← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 175

Sashe 38

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

makaranta da suka maido wuta na fara guga sallar azahar kadai ya tadani sai rigiman Ahmad na shiga Kitchen na Damamai kuni na basa yasha sai ya fara harkan gabansa yana ta wasa da yar motan wasan yara na Mutsy da suka taho da shi Daga Abuja. Hankalina ya tafi kan gugan da nake yi ban ji sallama ba,Kuma ko ma anyi in ba an matso kusa dani ba ne bana jin sallamr sai da naji an tabani na Juyo da Sauri har na Tsorata sai naga Tamadina da abokiyar zamanta Maman Isuhu suke kiranta. Ai basan Lokacin da na watsar da gugan gabana ba na Daka Tsalle na Rumgume Tamadina ina murnar ganinta Cikin yanayin mganarta na Rikeni tana fadin"Faaa...Izzzaa..' Sakin ta nayi na koma ina Dariya ina musu barka da zuwa,Ahmad ne motarsa ta makale jikin kujera sai ya fara kuka,Tamadina tayi Saurin zuwa ta Dauke sa,Ni kuma na kashe Soket din gugan da nake yi jikina na rawa Farinciki kamar ya sumar dani na nufi kitchen na Dauko musu ruwa na kawo musu ina gaishe su. Sun sha ruwan Tamadina kuma wanda ta rage ta bama Ahmad kamar ya ganeta ya ko lafe a jikinta shi da ya ke da kiwuya. Kafin ma na tambayesu daga Ina Mamar Isuhu ta ke shaidamin Matar yaron Uwargidan su ce ta haihu aiki akayi mata tana Asibitin katsina shine suka zo Dubata Tamadina tace su Biyo su yi sallah kafin su tafi. Aiko naji Dadi,Dakina na kai su suka shiga bayi domin alwala ni kuma na fada Kitchen na fara kokarin sama musu abinci Jallop din Shinkafa na Dafa musu da bushasshan kifin da Yaya Asiya ta kawomin ina ta lallabawa Sauran sa kenan nayi takaicin rashin kudi ko Lemu ban da shi ballatana na siya musu kuma bani da kayan had'a Lemu ko daya ballatana na Had'a musu. Har Daki na kai musu na iske sun Idar da Salla,Ahmad na kan jikim Tamadina yana ta wasan sa ta kalleni cikin mganarta tace"Suuuu...Saurrraaan...yarrran fa..? Nace"Suna makaranta Tamadina sai yammah zasu dawo" Ta gyada min kai Allah Sarki Uwa,uwa ce ko da akan bola take kwana,ita fa uwa ta gwammace tayi ma Abun da ta haifa ko da bazai rama mata wannan alherin ba. Gyad'a Soyayyiya da Masara gashashiya ta kawo ma su Amir da gurjiya dafaffiya Maman Isuhu na Dariya tace abakin asibiti ta siya Masaran nan da gurjiya. Ta turamin gabana tace na bama Yara sai hawaye suka kawomin cikin Idona na fara godiya Ahmad dai sai bare mai gurjiya take yi tana bashi yana Mamula da Hakoran sa guda Hudu Biyu a gaba biyu a kasa da suka fitomai. Falo na koma har sai da suka gama cin abimcin,Sannan na koma naga suna shirin tafiya sai naji kamar kar su tafi ammh ba Dama Hijabi na Dauka muka fito ina Tunanin me nake da shi da zan basu..? Na duba gabas da yammah ba ni da komai ballatana na basu haka muka tafi waje da su,ni nace su zo na kai su makota na da muke mutumci su gaisa. Sa'adatu kadai muka samu Habiba bata nan taje gidan su daman yar katsina ce acikin gari. Sa'adatu tana ganin Tamadina tace min"ga maman ku ko..? Na gyada mata kai ta gaishe su cikin Ladabi daga jin yanayin mganar Tamadina