Sashe 63
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
karfinsa,da na kirasa na fad'amai ga halin da ake ciki bude bakinsa sai cewa yayi na kyaleta tayi duk abunda taga dama" Mama tace"Uhm nima ai haka ya fadamin sai na kawo ido na saka musu daga shi har ita.Ni damuwata d'aya in ta fice ta bar masa gida ba kowa a shiga a sace wani abu ai shi ke da asara ba ita ba" Kaina na kasa ban dago ba araina nace ina abun sata a wannan gidan..?shi kan shi yasan bai ije komai ba kamar yadda ban yi mgana ba shima kala bai ce ba sai faman dannan waya yake yi ita kuma Zainab waya aka kirata daga gidan bata tashi daga Falon ba ammh ta sauya yare zuwa Fillanci.. Nan Mama tayi nata cin mutumcin Anty Binta na tayata daga karshe Mama tace"Ai tunda Uwar su ta rasu naga tana wani tashen iskanci, mutuwa ai d'ayace kuma duk abun ki dai baki isa ki dawo da ita ba.Ni Allah na tuba mq cewa nayi gwara da ta rasu ta Huta rayuwa ko'ina ba inda tayi kyau" Subhanallah na fada a fili na Dago ina kallon Mama bata damu ba tacigaba da Fadin"Shiyasa yana kirana yace suna tafe nace ya sauke Zainab anan yadda bata jin dad'in nan ga shi Fa'iza kuma ta saka Mugunta a ranta ai sai ta bar Yar mutane ta shiga wani Hali mu shiga uku" Anty Binta tace"gwara da kika yi haka Mama"ni dai ban ko kara Dago kaina ba,zaman duk ya isheni ga shi Badariya bata nan zainab kuma tana gama waya ta tashi ta shiga ciki zata kwanta Yaya ishaq ya bita har sai da na gaji da jiransa sannan ya fito yaran har sun fara barci,Mama Tuni ta Dauke Farhan ta shiga da shi Ciki Musty da Ahmad ne suka yi barci nan saman Cafet ammh Mama bata damu da su ba,Anty Binta ta rigamu tafiya mu bayan mun fito Mama ta kira Yaya Ishaq ya koma ciki fiye da minti goma sannan ya fito muka tafi har muka isa gida ci kanki bai ce min ba nima haka, Domin naga yana wani shan kamshi ne da cin mgani a raina nace Indai ta fa'iza ne kayi a banza domin ban ma san ka nayi ba. A satin yara suka yi Hutu daman sun gama jarabawa,karshen Team,Na lura wannan karon zasu dade tunda bayan zainab ta kwashe Kwana hudu gidan Mama sai ya maidota gida nan shashen shi inda ta fara sauka,su Anum nata murnan Farhan ya Dawo gidansu da kuma suka Dawo sai naga baya cewa nayi abinci da su, sai dai ya Rika fita yana siyo musu nima sai na kama kaina.Daman ba abincin gareni ba Shinkafa kad'ai ta ragemana itama Saboda wanchan cefanen ya siyo ta da yawa ne,Yadda bai nema ba nima ban Tusa kaina ba,Sai dai ina na shiga kullum da Safe mu gaisa da Zainab wani Lokacin ita takan fito falo mu gaisa har mu taba hira tana da Sakin jiki komai ta gani sai tace Maman Amir kaza maman Amir kaza. Shi megidan nakan gaishe sa, sai dai ba kullum yake amsawa ba sai yaga Dama ni ko ban damu ba saboda ban ga abun da nayi mai masa da zai nemi kara Rataye ni a sama ba,Farhan kuma ya zama d'an wajena nike dawaniya da shi har kwana yana yi a wajena,nasan Ko Yaya ishaq din yayi mgana ita Zainab zatace ya kyalesa a wajena Saboda ta taba cemin wai bana gajiya da goya yara da Dawaniyar su..? Ni kuma sai nayi Dariya nace mata ina son yara, kuma Dawaniyar su bai taba bani wahala ba. cikin mamakina tace zata kawo min Farhan nan da zarar ta yayesa bata son wahala ga aiki bata zama Allah yasa ma tana da mai renon sa ,ko ta kaisa gidansu a bakinta nake jin dukkansu sun samu Hutu ne shiyasa zasu fi sati kafin su koma. Ranar da suke da kwana takwas da zuwa sai ga Goggo da Yaya isa,ya sake kawota na rika ina zan saka da Goggo da tazomin da su garin kunu garin Tsaki da garin masara,yaji kayan kamshi wake mangyad'a da su manja,sai garin Danwake da Taliya yar Muji ina ta Murna sai dai ashe zan ninka Murnata Dubu Dari.Goggo ta kawo min tace Dubu Hamsin ya'yan Dakinta suka hada'min Dubu Hamsin yan'uwana Yaya Asiya da Yaya Mariya har da Hafsatu ta saka Dubu Biyar kunsan na fada muku tana kunshi kuma Sosai take da mutane. Kuka ya gocemin na karb'i kudin ina Fadin"Duk ni kad'ai Goggo.? Goggo tace"Duk Fa'iza ita kad'ai yar gatan Mutanen karofi sun ce ki kara jari.Allah ya sanya ma wannan sana'ar da zaki fara albarka" Na amsa da Ameen ina zuba musu Godiya ni muna Dakina ne ni da Goggo shi kuma Yaya isa yana falo shi da su Amir. Sai da muka fito domin muji shawaran Yaya Isa kan abunda za'a siya,Goggo ta lura da Farhan ta tambayeni waye nagayamata sai ta rike baki tana fadin"Ikon Allah girman dan mutum ba wuya.." Ta daukesa Dayake ba shi da kiwuya sai Dariya yake mata Goggo na shirin mgana