← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 175

Sashe 143

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

iske ya tafi cikin mamaki tace"kiran sa akayi hala..? Abba yace"Ko daya muna hira kawai naga ya sauya, sai kuma yace min zai wuce ban san abunda ya faru ba." Ammi ta zauna gefensa tana fadin"Topha Allah yasa dai lafiya" Ya amsa da Ameen. Abunda basu sani ba shi kanshi bai san meke damunsa ba sai da ya isa inda yayi masauki bayan ya yi wanka ya kwanta barci ya gagara yana da gida a kaduna ammh in dai ba tare da su Sweetheart suka zo ba, baya zama a wannan gidan shi kadai kowa ya san shi mai jama'a ne mai harkokin Rayuwa da yawa ammh yau wayoyin sa ma duka kashe su ya yi baya so a Damesa. abun kamar almara bai Taba jin wata mace ta tsaya masa arai ba tun bayan rasuwar Tauhidat,yasani ba auran soyayya ya yi da ita ba rigiman Granny ce ta hada shi da ita,ya ga mata kala kala yare yare dabam dabam na'i dabam dabam tsayin shekaru ashirin da wani abu bai taba ganin macen da ta hanashi Sukuni irin Faa'izaa ba..! Da ya runtse ido domin yayi barci ita yake gani,Dakyar a Daddafe ya kai asuba ko da ya tashi ya tabbatar ma kansa Fa'iza ce ta hana shi sukuni abunda bai faru da shi da kananun shekarunsa ba ne yanzu da girma ya kamasa zai faru da shi. bai son So ba amnh ko kaffara bazai yi ba SON Faa'iza ya kamasa daga kallon Farko da ya yi mata. Ko wanka bai tsaya ya yi ba, ya taso Direbansa daga shi sai farar Jallabiya da Dogon bakin wando ya nufi gidan Abba karfe shidda da yan mintina na safe. Abba ya dawo masallaci kenan sun gama waya da Abdul'ahad sai ga kiran Engr,domin jiyan ma yayi ta kiransa bayan ya tafi wayarsa a kashe. Ya dauka da kwarin gwiwarsa sai yaji ya Rude jin yace masa yana haraban gidan shi Abba ya mike yana Fadin"Cikin gidana dai..? Yafada cikin mamaki Ammi da ta fito daga cikin bedroom Da hijabinta na sallah taga Abba ya Sauke waya cikin mamaki da sauri tace"Baban Nana lafiya..? Kai tsaye yace"Wai yanzu Engr ya kirani yace yana Haraban gidan nan yana son ganina" Ammi ta zaro ido kafin tace"Yanzu..? Kawai sai Abba ya wuce bai mata mgana Ammi kuma sai ta fara Tunanin anya lafiya..? Abba dai bai kara shiga Rudani ba sai da ya fita yaga Engr da Jallabiya da takalmin wanka. ya firgita yana mika masa hannu ma su yi musabaha Engr bai karbesa ba, cikin wani yanayi da bai taba ganinsa aciki ba. ga idanuwansa sun yi ja alamun bai samu barci ba. Cikin dishewar murya Engr yace"FA'IZAA tana da aure ne..? Kai tsaye mganar tazo masa domin bayan ya Fahimci abunda ke faruwa da shi, zullumin ko matar aure ne yasa jininsa ke barazanan hayewa sama bai sani ba gwara ya farajin Tabbaci sannan. Abba ya kallesa yana mamakin kalamansa shi fa har mantawa yake yi da Engr ya hada jini da yarbawa Saboda komai na sa na Hausawa ne hatta Dabi'unsa,ammh yau sai yaga kamar ya juyo masa yau ya fito a bayarben nasa shiyasa ma cikin mamaki yace"Wata Fa'izan kuma Ranka ya Dade? Engr ya sauke lumsassun idanuwansa kafin yace"Fa'izaa dai..Ur Daughter." Sai Abba ya ware ido kafin yace"A'a bata da aure wani abu ne ya faru..? Yana jin sanda Engr ya sauke karfaffan ajiyan zuciya mai karfin da sai da ya kara kallon sa daga sama har kasa