← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 175

Sashe 89

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mun iske har su Anty Mahma,suna gida sun yi mamakin ganin mu dukkanmu a tare sannan cikin shiga mai kyau Anty Binta haka take ta kallona kamar idonta zai fad'o ina gaisheta ta amsa min cikin wani yanayi.Anty mahma ko ihu ta Buga tana fadin"ku zo ku sha kallo wajen Hajiyar Zobo da kunin Aya" Badariya na gidan tace"Kin manta harda Turaran humra da kwallacha" Dariya suka bani Zainab tace"Maman Amir yadda kika san bata haifi Amir ba" Anty mahma tace"Fa'iza nada jiki mai kyau gaskiya" Mun dade agidan kafin mu yi sallama Anty Binta dai sai kallo na take har muka tafi, sun yi mgana da zainab tace yaushe tazo tace shekaran jiya Daga gidanta Badariya ta biyomu muka taho tare da ita,jin nace har gidan hajiya zani mata yawan sallah. Ba gidan Hajiya mukaje ba da muka fita ba,sai da muka fara zuwa anguwan da muka tashi. Allah sarki gidanmu an buge sa ya zama sai Filin gwamnati Sa'adatu da Habiba sun yi murnan ganin mu sosai,na kullo musu nama da lemu da Zainab ta zo mana da shi, duk wanda yayi maka mutumci kada ka manta da shi, gidan Hajiya sai yammah muka je bata gidan sai su Raliya da yayyinta da suka zo sallah, ammh sun kirata a waya nan muka yi sallar mangariba muka ci abinci sai gata ta Dawo tana shigowa su Anum suka nufeta suna oyoyo Hajiya ta tarbesu tana fadin"Oyoyo Ya'yan Hajiya" Zama tayi muka gaisa Zainab ta gaisheta ta amsa sai na gabatar mata da ita sai ta kalleta tana fadin"Maraba da Fa'iza da Zainab naji dadin wannan ziyaran Allah ya hada kawunan ku" muka amsa da Ameen ta karbi Fadil tana fadin"Wannan ne kama da yan sudan di'n fa..? Ina dariya nace"Kanin Farhan ne" Tana dagasa sama tace"Naga kaman su da Amadin ki". Hajiya ba ruwanta tana da sakewa muna ta Hira da ita tun zainab bata saki jiki ba har ta saki yaran kuma tuni su Raliya sun jasa su cikin gida,duk yadda muka so mu tafi kafin isha'i sai da ta hanamu shi ko Babansu sai kira yake yi Zainab nace mai muna Hanya sai da muka yi sallar isha'i muka yi shirin tafiya ta bamu kyautan atamfofi super guda biyu,yaran kuma kudi sabbin yan Hamsin kowannen Bandir d'aya Badariya kuma tace ta dawo ta karb'i nata Sakon har haraban gidan ta rakomu ita da ya'yanta da sai tambayan Hajiya suke itace Fa'iza me Turare da dilka..?.Sai Hajiya tace itane sai kiga wad'anda basu sanni ba suna gaisheni cikin girmamawaa. Sai da muka kamo hanyar gida sannan Zainab tace min"Yar'uwan ku ce Hajiyar nan..? Na girgiza kaina ina fadin"Aa sune shugabannin wata kungiyar taimakon mata da marayu,wad'anda suka koya mana wannan sana'ar da nake yi. sanadin haduwar mu kenan sannan Raliya diyarta kawar Badar ce" Sai ta rausayar da kai tana fadin"Tana da kirki sosai" Na jinjina kai ina ba'a mgana,hirar ta muka rika yi har muka isa gida,Badar na fad'in irin kudin su ya'yan Hajiya manya maza duk ma'aikan gwamnati ne,matan ma suna auran manyan manya a garin katsina,itama aiki take sannan suna da manyan kungiyoyin mata na taimakon mutane" Ko da muka koma Gogan ya cika saura Kiris ya fashe sai hararan