← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 175

Sashe 112

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani abikin aikin su.Mr James mutumin osun State ne Daga office din sa sai na Ishaq,da shi aka had'a baki aka kwaikwayi saka hannu Ishaq Daga office dinsa aka fitar da wad'anan kudaden,yanzu Mr james din ya tafi gida chan Osun,abu d'aya ya rage bangaran Cibiyar Bincike ta EFCC ita zata ba da umarnin a kamo James ya fad'i gaskiya sannan ta wanke shi Daga zargi. Da murna ya fito yana fad'a mana,ni da Mama da muke tsakar gida ita tana shan iska ni kuma ina Dafa zobo,sai na manta da abunda ke tsakanina da shi na mike ina fadin"Alhandulillah. Ka kira Abba kira Abba ka fadamasa" Mama ko sai da tayi sujuda tana godema Allah sai kuka shi ko Jiki na rawa yace"Shima Daddyn haka yace na kira Abba..yayi ta kiransa bai same sa ba' Kiransa yayi sau biyu bai Dauka ba nima na Ruga daki na Dauko wayata na kirasa bai Dauka ba. Sai na Kira Ammi bayan mun gaisa na tambayi Abba tace ya tafi Office ina fad'ama Ishaq yace"kila ya shiga meeting ne. mu basa Lokaci" Anum na gefe tace"Daada me ya faru..? Cikin farinciki ya dagata sama yana Fadin"An gano gaskiya Anum.angano bani da hannu a satar kudin ma'aikanmu"Sai itama ta washe baki tana fadin"Congratulation Daada" Sai da yagama juyi da ita sannan ya sauketa yana kallona Lokaci da'ya yana Fadin"Fa'iza kinga abun Allah ko..? Sai na jinjina kai ina fadin"Allah yasa karshen wahalan kenan"Mama ta amsa da ameen ta mike tana fadin bari ta kira Binta Yaya ishaq ya hanata da fadin"ki bari mu yi mgana da Abba tukunnah" Da sauri nace"Eh Mama gwara labarin ya kamallah Tukunnah"Sai ta gyada kai yini mukayi Duba waya ko Abba zai kira sai Dare ya kira Yaya Ishaq,kafin shi yayi masa mganar ya fara yi masa. yace sun yi mgana da Dr.Lawal yanzu nan ya kira Engr sun yi mgana shima ya ce Mr ABDULGHAFFAR ABDULBASIT BABATUNDE ya dawo Office satin daya gabata,zuwa gobe ko jibi ya sauraresa" Nima Abban ya kirani yayi min bayanin komai ya karishe da fadin"Last friday ai muna Abuja da ni da Maman Nana mun je duba Hajiya Kudirat olamide,itace kakar Engr sun dawo gida bayan an yi mata Dashen koda,da mukaje mun samu Engr din a gida sai na kara tunasar da shi mganar aiko yana masa mganar yace a tuna masa in ya shiga office sai fara Duba Case din,balle da Engr ya fad'a masa Ishaq Inlow ne a waje na,ya tabbatar min da ba matsala mu jira cewarsa kawai" Da wannan labarin mai Dad'i muka kwana sai dai na Tsananta addu'a na Allah ya kawo mafita da karshen al'amarin. Har yara na saka suka yi ta addu'an Allah ya kawo ma Daada mafita shima nace yayi ta addu'a da ikon Allah sai an wanke sa daga wannan zargin. *Janafty* [7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2019* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Allah maji rokon bayinsa kwana Biyu Tsakani. ranar Litini da misalin wajen sha biyu na rana ya samu wayar Abba in da yace maza ya taho kano yanzu zai had'u da Abdul'Ahad a Airport din Aminu kano zasu hawo jirgi zuwa nan Abuja. A na nemansa a Office din Chairman na EFCC,daganan bai yi mai wani