Sashe 158
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* *ENGINEAR ABDULBASIT ABDULGHAFFAR OLUWATOSIN* Sheik Abdulbasit Abdulfattah Oluwatosin shine asalin sunan kakan Engr wanda ya haifi mahaifinsa. Su asalin su tun tale talen kakan kakannin su yarbawan Ilorin ne, ammh aiki da kasuwanci ya sa suka tashi garin Benue ,ammh ba Haifafun nan ba ne, nan dai suka girma suke kuma gudanar da Rayuwarsu a tsakiyar Birnin Beneu State. Sai dai aiki da karatu na fidda wasu Daga garin ammh kusan dukkan su ba su da tushe ko asalin daya wuce garin,Ilorin kuma shine Tushen su. Sheik Abdulbasit Abdulfattah ba bahaushe ba ne iyaye da kakkaninsa duka yarbawa ne,ammh sun fito daga Tsatson gidan malamai ahalin sunna Shiyasa ba sa kyamtar Hausawa ko wasu yarukan, suna auran junan su sannan sukan yarje ma mutum ya auro dukkan yaren da ya yi masa ma'ana babu tursasawa ko takura da lalle sai ka auri yar'uwan ka bayarbiya. Kuma hakan ya samo asali ne ga ilimin zamani da na addinin da ya lullube su kuma ko a garin Benue gindom din su na malamanta ne. shiyasa kaf zuru'an Abdulfattah a garin Benue ba wanda bai san su ba. Daga cikin ya'yansa sai aka samu wanda ya yi gadon sa shine kakan Engr wanda ya haifi mahaifinsa Sheik Abdulbasit Abdulfattah Oluwatosin wanda sunan shine Engr ya ci, Ma'anar Oluwatosin da yarbanci shine God is worthy to be Saved,tunda su a al'adan su ko da an saka maka sunan yanka wannan al'adace za'a rika kiran ka da sunan ka da yaren su ko da na ranar da aka haifeka ne. Mahaifin Engr, Mr AbdulGhaffar Abdulbasir Babatunde,shi kuma ma'anar Babatunde da yaren yarbanci shine The Father return,shi ne kusan manyan ya'yan Sheik Abdulfattah,yana da yayye maza da kanne mata,kusan dukkan su sunyi ilimin zamani da na addini matan suna Gidajen mazajen su suna aiki wasu kuma suna kasuwanci mazan kuma kowanne ya kai mataki mai girma na karatu kuma suna aikin gwammati. suna garuruwan da aiki ya ijiyesu duk da wasu har a yanzu suna garin Benue da zama su da iyalansu. Hajiya Kudurat Olaminde,itace kad'ai matarsa da tayi masa takaba sauran matan sa guda biyu duk sun rigasa mutuwa kuma Hajiya Kudirat Abdulghaffar kad'ai ta haifa ya tsaya sai da ta binne tara reras a kasa suna rasuwa sannan shi ne na goma Allah ya raya mata shi,shiyasa ya samu dukkan gatan duniya da kowani d'a kan samu a wajen iyayensa. Mr Abdulghaffar Abdulbasit a london ya hado Degree dinsa na farko kafin ya zo Usman dan fodiyo University Sokoto ya yi mastering Degree dinsa. ya zama Cadet na EFCC Officers tun wanchan Lokacin. Ya fara aiki da EFCC a matsayin Assistance Detective superintendent(ADS) kafin jajircewan sa a aiki yasa ya samu karin girma zuwa Deputy cheif Detective superindent (DCDS),Mr Abdughaffar ya yi gwargwamaya sosai a aikin sa Saboda yana da ilimin matakin Kwalin Degree hudu garesa a mabambata kwasakwasai,Sannan kuma ya yi anragama da masu cin hanci da rashawa da masu d'iban kudin gwammati kama daga yan siyasa ma'aikatun gwammati dabam Dabam kuma ya yi nasara shiyasa tsawon shekaru Tara yana nan a matsayinsa na Chairman na EFCC gabadaya. Mr Abdulghaffar