Sashe 126
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
acikinta sai zallar bakinciki sannan nace"In dai Saboda kalaman Baba ne kada ka damu Bazai kamaka da Laifi ba ko da yana raye domin ba'a so dole, sannan ba'a aure Dole. Maganar yara kuma Kai ne Uban su kuma Dolen su. ni kuma nan ne ya Dace dani kayi hakuri ka rike su domin bazan bika ba,mganar matarka kuma ta zauna mana ai daman bani na aurota ba, kai ne mijinta kuma kana Tare da ita daman kuma bamu taba zama waje d'aya da ita ba. ballatana Domin bani ya zama abun damuwa,masu kular muku da yara kuma akwai ma'aikata a gari in kuka nema zaku samu in sha Allahu" Na fad'a ina kokarin maida kwallan dake neman ziraromin,kowa sai mamaki ya cikasu na mganganun mu daga wannan ya kalleni sai wannan ya kalleshi Inno ta gyara zama ganin Abba ya kasa mgana cikin muryan data kwana Biyu tace"Kai mu duk bamu gane kan mganganin ku ba .Ku Bude baki kuyi mana mgana yadda zamu gano bakin zaren kai Usman ka yi musu mgana mana" Abba ya sauke Numfashi kafin ya kalleni yana bude baki yace"Fa'iza..". Ban bari ya cigaba da mgana ba ina kallon Ishaq nace"Abba shi zaka tambaya in dai bai yi mgana ba nima bazan yi ba. Saboda ina so na cigaba da yimasa adalci da ya rokeni nayi masa Tun a baya" Ina mgana ina kuka muryata na Sauyawa sai Abba ya maida kallon kansa sai zufa yake yi duk da Fanka sama data kasa dake aiki a Falon da ka gansa kasan ba gaskiya, bai taba zaton zan iya dawo da wannan mganar ba na Shammacesa. Abba ya kira sunansa ya amsa yana Rawan baki Abba mamaki ya kamasa sai dai bai nuna ba cikin Sanyi yace"Kaji abunda Fa'iza tace..?shin zaka iya yi mana bayani ne yadda zamu gane? Ko kuwa zaku cigaba da wasa da Hankalin mu ne..? Sai Ishaq ya fara share zufa da Farin Hanky din dake hannunsa ya Juya yana zare ido suka Had'a ido da Mama wacce ta kauda kai da Sauri ta kasa kallonsa ya dawo da kallonsa kaina ya kasa zama kansa na kan kafafunsa Cikin rawan murya yace"Plz Fa'iza ki bar wannan mganar mana" Nima kai tsaye nace"Zan bar ta kad'ai ne in ka sahalemin auran ka Ishaq" Marairewa ya kara yi kafin ya kalli Abba yana Fadin"Abba ka bani minti goma kacal mu yi mgana ni da Fa'iza" Har zai yi mgana Goggo tace"A baya da baku fallasa mana abunda ke Faruwa ba,ba wanda yaso yaji ammh yanzu tunda kuka fallasa a gaban kowa da kowa zaku yi mganar daga yau koma menene muna so mu ji kuma mu sani" Tafad'a tana kallona ina Kuka haka kurum taji duk abunda yasa Fa'iza mgana abu ne mai taurin da jinsa sai ya Girgiza zukata,kuma ta fi kowa sanin zaman hakurin da Fa'iza tayi a gidan Ishaq mganar ta yasa Inno da Baba Ati suka ce ya yi mganar nan kowa yaji ai Sulhu ake nema Abba ya kalli Ishaq ganin yadda yake rawan jiki yasa ya Dafa kafad'ansa yana Fadin"Kada ka damu ni ba Uba kad'ai nake ga Fa'iza ba. Har da kai,in ita ke da Laifi wlh da kaina zan tasata sai Dakinta bazata kara kwana a garin nan ba" Jin kalaman Abba yasa sai ya fara samun natsuwa yana Hango adalci a mganar Abba Cikin ajiyar rai ya koma ya zauna yana Fadin"Abba ku yafemin kuskure ne na aikata cikin Rashin Sani ammh wlh nayi nadama