Sashe 74
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Janafty* [7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2004* *Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* Itama cire hijabi tayi ta shige cikin mu. tana tayamu zuba zobon a sabbin Gorunan da na siya,muna yi muna hira cikin Annushuwa lokaci d'aya muna darawa in abun dariyan yazo,Yaya Ishaq ne bayan ya gama shan na shi zobon zai shiga cikin gari ya mike yana fadin"Fa'iza zan dawo daukan Goggo dole na tafin ma da Madam zobon nan domin itama tana min labarin sa" Hafsah na gefe tace"Yaya isa har da kunin Aya.." Da sauri yace"Eh har da kunin Aya a had'amin dashi" Gabad'ayanmu muka kara kwashewa da Dariya yana sosa kunnensa da key din motar dake hannunsa yace"Goggo kin jamin yara na min dariya ko.? Goggo tace"Kayi abun dariyan ne.Ke Hafsah bisa ya kwaso min tsaraban Fa'iza kafin ya tafi" Har zai fice daidai lokacin yaji Goggo na tambaya ta Yaya Ishaq sai nace mata ya tafi Abuja sai ya koma ya zauna cikin mamaki yana fadin"Daman bai daina zuwan Abujan nan ba..? Goggo tace"Kaji wata mgana shi da yake da mata da ya'ya kake fadin bai daina zuwa ba" Yaya isa yace"Haba Goggo.In a baya ya je yana aiki ne yanzu kuwa ba ya aiki ga wahalan rayuwa in a baya yana da motar kansa, yanzu ko babu ko na motar da zai rika zirga zirga ai wani abu ne mai zaman kansa shima ya kamata ya zauna yayi ma kansa Tunani haba.." Ni da goggo kamar had'in baki ba wacce ta tankansa ya cigaba da fadin"In har tana son shi ta baro chan ta dawo nan, ai gidan nan shima ban ga laifinsa ba inda rayuwa ta juya dakai sai ka juya kai ma ka fuskanceta" Goggo tace"Ya za'ayi ta dawo bayan achan take aikinta a kace" Yaya isa yayi tsaki yana fadin"Mganar banza ne Goggo in dai tana son shi kuma ya isa da ita duk inda yake zata bisa.ammh gaskiya wannan tsarin bai yi ba, duk wanda yaji haka sai ya raina ma wayaun Ishaq. baisan zama ba aikin yi ba ne, yana ganin kamar abun wasa ne sai rayuwa ta fara kwallo da shi zai Fahimci Shayi ruwa ne" Dariya ta kusa subucemin da mganarsa ta karshe ya mike yana fadin"Ita Fa'izan ba mutum ba ce, ba ga ta nan ta biyo sa inda yake a kuma yadda yake ta zauna da shi ba, sai ita yar gwal wahala ce bata ishesa ba Allah ya ba da sa'a" Daga haka ya mike bayan yace Hafsah tazo ta shigo da kayan ni kuma sai nace Amir ya bita ya tayata bayan fitan su ni da Goggo bamu tada zencen ba sai muka shiga wata Hiran na Dabam Goggo ta kalli falon ta kara kallo kafin tace"Nan din ma ba laifi sai ku lallaba kafin muga Abunda zai yi" Na gyad'a ma Goggo kai ina fadin"Ai anguwan nan tayi Goggo sosai nake samun Ciniki" Goggo na dariya tace"Dakyau Allah yasa albarka Allah ya tunkud'o ciniki Fa'i ta biyamin hajji da kudin zobo da kunin Aya" Ina dariya na rika fadin Ameen Ameen Goggo har da Umra ma goggo na Dariyan jin dadi tace'"Allah ya ida nufi Fa'iza" Hafsah ne suka dawo da kaya Nasan Goggo da Dawainiya bata zuwa Hannu Rabbana tace su garin kuni ne mu lallaba ina ta godiya har da Taliyar yar muji garin Danwake garin Tuwo da tsakin masara kubewa danya,kuka daaddawa,da bushashiyar Zogala da rama sai gyada mai bawo da Mai gishiri da ta kawo ma yara Tsaraba Dadi ya cikani sai cewa nake yi"Allah ya saka da alheri Goggo na zama yar gatan ki" Goggo tace"Daman ke yar gata na ne tuni zaman ki ne kawai bai yuyu a Hannuna ba" Nasan haka domin duk wata kauna Goggo ta nuna mana barin ma ni,Su Hafsah tuni sun ja gyad'a gefe suna ci ita da Amir na balla musu Harara ina warce ledan Lokaci d'aya ina fadin"Wannan na sauran yara na ne yan makaranta" Amir yace"Umma wannan yayi musu yawa fa..? Na bude ledan ina gani sai naga da yawa sai na debo a hannu na zube a gabansu na boye sauran ina fadin"yara kun ci rabon ku" Goggo na mana Dariya naji Dadin wannan zuwan na goggo muka yini muna Hira,Hafsah tayi abincin rana bayan ta gama nace ta dibar mama da Badariya da taje kai mata sai tace sai yanzu aka ga daman bata abincin..? Ita dai Hafsah bata tanka ta ba sai da ta Dawo daki take gayamin Ban ce komai ba Goggo tace"Sai kin kara Hakuri daman fa'iza yanzu Saudatu zatayi ta tsiro da abubuwa saboda ta kuntata miki, to kada ki biye mata Har a gobe uwa take gareki" Kai na jinjina ina fadin"Goggo ni ban da Lokacin wannan kina ganin bama zaune nake ba" Goggo tace"Ba shakka Sana'a ai mganin Damuwa ne da sha'anin Duniya," Sai