← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 175

Sashe 114

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki kara da fad'a musu a jirgi zaku tafi"Da sauri ta waro ido tana fadin"Daada jirgi fa mai tashi sama..? Ya daga mata kai kawai sai ta fara Tsalle tana murnan zasu hau jirgi Ahmad da Musty na tayata,Amir dai na zaune yana bin su da kallo. Yaro shi yana son sauyin muhalli,Amir ne yayi hankalin cewa'Daada in muka koma chan wata makarantar zaka sakamu? Yana dariya yace"Amir d'an makaranta. Kada ka damu makaranta mai kyau zan saka ku in sha Allahu" Daganan ya cigaba da biye ma yaran suna masa tambayana yana amsawa. Ni har zan shige daki yace yana son mgana dani,dole na hakura sai da yaran suka yi mana Sai da Safe suka shige Dakin su,sanin in yace muje Dakinsa bazani ba yasa muka zauna afalo ya fara da gayamin EFCC ta dawo mai da kud'insa kimanin Naira miliyan Sitti,Tunda ba lalle kudin mutum su dawo duka ba. Shine ya ke ce min yanzu ya yanke shawaran zai fara yin gaba yaga yanayin garin da komai,zuwa ya sama mana inda zamu zauna tunda Abba yace zai had'asa da mijin Nana Fadila. Ban yi mai musu ba nace shawaran shi tayi sai ya cigaba da fadin"gida nake son siya babba wanda zai wadace mu. In bai samu yanzu ba, sai na kama Haya zuwa gaba in na samu a hankali a hankali sai na siya na kaina" Kai Tsaye nace"Gwara ka mallaki naka zai fi. Kuma mganar ka siya babba kada ka yi asaran kudin ka,ka siya daidai zaman mata d'aya da Dakunan yara,kana da maza sannan mace Daya gareka Anum,Ga mama ga su Badariya duk da ita tace sai ta gama hidiman kasa tukunnah" Cikin mamaki yace"Bangane wajen mace da'ya ba.?ina miki bayanin itama Zeey na gayamata ta fara shiri,kila ku zaku fara yin gaba ita sai daga baya zata same mu achan" Mirmishi nayi kafin nace"Ka gane mganata mana. ni fa bazan bika Lagos ba" Sai ya yi karamin Tsaki kafin yace"To sai ki zauna a ina.?kai tsaye nace"A nan mana"harara ya sakar min kafin yace"kina Hauka ne.?ina wata Duniya kina nan?wazai barki di'n? kafata kafarki, kafar yarana Fa'iza" Sai ban ce komai ba na kauda kai bai Damu ba ya cigaba da fadin"Abba yace na siya mota saboda zirgan zirgan zuwa wajen aiki da sauran dai Bukatu"jin sa kawai nake yi ina tunanin ya dauka wasa nake yi sai na kara gyara zama nace"Da gaske nake yi. ni bazan bika Lagos ba" Sai kawai ya mike yana fadin"Bina ko kamar kin gama shi Fa'iza meyasa zan barki.?ba mai kara rabamun hankalina yanzu iyalaina duka waje d'aya zan had'asu" Kai Tsaye nace"Yanzu kuma.? Ni fa kada ka manta na saba zama ni kad'ai a baya ma kana Abuja ina katsina, kuma na zauna lafiya sai don ka koma Lagos..? Kallon sai ki yi yayi min ya shige Dakinsa ya bugo kofa sai ya bani Dariya ya Dauka wasa ne?lalle ko zai ga wasa alokacin da bai yi tsammani ba. Ya samu mun fara tattara kayanmu,ni daman ma na had'e nawa na yara ne ba'a gama had'awan ba,yace bazai saki gidan ba sai in ya siya wani inda zamu rika sauka inda munzo,tunda dagamu sai kayan sawa zamu tafi sauran kayan gida Sabbi za'a siya kawai,har sun yi mgana da megidan ma ya bashi kudin Shekara,Hafsah kuma daman bata da matsala Transfer dinta