← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 175

Sashe 175

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bikin ya matso sai shirye shiye ake yi gidan Ishaq na katsina za'ayi taron. tunda sai bayan wata biyu zasu tafi America. Amir na chan bai samu zuwa ba. ammh Anum tace zasu kai masa Ziyara ita da mijinta bayan bikin ***** *MURFI..* Bayan gama shagulgulan bikin Anum da angonta Mas'ud Ibrahim Mahuta. shima mahaifinsa dan garin Mahuta ne kamar mahaifin Aisha. Ta kuma tare a gidanta Katon gaske sama da kasa har da Swimming pool babu kuma abunda babu na kayan alatu iyayenta sun mata bajinta matuka Abba shi ya ba da auran Anum Saudatu Kanin gwamna mai ci alokacin Dr.Ibrahim Mahuta ya karbi Auran,an yi shagulgula sosai abunka na masu da shi duka dangin mu kwanmu da kwarkwatan mu a katsina muka yada zango har Yaya Abdul'ahada da Raliya sun zo kasar Saboda auran Anum Ni kaina nafi sati a katsina kafin na koma Abuja,Tauhudat kadai ke tare dani Tamadina da Paa suna Abuja saboda makaranta,da Maa zasu koma suka koma tare da su yaran sun saba da kakaminsu basa ma kewar mu ni da Baban nasu balle shi da baya zama. Mutane na sun min kara Hajiyar su Raliya bazan manta da ita ba taro na agidanta nayi shi manyan mata duk sun zo Sa'adatu da Habiba ba'a bar su a baya ba suma iyayen amarya ne. Ishaq ya danne komai an yi biki Lafiya an gama lafiya ban tusa kaina ba na kame kaina a matsayina na uwa na bar ma zainab da su Yaya mariya wannan bangaran. mgana kuna in dai ta gemu da gemu ne su Engr da su Abba ne komai. Sai ga shi Yarana da Ishaq ke kira bakake yake jin kunyar nuna su sanadinsu ya shiga gidan gwammati sannan yaga mutane da dama yan siyasa, sanadin Anum baisan iya Daraja da kimar da ya samu ba,ba shi da bakin mgana illah ya kara nadama ga abunda ya aikata a baya. **** Dagani har Engr muna da Gajiya a tare damu,Jiya ma Musty ya koma makaranta tare muka dawo Abuja dashi su Ahmad kuma suna katsina zasu koma tare da Babansu. Dagani sai Tauhidat agidan Engr na ta barcin gajiya sanda muka yi wanka ni da Taihudat mukaje gaisuwan safe. Gefensa na zauna ina mai kuramasa ido ina kallonsa cike da mirmishi. Addu'a da fatan alheri nake ta kwarara masa har sai da idanuwana suka ciko da kwallah. Tauhidat na kallah dake gaurancinta tana yafito kafar Baban nata kallonta nake yi ita kadai ta Dauko kalan Fatata da kamata,Tamadina da Paa kuma kaf din su ahalin su Engr ta Dibo Tamadina Maa tace kamar kafayatu tana karama. Kaina na kara kallo ina sanye da wani leshi mai Tsada ne,kimanin kudi dubi Dari da goma,na siye shi Saboda kalan mai ruwan zuma ne Engr na son kalan,a kayi min dinkin Buba yayi cif ajikina,Yau ba zan fita Shago ba, akwai yaran dake kulamin da shi ko bana nan in wani abu ake so zasu kirani a waya. Na kara kallon kaina naga yadda na koma cikin shekara shidda zuwa bakwai yadda Allah ya haskaka rayuwa ta. Ni Fa'iza ban taba zaton watarana matakin rayuwa zai kaini ga haka ba ammh nasan naci Ribar Hakuri ne da addu'a. Mijina kuma bani da bakin mgana sai masa fatan ya gama da duniya lafiya kuma yasa na zama matarsa