da yaransa ke kiransa Papa yana da mata aure guda Daya Hajiya Shukra wacce ta kasance bahaushiya ce gaba da baya mazauniyar kano, kuma haifaffiyar kano din ce sun hadu ne a sokoto inda yaje degree dinsa na biyu itakuma taje hada Degree dinta na farko a kan Economis. An yi soyayya kamar me,Itana ganin D'an mutan Beneu ta rude shima yana ganin asalin bakanuwa yaji duk duniya ba wata sai ita,kuma da yake yasan Family dinsa basu da matsala Sai ya saki jiki ta bangaranta ne aka so a samu matsala Tunda tun a baya mahaifiyarta Hajiya Tafeesu mafadaciya ce ta dinga fad'an yarta bazata auri yarbawa masu kashi a leda ba, sai da lokacin dangin mahaifinta da suka yi binciken gidan su Mr Abdulbasit suka kuma suka ga cancantan suka bashi auran Hajiya Shukra sai ga shi ko gidan da take ciki yanzu a kano shi ya gyara shi ya zuba mata ma'aikata sannan babu abunda ta nema ta rasa,sai gashi Hajiya Tafeesu tafi kowa jin dadin Yaron yarbawa masu kashi a leda, a cewarta ko banufe ne in dai nagari yazo zata bashi aure ta fahimci a kowani yare akwai na banza kuma akwai na kirki. Sun yi aure lokacin Hajiya Shukra ta gama karatunta a Benue suka fara zama tare da mahaifiyarsa Hajiya Kudurat,dalilin haka yasa ita bata cigaba ba,Saboda aikin mijinta ba na zama waje daya ba ne. Suna zaune lafiya cikin soyayya da kaunar juna ba su da matsalan komai,matsalan su ma farko shine sai da Hajiya Shukra ta shekara biyar da aure sannan ta haifo d'anta namiji mai kama da mahaifinsa sai dai ya Dauko hasken mahaifiyarsa. Bayan haihuwan Abdulbasit da yaci sunan kakansa Suna kiransa Oluwatosin sai da hajiya shukra ta shekara ashirin bata yi ko batan wata ba har sun fidda rai da kara haihuwa Allah mai kyauta da kari ya kawo Rabon Cikin yan biyu,cikin da ya wahalar da ita kamar bazatayi rai ba aiki akayi mata a wani asibiti dake India sannan aka ciro mata santalan santalan ya'yanta guda Biyu. Wadanda suka ci sunan Kafayatu da Sharifatu. To a yaren su yan biyu ana musu lakabi da Taye da kahinde bayan kuma haka suna da yarouba name din su,Bimpe da Erimipe,koda suka taso sun iske su Abdulbasit ya riga ya girma ammh duk da haka akwai shakuwa mai girma a tsakanin su sannan iyayensu sun yi kokarin basu Tarbiya,in ka gansu bazaka taba cewa sun sirka da wani yare ba sai dai ta Harshen su,kuma sai ma sun juya harshen ake ganewa. Gwara ma su kayafatu ana gane suna da jini da yarbawa saboda suna yawan zuwa Beneu hutu da kuma sanin kan wasu al'adunsu nasu kamar yanayin Shigar su da sauran su. sabanin Engr da makaranta kwana ya yi sannan shima University of Ibadan ya yi Degree dinsa na farko sannan ya tafi London shima ya hado Degree dinsa na biyu akan Chemical Engineraring, bayan haka ya hallaci manyan manyan kwasa kwasai a kashashe ketare akan abunda ya karanta ya fara da aiki kamfanin Narka karfe a garin Lagos na shekara Hudu kafin wani Uncle dinsa Uncle Tobi ya sama masa aiki a Edo Refinary and petrochemical Limited na karkashin Jahar Edo_Ekiti. Engr mutum ne na gari mai dattako da sanin ya kamata, duk wanda ya zauna da shi ko na kwana Daya sai ya tafi da Labarin