← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 175

Sashe 7

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ta ke tare da Asiya bata taba jin wani abu aranta game da ita ba.. Ana haka har ta sake haihuwan Aisha,lokacin ne Alhaji Sulaiman yazo mata da mganar da ta kusa girgizata wai zai auri Asiya saboda yayi jihadi sannan ta zama abokiyar zamanta na Har Abada. Ance a lokacin Hajiya Suwaiba tayi tashin Hankali har sai da ta koma gida Ma'ana tayi yaji kuma hakan baisan an fasa ba sai dai ta Dawo ta iske ya gyara ma Asiya dakin dake kusa da nata har an yi biki Asiya ta tare,Ance sillar wannan gabar daga wannan auran ne Hajiya ta kullaci Asiya da Mahaifiyarta Atika akan sun yi auran cin Amana ita kuwa Asiya bata mgana sai kuka ba Laifinta ba ne,Ita batace tana son Alhaji ba shi yace yana sonta batare da sun sani ba ya je ya gabatar da kansa wajen Dangin babanta su kuma sun ga Alhaji ga kudi ga Dattako nan da nan suka basa da Atika tayi mgana suka Rufeta da fada dole tayi shuru. Sanadin wannan auran ne komai ya fara ko nace shine sillar komai bazan ce Hajiyar karofi ta fara assasan wutar kiyayyar ba Tunda kafin ta Mutu ta yi Tuba tuba irin na Taubatul nasuha. Zan iya cewa Tsantsan Rabo ne kawai ya kawo mahaifin mu wannan Duniyan,Asalin sunansa ba Sidi ba ne Sidik ne Asiya ce ke kiransa da Sidi har ya bisa zuwa girmansa. Kusan Lokaci daya Asiya da Hajiya suka yi goyan yaransu ita tana goyan Babanmu ita kuma Hajiya na goyan Baban katsina. Hajiya ita ta ke zaunar da ya'yanta tana fada musu auran cin Amana mahaifinsu yayi da Asiya har aka samu Sidi saboda haka shi ba Dan'uwan su ba ne bare ne tunda auran cin Amana ne to ba d'an Sunna ba ne shege ne, mgana fa har ta fita Domin ba inda Hajiya bata yada mgana gidan biki ko suna har yakai ga Asiya ko Atika suka daina fita Saboda kananun mganganu. Har sai da Alhaji Sulaiman yaji ya tsawarta mata ya kuma ja kunnenta da sai ya iya Rabuwa da ita Saboda haka ance ta sha kuka Ranar Asiya tasha zagi da gorin ita ta zama gatan taa ammh Daga karshe ta saka mata da Auran mijinta. Adalilin irin wada'nan kalaman na bakin Hajiya suka yi tasiri a zuciyar Babbar yarta Hajiya Fatima(Hajiyar Dala) wanda har mahaifin mu ya koma ga Allah bata kaunace sa ba Duk da kuwa an ce Kafin Asiya ta bar gidan Duniya sai da ta rika rokon Hajiya gafara ammh taki yafe mata sai daga bayan ta jima ita da Atika a kushewarsu sannan Hajiyar Karofi ta gane kuskuranta ta gyara alokacin kuma komai ya kure mata. Babbar Bakincikim Hajiya ganin da tayi Sidi da Kabiru sun taso kan su daya sannan komai Alhaji Sulaiman zai yi musu tare ne,ita kuma bata so har ko yaushe a shege take kallon Sidi Tunda auran cin Amana ne..azaba da ukuba ba wanda Sidi bai shata a hannun Hajiya ba ko kasheshi Hajiya zatayi Asiya ko Tarin ta bamai ji a Tsakar gida tana da hakuri da kawaici sannan ga Ladabi da Biyayya ko da ta auri Alhaji bata daina yi ma Hajiya bauta ba sai dai bata gani Laifinta daya meyasa ta auran mata miji..? Babanmu ya fada mana yana d'an Shekara goma sha uku a duniya Mahaifiyarsa Asiya ta rasu da tsohom ciki ta