Sashe 32
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shigowa Dubani har da Habiba ina ta mata godiya tace bakomai wlh.. Har yammah tana tare dani sai da su Amir suka dawo makaranta sannan ta koma gida bayan har wanka sai da ta tsaya nayi na sauya kaya naci abinci dakyar na sakata ta D'iba abincin da ta Dafa tatafi da shi su Amir sun yi murna da ganina motsi kad'an sai Amir yace"Sannu Umma Allah ya baki lafiya' Sai na amsa mai da Ameen Amir su Anum kuma ba wayau suna ta wasan su sai dai sun yi murnan ganina Ahmad kuma saboda kwana Biyu bai sha Nono ba,sai ya manta da shi,Sai dai Habiba tace ya sha Rigima kunu take Damawa tana bashi,ya lafe a jikina yayi shuru Tausayin sa ya kamani na Rumgumesa ina jin kamar na fashe da kuka kwana biyu ne bana nan ammh ya'yana ma sai makota ne suka kula da su inaga in ba na tare da su gabad'aya Allah kad'ai yasan wani Hali zasu shiga shiyasa zan Daure zan kuma Jajirce saboda goben su Washegari da muka Dawo gida ma Tun Safe sa'adatu ta shigo ita ta shirya yaran tayi musu kari dayake ita bata taba Haihuwa ba,bayan sun tafi makaranta tazo ta gyaran gidan,ta koma gida chan anjuma kuma tadawo tayi ma yara girki nasan ko bata fada ba aranta tana so ta tambayeni bani da Dangi ne..? Ai rashin gatan yayi yawa sai dai bata ce min ba nima ban ce mata ba. Kwana na Hudu da dawowa asibiti na ji sauki Nace sa'adatu ta daina zuwa tana min wahala na samu lafiya,Ranar har gidan Habiba sai da na shiga na kara yimata godiya sai dai duk wanda yaganni yasan na rame duk na kara Lalacewa. Sati daya da faruwar abun Badariya tazo Dubani tana bani Hakurin bata sani ba sai abakin Halisa taji har asibiti na kwanta,ta yinin mu sai yammah da Halisa tazo dubani suka tafi tare,Ita ce ma suna mgana da Hafsah ta wayar Goggo ta fad'amata nayi ciwo har asibiti na kwanta ashe su Hafsah suna kano Yaya Asiya ce ta Haihu,suna kano shekaranjiya akayi suna Hafsa ke fad'ama Goggo tana ta Fadan ba wanda ya fadamata ballatana sauran yan'uwana kuma suna ta kiran wayata a kashe basu san ta Lalace ba.. Ranar laraba da Safe sai ga su A gidana Daga kanon suke Yaya Isan goggo yaje ya Dauko su a motarsa,Goggo ce sai Anty Nasara da Yaya mariya sai Hafsatu sai matar Isa Amina,sun zo sun ganni suna ta tafad'a gani na duk na fad'a na rame Goggo ta kalleni tana fadin"In wayarki ta lalace baki aron wata wayar makota ki kiramu Fa'iza"? Kaina na kasa nace"Goggo ban da lambar kowa a kaina kuma layin yana gida" Anty Nasara tace"to wa ya zauna dake..? Kaina na kasa tace"Matar makocin mu haruna mai kai su Amir makaranta" Su Goggo suka saka salati suka Dire,Yaya mariya tace"Daman wa kuke tunanin zai zauna da ita..? Mama ko Binta..?azzalumai bakomai a zuciyar su sai mugunta ayi dai mu gani" Goggo ta juya tana kallonta Lokaci daya tana fadin"Mariya..mariya ana rabaki da kiwon awaki kina fadin kyalla ta Haihu daga Saudatun har Binta ai ba sa'anki ko.? Yaya mariya ta tura baki kafin tace"Ai gaskiya na fada goggo wlh wani Hisabin sai a lahira kalli yadda Fa"iza ta koma kamar wata yar