← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 175

Sashe 109

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace kafin na koma Nana Fatima ta rakani har kano na gaida Hajiyar su tace in sha Allahu zata kaini,gani nayi dai ban kyauta ba, ranar da na kwana na yini na kirasa na fad'amasa ina Dutse gidan Nana Fatima. kai tsaye yace"Kika tafi har Dutse baki fad'amin ba Fa'iza..?ai naga dai duk lalacewar aure sunansa aure" Sai na kasa mgana nasan ban kyauta ba yasa nace"Kayi hakuri.." Bai ce komai ba illah yaran da ya mika ma wayan muka yi mgana Duk sun damu da in dawo daman mun yi waya da Hafsah ta fad'amin Ahmad nata rigiman bana nan,sai na fara Tunanin komawa gida kwana hudu nayi a Dutse kamar kar in dawo,Nana Fatima macece mai kirki ita da mijinta sun fita dani naga gari sannan zama da fatima yasa na kara sanin ita mace mai Daraja ce sannan yar kwalliya ce. A na gobe zamu tafi kano da ita ni dagachan zan wuce katsina take kara min mganar Zainab kai Tsaye nace"Ina da abokiyar zama ammh tana Abuja chan take zaune" Cikin karin mamaki tace"kuma tana da ya'ya..? Ina dariya nace"Sosai biyu har da cikin na uku ma" Sai ta rausayar dakai tana fadin"meyasa ita tana Abuja ke kuma kina katsina..? Ganin Nana Fatima ce akwai yarda Tsakanina da ita yasa na gayamata kadan daga abunda ya shafeni sai dai ban gayamata irin zaman da nayi da Ishaq da jinginar aurena dashi ba,sai dai na gayamata Dalilin da ya sa zainab ta zauna abuja ni ina katsina. Cikin mamaki tace"Tab kuma tana zuwa gidan ki na katsina ki sauketa a Dakin ki..? Ina Dariya nace"A'a dakin dai megidan" Sai ta bude baki tana mamaki Dariya ta bani na kwashe da dariyan ina fadin"Rufe bakin Mana" Sai ta rufe lokaci d'aya tana Fadin'"Lalle kina da karfin zuciya wlh bazaki kwanar min a shashe ba..Tabdijam" Dariyan yadda take jinjina abun nake yi a raina nace don ma bataji ni ke Dawainiya da su ba da sai ta zageni,a kwana Hud'un da nayi da ita na kara sanin wasu abubuwa na kuma kara yarda kwalliya da ado na duka mata ne,ba na bambamcin Fata ko kyawun Fuska ba. Na kuma kara sanin ko kana da kyau to ka kara da wanka sai kafi haka kyau gata dai mai kyau da ita ammh kwalliya da gyara bata rabo da shi har mgana nayi mata nace"Nana baki gajiya da kwalliya da gayu..?me zaki gyara ke da komai Allah ya baki mai kyau a jikin ki" Dariya tamin kafin tace"Ko kana da kyau Fa'i ka kara da wankan sannan ki yi shuru kawai ba komai Allah ya bamu ba. muma duk barazana muke da kwalliya da gayun yana karamana kwarjini" Kuma na yarda da mganarta,Domin naga gayu in da ake kiran gayu a wajenta tana fadin Ammi yar gayu ce sannan bata shiri da wanda bai son gayu,nace tabbas na shaida haka Sai naji nima ina so na fara gayun nan na shiga Sahun manyan mata Cikkaku. Washegari Direban mijinta ya kaimu kano har gidan Yaya Asiya tare da ita muka dumguma zuwa gidan su Ammi,sun yi murna sosai sai nuna ni suke yi suna tambayan ita ce Fa'in Azizat mai turaran kamshi sai Nana Fatima ta gyada kai wasu daman mun Hadu Bikin Yaya Abdul'Ahad,Balle kuma daman Yaya Asiya ta zama yar gida,Duk