karin bayani ba. shiyasa sai ya Rude,ya fito daga daki yana fad'amin cikin wani yanayi kafin ya kara da cewa"Gaba na ta fad'i Fa'iza. Allah yasa ba wata matsalan ce ta sake kunnowa ba" Cikin son kwantar masa da Hankali nace"Haba ba komai abunda muke fata ne jeka ka fad'a ma Mama,bari na saka maka ruwan wanka ka shirya kada ka b'ata Lokaci" Bai min gaddama ba ya wuce Dakin Mama ya fad'a mata ni kuma na je na kunna gas na saka mai ruwan wanka Tuna murhun gawayina yana waje girki na d'ora akai,sama sama ruwan yayi zafi na sake mai nice har bayi sai da na kai masa. Da kuma ya shiga wankan na Lalubo masa kayan da zai saka,yana wankan sai ga yaya Abdul'Ahad ya kirasa ni na d'auka muka yi mgana yace yana kano yana Jiransa, daman ya kawo Raliya ta gaida su Hajiya ne, sai ga kiran Abba so in ya taso ya kirasa yadda zasu hadu a Filin jirgin kawai. Ko da ya fito wankan mun gama wayar,Sai rawan jiki yake yi ya kasa natsuwa fad'i yake yi"yanzu a chan kano zamu hadu da Abdul'Ahad din? Kai Tsaye nace"Eh mana yanzu ma ya kira wayarka na d'auka muka yi mgana,yace in ka taso ka kira sa" Sai ya amsamin da toh fita nayi na basa waje ya shirya nasan ba shi da kudi cikin kudad'en sana'ata na kirgo Dubu Biyar na bashi Saboda nasan in dai suna tare da Abba bazai rasa kudi ba in yaje koda na dawowa ne, har ya shirya cikin shadda fara riga da wando,Sai Hula daya sanya ina shigowa yace"Ba sai na dauki wasu kaya ba ko.? Kai Tsaye nace"Me zakayi da kaya kuma? in ma kwana ya kama ka kana da Muhalli da wasu iyalan achan ka manta ne"Sai ya sauke ajiyar rai kafin yace"Wlh duk na Rud'e ne Fa'iza" Ina mika masa kudin Hannuna Lokaci daya ina fadin"Ka kwantar da Hankalinka babu abunda zai faru ai Yaya Abdul'Ahad yace Abba na chan shima in kaji zuciyarka bata natsu ba kayi ta ma Allah kirari da Hailala, yafi ka zauna kana wannan zullumin" Cikin gamsuwa ya gyad'a min kai kafin ya karbi kudin da nake mikamasa Lokaci d'aya yana fadin"Wannan fa na menene..? Nasan ya rude ne, kila ya Dauka haka zai tafi ba kudi sai na juya ina fadin"a kasa zaka je kanon.? Sai ya Dafe kansa yana fadin"Shaa..Fa'iza wlh na manta"ina jinsa yana bin bayana har Tsakar gida Inda Mama ke jiran fitowarsa. Sallama yayi mana ya tafi mama na sakamai albarka da fatan Allah yasa mu dace. ni kuma mun rabu kan sai ya kirani naji yadda ake ciki. Mun yi masa fatan sauka lafiya tare da Fatan Allah ya tsaresa ni da mama Anum bata san tafiyarsa ba taje kai min nikan Aya,sai da ta dawo nace tayi ma Daada addu'a ya tafi Abuja. Tafiyarsa ba Dad'ewa Yaya Abdul'Ahad ya sake kirana na fad'a masa ya kama Hanya sai yace ya yi ta kiransa bai Same shi ba,yana ga network ne, bari ya Saurareshi. Mu dai ya tafi ya barmu da zullumi,bayan ya isa kanon mun yi waya yace suna Filin jirgi yanzu zasu tashi zuwa Abuja . Daganan shuru bamu kara jinsa ba,Dagani har Mama muna ta zullumi ni kuma kunya ta saka na kasa kiran Abba ko Yaya Abdul'Ahad kada suga kamar na damesu shiyasa na daure Ammh ko Mama bayan mintina sai ta leko d'akina tana fadin"Fa'iza shuru Ishaq bai kiraki ba ko..? Ni kuma sai nace mata"Mama in ya kirani ai