cikin Dafe kirjinsa saitin zuciyarsa yace"Alhamdulillah..! Mu shiga ciki mu karisa mganar" Abba kamar gaula haka ya bisa ammh yana tunanin to lafiya..?Me ya hada Engr da tambayan Fa'iza nada aure ko a'a..? Wata zuciyar ta hasaso masa Dalili a razane ya kallesa lokacin sun shiga Falonsa yana shirin mgana kawai yaga ya zube a kasa yana fadin"Ina kwana Abba" Abba ga mamaki ga Dariya cikin Dauriya yace"Ranka ya Dad'e..Ni ne fa Baban Nana sai na koma kuma Abba.." Engr na shafa kansa yace"Ka zama Abba daga yau tunda zaka bani auran y'arka" Abba ya zaro ido cikin mamaki kafin yace"Y'ata wata y'ar tawa..? Kai Tsaye Engr yace"FAA'IZAA.." FAaa'izaa zaka bani Abba. I love her ganin Farko da nayi mata jiya, daga dare zuwa Safe na Fahimci ina sonta kuma auran ta zan yi, ni ba yaro ba ne kai ma haka bazan zo na zauna ina maka wasa ko karamar mgana ba, duk abunda nace maka i mean it form my Heart. Ya fada yana Dafe saitin zuciyarsa,Abba kamar ya kwashe da Dariya mutane suna kallonsa yana da barkwanci ammh yasan in da sun zauna da Engr sai sun san shi a barkwanci bai iya komai ba. Mutum ne free ba ruwansa mgana fadinta yake daya bayan d'aya a muhallinta. Ganin Abba ya tsaya yana kallonsa yasa ya gyara zama yana Fadin"Abba da gaske nake ina son Fa'iza. Zaka iya bama tsoho kamata auranta..? Abba ya bude baki ya rufe yafi a kirga,Zama ma Dakyar ya iya yi saboda mamakin wannan al'amarin Ganin haka yasa Engr yace"Kana mamaki ko..? Ka daina mamaki nima jiya haka na kwana mamaki ammh daga baya sai na Fahimci Hadin Allah ne shi ne mai Tsara abunda yaaso alokacin da yaso kuma ya faru a sanda yaso" Abba ya jinjina kai kafin yace"Hakane. Sai dai ka sani Fa'iza ba D'iyata ta cikina ba ne..D'iyar kanwata ce mai rasuwa da muka taba zencen ka da ita ta garin mu Karofi" Engr ya gyara zama kafin yace"Allah Sarki Allah ya jikanta na tuna wacce kace baka san kana da kanwa ba sai daga baya..? Abba ya gyada kai yana fadin"Mganar gaskiya Fa'iza auranta shari'a ita ya bama wannan damar, sannan ta rabu da mijinta ba domin shi baya sonta ba sai kaddara" Engr ya yi karaf yace"Kaddaran aure na ne Abba.." Shima sai ya mayar masa da cewa"Ya'yanta Hudu fa Engr" Shima cikin kwarin gwiwa yace"Masha Allah daman dagani sai su Taye Sweatheart Ta haifa. Ka fara fada musu ma sun samu wani Baban din bayan na su Baban" Abba ya murmusa sanin Halin Engr kafin yace"Fa'iza ba tayi boko ba fa Engr.." Shima mirmishin yayi kafin yace"A na addini a ina ta tsaya..? Abba yace"ta wannan fannin Mahaddaciya ce sannan ta sauke wasu littafan" Cikin Annushuwa yace"Good. Karatun boko! da nake da shi ya ishemu ni da ita har gaban Abada" Sai Abba ya kasa mgana Abba yasan waye Engr da naci kan abunda yake so. Shima kuma yasan ya san shi din Shiyasa ya yi mirmishin nasara kafin yace"Ka gama min gwajin tambayoyin..?zaka iya bani amanar rayuwar Yarka Fa'iza..? Abba ya girgiza kai kafin yace"Fa'iza ba kamar ko wacce mace ba ce,Tana da lalura.." Sai ya kalli Engr ya tsaya yaga yadda zai yi sai yaga yace"Lalura ai ta Allah ce Abba ko da lalura ko ba lalura ni Fa'izar nake so,kaga kenan da duk abunda ya danganceta ina son shi" Abba ya karbe da fadin"ko da laluran kurmanta ne..? Bata iya jin mgana