mu yake yi,Zainab tace"Honey mun dawo" Yana kwance kan kujera yace"Na ganku,sannan ku da zuwa sai a tube a sama min abunda zan ci" Ina kwantar da Fadil da yayi barci akan kujera nace"Yunwa kake ji.?ina abincin da na bar maka a kula..?. Yana daga kwancen yace"Ban yi ra'ayin ci ba,sabo nake so" Ni da zainab muka kalli juna sai ta zauna wajen kafafunsa tana fadin"Maman Amir barayin ki ne wannan, ni bari naji da lallashi" Ban damu ba,na shige dakina na sauke mayafina da kayan hannuna na shige kitchen. yaran kuma suna ta murna da Budirin kudin da aka basu suna nuna mai ya karb'a yana fadin"Tunda kun zama masu kudi kowa sai ya bani goron sallah" Suka fara Dariya yana taya su bansan ya suka kare da Amaryansa ba, ni dai Shinkafa na sake dafamai sai nayi mai miyar albasa da naman kaza na kawo mai da maltina na iske suna hira da matarsa sai na shige daki nayi wanka na Sauya kaya na gaji ga barci yaran ma da kansu nace suyi shirin kwanciya,Fadil kawai na karb'a mukaje muka kwanta Farhan tare da su Amir zai kwana Anum kuma sai ta gama iyayinta zata shigo ta kwanta. Mun so washegari mu je karofi ya hana,Sai da aka kara kwana sannan muka tafi gabadaya har da shi da Badariya da Jamal,sai dai su Goggo suka ganmu kamar daga sama mamaki da murna ya hana Goggo sakat sai fad'i take"maraba da bakin alheri. ni kadai da zaratan masu gida haka,Allah yasa kun zo da cefanen ku" Amir ya zaro mata kudi yana fadin"Nawa kike bukata Tsohuwa..?. Ta ko warce kudin tana fadin"Duka nake so" Sai ya fara fadin'Ke ko goggo baki san wasa ba" Gabadayanmu sai da muka yi Dariya Yaya Ishaq dai duk yaji kunya,Kansa na kasa yana gaida Goggo ita ko a Fuska bata nuna masa wani abu ba,Su Anty nasara duk suna gida aka gaisa sai fa alokacin wasu suka san Zainab da su Farhan,mune har gidan su Yaya Isa achan muka sallar la'asar daganan muka isa gidan Yaya mariya tayi mamakin ganin mu sai kallo na take yi cikin gatse tace min"To su Fa'iza dai akwai ki da son a sani yawo da kishiya" Allah yasa zainab ta shiga ciki tayi waya,da Yaya mariya tamin baramb'arama a gabanta,ban bata amsa ba ta kara kallona tana fadin"Naga kin yi wani d'anye ne ko dai ciki kika kunso ne..? Dariya na kwashe dashi ina fadin"Ciki? ai mun bar ma masu mazaje a hannu" Dariya ta yi lokaci d'aya ta daki kafad'ata tana fadin"Oh Allah! ji yadda Fa'iza ta koma shekaru biyar bqya, wazai ce Fa'izan nan ce mai shuru shuru da an yi mgana ta hau kuka tana kuyi hakuri" Tafad'a tana kwaikwayon mganata ni dai ina ta Dariya Hafsah na gidan daga barci ma ta taso na kalleta ina fadin"Sannu yar hutu gidan Goggon kenan..?tana sosa ido tace"Yau fa nazo chan hayaniyar yara" Yaya mariya tace"To ai ga hayaniyar nan Fa'iza ta tattaro miki har da gayyar sod'i ba katin gayyata" Sigina na rika yi ma Yaya mariya ammh ta nuna kamar bata gane ba,Allah ya taimakeni da Zainab din ta fito sai ta gyara bakinta sai dai Taki sakin jiki da ita sai ma had'e rai da tayi shiyasa bamu dade ba muka tafi sai ko ta rakomu har gidan Goggo nan suka had'e Da Yaya Ishaq akayi kallon kallo ta Dauke kai abun mamaki ammh shi sai yace"Mariya ba gaisuwa..?to ni bari