Sashe 147
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zai kwana sai gobe zai wuce Edo yana da Meeting da rana. Ayyah kawai na iya ce masa kawai sai ya karya wuya yana Fadin"Gaskiya Faa'izaa ba haka ake yi ba. Sai nayi ta kiran waya baki dauka ba. Sannan Dazu kin yi min laifi kika gudu bamu yi sallama ba" Sai nima naji ban kyauta ba cikin yanayin mganata nace"Kayi hakuri" Da sauri yace"An yafe miki. ai amarya bata laifi ko ta kashe dan masu gida" Ni ko nace bata dai kashen ba ne shi kuma sai ya gyara murya yana Fadin"To ki bari ki zo zan jawo miki Taye da kahinde ki kashe su ki gani ai Godiya zan miki ma duk cikin so ne" Ina mamakin sunayen da ya kira cikin sigar tambaya nace"Taye da kahinde..? Sai ya yi mirmishi kafin yace"na manta ke baki iya yarenmu ba ko..?kamar kin koya kin gama in dai muna tare. Taye and Kahinde Twins name ne da Yaroba,Sister na Twins ne ammh asalin sunayen su Kafayatu Abdulghaffar BIMFE,and Sharifatu Abdulghaffar ERIMIPE." Cikin jinjina kai nace'Tab kowa sai an sakamai sunan yaren naku ne.? Yana dariya yace"Sosai ke ma ai zan saka miki naki" Ina rike bakina nace"Fada mu ji" Sai yayi shuru kamar yana tunani kafin kuma yace"Naki wayan sai nazo,Gani ga ki sai na fad'a miki naki sunan" Dariya nayi ina hasaso ni da sunan yarbawa wayaga diskindarid'i,hira muka cigaba da yi yawan hiran daman nasane na barkwanci da ban Dariya sai 11pm yace naje na kwanta zamu yi mgana da Safe,ni ina ma na san Dare ya yi haka kai Fa'iza kam na zake da yawa haka na kwana mafarkin Engr da Safe da naje gaida Inno,bayan mun gaisa ta kalleni tana Fadin"Naji abun alheri wajen Aziza..Bawan Allah ne mai halin kirki ne matuka Baban ku yasan karamcin sa in kika amince masa bazaki yi nadama ba Fa'iza, sai dai bamai yi miki Dole kamar yadda Baban ki ya fada duk abunda kika zabama kanki daidai ne Allah ya sanya Alheri" Na kasa amsawa a fili sai acikin zuciyata haka na koma daki jikina a sanyaye,ina ko daukan wayata nagama ya kirani har sau uku ina shirin kiransa sai ga shi ya sake kirana ina Dauka yace"Gaskiya ni dai ba'a kyautamin ba gaskiya" Ina mirmishi nace"Da aka yi me ne..? Sai ya basar yana fadin"Kin ta shi lafiya?nace lafiya lau muka gaisa nan yake fadamin zai bar kano Jirgi zai bi zuwa chan Edo din ba zato fa tsammani naji yana mgana sama sama sai naji wata yar tsohuwa na kwalamin sallama na amsa na gaisheta cikin girmamawa da ta fara kwarara mana addu'o"i sai da naji kwallah ta zuromin tsohuwar nan akwai addu'a a bakinta. Sai da ya karbi wayar ne kafin nayi mgana ya rigani da cewa"Hajiya ce kakata ta bangaran uwa. na bata labarin ki ne sai kuma taji muna waya sai tace na bata ku gaisa,sai na bata ai kin ga yawan gaisuwa yafi yawan Fada ko Faa'izaa..? Sai nayi Dariya kafin nace"Hakane Engr" Yana kada Harshe yace''Laalaa aiko zamu bata ke ma Engr ne a bakin ki..? Sai da na rufe bakina kafin nace"To Ko Tosin zan ce...? Yanayin mganata yasa yadda na fadin Tosin sai da naji kyatatan Dariyan sa kai kawai yake girgizawa yana Fadin"Zan