zan gaya miki. kuma nasan in sha Allahu zai kiramu" Daganan sai muka koma muka Nad'e hannaye,muna jiran tsammani sai wajen karfe goma sha d'aya saura,ya kirani lokacin yara har sun kwanta Hafsah ce kadai a falo tana karatu,saboda sun fara jarabawa,ni kuma ina dakina sai dai ko da na Dauka bana jinsa har sau biyu,daga baya sai ya kira Wayar mama da ita suka fara mgana kafin ta leko da kanta ta kawo min waya bayan mun gaisa sai kawai ya bige da cemin"Wato Fa'iza ki ji tsoron Gwamnati da kuma in kana da Kafa a Gwamnati. kinsan 24hrs ya yi yawa Efcc ta saka an kamo Mr James tun jiya kuma yayi mgana. Dalilin dayasa ma aka kirani kenan ma" Cikin son jin ya aka haihu a ragaya nace"To ya kuka yi da su yanzu..? Cikin Farinciki yace"Ya amsa laifinsa Alhamdulillah an wankeni daga wannan zargin. ashe da wani suka had'a baki,kinsan kana zaune da mutum bakasan ya tsaneka ba ni wlh lafiya nake zaune da kowa,Yanzu haka dai an yi cike ciken Takardu an tura chan ma'aikatanmu,kuma Efcc ta bani Hakuri tare da alkawarin zata maidamin da kudina da ta karb'a sun rike Mr james a hannunsu suna kara Bincikensa. ammh ni nace na yafe masa Har abada" Cikin jin dadi nace"masha Allah. Alhandulillah gwara daka yafe masa, ammh shi miye riban abunda ya aikata..? Kai Tsaye yace"Matsayina ya ke so. Kuma ya samu tunda bayan Dakatar dani shi aka d'aura akan kujerata" Cikin mamaki nace"Ikon Allah daman ai abun duniya fararre ne kararre ga shi yanzu komai ya kare masa"Cikin jimami yace"Wlh kuwa. Muna chan har karfe Takwas na dare da ni da Abba da Daddy da Abdul'Ahad,da wasu cikin ma"aikatan mu, sai shi chairman na Efcc din da Sauran ma'aikatan su da wanda suka ja Ragamar case dina a hannunsu.Wh Fa'iza Abba yayi min kokari ke kinga yadda Chairman din nan ya dinga bama Abba hakuri.?gaskiya mutumin nan yasan karamci kuma ba fa ba Bahaushe ba ne, Fa'iza Bayarbe ne. abunda na Lura dashi Megidan Abba da yake kira Engr na ji da Abba sosai. tsakani ga Allah cikin gaggawa akayi komai aka gama,kuma Engr ma ba shi a wajen,naji Abba yace yana Edo ki tayani godiya Don Allah" Ajiyar rai na sauke kafin nace"Alhamdulillah Allah ya kara Tsarewa yanzu kana ina ne.?ko kuna tare da su Abba ne..? Da sauri yace''Ina wajen zainab nan zan kwana zuwa gobe. Abba daganan jirgi ya hau zuwa warri suna da taro gobe Abdul'Ahad kuma ya hau jirgin kano" kai na tsaye nace"Ba damuwa ai kana gida kayi zaman ka mu nan ba mu da matsala"Shima kai Tsayen yace min"Aa zan dawo ai ba wajenta nazo ba, itama" Ban tsaya jan mgana ba tunda ba Hurumina ba ne,in ba wajenta yaje ba, me ya hana yabi yo Ya Abdul'Ahad su dawo tare ya tsaya nan zai kwana?shine zai zo yana min wata mganar banza jin nayi masa shuru yasa ya kira sunana sai na amsa sai kuma ya kasa mgana sai kawai ya bige da Fadin"Sai dai na dawon" Yara ya tambaya nace sun kwanta yaso yajani da mgana nace mai barci nake ji duk nagaji cikin Dariya yace"Ai ina samun wani babban aiki duk zaki daina sana'ar nan ta wahala Fa'iza" Sai ya bani dariya har sai da na Dara kafin nace"To ai ko ni ce da kaina na samu babban aikin ban ji
Chapter 112 · 0% Book details