aiki kalli gidanta kalli kujerun ta duk sun Fita Hayyacin su kuma wai wannan mai kudi take aure Allah dai ya waddan kudin miji in dai na irin mijin Fa'iza ne bashi da amfani ko ni da mijina karamin ma'aikaci ne wlh d'akina yafi na Fa'iza kyau sau dubu Saba'in wlh" Anty Nasara na gefe ta kad'a baki tace"Ai ba gidan ne ya fita Hayyacinsa ba..ita kanta Fa'izan ku dubeta ku gani yadda duk ta fita kammaninta" Fadin haka yasa duk suka sakamin ido suna karemin kallo Goggo tace"Duk kubar mganar nan mganar kayan daki zamu sauya mata in sha Allahu ai mune yan'uwanta Dolenta na kanmu Ishaq ba wajibinsa ba ne yayi ma Fa'iza komai ba" Yaya mariya ta kad'a baki tace"ammh ai yana da shi..kuma bai gagaresa ba in da mutumci a wahalan da Fa"iza tayi da shi da danginsa ta chanchanci komai a wajensa" Goggo tayi saurin tare mganar da kallona tana fadin"Fa'iza wannan ramar tayi yawa me ke damun ki ne..? Sai nayi shuru na kasa mgana nasan in nace Hawan jini gareni na bude Sabon Shafi sai nayi kamar ban ji ba Sai da goggo ta kara mgana Sannan na ce mata Zazzabin cizon Sauro ne. Goggo nata fad'an ko bana kunna mganin Sauro ne ni dai nayi shuru ban ce komai ba. Hafsatu tayi girki Yaya mariya kuma ta ragemin wankin su Amir,daman sun taru Aminan isa kuma ta gyara Falon da Dakunan. Bayan sun ci abinci sun yi sallar azahar na saka Hafsatu ta shiga da su gidan Sa'adatu suka yi mata godiya daganan nace suce ta kai su gidan Habiba itama suka mata godiya sukace bakomai ai yiwa kai ne. Muna tare da su har La'asar akace Dan'uwa mai dadi naji Dadi sosai Yaya mariya ta nuna min Yaya asiya da D'anta a waya hoton da suka Dauka Ranar suna tasha kyau abunta sunan yaron Muhammad Auwal. Sai bayan La'asar suka yi shirin Tafiya,Yaya Isa daman ya shiga cikin gari ne sai ga shi ya Dawo Hafsatu ta sakamai abinci da yake tana fashin Sallah tana falo Aminan Isa da Anty Nasara na Dakina suna sallah ni kuma ina Dakin su Amir ina sallah da ni da Yaya mariya Ahmad na goye a bayan Goggo Tun da ya fara rigima ta karbesa ta goyasa. Ni dai na idar da sallah ina zaune ina azkar Sai naji mgana sama sama afalo Yaya mariya ta tashi ta fita,ba jimawa sai ga Hafsatu ta leko tace Goggo na kira na,Ina fitowa nagan su Tsaye sun yi cirko cirko gabana ya fad'i na zata ma wani abu ne,Goggo ta kalleni da Kwalin mganina a hannunta kafin tace"Ashe Fa'iza hawan jini gareki kikace mana wai zazzabin cizon sauro ne..? Sai na kasa mgana na Dukar da kaina Yaya mariya ta yi kyafci kafin tace"ai bazata fad'a miki ba Goggo..Na rasa me Ishaq ya bama Fa'iza ya shanyeta bata kaunar Laifinsa daga shi har Danginsa" Goggo ta kalleni ta kara kallo na kafin ta saka salati tana fadin"Na shige su ni Indo..Yanzu da ba domin Nasara taga mganin nan kuma tasan ko na menene ba da haka zata bar mu a matsayin Maleria ke damunta haba wannan ramar na Fa'iza ya yi wa ashe ashe Hawan jini gareta da kananun shekarunta" Yaya Isa na gefe yayi karamin Tsaki kafin yace"Ba Dole ta kamu da Hawan jini ba Goggo..An aura mata wanda baisan Darajanta ba..Ina jin