← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 175

Sashe 97

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya nufa ganawar sai a wannan lokacin ne" Yaya mariya tace"Naji dadi Goggo naji Dadi yau naga wani ahali daga Ahalin Tamadina murna kamar zata kasheni" Ta fad'a cikin farinciki Hafsah kuma ta Daka Tsalle tana fadin"Abba yace ni ce auta kuma muna da Big bros muna irin na ya'yan yan gayu" Ni dai sai faman washe baki nake yi farinciki ya gama cikani Yaya Asiya ta kasa zama sai kira take muna bata labarin abunda ya faru,Murna kamar me tace itama cikin Satin nan tana Tafe su Baba Ati sun koma gida da Tarin alherin Abba garesa muma kudi ne sun fi dubu dari ya zube mana,Goggo ko kwandala bata Dauka ba sai muka raba a tsakanimu,nan mukayi azahar da la'asar saannan muka tafi ni da Hafsah muna masu Farinciki ko da muka koma gida yara sun dawo makaranta Mama abun mamaki ita ta dafa musu Taliya Jallop muna shigowa Musty da Ahmad suka zo suka makaleni suna kiran Umma Umma daman nayo musu Tsaraban su Chaculate,Dakin Mama na fara shiga na gayamata na dawo ganin yanayi na fara'a yasa ta kalleni kafin tace"Ina fatan su Goggon lafiya..? Cikin Tsananin Farinciki nace"Lafiya lau Mama. Daman Abba ne yayan Tamadina ya zo yau shine goggo ta saka aka daukomu" Mama sai ta kasa gane kan mganar Cikin Mamaki tace"Bangane ba Wani Yayan tamadinan..? Cikin zakwad'i na fara bata labari Cikin karin mamaki Mama tace"Ikon Allah ashe tana da dan'uwa kuma shima yana da iyalansa..?. Kai tsaye nace"Sosai ma don ma tafiya ta kamasa yanzu, iyalan nasa kuma suna kano biki ammh yace da zarar ya Dawo zasu zo gabad'ayan su ganmu mu gansu muma..," Sai Mama ta kasa mgana mamaki duk ya cikata Dakina na shiga Anum ta tare ni tana fadin"Umma nayi miki wanke wanke." Amir kuma ya amsa min da cewa"Umma nayi miki shara" Ina dariya nace"Allah yayi muku albarka ya'yan Umma" Ahmad ke dane kafata yana neman kadani na murde kunnensa ina fadin"Umman zaka kada ko..? Sai ya fara Dariya Musty na tayashi,Kan kujera ta na fada ina Sauke Hijabin Jikina Hafsah ta shige Daki Amir har ya shiga kitchen ya zubomin abincin Ya kawo min kenan yana fadin"Umma ga abinci na kawo miki ruwa..? Kafin nayi mgana Anum ta Ruga taje ta Daukomin ruwan na karba ina fadin"Amun di'na ta zama yan mata fa" Sai ta rufe fuska wai kunya ina ruwan Anum,Mama ce ta kwalama Amir ya kira ya fita sai ga shi ya Dawo da kudi wai cinikin zobon da akayi bayan ba na nan mamakin Mama ya kamani itace har da siyar min da zobo..?ban dai ce komai ba sai da na Huta naci abinci na leka nayi mata Godiya bata amsani ba,Ranar cikin Farinciki muka karishe yini,Yaran har sun Fahimci ina cikin farinciki sai da Amir yace"Umma kina ta dariya ko kin samu kudi ne..? Dariya na saka ina mamakin wayon Amir yasan dariyata yasan Bacin raina,Kansa na shafa ina fadin"Sosai Amir, ammh ba kudi na samu ba abunda yafi kudi Daraja da Tsada na samu"Amir na mirmishi yace"Umma menene shi..? Cikin bayyana Murnata nace"Zan gayamaka kaji" Daganan sai ya bar mganar,Bamu yi mgana da Yaya Ishaq ba,sai washegari ban gayamasa ba ammh yanayin murna na sai da ta bayyana a waya sai da yayi min mgana yace"Fa'iza hala yau an