rama ne zan rama Faa'iza" Da wannan hiran muka yi sallama yace zamu yi mgana bayan ya sauka,ammh yana Filin jirgi sai da ya Kirani daman ina Daki waya a kirjina kamar yasan Tunaninsa nake ina Mirmushi ni kadai. Da rawan jiki na dauka ko sallama ban gama yace"Sharadin mu gobe ne ko Faa'izaa..? Cikin mamaki nace'Sharad'in me..? Sai kawai ya yi mirmishi kafin yace"Ashe zan dawo kaduna yau kuwa..?har kin manta..? Ina jin haka na fara dariya sai shi kuma ya kanne yana Fadin"Kwana uku zan yi a Edo zan shiga gida Benue dagachan zan je Abuja, wlh bakin nan nawa bai Haila sai na gama yadaki a Dangi gabadaya" Da Sauri nace"Kai don Allah kamar wata yarinya..'" Shima kai tsayen yace"Yarinya ce mana shekaran ki nawa..? Kai tsaye nace"35..ban karisa ba ma sai watan jibi" Irin Dariyan da ya yi ta nishadi kafin yace"Ashe ma da yarinya nake mgana. Ni ai ban ga baban mace ba yarinya danya Sharaf zan dauka nima ta jikani da yarintarta na dawo Dan Saurayi shar dani" Dariya ta kamani kafin nace"da Furfuran zaka dawo yaro.?ni kuma da ya'yan hudun zan zama yarinya sharaf.? Yana shafa kansa kamar ina kallonsa yace"Ke bar wannan mganar muma fa Tsiffon nan mun iya romancewan nan ko wasu matasan albarka,bar ganina haka Tsab zan dawo dake yarinya Dayan sharaf dake abun da duk mun san komai" Ya karishe fad'a yana Dariya kunya ta saka na kashe wayar yana ta kira ban Dauka ba kawai sai ga sakon shi. "Karya nayi Tosin da Faa'izaa basu san komai ba..? Lalle Engr yafi karfina haka na fad'a a cikin raina ina mirmishi in akace zan iya sakin ma wani namiji fuskata da zuciyata sai nace karya ne,yadda Ishaq ya karya duk wani kwanjina ashe ban sanu jarumin maza ba ne sai ga shi kwana Daya da yini Daya Engr na neman Sauya rayuwata daga Duhu zuwa Haske,sai ga shi ni mai ijiye waya sai ayi ta kira ban ji ba sai ga shi ina yawo da waya a hannuna Saboda kada Engr ya kirani bana kusa ransa ya baci. A rana ban san adadin sau nawa yake kirana ba,ranar dai har sai da nace masa"Kana kirana kamar kana kiran wata budurwa..? Kai tsaye yace"Budurwa ce mana ni kuma Saurayin ki ba" Ina Dariya nace"A ina na zama Budurwa ya'ya hudu fa suka fito daga jikina" Cikin Shakiyan cinsa yace"Allah..?ni ko kin ga da na ganki ban ga ta inda suka fito ba..?ta ina ne..? Ko sai nazo zaki nuna min.? Ai ranar yini muka yi bamu mgana ba ya kira har ya gaji ban Dauka ta bakin sa Tosin bakinsai ai ba Saiti. Sai dare na dauka muka yi mgana shi bai san ya yi wata mgana ba cikin Hade murya yace"Ni dai bana son wannan Horon Faa'iza. Ko aure muka yi ko laifi nayi miki kada kice zaki Daukemin zaki sakani cikin wani Hali, da kiyi gaba dani ai gwara ki ce Tosin Saka gwiwoyin ka a kasa ki saka Bulala ki zaneni zai fimin kwanciyar Hankali da ki horani da rashin jin muryan ki na yini d'aya" Jin yanayinsa yasa na basa Hakuri nan da nan ko ya saki yace an yafe min ammh next time in na kara to basan kuma wani mataki zai Dauka a kaina ba. Ikon Allah akace sai kallo sai ga shi na saki jiki na da zuciyata na bama Engr duka