← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 175

Sashe 40

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hearing sai ka daga murya" Ido ya ware kafin yace"is that serous.."? Kai ta gyada mai sai naga ya daga glass din sa sama yana kare min kallo araina sai naji girmamsa ya zube ai shi Babba ne kuma namiji irin kallon kurillah dayake bina da shi bai Dace ba. Su Amir kuwa da suka gaishesa ya amsa yana fadin"Bakaken ya'yan Ishaq kuna lafiya..? Naji abunda yace sai naji ban ji dadi ba saboda su yara ne abu kad'an za'a fada su dauka wani abu ne Jikansa ya amsa yana ta mai wasa Anum nata son ya bata ta Dauka yace"No..No..baza ki iya ba kada ki kada shi..Kinga farin yaron da babu a gidan ko..? Duka har su Mama suna falon Ammh ba wanda ya damu da mganarsa sai ma Dariya da Mama tayi tana fadin"Wlh kuwa Alhaji uwar ai sai dai in ta Haihu su dauko bakin Fatarta" Hajiya Halima ce duk bataji dadin Mganganun ba sai ta juya tana yi ma Zainab mgana,ni dai ina zaune kamar wata yar aikin cikin su na kosa mu koma gida,aiko sai wajen goma muka koma gida,Da safe ina yi ma su Amir shirin makaranta Amir ya kalleni yana fadin"Umma menene baki..? Gabana ya fadi na kallesa na kasa mgana ya kara cewa"Umma baki ba abu ba ne mai kyau..? Da Sauri nace"Da baki da fari duk abu ne mai kyau Amir kaji ko..? Ban kara basa damar mganar ba saboda bansan me zan ce mai a gaba ba,Bana so ya'yana su fuskanci abunda na Fuskanta tsawon shekaru Ashe basu tsira ba Dole dai sai an goranta ma ya'yana kwanansu shida Zainab din tagayamin washegari zasu koma saboda ayyukansu sun zo sun gaishemu tunda naki zuwa nace mata zan zo in sha Allahu. Zainab ba ruwanta macece Faram Faram ko ta na da wani abu aranta bata taba nuna min ba Kanwarta ne mai D'agawa da isa harta su Amir basa Rabanta,Har Anum da take da Son Jama'a basa zuwa kusa da ita ta cika Fad'a da isa da fadin rai. Ni ban isa na hana su Amir shiga bangaran Mahaifin su ba,Suna son Daukan Kaninsu ni kums ban isa na Hanasu ba ai dan'uwansu ne ni bansan ab unda ya faru ba da yammah bayan sun dawo daga makaranta Kayan su kadai suka cire ko abinci basu tsaya ba suka tafi chan wajen Farhan har da Amir da bai cika shiga ba in dai ba Tare da Babansu ba. Ina kitchen ina Zuba musu abimci Amir ya shigo har da hawaye a gefen Idanuwansa na kallesa ina Fadin"Babana wa ya tabamin kai..? Bai min mgana ba ya fita nima na Dauki abinci zuwa Falo na ijiye Saman Cafet din dake Falon na isa ga Amir daya zauna yayi Tagumi. Na cire hannun Tagumi ina Fadin"Uhm..gayamin wa ya tabamin kai..?ko Anum ce ta tsokane ka..? Cikin ido ya kalleni yace"Umma kin ce baki abu ne mai kyau..Ammh yar'uwan Anty tace min ni baki ne kada na Shafa ma Farhan baki na" A rarrabe ya fadi mganar kuka yaci karfinsa Amir na da zuciya shiyasa bai cika Hayaniya ba. Jawosa jikina nayi na Rumgume ina Fadin"Ya isa..Shiii..Ya isa" Na dagosa na Share mai Hawaye ina Fadin"Kada ka damu da mganarta Da fari da baki duka Hallitan Ubangiji ne sannan Duka d'aya suke a wajensa.." Zai kara mgana na girgiza kai ina Fadin"Ya isa zauna ka ci abinci" Bai yi