sai ga Yaya Ishaq ya shigo falon da farko yayi mamakin ganin su Goggo, Daga baya sai ya basar ya kariso suka gaisa da Isa. ya kuma gaida Goggo sannan ya shige shashensa Goggo ta kalleni tana Fadin"Har amaryan nasa na gidan kenan..? Nace"Eh tana ciki ko zamu je ku gaisa ne.goggo itama aiki akayi mata aka cire tsakuwar ciki fa" Goggo bata damu da cewa bai taba kai mata Zainab ba,tace min sai mu shiga ta Dubata kafin mu wuce yanzu dai mu fara abunda ya kawomu. Su Anum na fattaka zuwa Waje Farhan ya sauka a hannun Goggo ya Bisu duka kudin na zube ma Yaya Isa bayan nayi mai godiya sannan nace"Yaya isa ni dai a siyamin babban Fridge saboda zan fara gwada zobon da kunin ayan nagani" Yaya isa yace"Hakan shine Daidai ne Nayi mgana da wani abokina suna kawo su masu kyau daga Parthercourt, kayan suna jirgin ruwa sun kusa isowa yanzu abunda za'ayi zan tura masa kudin fridge din da katon sitafileza,Tunda kuna samun wuta basai kin had'a da injin ba. Sauran kudin kuma sai ki rike a Hannunki saboda siyan abubuwan hadin da zaki fara sana'ar da shi ko ya kuka gani..? Goggo ta jinjina kai kafin yace"Hakan ma yayi.Allah yasa zata fara cikin nasara" Muka amsa mata da Ameen nan take ya kira abokin nasa sukayi mgana yace a turamai dubu Dari da Hamsin dubu hansim sai na rike a Hannuna,Muna cikin mganar sai ga Yaya Ishaq ya fito ya sake fita ko sannu bai ce mana ba, muma ba wanda ya kara bi ta kansa, kamar yadda bai taba tambayata ba nima ban taba Tunanin na fadamai komai a kan abunda na je na koya ba Da gaske nake yi na zab'i Rayuwata da rayuwar ya'yana sama da nashi muradin. Bayan Yaya isa ya cire kudin sai ya bani Dubu Hamsin a hannuna,sannan suka yi shirin tafiya har Goggo ta manta na tuna mata na rakata har Shashen Yaya ishaq,Zainab din na ciki ni na leka nayi mata mgana ta fito tana mika nace mata Goggon mu ce tazo Daga chan karofi, bayan sun gaisa Goggo ta mata sannu da jiki ta amsa tana kallonta Lokaci d'aya tana kallona kafin tace"Ammh suna kama da Momyn kano sosai Maman Amir" Sai nayi Dariya kafin nace"Eh kanwartace fa Goggon" Sai ta rike baki tana fadin Honey bai taba min mganarta ba.Dagani har Goggo yake mukayi mun kasa bata amsa,Tana tambayana yadda muke nace mata da goggo da Momnyn kano da Mahaifin su Yaya ishaq da mahaifin mu Uban su d'aya,Ta jinjina kai cikin karin mamaki daga gani bata san wani abun ba sai abunda aka nemi ta sani kawai ta sani bamu jima ba Goggo ta mata sallama muka fito ta Daura After dress saman kayanta ta fito anan ne ma Yaya isa ya taba ganinta suka gaisa nace mata Babban yaron Goggo ne ta jinjina kai tana fadin"Suna yana yi da Honey" Sai da ta fad'a na kara kallon Yaya isa naga suna da'n dibar kama kamar yadda ta fada d'in. Mun rabu da su Goggo kan sai an kawo Fridge din Yaya isa zai kawo min Goggo tace na aika makotan mu na kusa nace zan fara saida Zobo da kunun aya da ruwa, saboda na samu masu siya aiko ban zauna ba su Goggo na tafiya na zari Hijabi nace ma zainab zan fita yaran kuma sukace sai sun bini Amir ne kad'ai ya zauna a gida haka na tasa har da Farhan gidan Sa'adatu na fara shiga na isketa tana yin shasshaka,kusan yara da Rigima su Anum suka saka Rigiman sai sun ci ina zare musu ido tayi dariya kafin tace"Kaji maman Amir kina zare ma yara ido ku zauna a gama sai kuci" Dariya kawai nayi ta mana shimfidar Tabarma a tsakar gida Farhan ta Dauka tana fadin"Basu koma ba kenan..?.Sai na Daga mata kai, Saboda ranar ta shigo taga zainab din sun gaisa sai a ranar tasan ma ina da Abokiyar zama,domin ko a hira ban Fad'a mata ba. Tana aikinta muna Taba hira cikin Hiran nan ne nake gayamata sana'ar da zan fara tayi murna cikin Murnan ne take fadin"Aiko zan aika miki kusa damu ana siya fa a baya, chan gidan akwai matar da ta zauna tayi sana'ar kuma wlh tana samun ciniki da kuma suka bar anguwan sai ba wanda ya kama gashi muna samun Wuta sosai za'a siya in sha Allahu" A fili na furta Allah yasa daga shiga na gayamata sai ga shi na shantake ba yara ba nima sai da ta zubo mana Shasshakan muka ci da manja da yaji. sannan na Tarkata su muka koma gida Yaya Ishaq da Zainab na Falo suna cin gashashiyar kaza, yaran suka nufesu ni kuma nayi dakina Zainab ce kad'ai tamin mgana Gogan kuwa ko kai bai ma Dago ba.ni ko a jikina nasan yana mamakina ya Dauka irin da ne da zan rika binsa jikina na bari yana min wulakanci,Sai dai yanzu shi kanshi yasan takun ya sauya. Sati biyu suka yi a katsina suka koma Abuja,har na fara sabo da