Sashe 84
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawai na sakin masa wankin na koma gefe ina kallon sa. Ganin haka yasa sai jikinsa yayi sanyi ya ciro hannuwansa a ruwa yazo kusa dani yana fadin"To na bari shikenan..? Ajitar rai na sauke ina fadin"Kana so ka jamin fad'an Mama ne in ta fito ta ganka kana wanki..? Na fada cikin fargaba har ga Allah yanzu ina gudun abunda zai sa a tozartani. Sai kawai ya koma ta bayana bakinsa gabda kunnena yana fadin"Ina ruwan Mama don ishaq ya taya Fa'iza wankin kayan ya'yan su" Jikina ya fara rawa nayi gefe ina Haki,sai ya bini da Dariya kafin ya shige Daki ya juyo yana fadin"Yau ba zobo ne da kunin aya kuma..? Ina zama kan kujeran tsugunno nace"akwai sai na gama zan Dafa kunin Aya kuma sai Hafsah ta Dawo" Ni dai har na gama wankin nan Ina auna wasu abubuwan a fili na furta"kamar wanda akayi ma wahayi'" Jamal Sati daya yayi mana ya koma makaranta, ni na basa kudin mota,da na kashewa Anty Binta ta hadamai yan kayan abinci,Ya tattara ya koma makaranta yanzu kam ina samun ciniki sosai,Har ta Badariya ni nake bata na mota da na laluran makaranta,Da dawaniyarmu na yau da kullum ba domin sana'ar na ba da Tuni asirin mu ya tonu. Yanzu in ina aikin Zobo haka Yaya Ishaq zai fito yace sai ya tayani ko nace ya bari bazai bari ba.sai na basa wani aikin zai kyaleni,sannan yanzu ya samu wata banzar Dabi'a ya rika shigemin yana so mu rika hada jiki da juna to banzan dabi'a mana yaushe jikina ya zama abun sha'awa a wajen sa da zai zo ya na rab'ata,da na ga haka sai na rika kauce masa ammh sai naga kamar bai Damu ba sai ya nuna kamar bai gane ba,yanzu ko Hafsah bata nan yana tayani zuba zobon a gorina ko ya wanke min Aya Mama dai bata taba gani ba sai ranar aiko tayi ta fad'a daga karshe ta fashe da kuka tana fadin"Shikenan Fa'iza kin asircemin D'a ya zama bawanki.Allah ya isa tsakanina da Dangin Sidi da tamadina sai mun yi shari'a da su ranar gobe kiyama" Raina ya baci saboda ta kira iyayena a Kabarin su sai na kallesa Idanuwana sun ciko da kwallah ina fadin"Kagani ko sai da nace ka bari.nasan Halin Mama ga shi yanzu ka janyo ma iyayena Zagi suna kwance a kabarin su" Ba zato kawai naji ya mike ya rikoni ban tsinci kaina a ko'ina ba,sai akam kirjinsa ya Rumgume ni dukkan mu sai da mukaji wani abu kamar wuta ya jamu Mama daman tana gama fadin mganarta ta shige daki tana cin mutumcina,Tuni naji na gigice na fita Hayyacina,da gaggawa na turesa na fizge jikina ina numfarfashi sai naji abun yazo min kamar daga sama wai Yaya Ishaq ni ya Rumgume..? Hawaye suka zubo bisa kumatuna sai ya miko hamnu zai share min,na matsa baya ina fadin"Me ye haka..? Bai damu ba,sai yayi mirmishi yana fadin"Hawayen da na yi sanadiyar fitar su zan goge miki" Wlh sai mganarsa ta bani dariya,har sai da na dara ganin ina dariya sai shima,ya biyemin yana Dariya ni ko baisan shi nake yi ma Dariya ba Sabon acting din nasa ne naga bai Dace da shi ba. Acikin Satin sai ga Hajiyar Dala tun da muka yi Hijara bata taba zuwa ba har