← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 175

Sashe 65

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gida yake zanawa mai kyau daman Tunda Musty ya fara wayau bai da aiki sai zane zane ni kuma in dai nayi sallah sai na rokar masa Allah yasa zane zanen ya zama Hanyar cin abincinsa.. Karb'a nayi na Dubawa lokaci d'aya ina fadin"Kai kai..Wannan gida ya had'u chanchad'i" Cikin nishadi yace"Umma irin wannan gidan zan gina miki,in na girma nayi kudi" Na kalli gidan sannan na kara kallon Musty wanda yake cikin shekaru na takwas har da wani abu,Kansa na Shafa ina fadin"Allah ya ida nufi yaron Umma,ka cigaba da dagewa da karatu watarana buri zai cika in sha Allahu" Anum na tura baki tace"Umma ni fa nace zan gina miki gida" Ina jin haka sai nayi dariya nace"To shikenan ke sai ki siyamin mota" Da sauri tace"Aa Umma sai dai Jirgi" Ina jinjina kai nace"Lalle waya ga Umma ajirgi babban mgana" Dariya na saka suma suna tayani Amir daya gama Rubutunsa ya tsaya kikan bayan ya goya hannuwansa a kirji kamar wani babba,da muryansa da ta fara tashi daga na yara zuwa na manya ya fara fadin"Umma kin makara kuma kin zo kin ta sa ya'yanki kuna ta surutu" Da Sauri na kama bakina ina fadin"To Mallam ayi mana afuwa kai kowa ya kama bakinsa" Da Sauri suka ko kama Hafsatu na gefe tayi Dariya tana fadin"Umma da ya'yanta" Juyowa nayi ina nuna mata Amir ji nayi yace"Umma.." Da Sauri nace"Anty Hafsat ce ba ruwana" Kai ya girgiza kafin ya juya yana kallon Ahmad sannan ya kara juyowa yana fadin"Umma kalli d'anki bai da aiki sai kallo" Ahmad muka kallah da ya bada hankalinsa kan abunda yan aljanu suke yi a tibi ko jin mu ma ba yayi Dariya ta na Danne ina fadin"Ayi masa afuwa Mallan yaya" Sai ya juya da yar sandansa yana fadin "Zamu maimaita karatun mu na jiya Umma ki karanta min" Sai na gyara zama kal momin Turanci ne da ma'anar su. Na fara karantawa daga Number 1,kamar haka. Mother _Uwa kenan da Hausa. Na biyu kuma Son_Yaro da Hausa. Na uku kuma Brother_Yaya. Husband_Miji. Wife_Mata. Sister_yar'uwa. Uncle_Kawu. Grandmother_kaka. Mother inlow_Uwar miji. Sister in low_Kanwar miji Friend_aboki. Tsab na karanta duka kuma na fassara Amir ya kalleni kafin yace"Please clapp for Umma" Sai tafi Raf raf har da Hafsatu cikin masu tafawa cikin jin Dadi nace"Mallam na dauke wad'anan sai na gaba kuma" Sai ya jinjina kai ya goge wannan ya sake Rubutu wasu. Sannan ya shiga karantawa yana Fassarawa. Beautifull_mai kyau Handsome_kyakyawa. Marrige_aure. Divorse_Saki. T.Shrt_Riga. Trolley_akwati. Money_kudi. Bayan ya gama karantawa sannan yace mu amsa bayan shi,da ni da su Anum muka bud'e murya muna amsawa bayan mun gama yab''i daya bayan daya yana mana bayani kowacce kalma da ma'anarta da Hausa kuma sosai na natsu ina ganewa lokaci da'ya ina kallon Amir daya girma shekarunsa yanzu sha Biyu a duniya ya gama primary zai shiga Jss1 ne,Anum kuma tana shekaru na goma ne Musty takwas Ahmad kuma shidda,Sosai na ke karuwa da ilmin ya'yana Tuni nasan kalmomin turanci irin su come,Sit Down,standdup,zagi ma nasani da Turanci,Nima fa yanzu ba wani karamin kalman da za'a fadeta da Turanci wacce bana ji. sannan ina kan koyan sanin kalmomin