← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 175

Sashe 73

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da Hakki akansa wajen wata daya da rabi bai je ya ganta ba,wannan ai sai mahaifinta ya yi fushi da shi Tsakani ga Allah wannan bawan Allah babu abunda bai yi mana ba ammh nasara uban me ishaq ke yi acikin gidan nan da bai tafi ba" Mamaki ya kasheni wato Zainab ce matar so ni sanda yake tafiya sai yaga Dama yazo ai bata taba cewa ina da Hakki akansa ba takaici yasa nayi mirmishi mganar ma ta gundureni sai ya kashe zaman nawa da cewa"Je ki abun ki Fa'iza" Mikewa nayi na fice a raina ina fadin daman ya koma chan wajen zainab din domin da zamansa da akasinsa duk daya ne a wajen fa'iza ba abunda suke Tunani ba ne. Bansan ya suka kare ba ammh sun kai ruwa rana domin ina jin tashin muryoyin su shi da Anty Binta ina Dakina bansan tafiyar ta ba,mama bata so ta gansa yana zaune agida gani take yi kamar wani abu yake min ko zamansa wani Dadi yake yi min,Abunda bata sani ba ni mantawa nake yi ma yana gidan tun safe in yara suka tafi makaranta zan kama sana'ata Amir na tayani in Hafsah bata gidan ita a tunaninta na tsare shi a Dakina ne yana bani wani abu tunda ta Furtamin da na shiga gaisheta washegari ta kalleni sama da kasa kafin tace"Ki sakar min d'a Fa"iza na rasa me kike son ya baki bayan wanda ya baki a baya ke ko gajiya da nanikan namiji bakya yi ciki ko goyo ne baki gaji da yin sa ba ko me..? Mganarta sai ta bani Dariya sai da na Murmusa kai tsaye nace mata"Ko d'aya Mama haihuwa ai Fa'iza ta gama shi in dai a nan gidan ne na bar ma Zainab ita ya dace ta cigaba da tara miki Jokoki" Tasan mgana na gayamata ammh sai bata kara mgana ba,ai kunyan marasa kunya a sara sannan tsohon da bai ji kunyar hawa jaki ba shima jakin bazai nauyin yarfa sa da kasa ba. Hajiyar su Raliya bata san mun sauya gida ba,taje camoron kanwarta zata aurar da Diya su Raliya kuma sun je lagos hutu gidan Yayan mahaifin su,suna dawowa suka hadu a makaranta Badariya ta fadamata ranar tare suka suka zo,a shashena suka zauna tare da Hafsah,suka ci abinci suna Hira Raliya tace Hajiya bata sani ba ammh zata dawo kwanan nan zata gayamata. Mama taji Haushin shigar su Dakina da Raliya ta shiga mata sallama har da ni sai harara ta takeyi har tana fadin''Haka ake yi sai ki shigar da yarinyar daki ai ba wajen ki tazo ba sai ki bar ta da Badariya kawar tata" Daganan na Fahimci Kishi Tsagwararon shu Mama ke yi da ni a baya don bamu zauna waje d'aya ba ne yanzu kuma Abun nata na fitowa ,Cigaba na ne bata so tafi kaunar ganin na wulakanta ko na Tozarta to ai ba ita ke da Rayuwata ba,in ita tana nata ne shi Allah kankat ne ya riga ya gama nasa tsarin mutum bai isa ya hana faruwar kaddara da ya Riga ya zana ba. Ba'a rufe sati ba sai ga Hajiya Tazo Raliya ta rakota tayi ta min fadan meyasan ban kirata ba ni dai hakuri na bata,Tana ta kallon gidan cikin wani yanayi,da zata tafi ta bani Dubu Hamsi sannan taji dadin yadda sana'ata bai tsaya ba tace na cigaba da yi in sha Allahu watarana sai na bama kaina mamaki sai da zata tafi ta shiga Dakin Mama suka gaisa,Ta bata dubu goma mama nata godiya. Har waje na rakata tace min Direba zai kawo min sako ba yawa,Sannan tace akwai Bikin diyar kawarta da zasu yi a kaduna tana tunanin kwangilan Hada turaruka ni zatace a bamawa sannan tana tunanin Amaryan zata zo gidan sai nayi mata gyaran jiki ina ta Murna daman ta wannan bangaran ita kan kawo min Costumer,sau daya na hada Turaren Rushi da na Humra da muka dawo gidan nan shima na riga na karbi kudin aikin su ne tuni yana hannuna. Da Daddare naje kai ma Mama abinci sai da tambayeni a wulakance wai a ina nasan Hajiyar Raliya..? Kai tsaye nace mata"Su ne shugabannin kungiyar da suka bamu tallafi bayan sun koya mana sana'o'in hannu domin Dogara da kanmu" Sai ta tabe baki kafin tace"Ina ce sanadin Badariya kika santa? Sai na daga mata kai sai kawai tayi tsaki kafin tace"Aikin mur in ji tusa." Ban tanka ta na fice washegari sai ga Direba da kayan abinci shake da Mota Ishaq na gida Lokacin nayi mai bayani sai kawai ya kalleni yana fadin"ina fatan ba rokon ta kika yi ba ko..? Sai abun ya bani haushi na wuce sa na shige daki ina fadin"To ba dole fa a fada masa ya juya da kayan kawai" Daganan ko kara bi ta kansu ban yi ba, sai naga ana shigowa da kayan a raina nace abun ma iskanci ne sai da na natsa na kirata nayi mata godiya tace bakomai indai ina bukatar wani abu na kirata kamar uwa take gareni nace mata in sha Allahu. Muna da wattani biyu da kwanaki a sabon gidan da muke ciki,Yaya Ishaq ya tafi Abuja ranar wata asabar shima din Mahaifin zainab ya kira sa akan yazo yana nemansa ba shi ko da kudin Mota Mama ta kira Anty Binta ta bashi ya kama hanya sai da ya bar gidan nan Hankalin Mama ya kwanta. Kamar yau ya tafi washegari Goggo tazo ganin wajen da muka koma Yaya Isa ya kawota,shima Hafsah ya kira tayi mai kwatance Dakin Mama ta fara shiga suka gaisa anan Mama wai ke Tambayan Goggo ina Hajiyar Dala..? Goggo tace"Baki sani ba ta tafi raka mijinta kasar awaje a duba lafiyrsa" Sai Mama ta kasa mgana tunda da Yaya ishaq ya fito daga hannun jam'an tsaro Mama bata kara jinta ba tun tana kiranta ta na bata uzuri har dai ta daina samunta goggo mamaki ya cika ta daman ana jin kan Saudatu da Fatima ne..? Da mamakin ta baro dakinta zuwa shashena ta iskemu muna ta Dura zobo a gorina,Goggo na zolayata fad'i take yi"A'a kaga Hajiya fa'i mai zobo da kunin Aya" Amir da Hafsah suka kwashe da Dariya Yaya isa na gefe yana taya su, shi sauran na jiya da yammah mai sanyi nace Hafsat ta kawo masa yana sha yana fadin"Goggo gaskiya Fa'iza ta iya hada zobo sosai yake da dad'i" Goggo ta kalleni kafin tace"Ke fa'i taso ki saka ma yayan ki waigi ya fara santi" Gabadayanmu muka fashe da Dariyan mganarta, shima Dariyan yake yi yana gyad'a kai kamar wani kadangare. *INGANTACCEN ZANCE*. *Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*. *Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin* *Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.* *Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*. *SAIWOWIN itatuwane da basu da illah* *Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.* *Kawai ki tuntu'bi Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani* *08032773332.*
Chapter 73 · 0% Book details