fito daga makewayi jirin Hawan jini ya fardar da ita kwananta Daya asibiti tace ga garin ku nan da Farko Mutuwar ta daki Hajiya ammh Daga baya sai ta saketa. An yi tashe tashen hankula Har sai da iyaye suka shiga ciki kan zaman babbanmu a wajen Hajiya kememe ko tace bazata rika dan shege d'an cin Amana ba sai Atika aka kai mashi ta rikesa Gefe D'aya Alhaji Sulaiman na kula dashi sai dai duk yadda Hajiya taso ta raba Kabiru da Sidi ta kasa wannan jinin na yawo ajikinsu..sannan Fatima ce kadai ta ke bayanta Aisha kuma babu ruwanta bata Cika Daukan mganarta ba.. Babanmu ya d'anda'na gudarsa a Hannun Hajiya tun da duka bai Rufe shekara biyu a hannun Atika ba,ta rasu sakamakon amai da guduwa shi kuma Alhaji Sulaiman yace hajiya bata isa ba Sidi zai zauna agidan nan tunda shima gidan ubansa ne kamar sauran ya'yanta wannan dalilin ya kawo babban baraka tsakanin ma'auratan,In yana gidan Sidi zai zauna cikin salama ammh da zarar ya fita sai abunda Allah yayi ukuba ba irin wacce bai gani ba,Hajiya ta taba Cire masa riga ta zane shi da wayar radio mai karfi kawai saboda sun fita shi da Kabir suka dawo jikinsu duk kasa shine ta rufesa da dukan meyasa yake jan Kabiru ai ba Daya suke ba shi da'n Shege ne Kabiru kuma yaron sunna ne da sahihin aure ya samar dashi Ance sanadin dukan har sai da Sidi ya suma saboda azaba wannan dalilin yasa Alhaji Sulaiman ya saki Hajiya saki daya sakin daya girgizata ta Dade bata gidan ta kuma kwashe ya'yanta duka ta tafi dasu shi kuma sai ya kyaleta iyayenta sun shiga ciki ammh ba'a samu daidaito ba Saboda Hajiya ta riga ta kara hawa dokin naki kan bazata rike Sidi ba shi kuma Alhaji Sulaima yace ba inda zai kai shi in bazata rikesa ba to ta barshi kusan shekara daya Alhaji sulaiman shi ya Dinga wahala da Sadi komai shi ke yi mai Hajiya kuma ta Dauka Alhaji Sulaiman zai sauko yazo ya bata Hakuri sai taga ba haka ba ne ga su kabiru suna ta Damunta da Babansu shi kuma tunda haka ta faru bai taba Takawa wajenta ba ai yace ba shi yace tatafi da ya'ya ba ita taga dama Saboda haka ba zai bisu ba in har ya'yansa ne zasu nemesa. Ganin Ba riba ne yasa da Umarnin Iyayanta Hajiya ta dawo gidan Alhaji Sulaiman ammh an yi musi tsakani da Sidi ba ruwanta da shi,Shi dai yana bata girmanta domin kamar uwa ya Dauketa ita kuwa ta tsani ma ta Bude ido ta gansa don dai bata da yarda zatayi. Cikin wannan Halin Rayuwa ta rika ganganrawa Alhaji sulaiman bai tara dukiya ya rika siyan kaddarori ba sai dai ya gina ya'yansa ya basu kyakyawan ilimin zamani,Matan daga Sakandiri yake aurar da su,Ammh dukkansu sai da ya kai su Hajji suka sauke Farali Hajiya fatima Soja ta aura dan kano ne chan aka kaita,ammh daga baya an sauya mai wajen aiki ya koma Kudu,Kafin zuwa yanzu sun zauna garuruwa da dama kafin ya yi ta samun karin girma har ya kawo matsayin da ya kai a yanzu. Sai Hajiya Aisha da ita kuma d'an karofi ta aura kuma kamar aboki yake wajen Alhaji Sulaiman sai dai tun alokacin ba'annin juna ba ne.. Alhaji sulaiman bai bar gidan duniya ba sai da ya gina ya'yansa sannan ya aurar da su bayan mata ma har da mazan har kuma ya bar duniya