Sashe 128
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tuna da auren sa a kaina" Na karishe Fada ina wata jijjiga Saboda kuka Inno na sharan kwallah tace"Tabbas ya wajaba a raba wannan auran Usman zaluncin ya yi yawa" Abba yaji gabadaya bai son ganin Ishaq da mahaifiyarsa dake kuka shi ko Uban gayyar kansa na kasa jiki na rawa. Cikin Daga murya Abba yace"Sai ya saketa..?ai wannan auran ba shi..Duk da ban da zurfi a sanin wasu hukunce hukuncen addini,nasan matsayin ka jingine auran ka a musuluci wata Hudu ne in baka Waiwiyo ba, ta nemi manya su Raba auran ita ko ta haura shekaru mganar ma yayi saki ko kar ya yi ya Rage nasa mgana D'ayace daga ita na gama Bilhil azim ko kusa da Y'ata Ya sake kusantowa sai na saka an Dauremin shi" Ya fad'a cikin bacin rai yana kokarin mikewa da Sauri Mallam yace"AlhaJi don Allah ka koma ka zauna ina da karin bayani kan wannan al'amarin" Girman Mallam yasa Abba ya koma ya zauna ina jikinsa ina kuka Yaya Mariya ma sai sharan kwallah. Kowa ka gani jikin ya yi sanyi Ishaq ko bakinsa ya yi nauyi ya kasa ma mgana. Mallam ya gyara zama yana fadin"Matsalace ta Ila'i wannan mganar ma'ana rantsuwa a shari'a,kamar kace kayi ramtsuwa ka iyakan cewa bazaka kara kusantar matarka ba har na tsawon Lokacin da ka Dib'a ma kanka. A shari'ance Wata Hudu ya bama mace dama ta zauna in bai Sauya ra'ayi ya Dawo ba ta saka manya Cikin mganar, ko ta kai kara Alkali ya raba auran,ita kuma Fa'iza ta Shafe wasu shekaru tana jingine bi masala ta addini auran su bai saku ba, sai in har shi da kansa mijin ya Saketa ko kuma ya bayyana mana matsayin jinginarsa gareta na saki ne ko ba na saki ba ne. Ammh Shari'a ta bata damar ta Nemi Saki in har bazata iya zama da shi ba" A fusace Abba ya ce"Ai ko yanzu zai sakarmin y'a don mai garin su.." Kai Tsaye ya maida kallonsa kan ishaq kafin yace"Zaka sakar min y'a ko sai na gwada ma ka nima d'an tasha ne? Abba ya fad'a yana Zare mai ido Lokaci daya kamar D'an tashan daya ambata. *Janafty* [7/26, 10:00 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3005* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* Ba domin halin da ake ciki ba, da abunda zai hana mutanen Falon Darawa da kalaman Abba. Ammh yadda zukata ba sukuni yasa ba wanda ya bi ta kan mganar ni dai kuka kawai nake faman yi gabad'aya ji nayi zuciyata ta rufe ba sarari ko kad'an shi ko Ishaq sai da Abba ya kara Dakamai Tsawa sannan ya Dago a Firgice yana rawan bakin fadi'n"Don Allah Abba kayi hakuri. kace zakayi min adalci wlh nasan nayi kuskure ammah na dade da yin nadama ita Fa'iza ta sani na nemi afuwarta da amincewar ta bama auran mu wata Dama Abba.." Abba ya katseshi a Fusace Lokaci Daya yana Fadi:n"ai baka sonta. ko ba haka ba ne..? Rantsuwa ya kwaso kamar ya yi kuka Cikin rawan murya yace"Da ne Abba ban da yanzu wlh ina son Fa'iza ita ta sani ina Sonta.." Ina jikin Abba na rika girgiza kai ina Fadin"Bani kake so ba. Bazaka taba sona ba saboda ba'a sauya Fa'iza ba,ni ce dai Fa'iza bakar nan mummuna, mai raunin ji mara gata yar talakawa wacce bata jin Turanci ba ni kake so ba. So kake na koma saboda ya'yanka da kuma yi maka gadin gida kamar yadda na Saba, tunda daga kai har matanka ba masu zaman gida ba ne kuna fita aiki" Na karishe fad'a hawayena suna shata shata kamar an Bude Famfo Goggo tace"Kibar kuka haka Fa'iza wannan ai sai hawayen naki ya kare" Inno tace"Na yaushe kuma?ku barta tayi kukanta na samun salama ne yarinya ta jima cikin kuncin rayuwa ba'a sani ba irin shi ke sa jini ya haye yayi sama kaji an ce mutum ya Fad'i ya mutu,kayi ta mamaki to shi kadai yasan irin bakincikin da ya rika Hadiya shi kadai" Kalaman Inno suka kara Tunzura Abba ya kara dagama Ishaq murya yana Fadin"Da baki zaka Fad'a ko sai an kawo maka takarda..? Rawan muryansa ya kara Daukowa Abba ya Dakatar da shi cikin Kaushin murya yace"Kada ka sake kirana da sunan Abba kirani Usman karaye na. Ishaq ni uban Fa'iza ne kad'ai" Ya karishe fad'a cikin kaushin Murya har ya nuna sa da yatsa Yaya mariya na gefe ta gyad'a kai cikin jin Dadi Ammi ma ranta fes,Daman tasan Baban Nana bashi da wasa. Cikin kankantar da kai yace"Kayi hakuri Abba ammh