Turanci masu saukin Fad'a da masu ma wahalan,Amir ke koya mana ni da yara Kokari garesa sosai kokarinsa har ya girmi shekarunsa. ina jin su ya tada Aum tana karantawa ni kuma nayi Tagumi ina kallon ya'yana sannan ina auna Shekarun da suka gabata.yadda na sha gwagwamarya da kuma yadda Daukakan Allah ta sameni Lokaci daya. Ina nan a fa'iza ta yar gargajiyata saboda ko zan sauya a komai Tunanin ado ko kwalliya basu dace ga mata munana irina masu nakasun hallita har yanzu bai bace daga tunanina ba,Sai dai ni Fa'iza na samu cigaba ta Fanni Rayuwata gabad'aya yanzu haka bazan ce kaf katsina ba ammh rabinta da kewayanta sun san wacece *SAFMA* Ko Fa'iza sidi karofi mai Turaran kamshi da dilkan amare Safma sunayen ya'ya na ne da ni kaina nake amfani da shi, a Kunin aya na da zobo sai kuma Ina saka Sticker ajikin Turaren wuta ko kwallachaa,Sannan ina amfani da shi wajen girken girken da nake yi na Birthday ko na suna ko wani biki wanda in nayi shi a gida,acikin Shekaru biyun da suka gabata ban san irin godiyar da zan yi ma Allah bisa tarin Ni'imarsa ba, da a baya Naira Biyar ma sha'awa take bani ammh ban da yanzu da na rike manya manyan kudade basan adadin su ba, Yanzu haka na bude acct inda nake tara kudad:e na,Sannan na mallaki wayar hannu Badariya da Hafsa sun yi matukar kokarin wajen koyamin yadda zan yi amfani da ita, sun kuma Bude min shafuka a instergram da Sauran su da sunan SAFMA,domin inganta sana'a ta suma ba'a bar su a baya ba wajen tayani tallata sana'ta. Ni kaina bazan iya kirga mutanen da nake hulda dasu ba yanzu,Sannan bansan adadin costumer na ba, abu da'ya na sani in yau nayi ma wata aiki gobe sai ta kawomin uku daga bayanta saboda na Tsaida gaskiya sannan na rike Allah. Nasan bani da kyau sannan bani da gata,ammh kuma ina da baiwa duk wanda na hadu da shi mu'amalan aiki ta had'amu shikenan mun zama D'aya Baban katsina ya Dad'e yana cemin ina da baiwa ban sani ba sai yanzu in na Duba kaina ayanzu da ban jiran ayin komai da ni da ya'yana, sai na Tuna Tamadina naso tana raye na jiyar da ita dadin Duniya?sai dai ban manta da ita ba ina yawan mata Sadaka da fatan Allah ya jikanta da Rahma. Matar da ta fara zame min uwa ita da ya'yanta a garin katsina itace Hajiyar su Raliya da ya'yanta ita ta zamemin makwafin Mama a garin nan ta Daukeni kamar yarta duk wani Cigaba ta bangaranta na fara samu ya'yanta da yan'uwanta a Dangi suka D'aukeni nima sai na Daukesu a Dangina ballatana da ta Fahimci halin zamantakewar da nike ciki sai ta zama tsanin dukkan wani Cigabana. A yanzu haka kaf danginta da zuru'arta ni nake had'a ma ya'yansu turare da gyaran jiki in za su yi aure,Sannan ni nake yi musu kwangilar girken girken sha'aninsu suna zuwa wajena kai Tsaye nima ina zuwa wajen su kaina Tsaye sun daukeni dagani har ya'yana ahalinsu susan yan'uwana da Goggo suna zumumci da su Hajiyar su Raliya mace ce mai mutumci da Sanin Darajan Dan adam, kuma ko da nake da abun hannuna a yanzu ni da ya'yana alherinta bai taba yankewa a gareni ba. Haka ma Badariya itama bazan manta da ita ba, Ita ta fitar da Zobo na da kunin aya na a jami'ar su ta Umaru musa yar'aduwa aka sanni na zama Dila ana sara, ni yanzu kusan