← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 175

Sashe 50

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tayi mana dad'i" Sai ya k'ara kallona ya kuma kalli Farantin gabana cikin yamutsa Fuaka yace"Fa'iza meye wannan..? Naji sa ammh sai nayi kamar ban jiba. sai da ya kara Daga murya yana fadin"Nace meye wannan kika bama ya'yana Fa'iza..? Na dago kaina ido cikin ido nace"Fate ne" Saboda naga abun na sa kuma ya fara zama renin wayau faten ne bai sani ba..? Ya maimaita sunan fate a ransa da Fili kafin yace"Me kenan..?ina mikewa nace"Abinci ne shima.." Su Anum na kallah ina fadin"Kun koshi ne..?dukkan su suka d'agamin kai sai na nufi kitchen da shi nasan ya bini da kallo ammh ban ko waigo ba sai da na shiga na sauke abun hannuna na wanke hannuna na fito ina Fadin"kuje ku wanke hannuwan ku" Kamar suna jirana suka sauka da gudu zuwa Daki har da Ahmad shi kuma sai ya kalleni yana fadin"Ina miki mgana kina basar dani Fa'iza? A kaikace nace"na baka amsarka nace maka abinci ne" Sai ya kasa mgana sai chan yace"Baku da abinci ne a gidan sai kin basu wannan abun sun ci hannunsu sai wari yake yi" Sai ma ya bani Dariya na murmusa na gyara zama na akasan cafet din Falon ban yi mgana ba da kansa ya mike ya shiga kitchen din yaga bakomai Sai Dubaruna irin na mace mai ya'ya Shinkafa kad'ai ta rage mana itama ko Tiya bata kai ba,ba domin Goggo ta taimakeni ba da Tuni asirina ya Dad'e da Tonuwa a idon duniya domin tun da na dawo daga Rasuwar Tamadina k'waran abincin ban gani ba.tun Cefanen da yayi mana kafin ya tafi shima bamai yawa ba ne,ina jin ba shi da kudi a tare da shi ne lokacin. Ina ganinsa ya fito cikin wani yanayi ya kuma daga waya ya kira Mama naji yana mgana ammh Dayake ban maida Hankalina akansa ba ban ji me yake fad'i ba.tunanina na chan inda mafita ta take, da Tunanin yadda komai zai faru jibi,Har na kosa ma jibin yayi mu fara kamar na matso da jibin gobe haka nakeji zumud'i kawai nake ji akasan raina kamar nama iya komai haka nake ji. Sunana naji yana kira da karfi sannan na Dago ina kallonsa cikin Mganarsa yace"Wani banzar Dabi'a kika samu ina mgana kina ji na,kina yi min banza..? Kai tsaye nace"Kayi hakuri abun ka ga mara karjin ji sai hakuri" Sai ya kasa mgana,Bata rai yayi yana Hararata kafin yace"Na rasa wata irin mace ce ke Fa'iza..? Yanzu kayan abincin ku ya kare bazaki iya kiran Mama ki fad'a mata ba..?jamal baya gida yana makaranta ita nake turo ma kudin cefanan ku duk wata da kudin bukatun yara, ammh yanzu da nayi mata mgana tace bata zauna ba sannan bata san cefanen ya kare ba" Kallonsa kawai nayi na kasa mgana shi kuma sai ya cigaba da fad'a yana fadin"Badar na zuwa gidan nan fa ko ita bazaki aika wajen maman ba..?Ko ke bazaki shirya ki je ki gayamata ba..? Sai kawai nace"Kayi hakuri.." Saboda na datse mganar ganin yaran sun fito kowanne da Biskit da minti a Hannunsu,Shima jin abunda nace ne yasa sai ya kasa cigaba da tijararsa,Daganan sai hankalinsa ya koma kan yaran yana ta tambayan su abunda suke so suna fad'amai da labarin makaranta ni ko araina ina kara jinjina kaifin ikon Mama akan komai shi kayan abincin sai naje na Fad'amata ya kare kenan zata fidda kudin da ya turo mata ta siyan mana kenan..?kamar tana yi mana alfarma a raina daman na Guduri niyar ko zamu mutu da yunwa na gwammace duk mu mace da naje wajen Mama nace mata bamu da abinci. Tara nayi na tattara yaran suka je suka yi shirin barci suka kwanta Anum ma da Ahmad na kwantar da su akan gadona,Na fito falo zan d'an gyarasa tunda yaran duk sun zubar da Ledojin Biskit din a tsakar falon na iske sa Lafe kan kujera yana waya a hankali yake yi shiyasa ban jisa ba sai na shiga abunda ya fito dani bayan na gama zan koma Daki sai ya kwalamin kira na Dakata na juyo ina kallonsa a kishingid'e yake sai ya Dago yana fadin"Naga zaki shige ciki ni me zan ci..? Sai nayi shuru ban ce komai ba ya kara maimaita mganarsa ya karishe da fadin"ina jin yunwa kuma ban tsaya gidan mama naci abinci ba' Cikin yanayin mgana tace"Sai Faten in zaka sha..? Yadda yayi da fuska ne sai da naji kamar nayi dariya sai dai na kanne cikin kaushinsa yace"ki sama min wani abu" Ko bakomai yaci darajan Zumunci da ya'yan da suka had'amu sai na juya zuwa Kitchen ina fadin"Sai dai shinkafa ita kad'ai garemu" Ina jinsa ya mike yana fadin"Dafamin ki yi min source din miya tunda naga akwai kayan miya dare yayi ba na son na sake fita ne" A daran nan ma dafamai Shinkafa araina ina kallon gas d'ina ina godema Wutar nepa ba domin anguwar da muke ana barin wuta ba, da tuni na raina kaina Gas ne mai shidda,wanda ke amfani