muna neman wattani shida Mama ta jata Daki ana ta Labarai,duk yadda suke da Mama bata kwana ba,Sai yatsina take yi,Ta shiga har Dakina ta gani duka sai wani yamutsan fuska take yi,ishaq na gida ta kallesa tana fadin"Shikenan Ishaq ka dawo zaman gidan aiki dai shuru..? Yana zaune kan kujera yace"Wlh Goggo a cigaba da tayamu da addu'a" Mama na daga gefe ita ta rakota ta tabe baki tana fadin"Ba shiyasa nake masa fad'a bai ji ba,Mahaifin zainab wlh tsab zai sake nema masa aiki ammh ya Tsaya yana shiririta ko da yake an mallakesa ya zama mai Duran zobo da kunin Aya" Hajiyar Dala tace"ke ko ta ga yana gida sai zaman kashe wando mana. Ya koma chan Abuja ya zauna nan din ai kina nan sai kiga in ana ganin idonsa an fi saurin sama masa aiki" Mama tace"Gayamai kila yaji ki" Hajiyar Dala ta wuce tana fadin"Ishaq kayi ma kanka fada dai" Daga haka ta fice Mama tabi bayanta shine naga ya Damu ammh ni ko agefen gyalena guga daman suka tarar ina yi sai na zama kurma na nuna musu kamar ban ji su ba,shine bayan fitar su ya zabga tagumi. Na zata wani abun arzikin Hajiyar Dalan ta kawo maman,ashe kwalin Taliya da macaroni ne sai kudi da ta bata naji tana fada ma D'anta,Tundaga Lokacin sai na daina Bashi Fuska,da ya fito zai karbeni aiki zan yi tuku tuku da rai sai jikinsa yayi sanyi shi da yaransa dai sai son barka ya maida kansa kamar wani kaninsu, ya Lura sun fi shakuwa dani fiye da shi,sai yake neman shima su fara wannan Shakuwar da shi ni baisan adadin Shekarun da na kwashe ina bama ya'yana Lokaci ba ne. Alhamdulillah da duka ni'imarsa gareni Domin kasuwar Turarukaa sun bud'emin Sanadin Turaren da Hajiya ta saka na hada ma Diyar kawarta Laila ta Kaduna,sai mutane suka rika gani suna suna yaba kamshi ina ta samun ciniki ba abunda zan ce ma Hajiya sai godiya ta aikomin da kayan sawa ni da yara na dauka Gogan zai yi fada sai naga har da shi ake duba kayan ana murna,na kirata nayi mata Godiyan kayan da kuma Godiyan Yayan mijin Laila da sanadin laila taga Turaruka na,suka burgeta ta aiko na had'a mata na Dubu hamsin kwallacha da Humra,kuma na samu alheri sosai da ita naji dadi ko da yaushe in nayi sallah sai nayi ma Allah Godiya sannan na gode ma Hajiya tare da wadanda suka yi sanadiyar tsayuwana da kafafuwana. Ishaq ya kafe bazai rika bin Zainab Abuja ba,mama ta kasa tankwasa shi ga shi mahaifin zainab ya kara kiran mama yayi mata gargadi mgana har Yamai sai ga kanin Mama da kanwarta Hure sun zo shi ya yi ta ma Ishaq Fad'a akan meyasa zai bijire ma mganar Mahaifiyarsa Dalilin daya sa ya yarda zai je kenan ammh sai yace bashi da na mota kamar Dole aka Turo mota tundaga Abuja tazo ta Daukesa. Ina Daki ina gyara kayan Dirowa ya shigo da Jaka a hannunsa daman tunda naga zuwan su kawun yamai nasan za'a rina. Kusa dani ya zauna ni kuma sai na zame na sauka kasa bai damu ba yace"Zan tafi Abuja fa'iza" Kai Tsaye yaji nace"Allah ya kiyaye hanya a gaida zainab da yaran" Sai yayi shuru ya kasa mgana ni kuma bana son muna kebewa a daki mu kadai sai