Tuni kuma naba Fa'iza Hakuri tace ta yafemin ban san me yasa ta kuma Dawo da mganar data wuce ba" Da sauri nace"Saboda itace mafarin duka al'amura. mganar yafiya kuma na Jima da fad'amaka na yafe maka Duniya da Lahira" Abba sai ya koma ya kalleni ya kallesa kansa ya Daure,da yasa ya kasa mgana Shuru falon ya Dauka Kafin Inno tace"Muna jin ka Isiyaku" Ya dago yana kallon Inno ga Tsoro ga Takaicin sunan da ta kirasa da shi ya Tabbata in bai yi mgana ba,ba mafita ammh kuma yana ji ajikinsa Abba zai Fahimcesa Mama ko Jikinta nata rawa,kunya duk ya kamata bata Fatan Fa'iza ta fad'i musgunawanta gareta duk da taga irin kallon da Goggo ke jifanta da shi ji take kamar ta tashi ta Fita sai dai ba Dama. Kamar Daga sama taji Ishaq na Fadin"Wato Abba..Lokacin da zan kara aure ne..Sai sai na ce ma Fa'iza..Mu mu.." Ya kasa karisawa Saboda kunya da nauyin mganar Abba ya kuramai ido yana Fadin"Uhm ina jin ka" Ishaq ya Runtse ido kafin yayi gundinbalan fad'in"Nace ma Fa'iza zamu jingine auran mu ni da ita" Gabad'aya sai Falon ya Dau shuru kamar Mutuwa ta gifta ni ko kamar a Lokacin yake min mgana Hawaye wasu na korar wani a saman Fuskata. Goggo cikin mamaki tace"Wani irin jingina kuma..? Inno ta karb'e da Fadin"Ni kaina na kasa ganewa fa" Mallam mijin goggo da sai a lokacin yayi mgana cikin kallon Ishaq yace"jinginar aure kala kala ne Ishaq, kayi mana bayanin wata irin jingina ce ka nemi ku yi ma auran ku kai da Fa'iza? Ishaq kansa na kasa ya Dago yana kallon Mama itama shi take kallo Cikin mamakin kalamansa kafin ya Sadda kansa domin ya kasa kallon Abba cikin rawam murya yace"na nemi alfarman Fa'iza kan mu jingine auran mu, ba mu'amalan miji da mata a tsakanin mu ,ba wani hulda ta ma'aurata Tsakanina da ita,sai dai kawai ta zauna ta cigaba da kularmin da ya'yana" Yana Dire mganarsa sai gabad'aya su Inno suka Dauki Salati suka Dire Baba Ati tace"Lalle lamarin Babba ne" Ni ko hawaye kawai na bari suna zobomin da mirmishin da ke saman Fuska sai dai a alokacin in za'a tona Zuciyata kamar zata fashe saboda bakinciki da kunci. Abba ya kasa mgana Saboda Takaici Goggo tace"Wannan mganar sharia"a ce ta ila'i dole muna bukatar malaman da zasu yi mana fashin baki kan wannan al'amarin" Da Sauri Mallam ya jefomasa tambaya da cewa"Har na tsawon wata nawa ka di'bar ma wannan jinginar? Ba zato kawai sukaji Muryata a Kausashe ina Fadin"Har na Tsawon Shekaru bakwai. Shekaru bakwai da Doriya Mallam" Gabad'aya sai suka had'a bakin wajen Fadin"Shekaru bakwai fa kika ce Fa'iza..? Ina kuka na jinjina kai kafin nace"Iya shekarun da nagaji ne na nemi mafita ammh Jinginarsa gareni ta har Abada Saboda baya kaunar kara Had'a zuru'a dani bana haifa masa ya'ya Daidai da Burinsa,tunda bazai iya sakina Saboda kalaman Baba akansa ba,sai ya Zabi ya jingine ni tunda zai auro wacce tayi daidai da Ra'ayin sa kuma wacce zata Haifa masa ya'ya farare kyawawa daidai da ra'ayin sa Shekaru sama da bakwai na kwashe Cikin kunci da bakinciki bayan wad'anda na kwashe a baya Abba ka gayamin nayi Laifi domin na nemi da ya Sauwakemin..?ba aikin da ya fara na nemi ya karishe ba..? Na