da Gas da Electric,basan shekara nawa na kwashe ina amfani da shi da wuta ba, tun Auran Ya Ishaq da Tarewansa a Abuja komai ya sauya,a baya yana mana Refliing ko ya aiko Jamal ya yi mana, ammh daga baya komai ya sauya sai da nayi da mai wuta,shi kuma baya da saurin girki,tunda bani da wata mafita hakanan nake hakuri da shi,Daman gas din Yaya Ishaq ya siya san da zamu dawo gidan. Har goma da wani abu sannan na gama na had'a komai na kai masa shashensa a falo na sauke mai komai yana ciki ko bari ya fito ban yi ba na koma Dakina nayi shirin kwanciya,na kwanta sai barci ban farka ba sai asuba,bayan na idar da sallah nayi ma yara shirin tafiya makaranta saboda yau Jumm'a ne basa dad'ewa sai basu je da Kwandon abinci ba sai ruwa da na Dura musu suna shirin fita su yi ma Haruna mgana sai ga shi ya fito yace zai kaisu suna ta tsallen murna. Shi ya kwashe shi suka fita ya kai su sai wajen goma ya shigo gidan,da amajirai guda biyu suna ta shigowa da kaya,kayan abinci ne ya siyo masu yawa har da Biskit din yara da Lemun su da ruwa har da kayan Tea wanda har yaran sun manta da shi sun saba da kunu har da su kwai kayan miya da kayan lambu,Dankalin Turawa da yawa haka ya siyo ina zaune ina karishe ma yaran guga afalo sannu da zuwa kawai nayi mai na juya na cigaba da aikin gabana har ya sallami yaran ya shige shashensa ya sake fitowa kayan na nan zube afalo ban kauda su ba cikin fad'a da bacin rai yace"Wai fa'iza wani salon iskanci kuma kika samo..? Na dago ina kallonsa ya cigaba da Fadin"nine kike nufin zan kwashe wad'anan kayan ko me kike nufi..? Ban ce komai ba na kashe soket din Abun gugan, na wuce na fara Daukan kayan ina shiga dasu ni ko na daina rawan jikin kan abunda bazai D'ore ba Sai da na kwashe duka na shirya komai a muhallinsa ina shirin na koma na cigaba da aikin gabana yace"ki sama min abunda zan ci" Kamar nace zainab bata aiko maka dashi ba ne..? Sai na fasa rashin kunya ba Halina ba ne sai na Tashi na shiga kitchen dafamai mai Dankalin Turawa nayi,sai nayi mai miyar kabeji da taji albasa sai na Dafa mai ruwan tea na Dafa mai kwai guda biyu kuma duka na Tattaramai ko abakina domin na koshi Faten jiya na dumama nasha abuna yaran, kuma Farar shinkafa na Dafamusu da Mai da yaji sukaci kafin su tafi makaranta. Yana zaune afalon na kawo mai ya kalli Filet da jug din da na sanya mai Ruwan zafin kai tsaye yace"Gabad'aya komai naki ya tsufa Fa'iza..Ji kwanukan cin abinci sun fita Hayyacin su mtswww.." Ya saki tsaki daga karshe ina jinsa ban ce masa komai ba na koma na cigaba da aikin gabana,sai da na gama na kashe komai na kwashe zan koma Daki naji ya daga murya yana fadin"Ki shirya in yara suka dawo makaranta zamu je gidan Mama a gabanta sai ki fad'amata in ni nayi miki iyaka da zuwa gaisheta" Sai abun ya bani mamaki.matar nan Kwata kwata bata kaunar ganin kwanciyar Hankalina, burinta ta samo hanyar da za'a tozartani, to da ikon Allah kanta zai koma ni dai ina Daraja ta ko ban auri Yaya Ishaq ba. kamar uwa take gareni, tunda ta rikeni bata barni na yi rayuwa a titi ba sannan duk tsananin wuya da Dadi ta killaceni acikin gida rayuwata bata shiga tsaka mai wuya kamar na sauran matan da rashin gata da mafita yasa suka fada harkan banza ba,ballatana ina auran Abunda ta Haifa har abada bazan ki Darajata ba. D'aya saura na rana yaran suka Dawo shi yaje ya Dauko su da kansa masallaci jumma'a ya tafi da mazan har da Ahmad ni da Anum mukayi tamu a gida,Shinkafa da miya Da salat nayi mana ni da Anum muka fara cin namu kafin su dawo suna Dawowa na zubo mai yaci tare da yaran,Suna ta Murnan tunda na saka musu sabbin kaya nace gidan mama zamu je. Wajen uku saura na rana muka isa gidan Mama,Mun iske gidan cike Anty Binta,da su Halisa da Anty mahma da ya'yanta kamar ana biki yaran muna zuwa suka had'u da abokan wasa suka tafi suna ta wasan su. Afalon kowacce tayi shigar alfarma har ta da Mama ko da taga jiya taga yau da na gaishesu dakyar suka amsa min gwara ma Anty mahma Halisa daman ita ta gaisheni har tana min gaisuwa,Ni da Badariya ne muke mgana kasa kasa kan gobe Badariya tace"Kin fad'a ma Yaya ishaq dai ko..? Na girgizamata kai kafin nace"Ban fada masa ba ammh zan shaida masa yau in mun koma gida" Badariya ta zaro ido kafin tace"in ya hana ki fa ?nasan Halin Yaya Ishaq barin ma in ya fad'ama Mama wlh bazaata bari ba" Kai tsaye nace"Wannan karon bazai iya hana ni din ba" Cikin mamaki take kallona bata samu zarafin mgana mukaji muryan Mama asama tana Sababi sai da na Saurara naji dani take tana cema Yaya Ishaq gatanan ka tambayeta yaushe rabon da
Chapter 50 · 0% Book details