na gaisheki tunda ta wani fanni ni kaninki ne an yi salla lafiya ne Ba ita ba har su Goggo sai da suka yi mamaki sai dai ba wanda ya nuna hakan,Yaya mariya ko da lafiya ta amsa mai kafin ta Dauke kai, daman taji labarin sa a wajen Hafsah kafin ta tafi sai da tajani gefe tana fadin"Ke naga wannan wawan mijin naki na wani rawan kafa akanki saboda yaga yanzu ba shi da komai, kina sana'a kina yi mai wahala to in kika sakar masa ke kika sani,kada dai ki manta da abubuwan da suka faru a baya wlh kada naji kin sakarmai ki bari sai ya samu aiki yi in har chanjin na gaske ne sai ki gani" Ban ja da nisa ba nace mata toh kawai nasan halinta yanzu ina ta wata mgana sai ajimu daga waje, Kafin mangariba muka tafi,da Tsaraban su gyada da aya,Sannan na taho da ayan na da ganyen zobon da Goggo tace na bada kudi ayo min Sautin su a kauye anfi samun sauki,To shine na ba ma Hafsah da zata zo ta zo mata da kudin, shine na dauko kayana ita dai Hafsah tace sai ta kara kwana biyu zata dawo. Tunda muka dawo bamu sake fita ba muna gida muna warware gajiya,Zainab sati daya tayi ta koma Abuja ni kaina sai da naji kewa ballatana yara da suka saba da kannensu,shi ko Yaya ishaq ranar da ta tafi har ce min yayi yaji dadin tafiyarta kila na sauraresa yanzu kai namiji sai a barsa, nan yake shigewa daki da ita fa yana amfana ammh baazai yarda ba sai ya yi dadin baki. An gama Hutun salla yara sun koma makaranta Mama dai taji dadin yamai bata dawo ba,Hafsat ta dawo saboda makaranta,Badariya kuma na gidan Anty Binta tsakani da sallah ba Dadewa suka yi graduation na gama makaranta,Raliya har walima Hajiya ta shirya mata agida,an yi waliman ko sati ba'ayi ba Hajiya ta aiko min da Kayan saka ranan Raliya,nayi murna sosai Badariya itama tazo tana fadamin har da na Halisa itama an saka,yar wajen Anty Binta zatayi aure a kano dan'uwan mijin Hajiyar Dala ne,ita kuma Raliya chan wajen bikin Laila suka hadu da shi,Yaron yayar wanda Laila ta aura ne. Bansan me ya faru ba sai gani kawai nayi Badariya ta had'o kayanta tazo ta Bude dakin Mama ta share ta dawo,kamar bazan mata mgana ba sai naga tana cikin damuwa ranar bayan fitan yara makaranta na bita har Dakin sai na isketa tana kuka. Na tsorata na zauna gefenta ina tambayanta me akayi mata take kuka..? Sai ta mike zaune tana cemim"Don Allah Anty Fa'iza aure na waye..? Kai tsaye nace"Aure na Allah ne Badar me ya faru ne..? Sai ta sakamin kuka tana fadin"ba na fada miki an saka ranar auran Halisa ba? Na daga mata kai sai ta cigaba da fadin"Shine shine fa tunda ta samu ssurayin nan take min gani gani har Anty Binta tana gani Halisa na min wulakanci don ina zaune a gidan su,Gori kala kala take min wai bani da Tsayayyen saurayi sai shirme shine fa a Shekaranjiya Salisun da zata aura yazo daman ya sanni don yace ta kirani mu gaisa muna gaisawa muna hira sai zuwa tayi ta cemin wai don Allah na fita tana so ta gana da saurayinta nayi kane kane kamar ina so nayi mata sinacin" Ta karishe fada cikin kuka cikin wani yanayi nace"Miye sinacin? Kai tsaye tace"Wai zan kwace mata shi Haba Anty Fa'iza ko Hali na ne ai
Chapter 89 · 0% Book details