← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 175

Sashe 148

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yanzu zai dawo gareni" Kwata kwata tunanin Abba bai basa mganar Fa'iza yake yi ba, sai yayi masa Fatan alheri shi kuma Ishaq bai fara ma Abba mganar ba yana jin kunya da nauyi yana Tunanin da Sanin sa Faa'iza ta yanke komawa gidansa. Abunda kowa bai sani ba tuni labarin zan koma gidan Ishaq ya Zaga Dangi har Karofi bakin su Goggo,Itama Yaya mariya tazo tana fada musu itama a bakin Anty Binta taji tunda Anty Mahma ta haihu sun je suna sukaji ana ta maida zencen Yaya mariya abun ya bata mamaki tazo ta samu Goggo ita kuma tace anya.? Bata sani ba ammh bari Mallan ya dawo taji ko Abba ya kirasa sun yi zencen to shima abakin Goggo yace yaji bai sani ba jin haka yasa Goggo sai ta Dauka shirme ne jin ko ni ban gayamata ba ballatana shi Baban namu. Labari har Bauchi Mama ta fad'ama Badariya ba wanda ya kaita Murna ita da Jamal,Anty Fadila ko har gida Ishaq yaje ya sameta da mganar kan zasu je tare ta zabamin Furnitures din da za"a sakamin a dakina,abun itama ya bata mamakin zan dawo ammh bataji ko a bakin Abba ba,sannan ta kirani bata Sameni ba Abba kuma data kirasa sai yace yana meeting ne zai kirata Daga baya. Ayyuka suka sha kanta bata ko yi zencen da kowa ba. a tunaninta ai za'a sake Daura aure tasan Dole za'a fadamata sai bata kara neman wani da mganar ba ammh da ita akaje aka siya min komai na kayan Daki masu kyau da yarari har ga Allah taji dadi ganin ma yaran nata Murna har da ita Zainab din da Mama yasan ta san gabadayan su suna maraban da dawowata a ranta tace nayi hankali da zan dawo saboda ya'yana mganar Engr kuma Ammi ta fad'amata ammh jin wannan mganar sai ta Dauka Abba ya basa Hakuri shiyasa ma bata Damu ba. Bani da masaniyar mganata ta zama zarar buni gabad'aya tunanina da komai nawa yana kan Engr,Sanda na fadamasa na amince masa kai tsaye a inda yake ya duka ya daidaici gabas ya yi sujudul shukur ta godiya ga Allaj sai da ya dago sannan yace min"Alhamdulillah nagode sosai Faa'izaa.ban yi miki alkwarin Farinciki har abada a tare dani ba. Sai dai nayi miki alkawarin zan yi iya kokarina wajen hana Faruwar bacin rai ko damuwa a kan fuskarki." Yadda kika amince dani kika bani amanar Ragamar rayuwarki ni kuma ina rokon Allah ya bani ikon rike ki bisa gaskiya da amana kada ya barni na zama silar zubar hawayen ki watarana" Kalamansa sun saka sai da nayi hawaye na tuna ban fa sauya ba ina nan a Fa'izata baka,mummuna mara gata da galihu,mai raunin ji mara ilimin boko wacce batajin Turanci bazawara mai ya'ya hudu ammh mutum kamar Engr da ya mallaki komai na matakin rayuwa ya ce yaji ya gani sai nima na sallama wata irin Soyayya yake gwadamin kulawa ko kamar tsoka daya a miya,Engr duk yadda zai sakani Dariya ya sani in muna wayar har hawaye ina yi Saboda Dariya ba shi da girman kai kamar sauran maza a baya na Dauka maza ire iren su suna da Dagawa sai da na hadu da Engr na karyata haka sannan na kuma gane me ake kira soyayyah ina jinsa a