Sashe 23
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dadaddare bayan mun gama sallar isha'i suna zaune suna aikin makaranta da aka basu Amir na taya mutsy nayi na shi Dayake shi yana primary 1 ne Anum Nursey 2 take Musty kuma Nursey 1 ni ban yi boko ba,ban san komai a bangaran su ba sai dai ina gane wasu abubuwa na y'an Nursey,iyakata da su bangaran islamiya da Hadda da karatun Qur'ani da azkar wannan bangaran ban yi waasa da shi ba,shi na iya shi kuma zan koyama ya'yana. Anum ce ta kara tambayata Daada sai nace mata ya kusa Dawowa Amir ya Dago kansa yana fadin"Umma Daada wata Umman ya samo mana achan Abuja..? Mamakin sa ya karamani na kallesa na kasa mgana Amir tun yana Shekara Biyu da wattani ya fara mgana yaro me mai wayau sosai cikin Mganata nace'wa..ya fada maka..? Kai tsaye yace min"Uncle Jamal..Ba mun je har chan ba..Umma naga Daada yaci gayu sosai" Daganan ban kara mgana ba ina jin Anum na girgizani tana fadin"Umma da gaske ne..? Musty na tayata da gwarancinsa,Dakyar na iya bude baki na amsa musu da hakane sai kawai suka fara Murna Anum kenan Amir kuma bai tashi ba Musty kuma ganin ta mike tana Tsalle shima ya mike yana Tayata Ahmad na jikina ya lafe ba barci yake yi jikinsa ne ba Dad'i zawon hakori sannan ba kudi ballatana na kaishi asibiti. Amir ne ya kalkeni kafin yace"Umma to ta na ina ita Sabuwar Umman tamu..? Kai tsaye nace"Tana tare da Daadan ku achan Amir" Cikin mganarsa ta kuruciya yace"Umma to me yasa Muma Daada bai tafi damu dake gabad'aya mu zauna achan ba? Mirmishi nayi wanda yafi kuka ciwo kafin nace"Watarana zamu je Amir in sha Allahu" Zai kara mgana nace su cigaba da aikin da aka basu a makaranta Anum kuma sai ta koma wasa da musty ni kuma sai na zurfafa cikin Tunanin haka rayuwa zata cigaba da tafiya har yara sun fara gane wani abum..?.akwai nan gaba akwai matsala in dai abubuwa suka cigaba da Tafiya a yadda suka faro. Ranar da Ya Ishaq ya cika kwana Talatin a abuja,ranar jumma'a da yammh sai ga Anty Binta batagwara tazo nayi mamakin zuwanta ammh ban nuna ba naje na Debo mata ruwa mai sanyi da nakan diba na saka a fridge saboda ruwan ledan ya kare na famfo muke sha. A wani karamin jug na dibo mata na Hado mata da karamin kofi na koma ma zauna a kasa ina gaisheta Amir da Anum suna Haraba suna wasa Musty kuma ya kwanta Ahmad ne ke goye a bayana. Ina gaisheta a wulakance ta amsa tana kallona da ni da Falon sama da kasa tana wani yamutsan fuska kamar taga kashi ruwan da na kawo mata ta kallah kafin tace"Wannan ruwan fa..?ba ku da na Gora ne..? Cikin Ladabi nace"Ya kare wannan na famfo ne nake sakawa a Firij Saboda yayi sanyi" Baki ta tabe kafin tace"Shi ne kuma D'an pure water bazaki iya siya ba komai kina jiran sai bawan ki yazo ya siya miki,ko ke irin Dubarun nan na mata da suke yi na taimakon mazajen su baki iya ba sai dai komai ki kwanta Shi d'an wahalan yayi miki ko..? Na kasa Dagowa ma in kalleta da karfi take mganar shiyasa na ji ta sosai duk da ba duka ba. ina jin ta har ta gama cin