basai ta nemi karin bayani ba tasan inda na gado Lalurata kenan. Ita ta fitar dani kunya ta basu siga da yawa cikin wacce take saidawa bani da bakin da zan gode ma Sa'adatun tamin komai shiyasa mata mu daina kuskure domin mazajen mu sun hanamu huld'a da makotanmu sai mu Biye musu mu sani Annabi ma yayi Mgamar Hakkin makota sannan mutane Rahma ne duk yadda mutum yake shiga Jama'a yana da Bambamci da wanda ba ya shiga mutane sosai. Har bakin Titi na rakasu suka samu Motar Dutsemah,Kunya naji da zasu tafi ban basu ko kudi ba Ahmad har da rigiman Tafiyar Tamadina nace Yaro yasan kakarsa. Sai da suka wuce sannan na koma gida Ranar cikin Annushuwa na yini kamar an mun bushara da gidan Aljanmah sai dai ina ta kallon Tamadina ta kara ramewa nima tana ta kallona duk sanda na kalleta sai mun Had'a ido,Ina Kaunar Uwata a yadda take domin bani da makwafinta in kuma na rasata har Abada nayi maraici gaba da baya. Haka kurum in na Tuna da kallon sai naji jikina yayi sanyi a raina nace kodai kallon karshe take yi mim..? Tuna haka yasa sai da gabana ya amsa da Sauri nace a fili"A'a ba haka ba ne Insha Allahu ba yanzu zaki barmu ba Tamadina." Da su Amir suka Dawo na basu tsaraban Tamadina suna ta murna sukace min waya siya musu ina Mirmishi nace"Kakar ku" Sai Anum tace"Mama..? Sai na kallesu nace'A'a mahaifiyata..Sunan ta Tamadina" Anum tace"Umma bamu santa ba meyasa ba ma zuwa wajenta..? Sai na kasa mgana nayi gefe da kaina araina ina auna yadda Ya Ishaq ya Rusamin rayuwata gabad'aya ace ya'yana ma basu san wacce ta Haifeni ba ? sai kirjina ya karayin nauyi da Dubara na share hawayena na Lallab'e su da cewa zan kaisu su ganta Amir dai zai iya ganeta shima ba lalle ba. A fili na furta"Na ga ta kaina ni Fa'iza wannan wata irin rayuwa nake yi haka..? *FA'IZA NA GODIYA TACE KU YI HAKURI KOWANI TSANANI SAUKI NA WAJEN ALLAH TACE MADALLA DA KU MADALLAH DA MASOYAN JANAFTY* *Janafty**KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT 08066726866 Ni MMN MUJAHID Ina da kayn gyara kala kala na kasa da sama Ina Saida supplement da kayan mata kala kala cikin sauki Mai kama da kyauta Hjy ta ki ajiye kunya kifitu kiyi bayani matsala ki abaki ABINDA yaddace Dake Ina matan da ke FAMA da bushewa gaba Ina maccen da take a bushe kamas ba niima miji sai yasa yawun sa ku BASILIN Ina matar da kishiya ta tayi mata zarra ga miji ke rasa Ina matsala take Ina wadda mijinta kamar kurma baya nuna ya gamsu Dake Dan ku ayi ku abari duk dai suke dashi Shin ke ku y'ar kuwa ga mijin ki baya Yi da sanbatu in kinji ana Fadi sai kece karya ce Nazo muku da hadin Zuma wadda duk zata magance way'anga matsalolin cikin ikon Allah wanna Zuma ta samu yabo ga duban mutane Sha yanzu magani yanzu ce Banda haufi akanta wanna Zuma tana ta yadda sha'awa Kai tsaye ruba babba 2500 karama 700 MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT MUNA SAKWATO DA KEBBI INA AIKAWA KU INA 08066726866 IN BAKI SHIRYA BA KIBARI HAR KI TASHI SAYE Tsakanin zuwan Tamadina da saukan su Ya ishaq da amaryan sa Zainab garin katsina kwana biyu ne,Ni bani da labarin suna