karamcinsa. Yana da barkwanci da Dad'in zama Mutum ne da yasan abunda yake yi,Ta dalilin Hajiya Shukra da ya ke kira Sweetheart su kuma su kafayatu suna kiranta Mah,ita kuma Hajiya Kudurit Granny ya san Engr Usman karaye saboda suna makota a gidan su dake kano, Dalilin haka har yasan abunda ya karanta ya kuma karbi Takardunsa ya nema masa aiki a NNPC dake kaduna da kuma matsayi mai girma kafin Abba ma ya nema ma mutane aiki da suka zama wani abu sun fi Dubu,haka ma bayan Haka kowa aka kira sunansa sai dai kaji ana fadin nagartansa da irin kyawawan Hallayansa,sannan in ba shi ya fad'i cewa shi ba bahaushe ba ne, yaroba ne,ba mai ganewa ko kuma in anji karshen sunansa tunda tun yana karami har girmansa bai cire Oluwatosin a sunansa ba,yace a san mutum asan Dabi'arsa da Rayuwarsa da inda ya fito ya fi asan ka batare da an san ko waye kai ba. Engr ya je kasashen ketaren da baza su kirgu ba,tunda aiki na yawan Fitar da su waje to karshen wayewa yana da shi,sai dai mata basa gabansa ko a cikin Danginsa akwai masu son shi ammh baya maida kai. A chan family din su kowa da Tosin yake kiransa Papa kuma yace Oluwatosin,Maa tace Babatunde Saboda sunan surukinta ne kannensa kuma suna kiransa Brother Tosin,a wajen aiki da mu'amalansa da mutane kuma Engr Abdulbasit ne,yana da kyakyawan shaida wajen mutane da wad'anda suka san shi daman wad'anda basu san shi ba. Engr mata basa gabansa ya jima bai yi aure ba, sai da ya shekara talatin da Tara har kannen sa su kafayatu sun shiga jami'ar Abuja,Maa ce ta ke damuwa shi Papa ba ruwansa Oluwatosin kamar abokinsa yake haka zasu zauna su yi ta hira ba ruwan shi haka da Uncle's dinsa kamar wani kanninsu haka zasu riga hira suna Dariya shi mutum ne mai Sakewa mai al'amarinsa ba kumbiya kumbiya mutum ne simple,ba kowani Lokaci ake iya ganin Rauninsa ba. yana dakiya da juriya mai naci kan abunda ya sakama gaba mai kyauta da Alheri. Sister's dinsa kuwa in kaji suna Brorhers Tosin kaza kaza,ya riga ya nuna musi bayan yaya shi din dan'uwan su ne da basu da kamar shi kamar wani kaninsu haka yake shigewa cikin su ana hira har da Shewa Maa ita bata da Hayaniya sosai ammh fa duk abunta in Tosin na gida sai ta saki jiki an sha hira sai dai bata yin irin yadda Papa ke yi ki ga har suna tafawa da Tosin ko suna mgana ta kunne ko su hada kafada ga shi tsawon su d'aya sai dai shi Tosin har yafi Papa budewa na jaruman maza. Abdulbasit Abdulghaffar Oluwatosin Dogon namiji ne ingarma kalarsa kalan Chaculate ne kalan yan maroco ne,sannan yana da karan hancin Paapa,kuma ya Dauko Doguwar Fuskar Maa,sai idanuwansa masu girma kamar na mace,yana da bakinsa mai Fadi kadan sai ya tsuke yayi Tudu kamar na mata,hakoransa masu haske da walwali yana da cikar gashin ido da na gira ba ma'abocin tara suma ba ne shiyasa duk sati sai ya yi aski,Mutum mai Fara'a da mirmishi cikin kowani Hali wannan mirmishin baya Bacewa daga Fuskar Engr. Matarsa Tauhidat da ya aura ta rasu Diyar yayan Papa ne Abdulwasiyu,Hajiya Kudirat ta matsa sai da akayi auran asali ita ke son shi Tana zuwa Hutun gidan su na Abuja kawar su Kafayace,shi kuma baya sonta