mutumcinta ban iya Dagowa ba,Sai chan ta mike tana zagayen falon tana leka Dakunan ta Dawo tana fadin"Gaskiyan Ishaq ne da yace gwara nazo na duba kada ya kawo Amaryansa yaji kunya..Ji yadda kika lalata ko'ina na gidan nan Fa'iza..? Tsiyan a kawo wacce bata dace da irin gidan nan ba kenan ba sanin Darajan sa kika yi ballatana ki Lura da shi" Taja karamin tsaki kafin ta koma ta zauna kafa kan d'aya ta Dauko Jakarta ta Ciro wayarta ta yi Danne danne ta kara kunne ina ji tana mgana ban ji me take fadi ba Daga karshe dai naji tace"kada ka damu ai zan ja mata kunne in ta yi ba Daidai ka dauki mataki a kanta" Daga haka ta Datse kiran ta kuramin ido kafin ta daga murya tana fadin"Ke wai baki da aiki sai goye ne..? Kaina na kasa nace"Ba ba shi da lafiya ne..". Baki ta tabe kafin tace"Uhm..Kina ji..? Tafada har da rike kunnewanta na Dago kaina ina kallonta na gyada mata Tsawa ta dakamin tsawa tana fadin"Matso kusa dani domin bazan iya Ihu ba ina mgana" Dole na ja jikina kusa da ita kunnena ta kama guda d'aya ta rike tana fadin"Abunda nake so na gaya miki shi ne..Gobe Ishaq zai zo shi da Zainab kuma nan zai sauketa da farko yace gidan Mama saboda yasan Halin ki kada ki basa kunya ni nace nan zai sauketa tunda tasan yana da gida har da Mata da ya'ya Saboda haka gargad'i na Farko shine zaki gyara gidan ko'ina yayi fes sannan ki shiga shashensa ki gyara ko"ina nan Zainab zata sauka har ta gama kwanakinta ta koma" Ta fada cikin daga murya Lokaci d'aya tana kara jan kunnina zafi nake ji ammh na Daure na kasa nuna mata Raunina cikin kara rike kunnina tace"gargadi na gaba shine ki kama kanki kin dai san ba D'aya kuke ba..Zainab yar boko ce sannan yar gatace gaba da baya ki kula sosai ki Tsaya iya matsayinki ki karbeta hannun Biyu ki mata Hidima duk abunda tace tana so ki yi mata kada kice zaki yi gaddama zaman ki lafiya shine Zainab ta koma Abuja ba bu abunda ya faru Ishaq yace na Fad'a miki kada ki kunyata sa agabanta yasan Halin ki baki da Tunani wani Lokacin kina jina ko..? Idanuwa sun kawo ruwa ammh sai na maida su cikin Rawan murya nace"Eh..e..Naji" Sannan ta saki kunnena tana fadin"Sannan ki yi wanka ki d'an gyara jikin ki in tazo ta ganki wannan yarkace yarkacen shi zai kunyata sannan yaran nan suma ki yi musu wanka ki sanya musu kaya masu kyau kina jina ko..? Nan ma kai na gyada mata key din Shashen nasa ta ciro a jaka ta bani na saka Hannun Biyu na karba sannan ta kara da cewa"Zaki yi musu girken girken Tarba sosai yace tana son Sakwara da miyar agusi,Sannan ki yi mata kunun aya da Ferfesun kayan ciki,ki soya mata Naman kaza ki yi pepe dashi" Kaina na kasa ban dago ba nace"kayan abincin mu duka ya kare shinkafa kadai garemu" Bata Damu ba ta mike tana fadin"Daman ai kamar ya san zaki kawo korafin babu komai anjuma Jamal zai kawo miki Cefane..Wlh Tallahi Fa'iza in kika kuskuere mganata ki ka bamu kunya gaban Zainab sai kin Raina kanki ki kuma sani ki kara Sani matsayin ku ba D'aya ba Zainab yar gatace gaba da baya sannan yar boko ce mai