Sashe 28
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai ta hakura iyayan su kuma Ilimin bai Dame su ba damuwa suka yi da karatun ba. Dr.Lawal bako dan boko ne sosai Domin Rayuwar boko yake yi a gidansa shi ya tsara hakan tun farkon zaman auransa da Halima,Ya'yan su biyu ya tsara zasu haifa Saboda a cewarsa bazai zo ya haihu da yawa ba ya kasa Rike ya'yansa ba,Sai dai Kana naka Allah ya riga ya gama nasa Sai da Halima tayi haihuwa Uku suna yin wabi sannan ta Haifi zainab ta Tsaya Tsakaninta da kanwarta Zeenat suna kiranta Zuzu Shekara Biyar ne daga kanta kuma sai ta Haifi namiji sai dai ko arba'in din sa batayi ba ya koma ga Allah Daganan suka tsaida Haihuwa a cewar Alhaji Lawal bako Kada ta kara Haihuwa kyanta da Nagartatan su Lalace ita kuma bata da yadda zatayi bata iya masa gaddama rayuwarta da ita kanta sai abunda ya tsara mata. Duka ya'yan nasa yadda yaso haka ya tarbiyarta dasu,Halima bata isa ta nuna wani iko kan ya'yanta ba tun suna kanana sai abunda Baban yace shi zasu aiwatar sannan baya shawara da ita gani yake bata san ne take yi ba Tunda bata da Ilimin Zaman duniya. Zainab da kanwarta Zuzu sun taso cikin Sangarta da Sakewa da kuma Tsananin gata,ba kwaba ba kyara ba Gyara haka suka taso a gaban iyayansu koda sun yi wani abun mara kyau in uwar zata kwaba musu sai Uban ya hana sai ya rika nuna su kadai ne ya"yan su in basu ji dasu ba da waye zasu ji..?Dole ne su ji da su tunda basu da kamar su,In tace hakan bai kamata ba sai yace duk wanda kika ga bai sakar ma ya'yan sa Gata ba bai da shi ne sannan bai san Darajan ya'yan ba ne. Daga karshe sai ta koma bangaran yaran sai ta Fahimci suma sun fi jin mganar Uban su fiye da ita tun suna yara sun Fahimci mahaifiyarsu kamar Hoto take sai Uban yayi shawara da su,ammh ita bai neme ta ba ko wani abu yace in suka ce Daddy mommy fa..?Sai yace su kyaleta kawai mommy bata san komai a wannan zamanin ba to har suka girma da wannan Tunanin aransu Daddyn su shine nasu uwar su kuma ta nan a matsayin Mahaifiyar su ammh bata da wani Say a gidan da Rayuwar su gabadaya. Sun taso da Yare guda biyu a bakin su Turanci da Fullanci saboda Daga Uban har uwar basu yarda Yaren su ba In dai suna gida daga Fillaci sai Turanci suke yi Hausa kuma sai dai a waje ko a makaranta,Sannan in sukaje ziyara chan Rugga basa wani yare sai Fillanci sai yaren ya zauna Sosai a bakinsu.. Zainab da Zuzu kyakyawan yan mata ne na gani na fada kamar su, sukayi kan su Saboda kyau da zati to bangaran Uwa da uba duk kyawawa shiyasa suke jajir kamar a taba jini ya fito sannan sun tashi cikin gata da jin Dadi,Zainab ta gama junior secondary dinta suka koma Abuja da zama anan ta ida karatunta ta fada Universty of Abuja ta karanta Chemisty,Gatan duniya ba wanda basu samu ba komai suke nema kafin su yi mgana sun same shi Tun suna kanana komai yan aiki ke yi musu shiyasa su Rayuwar Hutu suka sani da jin Dadin. Dr.Lawal bako Rauninsa Daya ne ya'yansa yana tsananin kaunar su,Zai iya batawa da duk wanda ya nemi ya tabasu sannan zai iya karta ma kowa rashin