba Laifina bane domin na kasance an Haifeni da Laluran rashin ji sosai da yanayin mgana taba, ba Laifi na bane Allah ne ya Tsara min Rayuwata Daki Daki. Sannan ba Laifi na bane domin ban zama mai ilimin zamani ba Domin duk yadda ka kai ga Tsara rayuwarka To KANA NAKA ne Allah na nashi kuma na Allah shine daidai kuma Tsari mai kyau. Ina cikin wannan halin bansan sanda na fara jin tunanin yadda yanayin rayuwata ya fara dawomin acikin kaina ba,tundaga farko har zuwa yau din da Ishaq yace zai jingine aure na saboda wata. Nafara da Tunano yadda yanayin Rayuwata ta fara ne cikin Farinciki Tun mahaifinmu ALHAJI SIDI KAROFI na raye. *ASSALAMU ALAIKUM* *KAYA SUN SAKE SAUKA*. *INGANTATUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*. *ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA. SANNAN BASU DA BAURI MASU KIDIMARWA*. *KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?* *INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*. *INA DA TABBACIN INGANCINSU*. *TUNTU'BI WANNAN LAMBAR DOMIN KARIN BAYANI* *08032773332*. *SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE* *Janafty**KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *Book 1* *Madallah da ku masoyana naji Dad'i na kuma yaba muku da yadda kuka karb'i Labarin nan fiye da Zato na..Nagode kwarai Allah ya had'amu cikin Ladan gabadaya,Madallah da masoyan gaskiya da Amana,nace Madallah da y'an Amanar Janafty* *ASSALAMU ALAIKUM* *KAYA SUN SAKE SAUKA*. *INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*. *ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*. *KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?* *INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*. *GADALIN MATA AKWAI*. *INA DA TABBACIN INGANCINSU*. *SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*. *TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU* *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI* *08032773332*. *NATION WIDE DELIVERY*. *SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE* Asalin kakanmu wanda ya haifi iyayan mu maza ni da Yaya ishaq bakatsine ne wanda ya fito daga Tsatson katsinawan Karofi. Karofi kamar Anguwa ce ko wata alkarya dake cikin Garin karamar hukumar Dutsenmah ta Jahar katsina. Tunda ga Dutsenmah,Katsina Kankara,malumfashi bakori,mahuta da Sauran kananan hukumomin dake zagaye da Garin katsina ba wanda bai san Waye Alhaji Sulaiman Karofi ba,Saboda tun lokacin yana Raye shekaru sama Hamsin da wani abu da suka gabata an yi Attijirin mai kudi,Domin kaf yankin nan ba inda ake siyan Siminti sai a wajensa manyan manyan Store yake kama haya ana cikamai su da Siminti tun yana matashinsa da wannan sana'ar ya fara kuma alhamdulillah ita ta Daukakesa har kuma Allah ya Dauki Rayuwarsa bai sauya sana'a ba. A yadda Babanmu ya bamu labari Lokacin yana raye Saboda muma ko da mukazo Lokacin Allah ya karbi Ran Alhaji Sulaiman sai dai mun sha Labarin kirkinsa da Dattakonsa bakin Babanmu. Ya sanar damu cewa Alhaji Sulaiman Kamfani kamfani na Siminti Mota mota ke shigowa Karofi Domin saukemai Siminti kuma ba'a sati duk sai ya kare bayan manyan yan kasuwa yana saida ma marasa karfi da masu siyan daidai misali sannan karin Daukakarsa baya tsawwalla kudi i ya abunda Allah yasa ya samu sai ya sanya musu albarka. Mutum ne akace nagari kamili mai sanin Darajan dan adam da Dattako,da kowa yake yabonsa Daga uwa har uba duka haifaffun karofi ne,Kenan ba shi da wani garin da ya wuce mai Karofi alokacin. Yana da matar auransa Daya Hajiya Suwaiba(Hajiyar karofi) ita ta Haifamai manyan ya'yansa guda Uku Hajiya Fatima ce Babba(Hajiyar Dala) sai Hajiya Aisha(Goggon karofi) Sai karamin su Alhaji Kabiru(Baban katsina) Sai Autan su Alhaji Sidi( Babanmu) Wanda rabonsa ne yasa aure ya kullu Tsakanin Mahaifiyarsa Asiya da Alhaji Sulaiman Karofi. Alokacin baya in aka auro mace daga wani waje ta shigo inda bata san kowa ba,to akan samu a makotan da aka kawo ki kina samu yar D'aki da zata rika shigowa tana tayaki zama da yan aikece aikece to haka ne ya faru da Hajiya Suwaiba ita din yar cikin garin Dutsemah ce kuma auran Soyayya ne ya kulla Tsakanin su mai karfi kafin ta kai su ga aure. Yadda na samu Labari Hajiya tun tana matashiyarta macece mai kirki da Sanin ya kamata sai dai akan mijinta bata da kauda kai tana son shi Shiyasa take bala'in kishinsa. Tun sanda aka kawota garin gidan da Alhaji Sulaiman ya gina gefen katangar gidan su Asiya ne, wanda garun gidan Alhaji Sulaiman shi ne garin gidan su Asiya talaakawa ne Futuk,mahaifinta mallan Haruna ya rasu bayan doguwar jinyar da yayi a baya masarin bishiya ne an ce Tun wani Sare wata bishiya da yayi shikenan bai kara lafiya ba har ya rasu Daga Asiya sai mahaifiyarta Atika suke Fafutukar Rayuwa to lokacin da aka kawo Hajiya Suwaiba Asiya ta kan shiga ta taimaka mata da yan aike ce aike ce tunda daman Asiya bata da kiywuya Lokaci kadan suka saba da Hajiya tun balle data fahimci suna cikin Halin matsi ita ke taimaka musu da abinci suturu har kuma ta saka Alhaji Sulaiman shima ya tallafa musu. Cikin lokaci kadan Asiya ta zama yar Dakin Hajiya Suwaiba duk wanda yasanta yasanta da Asiya,Suna tare ta yi goyon cikin Fatima ta haifeta kowa yaga Asiya sai yaba da kokarinta da Himmanta Hajiya kuwa har ga
Chapter 6 · 0% Book details