da muka yi sallar la'asar sannan Goggo ta yi shirin tafiya daman da La'asar Ya Isa yace zai dawo shima daga ma'aikatar su ta nepa dake Dutsemah ne aka turo su meeting babban Headquater su na katsina da ya gayama Goggo tace zata Biyosa. Aiko sai ga shi hudu da wani abu sai faman hon yake yi ma Goggo tunda yaki shigowa na zuba ma Goggo kunin Aya da zobo mai yawa shima Yaya isa na bashi na shi Goggo sai fada take yi tana fadin"bai yi yawa ba Fa'iza? kada mu karya fa jarin" Ina Dariya nace"Cikin Riba ne fa Goggo" Sai ta karba tana fadin"To Allah ya yi albarka Allah ya sanya miki nasibi da karama acikin Kasuwancin ki da sana'arki" Na dinga amsa mata da Ameen na rakata Dakin Mama tayi mata sallama ni da Hafsah da Amir har kofar gida muka rakasu Yaya isa ya zaro dubu biyu ya bani naki karba sai ya harareni yana fadin"Kyauta na baki ni ba kudin zobo ba ne" Jin haka yasa nayi dariya na karb'a ina masa Godiya Hafsah na ganin haka tace"Yaya isa kada ka manta yar makaranta marainiyar Allah" Dagowa yayi yana fadin"Data zaki saka ko..? Da Sauri tace"Eh Yaya ai muna Browsing sosai" Sai ya yi dariya ya zaro dubu ya bata yace a saka data ayi ta browsing ta karba tana godiya sai kuma ya bama Amir dari biyar yana fadin"Kai baka fara zuwa makarantar ba ne..? Da Sauri nace"Bai fara ba sai zangon karatu na biyu Yaya isa" Sai ya jinjina kai har Goggo ta shiga mota sai ta leko ta window tana fadin"Kinga na manta Maman isuhu tazo da kanta ta kawo min goro da mintin biki Isuhunta zai yi aure tace kada a yada zumunci don Allah" Fatan alheri nayi kafin nace"Da wahala zuwa na Goggo kinga ga Mama ina fita sai kiji ance ban kyauta ba" Goggo tace"Hakane ki yi zaman ki ni da mariya sai mu leka" Da haka muka yi sallama suka tafi muna Daga musu hannu sannan muka koma cikin gida,Danwake nayi mana da Daddare Hafsah kuma sai ta hada kunin Aya zobo ma bamu yi na yammah ba nagaji nace ta bari da Safe yan sari ma basu samu ba duk a gida ya kare. Aiko Mama tayi ta fad'a wai danwake ne abinci da daddare kamar a gidan yari..?yarda aka kai mata haka Hafsah ta Dauko kulan da safe da zatayi wanke wanke, Badariya bata dawo ba kila gidan Anty Binta ta kwana,haka na cigaba da Hakuri da Mama ammh Allah ke da kullum da Sabon korafin da take tashi da shi sai dai bana biye mata,Yaya Ishaq tunda ya tafi bai kirani ba nima ban damu ba sai dai nasan suna waya da Mama. Sana'ata na maida hankali bani da wani Hutu sai dare ya tsala wani Lokacin Saboda kada ayyuka su Chudemin karfe uku na Dare nake tashi na Dafa Zobo a tsakar gida tunda na koma amfani da gas na kasa 4kg,Sai na siya babban murhun gawayi ina amfani da shi wajen Dafa zobo,har girki ina yi akai saboda gas din ya rika yi mana auki sosai. In na tashi ukun nan kafin asuba na Dafa zobon,sai naji da saka ruwan wanka. wani Lokacin Hafsah ke abun karin Safe in zata fita da wuri in kuma tana gida sai nayi in ta tashi sai ta Hada zobon ta kuma share gidan da Dakunan in kuma bata gidan duk ni nake had'awa nayi kunin Aya saboda yana Saurin Lalacewa nafi hadasa da yammah saboda an fi samun Wutar Dare kafin safe yayi sanyi. Hakan ma bai burge Mama ba, duk yadda nake taka tsantsan sai da ta fito tace min wai warin ganyen zobo na tayar mata da zuciya ni ko sai nace sai dai ko ki yi ta sheka amai bazan daina wannan sana'ar ba,kuma duk kushen mai kushe da Hassada ta Allah ba tashi ba. Duk yadda nayi sai tace kaza kaza ita dai kada ta ganni cikin ni'imar Allah sai dai na zauna ta rika tusamin Haushi da tozarcinta nan kuwa bata isa ba,yanzu ba irin da ba ne an samu Sauye sauye da dama. daman haka Rayuwa ta gada Kifi na ruwan sanyi sai ya iya juyawa ya gansa ana zafi kamar yadda ya faru da ita. Na toshe jina da ganina na cigaba da sana'ata ina rufa ma kaina da ya'yana asiri,har da ita kanta Mama muna da kayan abinci ammh bamu da Cefane da Riban sana'ata nake mana komai Dawainiyar yara na makaranta na yau da kullum Badariya ma ina bata na mota har da wata matsalan in ta taso in dai tamin mgana ina da shi zan Dauka na bata. In da na biye mata na koma na zauna yadda ta matsa Yaya Ishaq ya tafi Abuja da ta gane bata da wayau.Anty Binta take takama da ita itama bata da komai yanzu sai karya da Girman kai da tijara fal cikinta domin ban ga abun arzikin da take kawoma Maman ba,Da farko da Mama tace Ucler ya kamata kayan Tea ta siyan mata da suka