sai an yi mata da karfi." Da sauri Engr yace"Alhamdulillah naji dadin haka. daman ni kadai ya Dace tarika jin muryata saboda ina da kishi kan abunda nake so" Jaruntar Engr sai ta bama Abba Dariya sai ya kanne kafin yace"Fa'iza ba yar kowa ba ce bata da komai bata ijiye ba kuma bata bama wani ajiya ba. Ba yar kwalliya bace ba yar kyale kyalen yanmatan zamani ba ne,Ba ta da wayewar yan matan zamani balle ka yi tunanin samun soyayyar da kake Fata Engr Fa'iza yar zuhuda ce duniya da abunda ke cikinta baya gabanta ba lalle ka iya zama da ita ba,kuma Fa'iza ba fara ba ce sannan bata cikin Sahun manyan mata kyawawa burin kowani namiji" Engr ya kura ma Abba ido har sai da ya tsargu kafin ya yi mirmishi yace"Na dauka kafi kowa sanin irin zab'ina. Kyau ko fata bai taba zama Dalilina ba." Engr zai cigaba da mgana Abba ya taresa da fadin"bazan taba ma Fa'iza dole ba Engr ammh ina ganin kai ba sa'an auranta ba ne.." Sai mganar ma ta basa dariya ya yi mirmishi kafin yace"Tafi karfina ko..? Abba yace"Kai ne kafi karfinta.." Sai kawai ya mike ya hau kan kujera ya zauna yana fadin"Naji dadi da ba ita bace ta fi karfina ba. in har ka aminta dani zan shiga layin zawaran Fa'izaa..'" Abba ya saki baki kafin yace"Engr.." Hannu ya dagamai kafin yace" *ENGR.ABDULBASIT ABDULGHAFFAR OLOWATOSIN..*" Lokaci daya yana Dora kafa d'aya kan d'aya yana girgizawa. Abba sai kwarjinin Engr ya dakesa ya kasa mgana kai Tsaye yacigaba da fadin"Engr Usman Karaye ka amince na shiga layin bazawaran Fa'iza..? Abba sai kawai yayi kayattacen mirmishi mirmishin hango Salama da aminci in har Fa'iza ta samu miji kamar Engr. Batare da fargaban da yaso yayi tasiri a ransa da farko ba yace"Na amince" Cikin karfin gwiwan da yakinin cewa Engr zai karkato hankalin Fa'iza garesa. Yana wannan tunanin ya tsinkayesa yana fadin"Ayi min mgana da ita,Daga yau zan fara zaawarci na" *Janafty* [7/30, 7:00 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3011* *Goron Tula* *Ingantaccen maganine dake saukarda niimar mace sannan dadin dadawa fruit ne ga dadi abaki zakine dashi chakwai sannan bashi da wata illa yadda kikasan fruit haka yake* *yana da matukar kyau da tasiri ga ma aurata daga mace harna mijin Kuma munada Syrup nasa da akataceshi sannan aka hada da ingantattun magunguna dasuke temakawa ma aurata kwarai don inganta lafiyarsu dakuma maganin matsalarsu ta auratayya yana saukar da niima sosai yana karawa mace dadi fiye dazatanku sai kingwada zak ibada labari insha Allah* *Sannan akwai zumar kiba* *Duk macen dake son ta murmure tayi kyau taciko tatada komad'a sosai shaf dinta yafito sosai da sosai to tasha wannan zumar insha Allah zaki gode min* *Zumar gyara nono* *Zasu yi kyau suciko ammanfa bawai su tsaya ba zadai suciko suyi kyau sosai insha Allah* *Zumar hips* *Indai kinsha zumar nan to hips dinki zai bude zasu yi kyau suciko sosai zaki godemin nina fadamiki insha Allah* *Note magungunan mu ingantattune basu da side effects kokad'an anyisu da ingantattun* *magunguna sosai* *Location Gombe munaturawa ko ina 08030861857* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* ABBA.." yaji muryan Engr ya kira sunansa cikin taushin murya. ya riga ya
Chapter 143 · 0% Book details