ya samu kaduna zata koma,ranar muna tattara kayan kitchen waje daya Anum tace"Umma shikenan kin daina zobo da kunin aya..? Kai tsaye nace"In ji wa..?zobo da kunin aya yanzu na fara" tuna ko ranar da Hajiya tazo min murna na fad'a mata lagos aka kaisa tun kafin na yi mata bayani tace duk inda naje kada na saki sana'ata domin sana'ar hannu abu ne mai kyau da amfani kuma na aminta da mganarta na Jaraba kuma naga riba,kuma dayake nima baama Lagos din zani ba ballatana ya dameni, inda zan koma da zama na tabbata zan rika yin ciniki sosai. Kuma ko da muke tattara kayan ina sana'ata ban fasa ba,Mama ma nata shiri tunda yace in yaje ya dawo har da su Anty binta za'a tafi saboda suga waje,Sati hudu Tsakani ya tattara ya tafi,jirgi ya bi daga kano zuwa Abuja,bayan ya isa headquater din su ya saka hannu sun bashi accepted letter,Daman yana zuwa ya kira mijin Nana Fadila shi Costume ne,gidanta ma ya sauka yaci abinci ya huta sannan suka fita duba gida,sun duba inda yafi kusa da ma'aikatan su anguwan Apapa lagos,ya siya apartmemt,gida ne mai girma ba sosai ba,Falo hud'u mai Dauke da bedroom da Tiolet guda takwas,yana da girma gidan tunda akwai Haraba sosai,sai kudi wajen miliyan Ashirin gidan tunda Sabo ne shima mijin Nana Fadilan wani kaninsa ke harkan gidajen shiyasa suka samu da sauki,Ya siya gidan sannan kuma yayi oder din gadaje da kujeru da sauran kayan bukatu da ya Kirani ya fad'amin sai nace"ka san kana da yara a siya musu kananun Gadaje. Ga uku anan ga biyu Farhan da Fadil,Anum kuma ko ita da Badariya sai ka had'asu,Mama kuma tana Dakinta ita kadai sai jamal kada ka manta da shi" Cikin gamsuwa yace"ban manta da shi ba wajen zai isa ba takura fa. na Dauko muku hoton gidan in na Dawo zan nuna miki"Da haka muka rabu sai da yayi sati sannan ya Dawo da shirin zai tafi damu gabadaya Zainab kuma sai daga baya zata biyomu ita. Sallama yace duk mu yi da abokan arzuka da yan'uwa da makota,Ranar a karofi muka yi yini,washegari kuma da muka dawo na zaga cikin gari naje nayi ma Sa'adatu da Habiba sallama saboda sabo har suna kwallah,makaranta yara daman tun kwanaki naje na sanar da su suka ce zasu yi kewar hazikan Dalibai. Hajiya ma naje mataa sallama,ta bani kyautan kaya da su Turaruka da mayama mai na gyaran jiki muka rabu cikin mutumci,Abba dai shi ya hana naje yi masa sallama duk da ko ba inda suke tunani zan tafi ba, yace shi zasu je har lagos suga muhallina. Anty Binta da da Mama sai Anty Hure da tazo zasu tafi daga bangarena yace a samu mutum biyu sai Goggo ta wakilta Anty Nasara da matar Yaya Isa tunda Yaya mariya tace bazata samu zuwa ba,Yaya Asiya kuma yaronta bai da lafiya yana fama da kyanda. Tafiyar jirgi yace zamu yi,zamu je kano daga katsina kenan,Ya siya mana Ticket gabadayanmu zamu tashi karfe uku na ranar talata,damu da kayan sawan mu,ana gobe Tafiyar na had'a komai nawa na kayan zobo na da kunin aya. Sannan na cire soket din Freezer di'na,duk kulle kullen da Goggo ta aikomin da shi na had'a cikin kayan yaran nasa zai musu amfani. Na zata ina da Dauriya sai ga shi na fara raunanaa, in naga yadda yaran ke Tsallen Murna ina Tunanin ya ya zasu ji gobe