musu ba ya zauna sai dai sai ajiyar zuciya yake saukewa Raina sai naji ya baci taya zasu rika Gurbatamin Tunanin yarana Amir dan Shekaru tara da wani abu suna neman sakamai Tunanin banza. Ina cikin Tunanin naji yace"Umma su Anum suna wajen Anty" Kai na gyada mai ina fadin"Bari naje na taho da su" Kai Tsaye bangaran nashi na shiga Zainab din bata falo sai kanwar nata,Sai yarinyar dake kula da farhan Tana rike da shi ita kuma Zuzu tana danna wayarta Anum da Musty suna ta wasan su ya'yan Anty ne su. Ina shigowa kai tsaye ita na Nufa ina Fadin"Me kika fad'ama Amir..? Da yanayin mganata ta Dago tana kallon kafin tace"Ni..? Lokaci daya tana nuna kanta tana wani tabe baki ban damu ba nace"Baki Tunanin shi yaro ne..?in bazaki bari ya Daukesa ba,sai ki hanasa ba wai ki gayamsa mganar da Hankalinsa bazai iya Dauka ba.." Ta kuramin ido tana kallona ban damu ba na cigaba da fadin"Kada ki kara gayama yara na abunda zai Dame su bana so..Ke bakuwace ki gama bakuntarki ki tafi bana so ki shiga Tsarin Tarbiyan yara na" Har na juya na juyo ina kallonta Lokaci da'ya ina Fadin"Sannan in baki sani ba ki sani da Bakin da Farin duka Hallitun Ubangiji ne sannan d'aya suke a wajensa Launin fata bazai taba zama wariya ga musulmin kwarai ba" Daga haka na juya na kama Hannun Anum Da Musty muka fice ina kallo Har Zainab din ta fito daga cikin Dakin ta tsaya tana kallona ni kuma ko kallonta ma ban yi ba. Haka kurum naji ni zan iya Daukan kowani cin zarafi ammh bazan aminta arika cin zarafin yarana ba a bata musu Tunanin su ba Shiyasa naja mata kunne tun da wuri. Ni ban san ashe wannan mganar tajawo min bala'i ba sai da Daddare sai ga Mama da mahaifan Zainab din Har da Anty Binta sun zo gidan,Ya Ishaq da bai yini a gida ba shima ya Dawo Kirana kawai yazo yayi da kansa Fuskar nan tasa a hade kamar Hadari Allah ya taimake ni yaran sun kwanta da wuri da a gabansu za"a cimin zarafi. Ima fitowa tun da naga mama da Anty Binta na sadakar wannan taron nawa ne sai kanwar Zainab da ke jikin Mahaifinsu tana ta sharban kuka Fuskar kowa ba fara'a na samu gefe na zauna ina gaida su Mama ko amsani batayi ba ta fara dakamin Tsawa tana fadin"Rike gaisuwarki mara Mutumci me wannan yarinyar tayi miki kika zageta kika ci mata Mutumci..? Sai da ta fad'a na Dago ina kallon Zuzu din har tana wani matse kwalla da majina sai alokacin na Fahimci komai ban ji nayi nadama ba cikin yanayin mganata nace"ni ban zageta ko naci mata mutumci ba..nayi mata fad'a ne" Anty Binta tayi zaraf tana fadin"Fada..?Sannu uwarta yarki ce da zaki tasata kina mata fada ishasshiya.? Hajiya Halima ce tace"a bi a sannu Hajiya" Mama tace"Hajiya ai bata da mutumci ne..Daman bata so auran Ishaq da Zainab ba,kuma tun tuni take neman daman cin mana mutumci bata samu ba sai yau" Ni dai sai na kasa mgana Yaya Ishaq ya kalleni ya watsamin Harara yana Fadin"Daga kawai ta hana Amir Daukan Farhan Saboda bazai iya Daukansa ba sai ki bita har Daki ki zageta ki zagi iyayanta sannan har kina ikirarin cewa gidanki ne uban wa ya ce miki nan gidan ki ne..? Ko da sunan ki na siya gidan ban sani ba..? Kaina