mutumci a kan wadanan ya"yan nasa,Yana nuna musu kauna a fili har tana wuce misali Hajiya Halima da suke kira Mommy ko tayi mai mgana sai yace me ta sani kan wannan zamanin tayi mai shuru kawai shiyasa ita nata ido ne sai dai tana addu'an Allah yasa kada su zame mai Raunin da zai zame masa Lalura watarana. Ishaq kabir karofi ba Zainab ya fara sani ba,Dr.Lawal bako ya fara sani Lokacin da aka mai karin girma da sauyin wajen aiki ya koma Abuja shine ke rike da babban Ofishin su na Abuja,Haka kurum Ishaq yaji Dr.Lawal na Burgesa saboda he is Educated and Innocent,sannan jajirtattace ne kan aikinsa,Shi kuma Ishaq yana da Ladabi da Biyayya ga manyan sa shiyasa suka Saba da Dr.Lawal,Kuma karin ma abun yana ganinsa Farin namiji gaye kyakyawa mai ilimi da sanin ya kamata Dr.Lawal na son harka da mutane masu kyau da wad'anda suka san abunda suke yi,Dalilin Sabawar su yasa Ishaq bai iya kiran sunansa Sai dai yace Daddy kafin shekaru su ja su san komai na juna har gida Daddy kan gayyace sa gidaansa yaje yaci abinci anan yaga Zainab ya nuna yana sonta lokacin tana shekarar karshe a jami'a tana masters d'inta lokacin daya ganta yaji aransa mafarkin daya Dade yana yi ne Allah zai tabbatar masa bai nemi zainab kai Tsaye ba sai da ya fara Tuntubar Daddy shi kuma yace ya bashi lokaci ya kara Bincika Ishaq din kuma ya Samu komai yadda ya sanar da shi Cikin Lokaci ya amince batare da Shawara da Hajiya Halima ba Ya'yansa kawai yayi shawara da su,Daman kuma achan Rugga an saka ido kan rashin auran su zainab din,Shi daman baya so ya aurar da su in da zasu sha wahala ne ya fi son ya aurar da su inda yake da Mgana a wajen zai iya kula da ya'yansa ya kuma Tofa komai a lokacin da yaso a kan Rayuwar ya'yansa. Zainab bata isa tace taki Ishaq ba ganin Farko da tayi mai taji ya shiga ranta suka fara soyayya sai dai da Farko taso ta Damu da taji yana da mata sai ya nuna mata kada ta Damu Fa'iza ba komai bace a rayuwarsa face Uwar ya'yansa ita ce First love dinsa da ta fadama Dr.Lawal Dariya yayi yaji Dadin da yarsa zata kasance Zara Cikin wata Hajiya Halima nata sai dai ido kawai har gwara ma Zuzu bata kai zainab rawan kai da Daukan duka Hallayar mahaifinsa nasu ba ita ta kan tsawarta mata taji,Ita ma tana nan tana karatu a Nile University of Abuja,zainab kuma tana gama karatu tayi Services a wani kamfani karafuna bayan ta gama kuma suka Riketa aiki a wajen,Batare da Ishaq din ya sani ba kuma Lokacin har an yi mgana ta iyaye lokaci kawai za'a sanya har zuwa Lokacin da akayi auran Ishaq bai fahimci bai da wani iko akan Zainab ba sai abunda Mahaifinta yace da shi ta ke amfani. Shi ya gina auransa kan Soyayya da kyau nasaba kudi da nagartan ilimin zamani,ita kuma ta auresa ne Saboda kyansa da kudinsa sannan saboda Mahaifinta,shi kuma Dr.Lawal bako ya amince da auran ne saboda yana Tunanin Daga Ishaq har Zainab suna karkarshinsa ne zai iya yanke kowani irin Hukunci kan yarsa batare da ya D'aga ido yayi mgana ba. Muje zuwa..! **** *Katsina..