bazan iya sakin Fa'iza ba" Abba ya kallesa a wulankance Baba Ati tayi karaf tace"Tunda har baka sonta ka saketa mana..?fiye da shekara goma kana cutar da yarinyar nan bata taba mgana ba sai yau kayi mata adalci kaima mana" Inno ta karbe da Fadin"Ahto mganar Sulhu ai batama taso ba. Mganace fa ta Shari'a Atika haba ai ya cutar da ita abun sam ba adalci aciki." Mita dai suka fara yi nasu na Tsoffi,Goggo dai tama kasa mgana Domin bata da abun cewa mganar gaskiya auren Fa'iza da Ishaq akwai tarin zalunci in akace Fa'iza tayi hakuri matuka an danne mata Hakkinta da shari'a ta bata. Mama ce tayi karfin Halin matsowa tana Fadin"Alhaji don Allh ku yi hakuri. Ku yi hakuri ku yafe mana gabadayan mu. In sha Allahu hakan bazai kara faruwa ba,Alhaji a Duba ko domin yaran nan a bama Fa'iza Hakuri tabi mijinta" Abba ba domin girman shekarun Mama ba,Tuna baya yaso yayi wato ya mulmulamata ashariya,ammh girman shekarunta yasa bai zageta ba. ammh fa sai da ya auno wata mganar cikin bacin rai yana fadin"Su ya'yaan sun ci kaza kazan su. shekarun ki nake dubawa Hajiya shiyasa na raga miki,Shi ai ba duba Darajan ya'yan ba ya Tozartata kema ai baki duba yaran ba sanda kike Cin mutumcinta,sannan ki saka D'anki shima yayi,yaran ai ba son da ranshi suka zo Duniya ba Tunda ba zabinsa ba ne .Bani da damuwa da yara in suma bai kaunar su ya had'o min duk zan iya Hada su da uwar su na rike in sha Allahu bazan gagara ba ammh Wlh tallahi ba mai maida ma Ishaq Fa'iza ko tace zata kuma. ni Usman karaye sai nayi shari'a da d'an ki wajen karban ma Y'ata Hakkinta. gwara tun muna ganin darajan juna ki sa kashi ya saketa kafin mu yi mara kyau ni da shi" Ya fad'a yana Huci ransa gabadaya ya gama baci da wannan renin wayau na uwa da D'anta. Mama ta kasa mgana sai matsar kwallah yau ga ranar nadama bata taba zaton akawai wannan Ranar ba ta dago tana kallon Goggo wacce ta kauda kanta alamun bani da ta cewa sai ta kalli Ishaq kafin tayi mgana yayi saurin ta shi yana cewa"A'a mama kada ma ki rokeni bazan iya sakin Fa'iza ba. Wlh bazan iya ba..! Fa'iza! Don Allah ki saurareni" Ya fada yana kokarin Tunkaro ni Abba ya mike ya taresa cikin wani Kallo na gargadi yace"Kada ka fara. Kada kuskura" Kaina na Tusa cikin gwiwata ina Cigaba da kuka sai ga Ishaq ya Duka gaban Abba ya rike kafafunsa yana Rokonsa Abba ya kwace kafarsa ya matsa gefe yana Fadin"Ka riga ka bata komai da kanka Ishaq. shi kan shi Dr.Laawal din da yazo har gida ya wulakantamin y'a sai naji Dalilinsa ka bani Takardan Fa'iza kaje ka zauna da wacce ka zaba ya'ya ko zan kara maimaita maka in bazaka rikesu ba ka dawo ma da uwar da su, ita zata rike su tunda tasan Darajan su" Abba ya fad'a yana kauda kai Ammi Daga gefe tace"Shikenan kuwa Baban Nana mgana ta kare masu cewa ayi Hakuri saboda ya'yaa an kashe bakin su" Ta fada tana kallon Mama tana Hararanta,duk sai ta zama kamar Mujiya acikin mutane,Ina kuka nayi Saurin Tsaigaitar da kukana na Dago ina Fadin"Abba ba ruwan Zainab da Mahaifinta wanda ya ijiyeni ne ya nuna musu matsayina. In da ace ya nuna musu ina da Daraja abunda ya Faru bazai Faru ba,Mganar gaskiya Zainab bata taba kyamatata ba ta rikeni ni da ya'yana tsakani ga Allah kuma ta kaunace ni shiyasa nima na kaunaceta domin Allah,Wlh ba ruwanta nayi zaman amana da ita da Daraja fiye da yadda mijinta ya Darajani taga kimata fiye da yadda wanda ya ijiyeni ya gani, ka kyalesu Abba mahaifin Zainab ba shi da Laifi kwata kwata. Abba sai faman Huci yake yi Falon ya yi Shuru Ishaq ya Dake yana ma Abba magiya shi kuma yace ya gama mgana ganin Haka yasa ishaq ya mike ya kalleni nima na kallesa da ruwan Hawayena kafin ya gyada,kai yana Fadin"In kina tsammanin zan sake ki ne to gwara ki sake Tunani Fa'iza.." Aurena dake har Abada babu Saki" Mama muje.." Yafada Lokaci daya yana Saurin barin Falon Abba ya bisa da kiran sunansa ammah yaki juyowa Mama ta mike jiki a sanyaye tana Fadin"Kuyi hakuri. Fa'iza Allah ya baki Hakuri" Daga haka itana tabi bayansa Abba ya kada kai cikkn takaici kafin yace"Wlh ko auren zobe ne sai ka saketa ishaq. mutumin banza da wofi kawai" Ina kuka Abba ya Durkusa gabana ya Rumgumeni yana Lallashina fad'i