kwashi cinikin zobo da kunin Aya ne kwasha kwasha naji jiki cikin Fara'a.? Dariya ya bani har sun Fahimci in na samu kud'i ina murna sosai ban gayamasa ba na bari sai ya Dawo kwana Biyu Tsakani sai ga shi ya Dawo,ban kai ga ma gayamasa ba Har Mama ta rigani sai da daddare yake min mganar na kallesa ina da'gama masa kai alamun hakane cikin kallona yace"Na tayaku murna.." Cikin farinciki nace"Mungode..Yace ai in suka zo har kai yana son gani" Cikin mamaki yace"Ni kuma..? Lafiya kuwa..? Sai na girgiza kai ina fadin"Ban sani ba ya dai ce dukkan mu yake son ganin mazajen mu" Daganan sai bai kara mgana ba,nima ban kara cemai komai ba kudin hannuna Jarin zobo na da kunin Aya na kara,Sannan nayi Humra makotan mu wata Amarya ta bani na yi mata,har da kwallacha. Kwana Takwas da zuwan Abba Ya kira Hafsah yace gobe shi da duka iyalansa,Daman su Nana Fadila Daga biki basu koma ba ya Tsaida su yace sai sun zo anyi zumunci Yaya Asiya daman ta kwana Biyu a karofi,Murnan kamar zan zuba ruwa a kasa nasha,Har chan karofi ya kira Goggo ta saka aka gyara bangaran Hajiya na gidan Yaya isa inda za'a sauke su,sai kuma mganar abinci Matan Yaya isa da Yaya Salisu zasu ji da komai,Ga Yaya mariya da itama mun yi waya tace zata shirya musu abinci mai da rai da lafiya ni kuma nace zan yi zobo da kunin aya na Taho dashi a goben dani da yara da Yaya Ishaq da sai da Daddare na fadamai. Yayi shuru kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Allah ya kaimu goben" Mun yi zencen da Badariya da yake ta dawo shekaranjiya tace itama zata je kawai da Safe sai Yaya Ishaq ke fadamin Mama ma tace zataje ban yi mamaki ba araina nasan zataje ganin komai ne,kenan duka gidan zamu tafi,Itama Yaya Asiya mijinta aranar zai kamo Hanya da sauran yaran ni ma dani da iyalaina,Har girki sai da nayi jallop din shinkafa mai rai da lafiya da taji kayan lambu da nama nayi zobo da kunin Aya mai yawa,Na daukan mana kaya tunda dawowa badai ranar ba Kulle gidan mukayi,Tashar Mota Ishaq ya samo mana har kofar gida,Karfe d'aya da wani abu muka tashi Hafsah suna ta mgana da Yaya mariya har da Abban sun yi mgana yace Tafiyar ta su ta Motace,suna hanya sun Tsaya su yi sallah ne ammh sun kusa karisowa Mun isa karofi Biyu da wani abu na rana, gida cike su Anum nata murna sun zo Karofi,har alokacin basu iso ba ammh sun ce sun shigo katsina suna gabda karisowa. Yaya Asiya ta fimu murna saboda ita basu taba Haduwa ba ammh mu kanmu murnan ya cikamu,Yaya Isa da su Yaya ishaq da mazajen su Yaya mariya suna kofar gida,mu kuma muna cikin gida muna Dakon zuwan su. *Janafty"* [7/17, 7:33 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2013* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Wajen misalin karfe uku na rana mukaji diran motoci da Hayaniya daga kofar gida,mu muna cikin gida sai muka kasa zama muka mimmike kan kafafun mu,muna masu kurama kofar falon Goggo ido domin ganin masu shigowa. Yara ne almajirai daga waje suka fara shigowa da jakunkuna da akwatina, sai kuma bayan su wasu fararan yara kyawawa mace da namiji suka shigo mace iyakar ta sa'ar Anum namijin kuma kamar Musty ne,Da gudun su suka shigo daidai Lokacin suma su Anum sun kwasa aguje zasu fita