← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 175

Sashe 79

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Zeey din taka mana, inace ita ma Matarka ce" Sai kawai ya koma ya zauna yana fadin"Fa'iza yaushe na fara mgana kina min gaddama sannan yaushe na fara mgana kina sa'in sa da ni..? Kai na tsaye nace"Tun ranar da ka furtamin da kanka ka zabi wata matarka fiye da ni nima tun ranar na zabi rayuwata da ya'yana sama da kai.Komai kaga ina yi maka don Allah da taimakon zumunci ne" Daga haka na fice na barsa da sanyin jiki Hidmar hada zobo na fara satin nan Hafsah karatun Safe suke yi,Allah yasa tamin shara da Safe wanke wanke kadai nayi sai na share tsakar gidan na wanke ina wajen Zainab ta shige bata fito ba, ni ko dakin ban koma ba Fadil ne ya dinga kuka a Hannun Mama ta kasa lallashinsa sai na shiga na karbesa sai na Fahimci yunwa yake ji ina da Sauran garin kuni nan da nan na dora ruwan zafi daya tafasa na Damamai na Duramai tas ya shanye sai barci,naja zani na goyesa ram a bayana na cigaba da ayyukan gabana Mama daman tagaji da renon ta shige Daki tayi kwanciyarta Tunda baiwarta ta Dauke komai. Da rana Danwake nayi da salat,aiki duk ya Chudemin Zainab kam da uban gayyar sun shige daki ba mai jin motsin su, Fadil na Dakina yayi barci da ya tashi nayi mai wanka nima nayi ban san fitan ta ba ta koma Dakin Mama tayi wanka ba,sai da ya tashi ya fara rigima na lekata sai na ganta na mika mata shi ina fadin"Ya tashi yana rigima" Ta karbe tana fadin"Daman tunda naji sa shuru nace yana Hannun ki" Mirmishi nayi mata na fice,ina komawa Daki na ci karo da shi ya fito Daga kitchen da ya gani sai yayi Turus ni kuma sai nayi kamar bangansa ba zan wuce dakina yace"Dama..dama kuna da ruwan zafi ne..?garin ai ko sanyi zazzabi bai sakeni ba kada na Dawo da shi da wanka da ruwan sanyi" Da nayi niyyar na yi wucewa ta ne sai wata zuciyar tace ashe ya Dameki..?sai na juya ina"Ka kira Zainab ta saka maka mana" Sai ya bude ido yana kallona,na ganin na juya yasa yasha gabana yana fadin"Don Allah Fa'iza don Allah nace.Zeey bata shiga kitchen achan komai ma'aaikata ke yi mata" Rashin kunya ba Halina ba ne yasa na juya na koma kitchen na kunna gas na Doramai ruwan zafin na fice na barsa nan falon inaga da yayi zafi ne ya kashe gas din ya juye,yau alhamis ne da la'asar yara suka dawo makaranta Amir ya taimakeni ya tayani Dura zobon a gorina Anum na shirya mana nayi na Safe har ya kare wannan na yammah ne,Addu'a nake yi Allah ya dawo da Hafsah ta dora girki sai biyar da wani abu ta shigo tana shigowa Amir yace'"Umma ga Antyn Hafsan ta dawo" Daga ganinta ta gaji ta sauke jaka tana fadin"Da Antyn Hafsah tayi me..? Ina Dariya nace'Yaji ina ta cigiyarki ne aiki yayi min yawa ban dora girki ba" Sai ta ce"Bari naci abinci na dawo hayyacina"Da sauri nace"Yauwa yar albarka mu in mun gama sai mu had'a kwanuka mu yi wanke wanke" Da Sauri Anum tace"Umma ni zan yi" Ina dariya nace"Ko baki ce ba tare zamu yi kafin nan gaba ki iya na sakar miki,ammh kafin sai kin share inda muka bata" Musty yace"Ummi ni zan share" Nace"To ya'yan Umma yan albarka" Ahmad na gefe yace"Umma zan wanke miki robobi" Amir yace"Kadai samu na wasa" Gabadayanmu muka saka Dariya gabadaya bani da damuwa indai ina ganin Dariyan ya'yana su nafi damuwa da su bangaran su Mama tunda zainab tazo ta bud'e musu bakin aljihu suna cin dadin su yau nama gobe kaza ni dai ya'yana suna daki basu gani ba,ballatana su saka rai ammh fa Fadil na wajena ni nake mai komai har wanka uwar tana nanike wajen miji ana shan soyayyah. Washegari da Safe bayan yara sun tafi makaranta na fada ma Hafsah yau zobo Sau daya zamu yi,sai kunin Aya shiyasa da Safen bayan yara sun tafi makaranata na samu kujera na kwanta sai barci Hafsah ke dafa zobon awaje basu da shiga makaranta yau,ai naji dadin zaman Hafsah a wajena tana bala'in taimakamin kan sha'anin gida da sana'ata wani lokacin ba domin ita ba,bansan ya zan rika yi da wasu ayyukan ba. Na fara barci sama sama na rika jin Hayaniya na gyara kwanciyata saboda ban ji hayaniyar ko ta macece ba,Sai da Mama ta shigo har Falona ina kwance kawai naji ta Dakamin duka na Bude idanuwana da suka yi ja Saboda barci sai naga Mama a saman kaina Tsakani ga Allah ina gajiya saboda aikin Hannu nake yi komai sai na sarrafashi da kaina. Ina kokarin tashi zaune kawai ta hau ni da fad'a nama kasa gane in ta dosa sai da nace"Lafiya Mama..? Cikin wani kallo tace min"Bansani ba.Kya ce lafiya mana kina kwance kina barci,shi kuma ga shi chan bai da lafiya shi kika bari da wankin kayansa" Sai taga na mike kawai zan shige cikin D'akina kai tsaye ta saka hannu ta fizgoni na dawo gabanta tana zare min ido tace"Don ubanki ina mgana kina wucewa,ni sa'arki ce.? *INGANTACCEN ZANCE*. *Akwai da INGANTATUN SAIWOWI na gyaran mejego ko amare*. *Haka uwargida ma ba'a barta a baya ba da irin nata tagomashin* *Kaya ne masu kyua ba garabiti ba, takanas ake kawo su daga chadi.* *Idan kina da kannen da za'a aurar, ki zo ki yi musu tanadi na mussaman*. *SAIWOWIN itatuwane da basu da illah* *Da sau'ki zaki same su, amma aikinsu yawa ne dasu.* *Kawai ki tuntu'bi Surayya HALIN YAU a wannan lambar dan samun gamshasshen bayani* *08032773332.*
Chapter 79 · 0% Book details