in ba na gida gida da suka saba siya makota ba, na daina saida zobo da kunun aya rabe rabe sai dai a sara kamar D'ari ko sama da haka. ballatana yanzu da Hafsa itama take aji daya a jami'ar itama tana zuwa dashi kuma ya kare,Har ta Yaya mariya duk sati tana zuwa ta karb'a Saboda ta fara yi da kanta sukace sun fi son dan'danon nawa sai kawai ta koma tana sara a wajena. Ta ko'ina budi ya budemin na Roki Allah mafita kuma ya bani sannan na rokesa albarka acikin lamarin shima ya sakamin,Yanzu har ma'aikata na Dauka su uku suna taimakamin wajen hada zobon da kunin aya sai Sa'adatu da ita nake biyanta duk wata Saboda tana taimakamin kuma bazan manta da alherinta ba. Sannan kuma Dawowar Hafsatu wajena sai itama na jawo mata Mutane Saboda Ina gyaran amare ita kuma tana kunshi sai gidanmu ya zama wajen shige da Ficen mata manyan masu abun hannuwan su, Ni da ya'yana mun daina jiran wani ya yi mana ko ya bamu,na daina jiran kowa,ko Kudin makarantar su na biya musu ya kai su biyu,mganan kayan abinci da Cefane mantawa nake ma ina da Miji,na riga na saka ma raina ni kad'ai ce sannan ni ce uwa da uban ya'yana.Iyakata duk abunda naga zai yanke min na shiga kasuwa na siyo. Ishaq ya dad'e da sanin Fa'iza yanzu bata jiran wani ko wata ballatana ta wulakanta. Snnan ni na saka Ahmad a makaranta, naga ya wuce misali a gida ban jira kowa ba na kaisa da kaina,nayi masa registration,sannan Sauran bukatun yarana ma ba na jiran sa,ko Maman da ya saba wakiltawa ta kawo musu in taga dama. Ya'ya na suma suna kece raini cikin Sutura mai kyau,da Tsada ashe rashin samun jin dad'i ne yasa fatar su ta Dishe da suka samu sauyin rayuwa da mayuka da sabulai masu kyau da Tsada sai ga shi sun yi tas da su, hatta ni bakin nan nawa ya rage nayi shar dani na kara kiba kamar ba ni ba. Don ma ban maida hankali wajen gyara ba,da kila da yanzu fa'iza ta sauya sauyawa ta sosai. Yaya Asiya da tazo kwanakin baya ta taga yadda rayuwata ta dawomim fad'i ta ke yi "Allah mai girma.Shi yasa akace kowa yayi hakuri zai dafa dutse har ya sha romonsa,ga shi Fa'i ta dafa tana shan Romon sa" Sai dai nayi dariya domin suma daidai misali ina taimakon su tunda ina da shi,Bangaran Yaya ishaq kuma zan iya shaidar sa ta banganran, bai taba nuna bakinciki ko hassada kan samuna ba,Kamar yadda bai tabamin mganar ta yaya komai ya fara Fa'iza..?nima ban taba gayamai ba kuma bai Damu da ya sanin ba. Nima ba ni da wannan lokacin,sai dai shi kanshi yasan Fa'izar da ya sani a baya yanzu ba ita bace wannan Fa'izar ta samu ingantattacen Rayuwa,da sauyin da na tabbata ko a mafarki bai taba tunanin ni Fa'iza zan samu ba,sai dai shi Allah ba ruwan shi da wannan in ya tashi,Daukakarsa ba nasaba ko chanchanta yake dubawa ba,Bayi duka D'aya muke a wajensa. Da gaske dukkanmu mun zab'i Rayuwar da muka ga zata Dace damu shi ya zabi zainab da iyalanta, nima na zabi ya'yana da sana'ata sai yayi wata uku bai zo katsina ba,ko yazo kwana d'aya biyu ya koma,ni ko baya gabana da zuwansa da rashinsa duk d'ayane a wajena,yadda baya shiga Sabgata haka nima ba na shiga tasa kowa tasa tafissheshi. Suma yaran suna girma suna kara Fahimtar Babansu yafi son zama
Chapter 65 · 0% Book details