raina Fiye da yadda nake jin Ishaq a baya acikin Raina. kada ku ga laifina na yi shekaru Cikin bautar aure da Tozarci bansan ace ana sona ko na Burge ba yanzu kuma na samu mai sona wanda yake nuna ma duniya ba kamar ni sai na Zama kamar wata sauna kira mana shashasha zuciyata da gangan jikina ta fara bin Umarnin Engr da duka Bukatansa. Duk da bai gayamin komai akansa duka ba ammh a Hankali na fara Fahimta,Nayi waya da mahaifiyarsa Hajiya Shukra matar nan tun bata ganni ba ta kaunaceni,cikin muryanta mai sanyi da muka yi waya ta rika min Godiya tana sakamin albarka sannan mun yi mgana da Sisters dinsa duk da Hausan su bata fita sun fi iya Yarbanci da turanci ni kuma ba Turanci sai Hausa kawai ahakan ma nagodema Allah,Mahaifinsa ne bamu taba mgana ba yace sai na zama amarya zamu je ya yi mana Nasiha Benue ko sai nagaji da zama cikin yarbawa akaso ne da kilose sai nagaji da ji,in ya fad'i haka sai dai nayi ta Dariya,ga shi ko da wani Lokaci muka yi waya sai yace ina yara..? In nace suna lafiya sai yace ina Fatan kin fara basu labarina saboda ina so ranar da zasu fara ganina na bude hannuwana su zo da gudu suna rige rigen kiran sunana da Baba..Baba..! Ina Dariya nace"Ba Baba Tosin ba..? Daure fuska ya yi kamar yana gabana kafin yace"Ni ai tosin din Faa'iza ne a wajen Ya'yana sunana Baba Abdulbasit' Kai Engr abun dariyansa basa karewa. Dakyar a Daddafe ya yi sati biyu yazo ya ganni ni kawai na kawosa kaduna yazo yayi awa biyu,Abuja ya koma Tunda a daran zai bi jirgi zuwa Lagos,A ranar hirar sa duk ta mganan auren mu ne yace zai je America next month,yana so kafin ya tafi a Daura mana aure,ni kuma sai nace ya Tuntubi Abba da haka muka rabu,ni in ana fadin Engr nada kyauta bana gani domin bai taba bani ko Biyar ba. sai da yana samun kati yace na kira Yara bayan haka bazan dora komai ba. nima ba wannan ne a gabana ba shiyasa ban damu ba. Ranar da yazo Ammi har kwalliya tasa nayi nace mata a hakan yace yana sona baya bukatar wani kyale kyale da Katon Hijabina har yana sharan kasa naje masa ko kayan jikina bai gani ba ammh haka ya rika zuzuta nayi kyau Allah sarki Rayuwa ashe akwai ranar da ni Fa'iza zan iya Burge wani..? Tabbas ko ban auri Engr ba ya yi sanadiyar kafa aya mai girma a Rayuwata. Kowa ya ganni yasan ina cikin Farinciki da Annushuwa sanadin Tarayyata da Engr,sannan na samu natsuwa tunda su Anum basu karamin mgana ba itama Zainab din sai dai mu gaisa,ashe ban sani ba shi Gogan ya hana su karamin mgana Tunda acewarsa yasan Halina da Taurin kai yanzu sai na iya Sauya ra'ayi. Kuma har alokacin bai nemeni ba ammh yana ta shirin dawowata Alhalin ni da shi bamu yi wata mgana ba. ****** Watan mu daya da Haduwa da Engr,Makarantar Haddanmu ta kiramu akan Karban shahada, mu goma Cif zamu karbi shahadar Haddan Qur'ani izifi Sitti,Dole zan koma karofi,Har ga Allah har zuwa Lokacin Abba baisan Halin da ake ciki ba ta bangaran Ishaq ba,ammh sun yi mgana da Engr sosai ta waya akan aurena yace masa ba shi kadai ke da ni ba ina da yan'uwa da iyaye achan karofi zai je ya same