← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 175

Sashe 144

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi nisa cikin Tunaninsa yana juyowa yaci karo da Engr gurfane a gabansa ya sadda kai kamar me neman gafara cikin mamaki yace"Engr..!" Kallonsa yayi kafin ya yi mgana ya cigaba da fadin"Haba ranka ya Dad'e.." "ABDULBASIT.." Eh ka kirani da sunana Abdulbasit Abba ni ai surukin ka ne,nema nake a wajen ka y'arka zaka auramin fa" Yafad'a har yana sosa kai alamun kunya Abba baisan sanda kyattacen mirmishi ya kubce masa ba. Duk da bai san Engr tun yana matashinsa ba. ammh yasan shi Lokaci mai tsawo shine zai iya ba da Labari da shedar nagartan sa. Yana kallonsa zuciyarsa na bud'ewa da wani farinciki yana kuma fatan Fa'iza ta karbi tayin Engr. Mganarsa ne ta katsesa cikin gyara zama yana fadin"Nagode Abba na yi maka alkawarin in sha Allahu bazaka yi nadaman bani amanar Faa'izaa ba.." Zan rike maka ita amana bisa gaskiya da aldalci" Abba ya murmusa kafin yace"Na fad'a maka tun farko bani da Hurumin yi ma Fa'iza zabi duk da ina matsayin Uba gareta, bazawara ce Shari'a ta bata Damar yi ma kanta wani zabin a karo na biyu" Ya fad'a yana dan dakatawa yana nazarin fuskar Engr da tayi wani haske da Haiba,wanda yaga ya karu na yau kada'i. Maimakon yaga sarewa a tare da shi sai yaga Jarumta da Kwarin gwiwa daman ya sani Engr ba shi da Tsoro ko Fargaba. ko karaya kan abunda ya saka ma gaba. Cikin irin Taushin lazafinsa yace"Ai nima ban ce ka yi mata Dole a kaina ba. Ina son Fa'iza kuma zan nemi soyayyarta ina fatan ta bani Dama har takai mu ga aure, in kuma hakan bai Faru ba ni musulmi ne na yarda da Allah zan rumgumi kaddara a madadin Allah ne bai yi ba." Yana mgana Abba najin yana kara Burgesa ko daman yasan shi mutum ne mai hankali da Takwalli yana ma Fa'iza fatan samun Engr a matsayin abokin Rayuwa. Mikewa Abba ya yi yana Fadin"Shikenan bari naje na saka Maman Nana tayi mata mgana." Da sauri Engr yace"Allah ya saka da alheri Abba" Abba ya kara kallonsa yaga ya ma gyara zama ne cikin gyaran murya yace"Ammh nake ga da kaje ka shirya ka dawo ko..?lokacin itama an fad'a mata ta shirya..? Kai tsaye yace"kirawota kawai kaji ni da zamu gina auran gaskiya ina ruwan mu da wani kyale kyale..? Ya fad'a yana kara tankwashe kafa sai kawai Abba ya girgiza kai ya fice Daga Falon shashen Ammi ya shiga su Hafsah na Falon suna kallo kowacce da Hijabinta alamun bayan sun idar da sallah ne suka fito gabadayan su suka Duka suka gaishe shi ya amsa yana tambayan su yau ba makaranta ne sukace sai 9am zasu tafi. Bedroom din Ammi ya shiga tana zaune tana duba wasu kayanta da aka karbo wajen dinki,Abba ya shigo daman tana ta zencen zucci na zuwan Engr sai ta mike ta tare shi tana Fadin"Baban Nana lafiya..?ina Engr din..?Abba ya riko hannunta zuwa bakin gado suka zauna yadda taga ya yi ne sai da gabanta ya fadi daman Ammi akwai rudewa cikin Rudanin ta Dafe kirji tace"Ba dai wani abun ne ya faru wajen aikin naku ba Baban ko Nana..? Mirmishi ya yi kafin yaace"Kwantar da Hankalinki abun alheri ne zan ce ya faru" Ammi ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Har