yadda naso na wuce katsina a ranar bai samu ba saboda mun jima muna Hira a gidan su Ammi ita kanta Nana Fatima tayi yammh don dai motar gida ce. Mun fito gidan su Ammi Nana Fatima ta nuna mana wani katon gidan Bene tana fadin"ina Engr din da zaku ji Abba na yawan mganarsa..? Sai muka d'aga mata kai Saboda duk wanda yasan Abba yasan Labarin megidansa Engr. Cikin Nuna mana gidan Nana Fatima tace"Ga gidan kakaninsa ta bangaran Uwa.nan aka haifi mahaifiyarsa dalilin makotansu da gidan su Ammi ma Suka hadu da Abba." A tare da Yaya Asiya muka jinjina kai ina kallon gidan daga gani masu gidan suna da kudi sosai,irin kamar fasalin gidan da Abba ke ginawa a karofi sai dai wanchan ba gidan ba Bene ba ne. Muna tsaye jikin motar da zata maida ta gida muke mganar Yaya Asiya ta ce"To ina masu gidan..? Nana Fatima tace"Hajiya Tafisu ce mahaifiyar Hajiya Shukra ce kadai a gidan sai ya'yan yan"uwa Datake riko megidan ya rasu da jimawa daga ita sai yan aiki a cikin wannan gidan" jinjina kai ina kara kallon gidan da akace mace d'aya ce aciki Nana Fatima ta cigaba da fadin"Shi Engr babansa bayarbene mutumin Beneu ne, Hajiya Shukra ce bahaushiya suna Abuja da zama. Sai dai dangin su kaf suna Beneu har kakansu tana chan da ciwo ya kamata ne ma ta koma hannun Hajiya Shukra,Engr kuma shi a Edo yake aiki" Ni dai har gajiya nayi da labarin Engr Nana Fatima ko ta zage har Yaya Asiya na tambayan"Tab.To ya"yansa nawa..? Nana Fatima tace"Tab. Bai da ya'ya fa, ya taba aure sau da'ya sati biyu matar ta kone da gas shikenen bai kara aure ba. kuma fa Abba ya girmesa, matashi ne sai dai yana da kirki sannan ya taka matsayi mai girma da kananun Shekarunsa" Gani nayi sun bud'e hirarsa da Sauri na katsesu da fadin"Nana kada ki yi Dare" Sai da nayi mgana ta farga Mukayi sallama Ta shige mota suka tafi,Dole na kara kwana gidan Yaya Asiya washegari motar asuba na hau sai katsina,Ance in mace mai ya'ya ta fi sati bata a gida sai abunda ta gani nima haka na tarar,kudin zobo da kunin aya sun ci ubansu,Hafsah sau Daya take yi a rana watarana ma in bata da Lokaci batayi,sannan kudin kuma suna tabaawa in zasu siya wani abu ,sannan yara wlh sun yi kewata ranar da na dawo yini Ahmad yayi Tsalle acikin gida,Shi kan shi Gogan bakinsa har kunne har da fadin"Mutanen kano da Dutse maraba"a Tsime na amsa masa nazo musu da Tsaraban Dutse da Nana Fatima ta bada a kawo masu,nafi kwana Biyu,gidana da kasuwancina bai Dawo daidai ba,Na yarda mace itace gida ranar da bata to sai kame kame har Mama tayi murnan Dawowata.. A satin kuma naje Karofi,Matar Yaya isa ta haihu naga ginin Abba an kusa gamawa a raina nace komai in da kudi an yi an gama,ammh duka duka yaushe aka fara ginin nan har an kusa gama shi..?ban kwana ba na dawo gida Hafsah chan na barta zatayi weekend,ina kuma Dawowa na iske wani sabon salo ban sani ba ko Mahaifin zainab ko ita wanda ya kirasa kan zainab zata baro aikinta ta biyo shi katsina ammh sai ta fara neman wani anan sannan zata zauna agidanta ne ita kad'ai in ya amince shi ko yace bai amince ba sai dai tazo mu zauna tare a wannan gidan. Yana