Sashe 161
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Dole akwai wasu kayan da za'a bar su a gidana na kaduna,shiyasa Ammi da rakiyar su Nana khadija suka kara komawa suka kai tunda akwai key din gidan a hannun su Ammi. Kaya kad'an suka ragemin wad'anda zan sassaka in mukaje chan sai turaruka da kayan kwalliya sai kayan gumbar mata na tsimi da Saiwar kazan da na siya wajen Surayya Halin yau,ta kuma yi min alherin turrukan wutan ta masu kyau da kamshi,Sannan har da garin daka na sha madara ko nono. Gaskiya Surayya ta na da kirki da iya mu'amala sosai na ji dad'in huld'a da ita,kayan ta kuma masu Inganci ne. Kazan saiwar nan ina fada muku duniya ce. Tun zuwan nan da Engr ya yi bai sake dawowa ba. aiki ya yi masa yawa yana Edo sai dai mu yi waya ni da shi duk tsaren tsaren ta waya muke yi. Ranar alhamis ya kama tafiyarmu Abuja tunda yaso mu fara ta chan Benue din ne ammh sai Sweetheart tace tare zamu tafi saboda haka mu fara sauka ta nan sai a wuce gabadaya. Ni kuma ranar Talata da Safe naje nayi gyaran kai Steaming akayi min tunda ban saka mai ba. Mai kitson su Ammi tazo ta yarfamin shi 2step kanana masu kyau,Ranar laraba kuma nayi kunshi Baki da Ja,a baya ina Dauka kunshi bai dace dani ba tunda ina baka ammh sai ga shi an yi min kuma ya fito ras har ya fi ma na Bikin Yaya Abdul'ahad kyau da fitowa ko don yanzu na kara haske ne sannan Fatata ta Murje tayi kyau. kamar bani bace Fa'iza nan ba sannan kuma nayi Dilka da Halawa,sai yanzu na kara yarda da mganar Hausawa da sukace in kana da kyau to ka kara da wanka to in baka da kyau in ka kara da wanka sai kayi kyau din. Engr sai min santi yake yi,yana jadaddamin ayi min zanen kunshi mai kyau in ya gani zai ba da tukwaici,shi a chan Benue zamu hadu tunda shi yana Edo Bazamu had'u da shi a Abuja ba Motoci kuma daga ma'aikan su Abba aka bamu manyan motocin su mai cin mutane sha takwas guda daya,Tare da Direban su shi zai kaimu har Abuja. Naso naje karofi nayi ma su Goggo sallama ammh ban samu dama ba, sai dai mun yi mgana ta waya kuma nasan Daga baya in nace Engr ya kaini bazai ki kaini ba. Tun ana gobe tafiyar masu harama suka zo,har da Hajiyan Dala tunda ta kwallafa rai sai tazo,Su hafsatu suna ta bakin rai bazasu samu zuwa ba. Yaya Mariya nayi musu dariya har ga Allah na cire rai da zuwan Anum tunda ban ji Anty Fadila tace min komai ba,Sai dare ta iso Lokacin an gamin min lalli har na cire nayi sallah ashe jirgin yammah suka shigo abun mamaki sai gata da Anum,sai D'iyarta Falaq sa'an Anum din sauran suna gida saboda makaranta. Sai gani ga Anum baki har kunne muka Rumgume juna tana Dariya tace"Umma.." Irin cikin mamakin nan nima sai na Dago kanta ina kare ma girmanta kallo yarinya ta kusa ma kereni a Tsawo Cikin Dariyan jin dadin ganinta Tsab cikin kamala na ja kumatunta ina fadin"Anum d'in Umma" Hannayena ta kama ta kallo sai kuma ta kara kallona kafin tace"Umma kin yi kyau kamar ba ke" Sai na kara Rumgumota ina jin wani farinciki na ratsani ba wamda ya nemi takura mana muka shige daki ina ta faman tambayanta ya sauran yan'uwanta ina su Mama da Antyn su..? Tace min duk suna Lafiya Anty ma ta bada sako ta kawomin yana cikin akwatin Anty Fadila Allah Sarki daman tace min zan ga sako,bazan mata da alherinta ba taso zuwa ammh awajen aiki ba'a bata dama ba. har ina mata tsiyan ko megidan ne ya hana cikin Dariya tace"Wlh ya barni maman Amir daga wajen aikin ne. Ai yanzu Honey ya sauya sosai wlh,Karin ma barina da yayi yace in mun had'u na kara roka masa gafaran ki" Ni ko kai tsaye nace"Bai min komai ba na yafe masa" To ashe sai da ya kara aiko Anum,Takarda ce karama fara ya bata ta tura cikin sikat dinta rubutun Hausa ne layi biyu yayi aciki. "Ki yafemin Fa'iza. Daga karshe ina yi miki fatan Alheri da rayuwa mai inganci. fiye da yadda kika samu a zama na tare dake" "Ishaq sidi karofi" Sai naji Tausayinsa kad'an ya kamani yaga Takardan nayi ban ce komai ba Anum tace"Umma ya ki ka ga yaga..? Sai na kalleta kafin nace"Bata da amfani Anum. na yafe ma Daadan ku ko Saboda ku! Allah ya yafe mana Gabadaya" Sai ta rumgumeni tana fadin"Yauwa Umma daman ai Allah na son mai yafiya ko..? Sai na daga mata kai ranar dai uwa da y'a tare suka kwana har abinci tare mukaci bini bini tace Umma kaza tana kuma nane dani ranar ma