na samu salama me ke faruwa ne..?ya tafi ne..? Abba yace"yana nan..Ina Fa'iza..? Ta tashi.? Ammi cikin mamaki tace"Eh yanzu ta bar nan tazo mun gaisa ka sakani a duhu meke faruwa ne Baban Nana. ? Ganin ta fara rud'ewanta ne yasa ya rike hannayenta yana Fadin''Ki natsu mana..Bafa wani abu ba ne Engr ne jiya da yaga Fa'iza.." "Eh sai yace Fa'izan ta masa me..? Ammi ta katseshi cikin Firgici har acikin Idanuwanta. Yanayinta yasa sai da ya yi Dariya kafin yace"Ba abunda yace ta yi masa sai abu d'aya" Ammi taji wani ras! fad'a da masu gwammati da yarbawa ai bala'i ne Cikin Kara rudewa tace"Mun shiga uku me yace ta yi masa..? Abba na kanne Dariyan sa yace"To laifin D'iyarki daya da ta sace mai zuciya" Kyam Ammi ta tsaya da kifta idanuwan da take yi tana auna mganarsa kafin kwakwalwarta ta hasaso mata zencen Abba ai sai ta ware ido kafin tace"Wai kana nufin Yana son Fa'i? Sai Abba ya jinjina kai yana Fadin"Haka yace" Nan ya shiga bata Labarin abunda ya faru Tsakaninsa da Engr a falo yanzu ai Ammi bata jira komai ba ta kwace hannunta cikin na Abba ta mike ta rike Hanci ta Rangada kyakyawan guda,Sai da Abba ya saki baki yana kallonta kafin yace"Aziza me ye haka kuma..? Juyi tayi a gabansa kafin tace"Bar ni nayi gud'a babban gwaska fa Irin Engr yaga d'iyata yana so..ah ban ga ta zama ba kai Allahu akbar,wani Hanin ga Allah baiwa ne sannan KANA NAKA Allah ya riga ya gama nasa Baban Nana kaji Rabo ko..? Take fad'a bakinta kamar ya tsage tsaki yaja yana kokarin yi mata bayanin yadda suka yi taki Tsayawa ta Fahimta tunda taji Engr na Falo yana Jiran Fa'iza ta fice tana Fadin"Bari naje na sakata ta kimtsa taje ta same sa" Yana kiranta ammh bata dawo ba sai dai Fadi take yi"Ina zuwa Baban Nana" Kai kawai ya Dafe a fili ya furta"Yaushe Aziza zata girma ne..? Bai ga ranar ba, tunda takai ga jika bata Sauya ba,kila sai cuta mai Tsanani da ba'a fata shi kanshi a hakan yake tsananin kaunarta mace ce tagari son kowani namiji mai kima. Ammi na shewa ta fito falon su Hafsah ganin yanayin ta yasa Nana Khadija tace"Ammi hala Abba ya biya miki Umra ne..? Ammi na Dariya tace"A'a Abban ku ai ya gama kaini Umara yanzu fanni na Surukai ne. in da rai da rabo bana ai dani za'a keta Hazon hajji ya'yan nan haihuwa mai Dadi" Take fada tana Dariya sun san Halinta yasa suka saka Dariya Hafsatu na fadin"Ammi mijin Anty Fadila ko Anty Fatima ne zai biya miki..? Ta wuce tana fadin"Kash kuna da gajen hakuri ku jira mana Lokaci ya gaya muku" Murnan da take yi ya isa yasa su san wani abu na faruwa. Abba kuma kin fitowa ya yi saboda ya bama Fa'iza daman sakewa kada ya koma ya takura musu yana suruki guda duk da yar kunya Tsakaninsa da Engr ammh ya Lura daga yau da Safe ya sauya mai matsayi da suna daga baban Nana engr ya koma Abba,baban Fa'iza. ***** Ni ko ban san wainar da ake toyawa ba,Tsakani har ga Allah nima cikin wani yanayi na kwana abun mamaki da Haushi mafarki na yi ta yi masu cike da Engr a cikin su,sannan ko yaya na yi zurfi a tunani sai na hango kamilalliyar Fuskarsa na min mirmishi gabad'aya sai na tashi a jagule na rasa gane kaina Na tambayi kaina Fa'iza