← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 175

Sashe 105

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai fad'amin yadda suka yi da Abba ba, sai bayan kwana Biyu da muka natsa sannan yake gayamin nayi murna sannan nasan tabbas tunda Abba yace zai shiga mganar an yi an gama. Har Mama ya fad'amawa sai addu'an Allah yasa adace take yi,da fatan a gano gaskiya. Ko da aikinsa bazai dawo ba,ammh yana da kyau kada sunanka ya zauna a matsayin barawon Gwamnati. *Janafty* [7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2016* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Wannan shekaran data zagayo. bamu sha wahalan rayuwa ba,saboda Abba ya tsaya mana,shi ya biya kudin makarantan yara da sauran bukatumu na yau da kullum. hatta da kayan abinci ya cike mana wannan bangaran,Yace komai muke bukata mu kirasa bamu da damuwa Ishaq kuma daman ya fad'a masa shi a D'a ya dauke sa ba suruki ba, shima uba yake garesa kamar yadda yake uba gareni Shikenan shima sai ya saduda yana karban komai da girmamawa,Mama ma haka tana ta min godiya,ni ko nace mata bakomai,Badariya ta koma kano wajen Hidimar kasarta Jamal ma ya koma makaranta sun shiga Semister karshe a makaranta. Gefe daya ina cigaba da sana'ata ban Dakata ba,Sannan ayyuka sun karu min yanzu saboda akai akai nake hada Turaruka yanzu daga chan kaduna da kano ko'ina akayi mganar Turare sai Ammi tace Fa'in mu tana Had'asu masu kamshin Dadi,in nayi sai dai na bama Hafsah ta kai tasha a saka a mota kuma kudin aikina cas a Hannuna,Allah yasa ma Anum na gida ta gama primary zata shiga JSS Section. Muna waya da su Nana Fatima kusan kullum muna sanin Halin da juna ke ciki,Yaya Ishaq yaki ya gyara wayarsa sannan yaki ya siya wata. Matarsa sai kirana take yi ni na zama alkali a Tsakaninsu wani Lokacin sai ta kira baya gida sai ya barni da gayamata ya fita,gajiya nayi ranar muna zaune da Daddare shi ya gama yi ma yara karatu sun kwashi Littafan su zuwa Daki,Hafsah na kitchen tana Dafamin zobo wanda zan yi na safe da shi,ni kuma ina gefe zaune a kasan cafet,shi ko har ya koma ya kwanta a saman kujera. Dagowa nayi ina kallonsa kafin Nace'"Na manta. matarka ta kira d'azu baka nan" Yana ji na bai yi mgana ba sai na tura masa wayar gabansa ina fadin"Gaskiya ka siya waya. ko ka gyara taka, nagaji da Damuna da matarka take yi, kana kuma barina da bayani in baka gida" Sai alokacin ya bud'e ido yana kallona cikin shakewar murya yace"Ba zan siya ba sannan ban yi ra'ayin gyarawan ba" Ban yi mamaki ba daman nagansa yau sai a hankali yana jin yan tsiyan nasa, sai na rabu da shi aiko ko tashi bamu yi a wajen ba sai ga kiranta na leka naga itace na mike na fice daga Falon zuwa tsakar gida ina faman kaye kaye ban sanin masa ba ko sun yi mgana. ni dai da nadawo naga wayata nan saman kujera na Dauki kayana na wuce Daki. Abunda na lura Zainab da mahaifinta sun sauko suna neman sulhu da Ishaq shi kuma yaki basu wannan damar Saboda bayan kwana Biyu ta sake kirana baya nan domin yakan d'an fita ya mike kafa ina ji a gefenta tana mgana tana fadin Daddy wai baya nan ya fita sai naji an yi mata