← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 175

Sashe 59

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi mamakin ganin Hotona da sunana da dukkan bayanan abubuwana ajikin katin sai ya kara Dagowa yana kallona cikin mamaki ya kara fadin"Fa'iza duk wannan abun na menene..? Sai na duka a gabansa na gyara zama na Dakyau kafin nace"Kune yan boko ka karanta Dakyau zaka fahimta" Ya sake karantawa ya Dago cikin mamaki yana fadin"Naga Katin shaida ne na Training din da za'ayi na koyon sana'o'i daga karkashin kungiyar Women charity Foundation." Shine nace ban gane ba naga hoton ki da sunanki shaidar katin naki ne" Mirmishi nayi Cikin karfin gwiwa na fara mai bayani da yadda kawar Badariya da ita kanta suka samo min form din na cike,da kiran mu da akayi wanchan satin mukaje da bayanin komai na karishe mganata da fadin"Gobe zamu fara koyan abubuwa kuma na tsawon sati goma sha Biyu ne,Sannan sau biyu za'a je a rana ni kuma abubuwan da nake so na koya da Safe ake koyar da biyu da yammah biyu kenan kaga a rana sau biyu zan rika zuwa kenan safe da rana" Har na gama bayanina yana kallona cikin mamakina daya nuna har a saman fuskarsa,Cikin kaushinsa yace"Duk a yaushe kika fara yanke ma kanki hukunci yin wani abu batare da sanina ba Fa'iza? Nima kai tsaye nace masa"A ranar da ka zabi wata matar sama dani.Nima aranar na zab'i yanke ma kaina da Rayuwata komai batare da na saka ka aciki ba" Maganata ta girgiza sa ya tsaya kawai yana kallona,ban damu ba sai ma naji kamar gwarin gwiwan. da na shigo da ita ta ninka wacce na samu yanzu tsoro ko fargaba sun fice daga raina kwata kwata. Hanuna na saka na karbi katina daidai Lokacin da yace"Ni ki ke gayama wannan mganar Fa"iza..?Rashin kunya zaki yi min.? Kai na girgiza kafin nace"Ko d'aya kada ma ka dauka ahakan Yaya Ishaq ai ko ba aure tsakaninmu kai yaya na ne,kuma babu rashin kunya har Abada tsakani na dakai.kawai akwai lokacin da in mgana tazo a muhallinta gwara a fad'eta kawai da a barta tayi ta zama a inda ba Muhallinta ba" Sai ya kasa mgana sai kallona yake yi cikin mamaki nasan aransa mamakin ya akayi na samun bakin yi masa mgana yake yi ni ko araina nace daga yau bakunan fa'iza sun bud'e kenan Har Abada. Cikin Ajiyar numfashi yace"Naji yanzu meyasa kika fad'amin..? Na gyara zama na nace"Saboda ya dace ka sani ko ba komai ina gadin gidan ka. da kuma kula da ya'yanka in fita ta kamani naa jera sati ba ma wata ba, yana da kyau ka sani d'in shiyasa nake shaida maka" Kai tsayae yace"In kuma nace baza ki fita ko'ina ba na isa ko ban isa ba..? Ya fada yana kallona cikin ido nima sai na Dago ina kallonsa bansan Lokacin da bakina ya furta"a wannar gabar Isar ka bata isa ba Yaya Ishaq.." Sai ya zabura yana kallona cikin bacin rai ya nuna da hannu yana fadi"Ni kike cema isa ta bata isa ba Fa'iza"? Sai ya mike yana Huci Lokaci d'aya yana fadin"Lalle kin fara rai na ni kin manta waye ni a wajen ki kenam? Gantalin da kika farayi na shiga makota yasa kika koyi rashin kunya da rashin Tarbiya ko..? Sai nima na mike kai tsaye nace"Na fada maka kada kawo mganar rashin kunya a wannan muhallin saboda kai kanka kasan ba Halina ba ne yanzu ta kamane kasan wasu abubuwa.." Cikin Hargagi ya katse ni bayan ya tasomin yana fad'in"To nace bazaki yi ba in kuma zaki nuna ban isan ba ne bismillah Fa'iza wlh sai na nuna miki Oder side of me da baki taba gani ba" Ban bari ya sauke mganarsa ba nace"A matsayin ka na waye kake fad'in bazan yi ba..? Yadda nayi mganar ta basa mamaki sai ya tsaya yana kallona Lokaci d'aya yana nuna kansa cikin mamaki yace"Ni ki ke fad'ama wannan mganar..? Kai tsaye nace"Eh tambayar ka nayi a matsayinka na waye..? Mirmishin gefen baki yayi kafin yace"Ina da matsayin yaya gareki sannan kada ki manta ni mijinki ne" Nima mirmishin takaicin nayi kafin nace"Mijin jingina..?ko yayan da baisan Hakkin kanwarsa a kansa ba..? Nace mijin Jingina Yaya Ishaq ka ke kira Miji..? Mgana takara girgizasa ban bari ya fita daga Girgizan ba na Dora da Fadin"a shari'an ce kai ba mijina ba ne yanzu.Saboda ka zabi wata matar sama dani,ka jingine aure na shekaru biyu kenan,ni matsayina kawai ina kula da ya'yan ka ne sannan in amtsayin Yaya kake mgana baka da wannan Hurumin saboda sai yaya ya zama nagarttace nagartansa zai yi yab'o har ta yab'anyan, da k'anwa bazata iya zarta da wani abu batare da yardan sa ba,Duka baka cike kowani Gurbi ba shiyasa nace isar taka bata isa wannan karon a wajena ba" Baya ya juyamin ya kasa juyowa ya kalleni, ban damu ba sai nayi kokarin Dauke Hawayen da suka kawo idanuwana na cigaba da fadin"Tun