amanar rayuwata batare da Tunamin komai ba tunda da kwana Biyun da na dibar masa ya cika ya rika Damuna da naci mganar. kwanan sa Biyu a Edo ya koma Abuja ya kirani a waya ya Hadani da mahaifiyarsa da yake kira Sweetheart. Ce mata ya yi ga Faa'iza na son su gaisa cikin kunya muka gaisa yana karban wayar tun kafin nayi mgana yace"Ko ki bani amsata ko kuma wlh mu yi miki gayya har da Papa ga shi nan zaune" Nasan hali fa zai aika sai nace zan fad'ama sa gobe shima bai barni ba sai da na fadi Time nace da Daddare,ai ni nama manta da kowa da komai Tunanina da mafarkina Engr ne ciki da bayana,Ammi daman ta rigani ta fad'ama su Nana Fatima sun kirani Anty Fadila ce ma bamu yi mgana ba,ta kirani ban gani ba sannan nace zan kirata daga baya ni kuma sai na manta tunda na zama bani da wani Tunani sai na Engr. Nana fatima kuma ta nuna min goyon bayanta sosai kan al'amarin,Abba ne dai bai ce min komai ba har ranar ni kuma naga rashin kyautarwa na yanke ma kaina hukunci batare da saninsa ba har ga Allah na Ture ishaq da komai a gefe yaran ma bamu kara mgana da ba,su ni kuma ban kira su ba. Ganin Lokaci na ta tafiya ga Engr bazai bar ni nayi sukuni ba yasa Abba na dawowa naje har falon sa na samesa. Kunya da nauyi suka lullubeni na kasa mgana shi kuma sai ya gane me ya kawo ni cikin mirmishi yace"Fa'iza mganar Engr ne ko..?. Sai na gyad'amai ammh na kasa hada ido da shi nauyi nake ji yaushe nasan Engr..?Sai nake ganin kamar Abba zai ce nayi gaggawa kuma ni dai bansan me yake fizgata ba nasan dai ina adddu'a ammh duka mafarkaina na Engr ne bana ganin kowa sai shi. Kamar Abba ya karanta abunda ke raina ya gyara zama yana kiran sunana sai da na amsa sannan ya cigaba da fadin"Fa'aiza kamar yadda na fad'a a farko yanzu zan kara maimatawa bazan yi miki Dole ba. kamar yadda shari'a ta baki Dama nima na baki. Engr mutumin kirki ne mai Halin Dattako in nace zan fada miki Tarin hallayansa sai kice ina yabonsa ne ammh ni nasan kin fara gani Saboda shi mutum ne Free da kowa ya zauna da shi ko na yini Daya ne sai ya tafi da halinsa masu kyau a baki. Bazan ce ki amince masa domin yana Tare dani ba sai domin zabin ki. Ki natsu kada ki yi gaggawa Fa'iza abunda duk kika yanke ni ina Tare dake har Abada" Sai naji kalaman Abba sun sakamin natsuwa cikin gyada kai na amsa mai Tare da godiya Abba yace"Allah ya sanya alheri Fa'iza.' Na kasa amsawa da Ameen sallama nayi masa na fice ya bini da kallo ko da ban fad'a ba labarin zuciya ai a tambayi fuska yasan Engr ya gama Siye zuciyar Fa'iza da Halinsa shifa Dan baiwa ne yana ma siye zukatam maza ba ma mata ba. Tabbas in Fa'iza ta amince ma Engr sai yafi kowa murna ba saboda komai ba sai saboda Halin nagartansa,ammh kuma yaji matsanancin Tausayin Ishaq ya kamasa ko dazu yana Office ya kirasa sun gaisa suka yi ta Hiran aiki,sannan ya jisa cikin farincikin da har sai da ya tambayesa ko ya samu karin girma ne sai ya yi dariya yace"Abunda na samu yafi karin girma Abba.wani abu ne mai muhimmanci da ya kubcemin har na Fidda rai