mgana kafin tace min in ya dawo nace ya Kirata Daddy zai yi mgana dashi. Da ko ya dawo na bi shi har Daki na Fad'amasa sannan na bar masa wayan a wajensa sai gashi ya biyoni nima har Daki ya mikomin wayata yana Fadin"Ki daina kawo min wayar nan Fa'iza wai sau nawa zan fad'a miki ne.? Sai na bude baki ina kallonsa cikin mamaki nace"To in ta kira sai nace mata me..?kai tsaye yace"ki fad'a mata gaskiya bana son mgana da ita" Nima kai Tsayen nace"Tace ka kirata Daddy na son mgana dakai" Yadda ya wurgamin wayar ya fice a Fusace ne yasa sai da nayi Dariya Allah yasa wayar kan gado ta fad'a,Na dauki wayata ina fadin"Bani na kar zomon ba" Zainab bata barni ba, ta rika addabata da kira kunya sai na rasa me zan ce mata sai taga kamar ni ne bana son had'asu,Gajiya nayi nace gwara na fito nayi masa mgana Tattara yaran nayi zuwa Dakin Mama harda Hafsah saboda chan yafi kusa da tsakar gida yafi iska,Kayan sa da na wanke masa na ninke masa basu kawo wuta ba,ballatana na goge masa,Sai na Tattara na kai masa Dakinsa tun da ya shigo ya shige ciki sannu da zuwa ma dakyar ya amsamin Abincin sa Anum na bama ta kai masa ko da na shiga yana wanka domin naji karan saukan Ruwa a makewayi. Sai na sauke kayan Hannuna saman katifarsa na zauna gefen katifar ina jiransa bai jima ba ya fito da Dogon wando a jikinsa,Kansa na digan ruwa yana gogewa da karamin Towel,Sai da ya tsaya yana kallona alamun yayi mamakin ganina ni kuma ganinsa ba kaya yasa na mike ina fadin"in ka shirya sai na dawo' Ban jira cewarsa ba na fice shima bai Dakatar dani ba,Na koma Falo ina yan kaye kaye yara dai ba'a rabasu da Lalata waje ko sau goma zaka gyara shi kuwa,ba jimawa sai ga shi ya fito da jallabiya da farantin abincinsa a nan falon ya zauna ya ci abincin ya sha ruwa,sai ya koma ya kishingid'a yana Hamdala ni kuma falon na Tattara domin ina taka datti Musty ne yayi sharan,ba domin ya share dakyau ba. Ina ta jira ko zai ce me nake son fadamai sai naji yayi kamar bai ma ganni a falon ba,Sai na samu gefen kafafunsa na zauna ina fadin"Mgana fa nake so mu yi" Kai Tsaye yace"kunne ke ji ai" Sai na bude baki zan yi mgana sai na Rufe saboda ina tunanin bazai karb'i mganata ba Sai ya dago yana kallona kafin yace"Uhm ina jin ki" Sai na dukar da kai ina Fadin"Tsakani ga Allah baka kyautawa abunda kake yi"kai tsaye yace"Da na yi me kuma..? Ina gyara mganata nace"Kan mganar Zainab mana ka barni ina mata karya. Haba don Allah baka je bafa tun zuwan nan da kayi kafin azumi,Itama ai tana da Hakki a kan ka, kuma Allah zai tambayeka akan hakan ka dauki waya ka kirata ku yi mgana don Allah" Kamar bazai ce komai ba har sai da nace"Kaji.." Sai ya gyara zama kafin ya mike ya zauna dakyau yana fad'in"Kina bani mamaki Fa'iza wai wani hakki kike mgana..?ke sau nawa ina zuwa wajenta na tare kuma tasan hakkin ki na shiga ammh bata taba min mganar naki Hakkin da ke kaina ba, sai ke ki bi ki dameni Haba." Ya karishe fad'a yana Tsareni da idanuwansa da suka fara shigewa Ciki,sai na sunkuyar da kai ina Fadin"ni ba ruwana da wannan. Abunda na sani ne nake gayamaka kai ma nasan ka sani,Tunasar dakai