waje sai suka had'e da yarinyar nan,Tsayawa suka yi suna kallon juna kamar susan juna sai kuma dukkansu suka washe baki suna Dariya Anum tace"Laa..Ke.." Itama yar yarinya sai tayi dariya sai da Kumatunta suka loba kafin tace"Kema kinsan Gidan nan ne..? Sai gabad'aya mamakin su ya kamamu kafin mu samu mu fita daga mamakin Ina Anum ta san wannan yarinyar mai kyau da ita,sai ga wasu mata Farare yan gayu sun biyo bayansu,da yi sallama sun shigo d'ayar Babar itace ke dauke da karamin yaro a Hannunta sai d'ayan da bata kai ta Tsawo ba tana rike da jakunkunansu na Hannu da wayoyinsu dukkansu Bakin less ne mai adon pink ajiki da mayafansu, a kallo farko in kayi musu zakasan yan gayu ne sannan masu ilimi ne da Nasaba mu dai muna ta bin su da maraba ji kawai ka ke yi ana"Maraban ku." Sannunku da zuwa" Goggo kuma ita ke faman fadin"Maraba da baki maraba da bakin mu" Suna amsawa cikin sakewa lokaci daya suna kallon mutanen dake falon bayan su kuma wata matashiyar yarinya ce tsawon Hafsah inaga itace Nana Khadija itama kayanta iri Daya da na yan'uwanta,tana tafe da wata karamar jaka ta mata a bayanta,Daga ita sai ga wata Farar Mata ta bayyana Tare da Inno dukkansu cikin Fara'a mu dai bakin mu bai daina kiran musu sannun su da zuwa ba. Gabadaya waje suka samu suka zazzauna,Yaya Asiya tayi ma Inno barka da zuwa data zauna a kasan Cafet ta mike kafa Saboda gajiyan zaman mota.ta kalleta lokaci d'aya tana fadin"Mariya ce ko.? Kan Yaya Asiya na kasa tace"Aa Asiya ce" Sai Inno ta rike baki tana fadin"Asiya..Sannu Asiya kece bamu had'u wanchan zuwan ba,ba shakka Allah ya jikan Hafsatu da rahma" A ka amsa da Ameen Nana khadija tace"Don Allah ina so zan shiga toilet"ina kusa sai na kalli Hafsah ina fadin"Hafsah rakata" Sai Hafsah ta mike tace tazo ta rakata ta mike suka shige bedroom kowa ya bisu da kallo gwanin sha'awa. Yar farar matar nan tace"Inno lalle Jini d'aya ba wasa ba, kinga Nana khadija kamar ta da wannan yar sa'arta ta ta, hala tana cikin ya'yan da marigayiyar ta bari ne..? Inno tace"Itace Auta Hafsatu kenan. Ga Asiya nan itace Babban su sai Mariya sai Fa'iza gasu nan kun gansu ku bari Shi Baban Nana ya shigo shi da Abdul'ahad zaku ji sauran bayanin" Daganan Goggo tace ko zasu yi sallah sukace sun tsaya a bisa hanya sun yi sallah,Sai dai aka fara kokarin gabatar musu da abinci Farar matar nan da daga ganinta itace mamansu tace"mu fa ba baki ba ne mun tsaya a inda muka yi sallah mun ci abinci zamu ci anjuma mu da mun zo kenan sai mun gama Zaga dangi gabad'aya ai abinci sai kun gaji da Dorawa kuna saukewa ko Inno..? Tafad'a cikin barkwanci Inno tace"Kwarai kuwa" Goggo tayi Dariya kafin tace"Ina shi Alhajin bai shigo ba..? Inno tace"Ya tsaya da mazan dake waje" Bata ma gama rufe baki ba sai ga su sun shigo,Yaya Isa ne yayi musu jagoranci,Abun mamaki da zugan yaran nan su Amir kamar sun san shi Bayan shi kuma wani zankaded'en Saurayi ne kamar shi, sai dai shi Saurayin fari ne sannan ya fishi jikin Murjewa,suna shigowa yaran na biye da su zuga guda Maman Nana tayi dariya tana fadin"Baban Nana baban yara kenan" Baya ya juya yana fadin"Ina ya'yan nawa..?ku shigo mana ku ai ba surukanta zamu yi
Chapter 97 · 0% Book details