* Bayan wata daya. Mutanen Umra sun dawo an kawo Tsarabobi kala kala nima Badariya ta kawo ma su Amir nasu,abakin ta nake jin Tsaraban ma aiko da shi sukayi ta Abuja suka sauka,Ya Ishaq din kuma bai zo ba,an kawo ma yaran Jallabiya Amir da Musty,Anum kuma Riga da wando,Ahmad kuma kaya riga da wando masu kyau da yarari,Sai Dabino da ruwan zamzam na amsa nayi godiya Daman ni ban saka aka ba ballata don ba'a bani ba na Damu Badariya ta fadamin har Hajiyar Dala an aika mata Da Tsaraba to daman ai ya kamata a aika mata ta chanchanta. Damuwa ta daya ne yanzu yadda komai ya ke kara lalacewa,Ni ba na jin kaina sai ya'yana sune a gaba,Ko Haruna ni da kaina na shirya na shiga har gidansa Daman makota muke bamu da nisa,Na taba shiga sau biyu tun Fara kai su Amir makaranta,Sunan matarsa Sa'adatu,dayake bana harka da kowa sau daya ta taba shigomin gidan daganan bata kara ba Ishaq bayan Yan'uwana da Dangina har da Mutane ma ya rabani da su Ahalin kuma an ce Mutane Rahma ne. Naje na same sa na bashi Hakuri akan rashin Biyan sa kudin sa wajen wata uku sai ya nuna min bakomai an zama D'aya tunda Hakkin makota ya hadamu matarsa Sa'adatu ta karbe ni Hannun Bibbiyu,Na isketa tana ta Saida Saide kayan miya da su maggi da gishiri kayan dai kulle kulle na gida na mata sai kuma zuwa ake yi ana siya sai abunda ya bani sha'awa naji Dama ni ce ban iya shuru ba har sai da nayi mata mgana nace dama nice ita ina son nima na Fara sana'ar cikin gida na mata, bata ji ba sai da na kara maimaita mata sannan taji ni Dariya tayi kafin tace"Haba Hajiya kamar ki ina ke ina wata sana'a..?kuna da Rufin asirin ku..Sana"a ai sai irin mu matan talakawa mu samu na Rufa ma kanmu asiri damu da mazajen mu" Naji mamakin mganarta ni kuma sai nace mata"ai sana'a bata ga Talaka bata ga mai kudi..Muna yin sana'a ne Domin dogaro da kanmu da kuma ya'yanmu sannan ita mace da neman na kanta a kasanta saboda kada gazawa ya zame mata nakasu watarana" Sai ta jinjina kai kafin tace"Kuma hakane Hajiya" Ina kallonta kai tsaye nace"Ba sunana Hajiya ba..Sunana Fa'iza ko ki kirani maman Amir" Daganan tayi dariya muka cigaba da Hira sama sama,Ban jima ba na koma gida tundaga Lokacin araina na saka ma raina bazan zauna na mutu ni kad'ai acikin wannan gidan da bama ceto sai Allah ba nima zan rika fita na shiga jama'a domin su din Rahma ne. Muna cikin Haka aka kore su Amir daga makaranta suna dawowa suka fadamin suna zuwa aka koresu kudin makaranta acikin makarantar suka zauna har sai da aka tashi Haruna yaje ya Daukosu hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi na so na kira Ya Ishaq na fadamai sai kuma bani da kati ko na flashing kuma bani da ko asi a hannuna sai na koma na Rumgume hannunawana kawai na rasa mafita,kawai sai nace su dakata da zuwa makarantar sai an biya a baya duk Lalacewa yana biyan musu kudin makaranta akan Lokaci basai ta kai ga an koresu ba,ganin sun kwarari sati a agida ba bokon ba islamiyan sai dai nayi musu na Islamiyan agida,Sai suka fara Damuwa suna ta tambaya na Umma meyasa muka Daina zuwa makaranta..?Anum da Musty kenan Amir shi yafi su