daga ganin mutum baki san komai a kansa ba sai Tunanin sa..? Abunda ban taba yi ba ko zamanin Ishaq wlh tallahi bana zama nayi Tunanin sa to basai da kwanciyar Hankali da so da kauna kake tuna mutum ba..?ba auran soyayyah nayi ba shiyasa ban san kallon so ko mirmishin soyayyah ba,ni bani da sani ta wannan bangaran a bangaran auran ma akwai ta bangaran da ni Fa'zan ban san komai ba. Na idar da sallar asuba ban d'aga daga kan Darduman ba ina ta azkar dina daman kuma jiya da daddare sai uku na kwanta nayi istikara,sai kuma na ga akasin haka maimakon naji na samu natsuwar Komawa gidan Ishaq a'a sai mafarkan Engr nake yi acikin barcina. Kuma in bude baki in fad'ama wani wannan iftila'in daya sameni abun kunya ne to abun kunya mana Daga ganin Sarkin fawa ni Fa'iza sai miya taki zaki...? Da hannu bibbiyu nayi Taguni ga Uban Hijabi ga carbi ina ja har bata lissafi nake yi saboda Tsabar Tunani ana ta ma kiran wayata ban ji ba sai daga baya ina Dauka Zainab ce sai dai ba muryanta ba ne na Anum ne na Tsorata ganin bakwai saura. Cikin tashin hankalin daya bayyana har amuryata nace"Ke Anum lafiya kuwa..?ina Antyn naku..? Sai naji ta saka Tsalle da Ihu tana Fadi"Eyee Umma wai da gaske zaki Dawo gidan Daada gabadaya ki zauna tare damu da Daada da Anty..? Sai da gabana ya fadi Zainab ta gama dani daga ce mata zan yi Tunani har ta Yadani na kuma san gabadaya yaran ta fad'a musu har da uban gayyan. Kafin na bata amsa naji hayaniyan sauran yaran suna ihu suna kiran sunana dakyar na iya tambayanta su Ahmad ne tace min"Eh Umma kowa nata Murna zaki dawo har da Yaya Amir baki ga Daada ba,yace yau zamu fita shopping gabadayan mu zamu gyara miki daki Umma don Allah ki Dawo.." Miyau na naji ya kafe nama kasa hadiyewa,saboda rudani ni yaushe nace zan dawo..? Ina jin hayaniyar yara kamar zan kashe wayata ammh Anun taki bari fadi take"Umma don Allah ki dawo kawayen mu fa kowa gidan su Umman su daadan su na waje d'aya sai mu ne Umman mu bata nan,Sannan Umma Daada yace shi ya yi miki laifi mu tayasa bashi hakuri don Allah ki yafe masa.." Tafada cikin wani yanayin da yasa sai da Hawaye suka kawo cikin Idanuwana,Anum da iya zencen Amir ne daman mara Hayaniya. Damuna tayi da fadin"Kin ji Umma ki yafe ma Daada don Allah ki dawo" Sai na samu kaina da fadin"Na yafe masa tuntuni Anum" Sai ta saka Ihun murna tana fadin"To Umma zaki dawo din.? Da gaske ne..? Kasa ba ta amsa nayi ina fadin"Yau ba makaranta ne..? Da sauri tace"Umma muna shiri ne..Ni ki fad'amin zaki dawo..? Da kai na daga mata kamar wacce aka zare ma lakka naji jikina ya yi min nauyi kafin nace"Ehh.." Kamar ashe a amsa kuwwa a ka sakani ina jin ihun yaran gabadaya Da mganar Anum tana fadin"Umma Umma yaushe..?gobe..? Don Allah ki dawo gobe.? Kaina na Dafe da naji yana Saramin kafin na samu damar mgana naji sallamar Ammi da shigowarta yadda naga tana hanzari ne yasa na katse wayar na mike da sauri kafin ma nayi mgana tajani gefen gado muka zauna tana Fadin"Fa'i albishirin ki..? Cikin kallonta nace"Goro Fari kal Ammi" Tana Dariya tace"Sauya Hijabi kije falon Baban ku ki dawo sai na
Chapter 144 · 0% Book details