gayamin takaici ya kume ni na kallesa nace"To gidan da zata zauna wazai Dauki nauyin sa..? Kai Tsaye yace"Daddy ne mana" Nima kai tsayen nace"To meyasa bazaka barta ta zauna inda zata Sake ba.?Mganar gaskiya gidan nan yayi mana kad'an ban ga inda ita da yara zasu zauna ba abun kuma yayi yawa" Hade rai yayi kafin yace"To wai haukatani zaku yi ne..? Nace Haukatani zaku yi ne..? To anan zata zauna nace" Sai na bude ido kafin nace"Ba damuwa ta zo mu zauna din na d'an Lokaci ne, kowa zai san matasayinsa" Mgana na gasa masa ammh bai gane ba,Ya gimtse bakinsa nima na kama kaina ina ji har Mama sai da tayi masa mgana tace gidan yayi mana kad'an ammh bai jita ba. Har Anty Binta sai da mama ta kira ta shaida mata, itama fad'a ta hau yi masa na gidan ya yi mana kad'an,shi kuma yace ba ruwanta shi ya yi alkwarin bazai kara yarda a rika juyasa ba. Karfin Hali kenan baka da ko asi sai bakin rai da isa,tab zan ko ga yadda wannnan zaman zai kasance. Sai dai na roki Allah kafin hakan ya faru Allah ya bani mafita. *Janafty* [7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2018* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Magana fa taki ta kare,Saboda Yaya Ishaq yayi rantsuwan Zainab bazata zauna a ko'ina ba sai gidan nan tare da mu,kuma bazai amince Mahaifinta ya kama mata gida ba. Kowa yayi mishi mgana ammh bai ji ba,daman yana da Taurin kai wani Lokaci sannan rashin aikin nan nasa yasa zafin zuciyarsa ta karu,Mama gajiya tayi da mai mgana ta kyalesa har da kaninta Dake yamai ta had'a shi ko zai ji mganarsa ammh yace matsayarsa kenan. Ni tunda nayi mai mgana yace nan din zata zauna ban kara masa mgana ba,na cigaba da Harkokin gabana. Ammh ganin ya dage da gaske yake yi yasa naji kamar nima in kai k'aransa wajen Abba ko Yaya Abdul'Ahad da kan kirani shima duk bayan kwana Biyu yaji lafiyata,Sai kuma na fasa saboda kai kara ba Halina ba ne sannan bayyana sirrin aurena ba Halina ba ne shima,ammh mganar gaskiya Yaya Ishaq zai tauyemin hakkina,Kuma gani yayi ya saba shiyasa yake so ya gwamatsa mu acikin wannan gidan. Ni ban ma jin kaina nafi jin yarana Saboda komai daman nake yi saboda su ne, an saba tauyemin hakki na Hakura saboda su daman. Sai nafara tunanin in Zainab ta dawo gidan nan a ina zai sauketa..? Dakinsa dai falle d'aya ne,Sai bayi rayuwar mace bazai yu yu acikin wannan Dakin ba,bansani ba ko Dakin yara zai sauketa ko kuma ni yake so ya fitar dani daga dakin ya sakata ban yi dai mgana ba na zura ido ina ganin ikon Allah. Ban sani ba ko sun yi ta ja'in ja da Zainab din ne,kan mganar sai kuma Kwana Hud'u da fara mganar sai ga Mahaifinta Dr.Lawal ya diro gidan Dakin Mama ya sauka sannan,sun jima suna mgana da Mama domin da kan shi yace shi Ishaq din ya basu waje zai yi mgana da Mama, daman wajenta yazo sai ya koma Daki yana cika yana batsewa ina tsakar gida ni dai ina Harkokina ban bi ta kansa ba. sai bayan awa D'aya da wani abu Mama ta leko ta kirasa,ya shiga shima ba jimawa sai ga shi ya fito ya kirani Lokacin kuma na gama Dafa zobo ne, sai na bar ma Anum ta kular min da
Chapter 109 · 0% Book details