nake yi ciki fa gareta tana Bukatar kulawarka" Kai Tsaye yace"ke ciki nawa kika Dauka kika haifeshi batare da kulawata ba..? Sai na kasa mgana kafin nayi mirmishin takaici nace"Ni sunana Fa'iza ni ba yar kowa ba ce. sannan ni ba yar gata bace Fa'iza ba Turanci komai nata zero ne Zainab kuma mai kyau ce yar gata yar Dangi tana da ilimi tana jin Turanci sannan kowa na sonta, kaga kenan Tsakanina da ita akwai Tarin bambamcin da ko a wajen Daidaito na miji bazamu zo Tsara d'aya ba". Ina kallon cikin Idanuwansa na fadamai haka sai kawai ya rausayar dakai yana fadin"Ashe bazaki bar wannan mganar ba Fa'iza..?baki manta komai ba kenan..? Ko daman kin fad'ane kawai baki yafe min ba..? Da Sauri nace"Wlh na yafe maka duniya da Lahira" Da Sauri ya Tareni da fadin"To me kike son nayi ne ki daina damuna da wad'anan mganganun ne" Kai tsaye nima nace"ka Saurari zainab sannan kaje ka dubata tana bukatar kulawarka" Sai ya kankance ido ya mike yana fadin"To bazani ba. Nace bazani ba,Sai ki sani naje dole..Haba mata kin bi kin dameni..?zaman ki nake yi a gidan da zaki rika min kora da Hali.?na riga nayi rantsuwan da bazan kara bin Zainab ba, in tana so na tasan inda nake zata Biyo ni. kuma kin ji ma na rantse bazaki sakani yin kaffara ba. Ba ruwanki in ta kara kiranki kada ki sake d'aga wayarta Umarni ne na baki ba Shawaran ki nake nema ba Fa'iza" Ya karishe fad'a yana kureni da ido,na bude baki zan yi mgana ya saka min yatsa a saman bakina yana fadin"Shii..Mu rufe babin wata zainab mu yi mganar mu Fa'iza ina mganar mu ta kwana..?baki ga duk na galaibata ba ne saboda rashin ki..? Kai Tsaye nace"Shiyasa nake so kaje inda zaka samu abunda kake muradi" Sai kawai ya mike tsaye yana Nuna ni da yatsa cikin bacin rai yace"Rashin kunya zaki yi min Fa'iza don kinga ina Lallaba ki ko..?ko karfi na saka miki Bani da laifi Saboda ke Halaliyata ce. ina binki a Hankali ne Saboda nayi miki laifi ba domin kin fini iko da kanki ba" Mamaki ya kamani kamar zan yi mgana sai na fasa sai kuma ya Saussauto ya koma ya Duka gabana ya Riko Habana ya dago fuskata yana Fadin"Don Allah Fa'iza ki manta komai mu bama auran mu wata Dama nayi miki alkawarin bazaki kara kuka dani ba don Allah. Wlh na wahala na fara susucewa" Ya fada lokaci d'aya yana langwabe min kai kamar karamin yaro,sai nayi wuf na kwace fuskata na mike shima sai ya mike zan gudu ya rikoni kafin nayi wani motsi ya kamkameni a jikinsa duk mutsu mutsu na na kasa kwace kaina sai na Saduda kaina ya Dago yana kallon cikin Idanuwana yace"Saboda kin ga ina kyale ki ko..?ni kuma sai na bude baki zan yi mgana, sai kawai naji ya Had'e bakina da nasa waje daya ya fara sumbatata lokaci daya yana kara kaina da Hannayensa a cikin jikina. duk iya kokarina na kwace kaina na kasa tun muna Tsaye har muka zube saman kujera yana Jagwalgwalani fargabana D'aya kada wani cikin yaran nan ya shigo gashi yaki barin bakina ballatana na yi masa magiya sai da ya maidani Tubus ko yatsana ban iya dagawa, Saboda yadda Hannayensa suka Ladaftar dani,Mganar Ahmad muka ji daga kofar daki yana kiran"Umma.."Umma"
Chapter 105 · 0% Book details