Lokacin da ka zabi iyalan Zainab sama da ni da ya'yana.isar ka ta zama bata isa akaina ba, sannan tun alokacin na Zab'i ya'yana sama da kai,kuma tun lokacin da ka zabi Dangin zainab Sama da Dangina nima na zabi Dangina sama da naka dangin, ban ce Dole sai ka amince ba ina fad'a maka ne Dole zan fita na nema ma kaina mafita Kuma Dolenka, ka kare mganar hakan daga bakin kowa in kana gudun fallasar Jinginannen auran mu zuwa kunnuwan da bazaka so hakan ba" Shuru yayi ya kasa juyowa ni kuma da nagama mgana sai kawai na kama Hanyar fita cikin Shakewar murya yace"ya'yana fa wazai kula da su.? Na juyo muna kallon juna ido cikin ido kafin nace"Nima ai ya'yana ne..Ni nake kula da su Lokacin da ka zab'i zainab da ahalinta sama da su.ai a yanzu ba'a wulakance ka gansu ba, nayi alkawarin zan kula da su domin nan duniya nice gatan su nima sune karfin gwiwata da dalilan da yasa nake zaune cikin kaskantataciyar rayuwa" Ina gama fadin haka na bude kofa na fice har nakai dakina hawaye ne ke kwaranyomin sai na zauna agefen gado na rumgume abun hannuna a saman kirjina,na fashe da kuka,a hankali a hankali kuma ina samun salama da Sauki acikin zuciya ta. Sama na kallah nace a fili"Allah kana ji kuma ka na gani. Ya Allah ka sama min Mafita, mafita mai amfani a rayuwata da ya'yana. ka hananin jin kunyar duniya ka bani dukkan karfi da juriyan daukan duka Jarabawowinka." *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?* *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.. *Janafty* *KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *Fatan alheri,ga mutane masu kirki da karamci.* *Aisha muhammad alto(Sisinah)Sannu barka da arziki kin yi kokari da kika Haifa min D'a,Allah ya raya mana Baby boy.* *Fatan alheri zuwa ga Khadija Salisu yusuf(Ummina)* *Halima yusuf gwarzo(Besty) ina miki fatan alheri* *Nana Halima(Masoyiya)ina gaishe ki Fa'iza tace na fada miki,tana kaunarki kamar yadda kike kaunarta.* *Ina gaida Uwar biyu Mrbb,Allah ya raba lafiya* *Sannu gwana uwar Dakin gwanaye,Feedhom nace Allah ya sa afi haka.* *An gaida Uwar Muwaddata da Anum Ramlat Abdurrahaman Manga,Maidambu,ina godiya Allah ya saka da alheri* *Ina miki Fatan alheri Uwar Farha Fatima miss flower(Rabin raina).* *Sannu Amina minajo na,Fa'iza na gaida Masoyiyar asali.* *Sannu Anty maryam,Fa'iza tace nayi miki godiya,da shawarwarki ta fara sanin cewa itama Yar Adam ce.* *Madallah da mutane masu karamcin irin ku,Nagode sosai Allah ya bar zumunci,ya kuma had'amu a aljannah* Saboda Zumud'i ko fargaba zan ce, sai wajen uku saura na dare na iya samun, barci kuma cikin ikon Allah Kasala da nauyin jiki sun kasa barina na tashi na dauro alwala. nayi salollin Nafila sai dai ina daga kwancen ban daina Hailala da ambaton Allah akan dukkan lamurana ba. Washegari kamar yadda na saba tashi da wuri haka na tashi, na shirya yara na sama musu abun kari. sukaci sakamakon sun saba tafiya ba abinci,yau din ma haka suka tafi sai dai kamar yadda na sabar musu sai sunci sun koshi suke tafiya yadda kafin yunwa ta jigatasu, lokacin sun dawo gida sai na ba ma kowannen su Goran ruwan faro guda d'aya sun tafi da shi koda bukatar shan ruwan ya taso musu. Suna tafiya nima ban zauna ba, na fara shiri falo kawai na gyara Dakin yara kuma nace sai na dawo nayi wankana na shirya kaina shima Ahmad na shiryasa bayan na Dama mai kokon sa. na duramai a wani karamin jug,Sauri sauri nake yin komai kada farkon fari kuma nayi latti na samu Tsoffin littafan su Amir da suka gama amfani da shi na Dauka da pencil saboda rubutu duk da ban iya Turanci ba, kuma ban iya Hausa ba, ai na iya rubutu da ajami kuma ina iya karantawa shiyasa ban damu ba. na tabbatar ma kaina duk abunda na Rubuta zan iya ganesa. Na hada da katin shaidana na goya Ahmad a baya na daukan mai wasu kayan. ko da ya bata na jikinsa na fito Falo Tara saura,naci karo da Yaya Ishaq a falon yana waya kallo d'aya nayi mai ban kara ba,shi kuma ganin kamar tafiya zan yi yasa ya katse wayar Hannunsa,ta gabansa na gifta cikin yanayin mganata nace"Ina kwana.." Ina fad'in haka na kama hanya zan fice sai ya mike jiya ya kwana yana mamakina sai da yaga abunda nayi yau sannan ya amince da gaske nake yi,sai ya saka baki ya kirani da karfi na Dakata na juyo ina kallonsa kai tsaye yace"Ina kike shirin zuwa..? Ni kuma sai naga kamar yana batamin Lokaci sai na juya ina fadin"In da na fad'a maka jiya..Ina Sauri ne kada na makara" Na fada ina jimke dubu d'ayan da na Dauko cikin kayana sun sha ajiya tun Kudin da Yaya Isa ya bani ne Lokacin da ya maidoni gida,
Chapter 59 · 0% Book details