a gidan aljannah bani da abunda zan iya rama masa alherinsa gareni. Ashe Tauhidat tayi barci a hannuna ban sani ba sai da naji ta sunkuya sannan na kwantar da ita ta chan gefen na dawo na Zauna kusa da kafafun Engr na fara masa Tausa ina Fadin"Sannu Baban Anum aurar da y'a ba wasa ba.." Nazata barcinsa ya yi nisa sai gani nayi ya Bude idanuwansa tar a kaina Ido na waro kafin in yi mgana ya yi caraf da hannayena bai yi wata wata ya fad'o dani jikinsa bayan ya jawoni. Saman kirjinsa na fad'a ya kamani ya Rumgume kamkan na wani Lokaci muna jin bugun zuciyar juna Kafin ya sausauta rikon da ya yi min yana Fadin"Ban gaji ba domin yanzu zan dora da shagalina ki bari in nagama sai ki min tausan gabadaya" Na dago kaina zan yi mgana ya hade bakin mu Waje daya ya dade kafin ya Sararamin yana Haki yace"Tsakani ga Allah nayi hakuri yaron nan Mus'ab haka ya kirani yana godiya kuma nasan shima yaji dadin da nake ji ne indai Anum tayi gadon ki. ammh ni sai dai ayi ta min kwalele bata sab'uwa fa ina son kanwar Tauhidat ko kaninta.." Dariya na saka ina fadin"Surukin zamani..' Engr ya karishe da fadin"Kuma ya had'u da surukan zamani ba.." Kai na girgiza nasan waye Engr har aransa shi Surukin zamanin ne ina fatan kada watarana ya bani kunya gaban mijin Anum. Biye masa nayi muka sha shagalin mu Tauhidat na gefe tana ta sharan barci muka juya muka kalleta ni da shi kafin mu yi mirmishi. Cikin sigan rad'a yace"Allah yasa na jefa kwallo a raga." Yafad'a yana shafa cikina sai na Danne hannunsa kan cikina yana Fadin"Ameen Habibina Allah ya barni dakai har a Ajannah" Saboda burina kawai na kara samun ciki ni da Engr mun yanke shawaran in mace na Haifa. Goggon Karofi zan yi ma takwara. In kuma Namiji ne Abba ne. Ya amsa min yana sumbarta wuyana kafin yace"Allah ya yi miki albarka kin bani komai Faa'izaa. ya'ya mata,Kanwa,yaya,abokiya kece komai nawa kodayaushe fatana mu Dauwamana tare har Mutuwar mu kin zama ni na zama ke,Allah ya bamu Tsawon rai mu aurar da Amir da Musty da Ahmad sannan mu kai Tamadina da Tauhidat gidajen mazajen su" Ina dariya nace"Ameen Lokacin ka zama Kaka Kenan..? Wata muguwar Dariya ya yi kafin yace"Granny zamani ba. Ban yarda na Tsufa ba fa,ke kuma ai lokacin kin zama su Goggo Faa'izaa. Haka zaki ji ya'yan su Anum suna Goggo..Googgo..'" Har yana kwatantawa na mintsine shi da hannu ina fadin"Kai kuma fa ya sunan ka..? Yana dariya ya karya murya kafin yace"Granny. Granny mana is in Stayel haka.." A yadda ya fad'i sunan ne yasa muka fara Dariya dagani har shi. Dariya mai cike da farinciki da nishadi. nishad'in da nake fatan ya Dauwama har abada a rayuwarmu. *ALHAMDULILLAH*! *ALHAMDULILLAH*! *ALHAMDULILLAH*! *Nan na kawo karshen Labarin KANA NAKA. Kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min,in da kuma nayi daidai Allah ya ba ni lada* *Godiya ta Musamman ga Masoyana da suka yi Tururuwa wajen siyan wannan labarin Tabbas kauna ce,nagani kuma na yaba Allah ya saka da alheri VIP001 Tare da FA'IZA'S HOUSE,jinjina ta musamman gareku tare da kyatattun Sharhin ku, Allah ya had'amu a gidan Aljannah Firdausi Ameen* *Kafin na sake dawowa da wani sabon Labarin in muna raye,zan tallata muku sabon Littafin mu mai suna BAKAR TA'ADA.