kyau yar babban gida" Har Haraban gidan na rakata tana kara ja min kunni da kara Jaddamin matsayina sai naji ban damu ba Domin ko bata fada ba ban isa na Hada kaina da wacce suke kira da Zainab ba,na ganta a hoto na kuma san ruwa ai ba'asan kwando ba ne. Nayi kokarin yakice duk wani abu dake cikin raina Hankalina ya tafi kan Ahmad da Zazzabin jikinsa yayi zafi panadol na ruwa nake basa shima Sauran na Musty ne da yayi zazzabi kwanaki Ya Ishaq ya siyomin Hankalina duk ya tashi,ga shi yana ta zawo bani da pampers sai napkin nake yi mai kafin Safe ya bata kaya da yawa ina tashi da wankin na tashi,Sai da na gama tsabtace sa sannan na yi musu shirin Tafiya Hadda. Saboda bani da masaniyar sanda Bakin da zasu iso,Bayan tafiyar su sai ga Jamal ya kawo min cefane nake tambayansa ashe bai koma ba..? Sai yace min bai koma ba sai sati na sama shima ko zama bai yi ba yayi min sallama ya tafi. Sai da na fara zagewa na gyara Shashensa,tas na turara turaren wuta mai kamshi sannan na gyara Falon da Sauran Dakunan daidai yadda zan iya sannan na Fad'a Kichen Hankalina ya kwanta Ganin jikin Ahmad yayi sauki har ya samu barci. Cefane ne da yawa saboda bakuwa zata zo shiyasa aka siyo aka kawo har da Lemuka da ruwa kwai,Dankali Doya,Kayan lambu taliya macaroni da Buhun Shinkafa sai Couscouss,na Sauke komai a muhallinsa har da aya nagani Saboda ai Anty Binta tace Zainab nasan kunun aya. Banji kyashi ko mugunta ba na zage na fara aiki kan jiki kan karfi miyar Sakwaran na fara yi sannan nayi ferfesun kayan cikin araina ina jin Dadin Dalilinta yara ma zasu samu chanjin abinci. Na zuba a kololi na rufe naje nayi sallar azahar na zauna na Huta saboda ina Tunanin sai yammh zasu shigo,ashe ma sun zo garin gidan Mama suka fara sauka Badariya ta shiga makaranta sai ta Biyo ta iskeni ina makarda ayan a blander dina wacce Dakyar ma take yi tana yi ta na mutuwa ta tsufa duk taji jiki. Tana ta fadamin uban kayan da Zainab din ta kawo ma su Mama har da ita an zo mata da abaya ni dai sai dai yake na kasa cewa komai. Bata jima ba ban yi sakwara ba Ferfesun ta Diba taci sannan tayi sallah Tatafi jin sun iso yasa na mike na Cigaba da aikina kafin La'asar na gama komai hatta dakan sakwaran,nasha wahala sosai ga Ahmad a baya na ya tashi ya saka Rigima Dole na goyasa haka na yi ina yi ina Hutawa ina Haki,Kazan a karshe na Soyata kamar guda biyu ce ta Turawa sannan nayi pepe chicken na shirya komai na ijiye anan kichen din sannan naje nayi wanka na Sauya kaya na saka Atamfa ta riga da Sikat,ko Hoda ban shafa ba domin bani da ita,ban kuma ji ina son na Burge kowa ba sanin ko nayi bazan burge kowa ba. Karfe hudu daman nace Haruna yaje ya Dauko min su Amir,Shima din yana da Hakuri da Darajan makota wajen wata biyu Ya ishaq bai basa kudin sa,ina Tunanin ranar da yagaji ya daina kai su sai dai na kai su a kafa kuma akwai tazara mai yawa Tsakanin gidanmu da makarantar tasu. Suna Dawo na taya su suka cire kayan makaranta ko alama ban gaya musu Babansu zai dawo ba Na riga daman