na dakatar da abunda nake yi na mike zan fita karaf ya riko Hannuna. Sai naji wani iri na ratsani na juyo da Sauri ina kokarin kwace hannuna sai ga shi ya mike gabda ni yana fadin"Ki kula da gida da yara" Ina kwace Hannuna da ga rikonsa nace"In dai wannan nan ba sai ka bar min Sallahu ba kaima kasan aikina ne" Ina shirin fita ya kira sunana ina Juyowa,har ga Allah bansan ya taso ba sai ji nayi ya sakar min sumba a kumatuna na gefe n dama Lokaci d'aya yana fadin"Fa'izan Ishaq ki kulan min da kanki" Har ya fice ina binsa da kallo Gabadaya sai da gabban jikina suka yi sanyi zuciya bata da kashi,sai ga shi na yini ina tuna yanayin da na shiga da ya sumbaceni sai da wata Zuciya ta ankar da ni da fadin"A kul din ki Fa'iza ki tsaya iya matsayin ki" Sai nayi kokari na yakice wannan Tunanin Lokacin Hafsah taje korafi ta kwana Biyu sai ni kadai sai yara suma sun ji ba Dadi da baya nan Anty Hure kuma ta nan tare damu Badariya yanzu tafi zama gidan Anty Binta. Azumi ke gabato mu ina ta kokarin na siya kayan zobo da kunin aya masu yawa tunda nasan in Allah ya Budamin zan samu ciniki sosai a raina na guduri niyar ba Jamal ba Har Yaya Ishaq sai nayi ma kayan sallah ko guda D'ai d'ai ne ya'ya na ko sai na gwangwaje su da ikon Allah. Yaya Ishaq sai da yafi sati uku sannan ya Dawo,Namiji kenanbyana baya son zuwa sai gashi ya shantake har da kiba yayi,Sai da ya dawo yana min dadin bakin cewa mganar neman aikinsa ce ta taso shi shiyasa ya tsaya,ni ko bi ta kansa ban yi ba,tunda ba sabon abu ba ne, Ba laifi wannan karon yazo da kudi har ya siya mana kayan abinci,ya rage rabin kudin makarantan yara daman na biya musu rabi sai ya cikasa. Watan azumin Ramadana yazo,ba laifi albarcin watan alfarma mun samu tallafi Goggo ta aiko mana da Buhun shinkafa da taliya da su garin Danwake garin kuni,taliya yar murji,Ni kuma da abun da nake da shi na shiga kasuwa nayi mana kananun Cefane Mijin Anty Binta ma ya bamu gero da shinkafa da siga,Bamu da matsalan abinci a lokacin sai godiyar Allah, Anty Asiya ta aiko min da yaji da kori da Shadda na Ahmad kala biyu,Ganin mun samu rufin asiri bangaran abinci sai na maida hankali ga sana'ata da azumi na chab'a ciniki sosai Hafsah ke taimakamin tare da yara saboda basa makaranta da azumi. Da kudin ciniki da na tara na azumi. na siyan mana kayan sallah da ni da yara nayi ma Hafsah kala da'ya da ita da Badariya na yi ma Jamal shadda shi da yara sai kuma Yaya Ishaq na siya masa nasa shi kad:ai daga gidan Hajiya aka aiko mana da Naman sa mai yawa ana gobe salla da Sakon kudi dubu Hamsin muyi Hidiman Salla kamar nayi kuka ni da ya'yana mun zama abun son mutane ban tsinke ba sai da Raliya ta kawo kaya masu kyau na mata na Anum in ji Laila Daga kaduna. Sai ga Mama bakinta Gum ba karofi Tunda taga an rufa asiri har da ita ake cin arzikin,Anty Hure ma tana nan a wajen mu tayi azumi har ta zobo da kunin aya suna sha har suyi kyauta dashi, daga karshe ce min tayi zan koya mata,tana so ta siya komai anan in taje chan ta gwada