* *Na marubuciya Surayya Dahiru gwaram,marubuciyar Halin yau da Sabo da kaza,ba domin tana kawata zan tallata muku labarinta ba,a'a sai domin yabon gwani ya zama dole kada ku bari a baku labari,Na tabbata zaku ji dadin sa kamar Kana naka kila ma fiye da Hakan in sha Allahu* *Allah ya jikan iyayenmu da magabatanmu,Allah ya jikan Kawu Abdullahi Allah yasa yana Dausayin Aljannah Allah ya jikan Muhammad Tukur mijin kanwata Allah yasa yana Kyakyawan matsayi,Allah ya gafartama Alhaji Abubakar Mijin Ummi Allah yasa chan ta fiye musu nan Gabadaya. Mu kuma Allah yasa mu cika da kyau da imani Ameen ya Rabb* *INA SON NA MAIDA KANA NAKA ZUWA HARDCOPY.* *AMMH HAKAN BAZAI SAMU BA SAI DA HAD'IN KAN KU,IN AKWAI MASU BUKATA ZASU IYA MIN MGANA TA WANNAN LAMBAR 09069067488* *Janafty* *02/08/2023* *JAMILAUMAR* [8/2, 7:21 PM] Hauwa Galadima: Akwai kura kurai da yawa da writers ke yi yanzu Kuma ina mamakin yadda manyan writers na gani amma basu kwaba ma yaran. Sbd writer malama ce, rubutu kuma wata makaranta ce da makaranta ke daukam darussan da ake zubewa a ciki. Allah yayi mu daban daban, wasu na gane fari su dauke shi su bar baki, wasu kuma bama su iya banbanta farin da bakin. Sbd haka dole a tsaya matsayar da kowa zai fahimci fari da bakin komin kankantar fahimtar. A kullum zaku ga idan anzo gabar auren mai mata. Suna ba yaranmu high hopes na karya da wofi wanda kowa yasan ba haka bane ba cos we are not living in fairytales, we are living in real world. Abun ya zama mindset dinsu an saka masu wannan mugun mentality din, a lot are rushing to marry married men thinking that ai uwayen gidan duk buge ne sun gaza ne shiyasa zaa aure su. Uwargida itace mara kirki Uwargida bata iya girki ba Uwargida bata iya kwalliya ba Uwargida bata yi boko ba Uwargida bata da kyau Uwargida alfarma akayi mata Uwargida kazama ce Uwargida bata da Ni'eemah Uwargida bata iya kwnaciyar aure ba Uwargida this uwargida that At the end zaa saki uwargida, sai amarya ta zauna a gidan, sbd duk lapses na dunia na uwargida ne. Amarya ce kyakkyawa Amarya ce yar boko Infact amarya ita ta iya komai Amarya is perfect in any aspect. Which is not true and totally wrong Abeg this is not our reality..yawanci iyayen masu rubutun ma iyayen gida ne ko sisters dinsu. Yawancinmu iyayen gida ne, amma hakan ya same mu ko iyayensu, mace nawa ce uwargida tana da amare 3 bayanta she still rules her house, they are living a peaceful marital life and ko amarya ta zo ba lallai tafi uwargida ba sbd yawanci mazan yanzu ma ba gazawar mace ke sasu kara aure ba, raayi ne kawai. Kuma sai amaryar ta shigo taga duk buge ne abun. Sometimes wasu books din are not helping at all. Kuma ina amfanin abunda zakayi ba zai amfani jamaa ba sai dai ya tura ma wasu wani raayi na daban wanda gaba zasu sha wahala. Documented by H.M.G B D X!Z! (<)>) )|*~* *R+T+ +$,&, -$.&. Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office 03c6eb391d604be8a52adcd1d889f92f
Chapter 175 · 0% Book details