fad'a ina kallon Abba Hawaye kamar ana tunkudo su haka suke zubomin Abba yaji jijiyoyin kansa na tashi,Saboda bacin rai ya kalli Ishaq yafi sau uku shi kuma kansa na kasa su Inno jikinsu duk yayi sanyi Ammi ko har tana tayani kuka. Abba ya kalleni ina kuka Tsausayina ya kamashi,ya rikoni gefen kafadarsa yana Lallashina jina acikin jikinsa yasa na barke da kukan da shekaru sama da goma ina neman Kafad'an da zan kwanta nayi wannan kukan ban samu ba sai yau sai kawai suka ji muryanta na saki kukana da Dukkan Karfin zuciyata sai Ran Abba ya kara baci ya Dago Cikin Fushi yana kallon Mama cikin Tsawa yace"Da Sanin ki D'anki ya jingine auran yata shine baki yi komai a kai ba..? Jikin Mama na rawa zatayi mgana da Sauri nayi Wuf na tashi daga kafad'an Abba cikin kuka nace"Bata sani ba Abba. Dagani sai shi ne muka sani.." Abba ya dakamin Tsawa nima kafin yace"Meyasa baki fad'ama kowa ba..? Tunda Lokacin bana nan meyasa baki zo kin Fad'ama Goggon ku ba..? Kuka na kara sawa ina Fadin"Ya zan yi Abba..?yace nayi masa adalci da ya shekara takwas yana min na aurena a yadda nake ya zauna dani. to nima ya Roki da nayi masa adalci na barsa yayi Rayuwarsa da amaryansa Abba ina son na zauna da ya'yana Wlh Sabo da su ne. Sannan alokacin bana so na Dorama kowa nauyina Abba Shiyasa ban taba Fad'ama kowa ba" Na karishe Fad'a ina kuka gaban Hijabina ya jike da kuka. Abba sai sakin Huci yake yi yana kallon Ishaq da ya gama Tsurewa Mallam ya yi gyaram murya kafin yayi mgana Goggo ta rigasa da Fadin"Tabbas nasan Fa'iza bata ji dadin zama da Ishaq ba .bata da mutumci a idon sa da shi da Mahaifiyarsa da yayarsa, ni shaida ce ba irin cin kashin da basa mata Har ni kaina da ya'yana bamu Tsira ba Saboda ina kaunar Fa'iza" Abba kamar zai dagi Goggo yace"Kuma kuka kasa Raba auran dake cike da Zalunci Goggon su.? Sai Goggo ta saka kuka tana Fadin"Ya zamu yi Alhaji..?ina tausaya ma Fa'iza ina Tausaya yaran nan nata Sannan ita bata mgana ko yan'uwanta su yi tambayan duniyan nan bata Fad'a musu komai, sai dai tayi shuru bakincikin na cinta,sai dai muga tana ta rama da kamjamewa" Ta karishe fad'a cikin kuka,Abba ransa ya kara baci ya mike a fusace cikin Fusata yace"To ana aure Dole ne..?meyasa aka bashi auranta tunda baya sonta..? Mallam ne yayi mgana cikin lallashi yana fadin"Alhaji koma ka zauna ayi mganar nan a tsanake" Sai da inno ta kara mgana sannan ya zauna yana Huci,Kukan Fa'iza na soya masa rai Mama ma kukan datake yi ya sa kowa ya maida Hankalin kanta. Cikin kuka tace"Alhaji ku yi hakuri wlh ban san da wannan mganar ba,Ishaq bai gayamin ba sannan ita kanta Fa'iza bata gayamin ba. abu daya na sani a baya na musguna ma Fa'iza ina kuma neman afuwarta data yafemin" Ta fad'a tana share kwallah da Haban zaninta Abba kyafci yayi kawai ransa na Cigaba da kuna sai kiran wayarsa ake yi yana Kashewa baya son mgana ma alokacin Saboda yadda ransa ke kuna Ishaq ko motsi ya kasa Saboda Fargaba da yadda yaji muryan Abba cikin zafi da kaushi. Mallam ya gyara zama yana Fadin"Duk ba wannan ba ne Alhaji. A kokacrin Alhaji kabiru shine namiji babba ga su Fatima da Aisha