na kasa na kasa mgana ina jin wannan cin mutimcin Mama tayi kafyci tana fadin"Ahto tambaye ta dai" Sai kawai na samu bakina da Fadin"Ku yi hakuri ba.." Muryan Dr.Lawal ta katseni a Fusace yana fadin"Sorry for ur self..Akan ya'yana zan iya shari'a da koma waye..Daga tazo gidanki sai ki ci mata Mutumci..?ke ba domin Ishaq ba kin isa ki ga Zuzu a inda kike..?ai kalan zaren ba kalan yadin ba ne..Ba domin ina jin kunyar shi da iyayansa ba da sai kin gayama aya zakinta akan kukan da kika sa yata tayi kin san wacece ita..?ko ni bana sakata kuka Koda yaushe ina Tattalin Dariyan ya'yana ne ba Zuzu ba ko Zeey da kuka Hada miji kika kara yarda kallon Banza ma ya had'aku sai nayi maganinki sai na saka an batar dake da Dangin ki gabad'aya" Yafad'a cikin Kaushin murya Hajiya Halima kunya ya kamata ta kasa mgana ta Dafe kai Zainab ce tace"Is ok Daddy. " A fusace yace"No zeey kinsan ba na Had'a ku da komai a nan duniyan ko..? Ko mommy ku ta sa ku kuka ina jin Dalili ballatana wata shara chan" Hawaye suka wankemin Fuska ni ce shara..?ina jin Zainab din na fadin"I know Daddy..Forgive her bata sani ba ne zuzu plz ki bar kuka kada kanki ya fara ciwo..Gobe zamu koma Abuja is ok kin ji..? Kai ta d'aga mata ta koma ta lafe jikin Baban nasu yana share mata hawaye yana fadin"Am sorry Angel..am sorry" Mama tayi kayci kafin tace"Ai daka Dauki matakin da kayi niyya Alhaji da sai tafi gane matsayinta" Hajiya Halima tace"Hajiya komai ya wuce insha Allahu" Ni ko ina zaune jikina ya gama mutuwa hawaye suna zubomin na saka gefen Hijabina na share Yaya Ishaq yace"Ki dago ki bata Hakuri tunda ita kika yi ma laifi" Na kasa Dagowa sai ya dakamin Tsawa haka na Dago fuskata Shabe Shabe da Hawaye cikin yanayin mganata nace"Ki..yi..hakuri.." Juyawa yayi yana fadin"Ta baki hakuri am sorry Zuzu.." Kai ta gyada ta na kara kwanciya jikin Baban nata,Mama ta kalleni tana fadin"Sai ki tafi ki bamu waje mara mutumci" Na tashi da Sauri na shige Daki na,na fada kan gado ina sakin kuka na bansan Lokacin da suka tafi ba sannan ni kaina bansan adadin Lokacin da na Dauka ina kuka ba kaina ya fara ciwo,ko sallar daren da na Saba a daddafe nayi saboda Jiri naji yana Dibana da Safe dakyar na iya tashi na shirya yara suka tafi makaranta kuma ahakan nayi musu abun karyawa na bar musu a kitchen na koma Dakina nasha panadol na kwanta ina jin kamar zazzabi zai kamani. Ban san tafiyar su ba Domin Wanda ya ijiyeni bai min sallama ba Ballatana Dangin da sukace zasu batar dani,ni da Dangina Saboda an saka yar gata kuka,fitowa kawai nayi naga gidan wayam,sannan na Fahimci Daga ni sai halina acikin gida Zuwa yammah jikina ya Rikice jiri da Ciwon kai nasan jinina ne ya hau Allah gafurin Rahimun a ranar sai ga Hafsaatu ta zo Allah ya aiko ta Domin ta taimakeni ta iskeni kwance ba Lafiya ita ta taimakamin tayi ma yara Girki ta kula da su. Ina da Sauran mganina na Hawan jini shi na sha bayan naci abinci,Gari na wayewa kamar waraka daga Allah sai naji Sauki,Naji dadin zuwan Hafsatu Goggo ta aiko ta ta dubami tazomin da su Kuka,kubewa,tsaki,garin kunu da
Chapter 40 · 0% Book details