Labarin zaman Hakurin da yarinyar nan ke yi ku kuma su goggo kun kasa D'aukan mataki akan haka ai aure ba Bauta ba ne ibadan ubangiji ne ba na abokin Hallita ba..Ya maida matarsa kamar wata yar aiki ko baiwa yana chan Abuja ya tare sai yaga Dama yake zuwa Fisabillahi wannan adalci ne..? Goggo tayi saurin tare shi da Fadin"Mijinta ne ya fi mu iko da ita..Sannan zaman aure ai zaman hakuri ne,Kuma ibada take yi Isa kada kace bamu Dauki mataki ba in ba so kake mu kashe mata aure ba" Yaya mariya tayi karaf tace"Wlh Goggo da auran Fa'iza dai gwara zawarci" Goggo ta aika mata da Dakuwa tana Fadin"Ya'yan nata fa ke zaki rike mata su in ta fice ta barsu da kananun shekaru..? Yaya mariya ta tura baki kafin tace"Su zauna gidan Uban su mana Goggo" Goggo tayi dariyan takaici kafin tace"Kayya mariya ai rikon ya'yan wani ba kowa zai iya ba sai wanda Allah ya bama wannan..Sannan kuma ya'ya sai uwar su mariya..Yanzu dai Allah ya kyauta..Tunda abun ya zama haka Mariya in ba Damuwa ki kara kwana ko zuwa gobe jibi in megidan naki zai bari lokacin ta kara watsakewa kinga Hafsatu suna da makaranta" Yaya mariya tace"Bakomai da na kirasa bazai ce komai ba su Abba kuma suna gidan kakkaninsu daman." Goggo ta kalleni tana fadin"Ga mariya nan zata zauna ta kara taimaka miki zuwa jibi ni kuma zan tafi da Ahmad tunda kin yayesa in kika ji Sauki kika warke sai na Dawo miki dashi" Ban iya ma Goggo musu ba na tafi na Had'o kayan Ahmad na bata,Nasan tayi hakane saboda ta ragemin wahala sannan duk da ina jin Tsoron me zai biyo baya,ammh bazan iya ce ma Goggo A'a ba saboda ita kamar makwafin Tamadina ne a wajena duk da tana raye. Ya Isa nata fad'a Goggo bata Biye masa ba Ta lallasheni tare da kara Jadaddamin nayi hakuri watarana sai Labari Goggo ta bani dubi biyar Ya Isa dubu uku kafin su tafi,Suka barni da Yaya mariya ta tasani tana ta min Fad'a wai na zauna na zama sakarya miji da Danginsa suna yadda suka ga Dama dani ni dai ban ce mata komai ba sanin Halinta. Da yammah ko da su Amir suka Dawo basu ga Ahmad ba,na fad'a musu Goggo tazo ta tafi da shi suka fara Tsallen suma Yaya mariya ta tafi da su ta kyabe baki kafin tace"Wannan uban naku mai bakin hali ai bazai bari ku rabemu ba duk dai abun su bai isa ya sauya ma Tuwo suna ba" Ban tab'a kawo ma raina Ya ishaq zai iya Dawowa ba sai ga shi washegari da yammah ya Diro dirowan bazata yayi mana Muna falo ni da yaya mariya,ita wayarta take latswa ni kuma ina kwance kan kujera mai zaman mutun uku duk da naji Sauki ammh jikina ba karfi su Amir na makaranta basu dawo ba. Ko sallama ma bai yi ba sai da ya shigo Falon kuma da Yaya mariya ya fara cin karo suka yi ma juna kallo daya suka Dauke kai ni kuma jikina na rawa na tashi zaune ina gyara Wuyan rigana cikin rawan jiki da na zuciya nace"San..nnu..da zuwa.." Wani irin kallon da ya bini da shi yasa Hantar Cikina ta kad'a na fara maimaita innalillahi acikin raina ko amsani bai yi ba kamar Hadari haka ya shige shashensa ya Banko kofa. Na dago na kalli Yaya mariya sai tayi kamar bata ganni ba ta mike