tafe,Sai da yammah da suka iso gidan nagan su,Ashe wai Mama aka kawo ma Farhan ta gani shine suka zo gayya guda bayan kanwarta zuzu har da wata yarinya mai yi mata reno,sai Iyayanta Guda biyu,ban taba ganin inda iyaye ke rako ya'yansu ganin Dangin miji ba sai akan Amaryan Yaya ishaq na fara gani sai abun bai wani bani mamaki ba ya'yan yan boko ne da suka mallaki dukkan wani kawan duniya. Shashen sa suka yada Zango dukkansu ni dai iyakata nayi D'awaniya da su kamar yadda na saba na abinci da shimfidar fuska wacce Hausawa sukace ta fi na tabarma. Har shashen nasa na shiga suna ciki ita da kanwarta mai renon ne ke falo tana Fama da Farhan Yaya Ishaq kuma suna shigowa ya fice bansan ina zashi ba daga gani dai fitace mai muhimmanci. Hannun mai renon sa na karb'esa ina kallon yaron yayi wani girma kamar dan wata biyar,Tsarki ya tabbata ga Allah nace acikin raina,Saboda ashe a Hoto ban ga komai na kyau da zatin yaron ba sai da na gansa a hannuna Jajir da shi kamar ka taba jininsa ya fito yafi kama da Yaya Ishaq sai dai Hancinsa irin na mamansa ne har da Idanuwan ma kuka yake ta yi yarinyar ta kasa lallashinsa na kalleta Lokaci daya ina fadin"me yasa ya ke kuka..? Kamar zatayi kuka tace"Ni ma ban sani ba kuma ba yunwa yake ji ba yanzu na basa madaran sa" Rikesa nayi a jikina ina kara Tattaba jikinsa naji zafi kad'an alamun yana Tare da zazzabi sai na kalleta lokaci daya ina fadin"Kamar da zazzabi a jikinsa bari nayi mai wanka sai a bashi mgani" Kamar zatayi mgana sai kuma ta fasa ni kuma na fice da shi zuciya ta daya,Daman su Amir na makaranta basu dawo ba,kitchen na shiga na saka Ruwan zafi bayan na goyasa luf kuwa yayi shuru ruwan na zafi na juye a baho na shiga Dakina nayi mai wanka tas da ruwa masu dimi ina cikin yi mai wankan na fahimci Cibiyarsa ne ta dan kumbura ina da wani mgani da Goggo ta bani Tun Ahmad na karami da cibiyarsa ta fara kumbura ina fara shafamai ta koma ta daina ciwo kuma ta Daina kumburin,sai na Dauko daman ban cika banzarta da irin wadanan kayan ba tunda ina da yara na mulke mai Cibiyar da shi cikin kayan Ahmad da suka yi mai kad'an na saka mai riga da wando,na goyasa ram a bayana ba jimawa sai barci ya kwashe sa da shi a bayana na cigaba da Hidima ta Ahmad daman yayi barci ne yana tashi ya kafa rigiman sai na Sauke Farhan dake bayana na goyasa. Ina Dariya shima na Sunkucesa na Saba a kafad'ana ina fadin"Haba babban mutum ka girma ka bar ma kaninka bambon mana" Kuka ya fara min na fita da shi Falo na Zubomai abinci na zauna ina basa Shidda Saura sai ga yaran sun Dawo daga makaranta suna ganin goyo a baya suka fara tambayana Umma wa kika goya kamar ma Anum taji Labari. Ina mirmishi nace"Sabon jaririn Anty ne" Anum ta daka tsalle tana lekonsa ta bayana kafin tace"Umma waya zo da shi..? Sai nace"Tare da Daadan ku suka zo da Antyn ku" Anum ta fara tsalle tana oyoyo oyoyo Daada Musty na tayata Amir dai Dakin su ya shige ya Sauya kaya gudu ta kwaasa zuwa shashen baban nasu nace mata ya fita ta bari ta sauya kaya taci abinci in suka yi sallah sai ta
Chapter 38 · 0% Book details