bai ga Nadamar Hajiya suwaiba(karofi),kan Asiya da zuru'ar ta ba,har alokacin bata ganin duk wani daya shafi zuru'ar Asiya da Atika da Daraja saboda abunda ya faru. Daga kabiru har Sidi sai da suka fara samun Takardan Education kafin su Dora degree din su,Baba kabiru fanni Biology ya karanta,shi kuma Babanmu sai ya karanta Fanni Kasuwanci Business admistration. Bayan kamallah karatun su dukkansu sun samu aiki Kabiru ya fara koyarwa a wata makaranta gwamnati dake Karofi shi kuma Sidi sai ya samu aiki a wani ma'aikatan littafai dake katsina chan ya tattara ma ya koma Saboda gidan baya mai dadin zama Hajiya ko zai gaisheta sau dubu bazata amsa ba sai tayi kamar bata gansa ba,Sai dai yana bata girmanta a mats ayinta na uwa bai taba riketa aransa ba kuma kullun haka Alhaji Sulaiman ke gaya masa Hajiya uwa ce garesa komai zatayi mai kada ya Daukesa a wani abu ya Dauka ajizanci ne na D'an adam. Shiyasa bai taba kallonta da wani abu ba,Balle da suka taso kamar uwa daya uba daya shi da Kabiru in ba mutun bai sani ba zai dauka uwar su daya ubansu daya sai an fada maka ne zaka san ba Uwa dayace ta haifesu ba ammh suna Diban kama Dukkan su Dogayen katsinawa ne marasa Lalaci Sannan shi kabiru yafi Sidi haske Saboda Hajiya farace,Sakamakon ita Asiya baka ce shiyasa sai hasken sa ya zama mai Duhuwa.. Yana shigowa karofi duk bayan Sati hudu kuma duk alherin da zai yi ma Dangin Mahaifiyarsa,zai yi ma Hajiya sai dai bata karba yana sauke ledan zata Dauka ta kone daga baya sai ta Daina konawa Tunda Alhaji Sulaiman ya ja mata kunnen tana albuzuranci da Dukiya da kaya watarana zanin Daurawa sai ya gagareta sai ta tsorata ta Daina Konawa sai dai ta Sadakar da su. Kabiru ya riga Sidi aure saboda shi Daga baya shima katsinan ya koma da koyarwa a wata babbar sakandiri,Achan ya hadu da Saudatu ita din buzuwar yamai ce Kasuwanci ke shigo da su Katsina ta Jibiya anan suka Hadu Allah ya hada kauna Tsakaninsu har ta kai su ga aure Saudatu(Mama kofar soro) farace Doguwa kyakyawa kin kowa kin wanda ya rasa ga gashinta har gadon Baya Hajiya tayi alfahari da wannan auran ganin kamar Kabiru ya kece sa'a cikin maza zai auri buzuwa,Barin ma Hajiya Aisha da itace kamar makwafin Hajiyar tafi kowa Fi'ili da karairata Ita Hajiya Fatima babu ruwanta ita datake ma kusa. Har chan yamai akaje aka nema ma Kabiru auran Saudatu,suka kuma Tare a gidan su dake karofi inda Alhaji Sulaiman ya gina musu barayi guda biyu,Na kabiru da Sidi shima sai da Hajiya ta rika yada mganar ai shi ba Dan gida ba ne bashi da gadon Alhaji shi dai bai kulata ba sai dai yayi mata addu'an shiriya tunda ganin Shekaru sun fara ja Hajiya bata Sauya ba,bai tunanin zata iya sauyawa sai dai shiriyan Allah kawai. Tun zaman Saudatu karofi taga gata wajen Hajiya kamar ta lasheta barin ma har zuwa ake yi ganinta Saboda kyanta da gashinta,sai taji dadin haka Domin daman tana bakincikin Sidi na aikin kamfani Kabiru kuma ya zama malamin makaranta in tayi mai korafin haka dariya yakan yi kafin yace"Hajiya kenan ko wani bawa da kika gani yana tafe da kaddaransa arzikinsa da
Chapter 7 · 0% Book details