in har na ce musu ba Tafiyar mu d'aya ba..? *Janafty* [7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2020* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Ko yaran ban bari sun fahimci Halin da nake ciki ba,daki na shige ina kokuwa da yanayina. Nace kada su dameni da Hayaniya Hafsah bata nan daman tun jiya ta wuce karofi daganan Abba zai turo mota a Dauketa zuwa kaduna. Yaran ne kad'ai da babansu ke ta Budurin su da murnan gobe zasu hau jirgi,sannan zasu koma Lagos da zama,kayan su dai masu muhimmanci na hada musu saboda tafiyar jirgi ce yace ko shi daga baya zai saka a taho mana da komai gabadaya,Badariya tana kano sun kusa gama Hidimar kasa bata da Lokaci sai dai zata taho daga baya. Kwana nayi ina kuka Sai dai ban kwanta ba ina sallah hawayena sun kasa tsayawa sai kuma naji kamar abunda nake shirin yi bai kyautu ba.?kamar in nayi haka na karya raunin zukata da dama ciki har da ta yarana. da suka fi kowa shakuwa dani ammh sai wata zuciyar ta tunasar da ni Babban Dalilina da yasa naji na kara samun karfin zuciya. Sai dai a komai in zan yi ba ma yin gaban kaina Allah nake fara sawa cikin Duka al'umarana,Shi na daga hannu na roka da kyawawan sunayensa sannan na yi masa magiya na yi masa naci ina kuka ina fadim"Ya Allah kasan damuwar dake damuna acikin zuciyata, sannan kasan wahalwahalun da nayi ta fama da su yayin biyayyan auran da kai ka Umarcemu da yin sa. Sannan kasan komai da ya faru tunda kai mai ji ne kuma mai gani ne na yanke wani Kuduri a raina ya Allah in har ba alheri acikin Tunanina, Allah ka hanani aikata wannan kudurin nawa in kuma Hakan shine alheri a gareni da Duniyata gabad'aya Allah ya bani Hakuri ka sanyamin juriya kada kuma ka barni ni kad'ai kayi Riko da Hannayena sannan ka yimin Jagoranci a duka al'murana,sannan ya'yana Allah ka tallafe su, kayi musu albarka, ka kara shiryamin su cikin addininka" Ina addu'an kukana yaki Tsayawa sai na kife kaina a kan hannayena ina ta rafzan kuka,ni da barci sai wajen hud'u na asuba shiyasa na makara sallar asuba sai da naji sa a kaina yana Tab'a kafafuna na bude idanuwana jajir da suka kumbura saboda kuka,na sauke a kansa cikin mitsike ido na ce"An yi sallah ne..? Kai Tsaye yace"Har mun dawo masallaci ni da yara kina kwance ashe baki tashi ba..? Jin haka yasa na yunkura Dakyar na mike ina fadin"Ban yi barci da wuri ba ne" Kai tsaye na wucewa zuwa Tiolet sai ya bini da kallo yaga idanuwana sun tasa ammh ganina a kan darduma sai yayi tunanin sallar Dare nayi,Ficewa yayi falon wajen yaran har Anum ta kunna gas ta Dora ruwan zafi saboda wanka,Amir kuma ya saka a Heater tunda akwai wuta. Sai da idar da sallah na fito falon ina ganin an saka ruwan zafi nasan Anum ce uwar zumud'i ban dora abun kari ba sai da duk sukayi wanka har da Baban nasu,sannan na fere dankalin Turawa na soya musu sai ruwan Tea muna da sauran kayan ciki sai nayi mana Ferfesu da yawa saboda Mama da Anty Hure,su Anty Nasara suna Karofi sai yau zasu taho ammh ina Tunanin zan Dakatar dasu. Saboda tafiyar dake gaban mu yasa suna gama karyawa suka fara shiri ni dayake ban iya saka komai aciki na
Chapter 114 · 0% Book details