su,abunda suka yanke zai Fada masa da haka ma suka rabu. Sai dai kuma bayan ya samu Inno sun Tattauna itama ta goyo bayan yaje ya samu Goggo da Mallam su tattauna,Ya shirya tafiya ma karofi sai kuma Ishaq ya kirasa da wata mganar data sa ya kasa gane ina aka nufa. Abunda ya faru shine Mama ta yi ma Ishaq maganar yaushe za'a maida auran..? Har ga Allah ya ma manta da sai an kara Daura mana aure,ya dauka kawai zan dawo ne ita ta ankar da shi,Sai alokacin ya tuna da sai fa an kara daura wani auran shine Dalilinsa na kiran Abba bayan sun gaisa da Tambayan aiki Ishaq cikin jin nauyi ya yi kasa da Murya cikin Ladabi kafin yace"Abba nace ba..yaushe kuka saka ranar Daurin auran..? Sai abun ya bama Abba mamaki cikin mamakin yace"Daurin aure kuma..? Auran wa..? Ishaq na jin kunya yace"Ko bata fad'a maka ba ne Abba..? Abba da ya fara hasaso abunda ke faruwa yace da sauri'"Ita wace ce bata fad'amin ba? kuma me zata fad'amin" Sai ishaq ya yi tunanin kila Fa'iza bata fad'ama Abba ba tana jin nauyi sai yace"Fa'iza mana Abba. kan mganar maida auran mu ni da ita" Sai Abba yaji zufa na ketomai cikin mamaki yace"Topaha..Fa'iza bata fad'amin ba ban ma san da wannan mganar ba" Ishaq yace"To ban san meyasa bata fada maka ba,ammh ta sanar da yara da Zeey cewa zata dawo har ma ina mata shirin dawowa Abba" Sai Abba ya jinjina kai kafin yace"Ba shakka. to ka bani Lokaci zan yi mgana da ita abunda muka yanke zan nemeka a waya" Da haka suka rabu da Abba da ransa ya baci a fili ya furta"Meyasa Fa'iza zata min haka..?domin na bata dama bai kamata tayi wasa da Hankalin mutane haka ba" Shi kunyarsa Daya Engr ya zai yi da shi..?da tasan tun farko ga inda zata koma meyasa ta amsa masa ai da ta basa Hakuri gabadaya ya shiga Tunani Saboda wlh tallahi yana ganin girman Engr baya so ya yi abunda kuma rai zai zo ya baci ta turo sa sannan kuma ga Ishaq da wata mgana a gefe. Da bacin ran ya koma gida sai kuma Ammi ta tare shi da mganar Fa'iza zata koma karofi Saboda walimar Saukar su,Da farko ya so ya kirata ne ya tambayeta ammh sai kuma ya Sauya shawara yana so yagani ko zan nemesa da mganar ammh har akayi kwana Biyu bai ji komai daga bangarena ba, sannan Engr ma ya kirasa akan ko yaje karofin yace bai je ba sai weekend sai ya Fahimci shi kan shi bai san abunda ke faruwa ba in ma ni na sani to ban Fad'a masa ba. Ranar alhamis da Daddare bayan ya Dawo gida yana shirin kirana sai ga shi na shigo Falon,da rana ya Kira Nana Fadila sun yi mgana itama yaji mganar komen a bakinta sai bai nuna mata yaji wani batu ba,Abunda kuma ya kara Dauremai kai da suka yi mgana da Mallam mijin Goggo yace masa zai zo akwai mganar da zasu yi Bude bakin Mallam sai cewa ya yi"Masha Allah Allah ya kaddara da Sauran zama Tsakanin Fa'iza da Yaron nan ai gwara ta koma Saboda ya'yan Dake Tsakani" Sai ya tabbatar da ba shi kadai yaji wannan mganar ba mutane da Dama sun sani,da ya dawo yau ya tambayi Ammi kan yanayin alakata da Engr Ammi cikin Fara'a ta labartamasa yanayin Farincikin da nake ciki sai
Chapter 148 · 0% Book details