ko waya bamu yi sosai da Engr ba jin Anum tazo kai tsaye yace"Ah'a muna da babban bakuwa to bari Baba ya daga ma yarsa kafa. na ara miki kanki ki kularmin da Diyata Sosai" Bai kuma hakura ba sai da na bashi Anum suka gaisa cikin sakewarsa kamar yadda ya Saba Radam ya rike sunayen su Amir yana ta tambayanta su Daya bayan Daya sannan ya tambayeta karatu tana bashi amsa daga karshe yace sai sun hadu a Benue. Bayan sun yi sallama ta bani wayar nima bamu jima ba muka yi sallamar ina sauke wayar Anum tace"Umma Sabon Baban mu yana da kirki" Kai na daga mata ban yi mgana ba,Sai da Safe ne Anty Fadila ta kawo min Sakon Zainab a wani kwali ne ashe Sleeping dress ne kala uku masu kyau da Tsada sexy na rike baki ina mamaki da na kirata in yi mata godiya sai tace"A sa ayi ma Yallabai kwalliya da shi. Don Allah white din nan ranar First nigt zaki saka shi" Kunya ma ta bani ina yar Dariya nace"First Night sai kace wasu yara" Shewa ta saki kafin tacr"ke kika san wannan, namiji baya tsufa ko shekara Dari yayi zai yi shagalinsa ni dai don Allah ki saka maman Amir ni fa a yar'uwa na Daukeki kin sani" Sanin Halin nacinta yasa nace mata zan saka mun jima muna taba hira kafin tayi mana fatan isa Abuja Lafiya sannan muka yi sallama. Duka shiri ake ta yi,su Ya Mariya da Anty Nasara sun fi kowa zumud'i tun asuba suka shirya karyawa ma sama sama suka yi nima nayi wanka cikin kayan lefena na saka Abaya doguwar Riga sukayi suka yi na yana mayafinsa naki na zuba Hijabina fari har kasa,sannan na fesa turare duk inda na Gifta ina tashin kamshi. Anum ma da Falaq sun yi wanka sun saka kaya iri d'aya na wani leshi sun saka mayafai sun kyau kamar yan Biyu. Mota bata zo ba sai karfe sha daya na Safe tun safe da muka yi waya da Engr ban sake jinsa ba. nima da zamu tashi na kirasa bata shiga sai nayi Tunanin network ne. Motar nan gabadaya ta Daukemu mu da kayan mu har da rara ma su Hafsatu kamar zasu yi kuka suna Dagamana Hannu Hajiyar su Raliya tace sai gobe zata taho Abujan tana taro yau Abba har da shi a masu rakiya ya yi min kuma dukkan nasihan da Uba zai yi ma yarsa. Shi da su Baba Ati da Inno tunda tun Daurin auren suke min har kuma da zamu tafi sai ga shi ina sharan kwallah Rayuwa kenan kana naka Allah na nashi kuma na shi Tsarin shine daidai. Da yake motar Sabuwa ne ga Lafiya karfe biyu muna garin Abuja,Direban baisan wajen ba,na kuma ta kara kiran Engr lambarsa bata shiga muna cikin Tararradi ne sai Kafaya ta kirani ita ta agaza tayi ma Direba kwatancen gidan su na gwarimpa tunda daman nan zamu fara sauka kafin Su rakamu gidansa na Abuja mu kwana kafin gobe mu wuce Benue din. Gidan su Engr wani katon gida ne Aljannar Duniya har ta Hajiyar Dala mai takama da suna da shi sai ta ce"Kai kun ga gida kamar a turai" Komai ba hayaniya cikin aji da kudi,Gida ne mai girma daga su sai ma'aikata acikin wannan wargajejen gidan Hajiya Shukra da kannenta mata su suka tarbemu tare da su kafayatu,munga karamci irin karamcin da bamu taba zaton suma sun iya ba,ko don ita Hajiya Shukran Bahaushiya ce..? Wani shashe mai falo biyu suka saukemu ashe shashen Engr ne Sharifatu ke fad'a,babu abunda babu a shashen na kayan more rayuwa,abinci ko kala kala da ababen sha ga su nan nama ko harda na Dawisu sai wanda kake jin ci. Sallah muka farayi kafin zaman cin abinci ni dai na kasa ci saboda rashin jin Engr,nasan kuma nasan shima bai Sameni ba ne shiyasa ban jisa ba. Direban da ya kawomu shima an sauke shi a daki na musamman an bashi abinci da abun sha ya huta zuwa Gobe tunda Har Benue da shi zamu je. Dakyar na iya tsakuran abinci shima sai da Ammi ta matsamin sai bayan mun gama cin abincin sannan Hajiya Shukra ta shigo sanye cikin wata shadda Doguwar riga taji aiki,ta ci Daurinta daga ganinta kinga bahaushiya mai ilimi da wayewa da sanin ya kamata ga ta da fara'a,haka hakoranta duk a waje ita da Sister dinta suna mana maraba da zuwa da tambayan Hanya. Su kafayatu ma basa kama da Engr sai dai kama ta jini ammh yanayin Fatan su iri daya ne,tsawon kuma ma Hajiya Shukra suka Dauko dukkansu zabga zabga ne masha Allah. Tana ganin su Anum ta kirasu tana tambayan su sunayen su dayake sun san juna da Ammi suna ta Hira tace"Wannan jikata ce ko..? Tafad'a tana kallona ni daman Tunda ta shigo kaina ma kasa tun kafin ma Anmi