Sashe 42
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bamu kuma da wata mafita sai dai su kofofin ubangiji ba su da iyaka in ya kulle maka wata kofar kafin wani Lokaci sai ya sake bude maka wata Sabuwar kofar. Dama bana ganin kowa kuma hakan bai dameni ba jamal ma ya jima bai leko ba ashe sun janye yajin aiki an koma makarantu,Nima ban sani ba ni ba Tibi ba Radio ba, ina nan dai Dim d'in sai abunda akazo aka fad'amin yaran ma tun suna damuwa da kallon har ya fita ransu na rika na cusa musu karatu acikin ransu shiyasa lokacin wasan su kad'an ne lokutan karatun su yafi yawa. Badariya ce da tazo ita da abokiyar karatunta Raliya sun taba zuwa sau biyu da ita,ita take fadamin sun koma makaranta cikin Satin nan sannan Jamal kuma Yamai sukaje shi da Mama sai shekaranjiya suka dawo jiya kuma ya koma makaranta,Sun iske na yi Tuwom masara miyar kubewa Bushasshiya Da yaji caryfish,sai tayi Dad'i sosai Badariya tace na zubo musu na kawo musu suka zauna akasan Cafet ita da kawarta ta suna ci suna Fira ni kuma ina gefen su Ahmad na jikina ya lafe. Kawar Badariyan ne ta Dago tana kallo na kafin tace"Gaskiya Anty Fa'iza kin iya girki sosai kiji kamar ka tsinke Hannu" Mirmishi nayi kawai ban yi mgana ba Badariya tace"ai in dai bangaran girki ne in kika zo wajen Anty Fa'iza ki yi Salute kawai Raly." Raliya tace"Naga alama irin su ne watarana sai ki gansu da Babban Wajen cin abinci" Badariya tace"Allah ya amsa bakin ki ai zata iya ta iya girke girken kala kala na zamani da na gargajiya" Raliya tace"Nasani ai wanchan zuwan Danwake mukaci da salad haka na koma gida ina ma su Hajiyarmu Zencen suka yi tamin Dariya suna fadin Duk Santi ne" Badariya ta kwashe da dariya kafin tace"basu karya ba santin ne" Atare suka yi dariya kafin su cigaba da cin abincin su sai chan Raliyan tace"Badar wai ina matar bro din ki da Lokacin ina Kaduna kikace an yi bikin?ko ba anan gidan take zaune ba..? Badariya tace"Tana Abuja tare da Yaya Ishaq ai yar chan ce ya aura har ta Haihu ma namiji Lawal suna kiransa Farhan" Kai ta jinjina kafin tace Allah ya raya sai da suka gama cin abincin Badariya ta kwaahe komai ta kai kichen,tazo ta sharemin Falon ina ta barshi bata ji ni ba,Wayoyin su suka dauka suna ta Latsawa suna Hira jefi jefi ni kuma ganin Ahmad yayi barci na mike da niyyar naje na shimfidar da shi sai naji Raliya na fadin"Ke Badar na manta ban fada miki ba, kinsan Hajiyar mu tana shiga kungiyoyin tallafa ma mata da marayu ko..? Badariya ta daga mata kai batare da tayi mgana ba ita kuma sai ta cigaba da fadin"To akwai wata kungiyar Womens Charity Faundation kungiyace ta manyan mata da suke tallafama mata da marayu domin su Dogara da kansu suna koyar da Training din sana'o'i da Dadama sannan in sun gama,suna ware kamar Mutane ashirin Hazikan ciki su tallafa musu da jari kyauta" Kasa kunnina nayi tun da naji mganar tallafama mata sai na koma na zauna inaji Badariya na fadin"Ni kuma meyasa duk kike fadamin wannan..? Raliya tace"Banza baki cin Ribam zencen..duk shekara suna zaban State din mu na arewa su zo su koyar da sana'o'in da kuma bada tallafin wannan shekarar katsinan mu ne har anbuga Form din Hajiyarmu guda Goma aka kawo mata shine nace bari nayi miki mgana ko zaki yi sai mu cike mu yi tare Allah Foudation di'n suna koyar da abubuwa masu kyau matuka komai da kika sani ko banza muma zamu karu" Badariya tace"Da karatun zamu ji ko da Koyan sana'a? Raliya tayi dariya kafin tace"Haka Hajiya tace da nace ta bani Form guda Biyu ni dake sai tace mu ji da karatun ma tukunnah yadda muke da son jikin nan ba abunda zamu iya koya" Badariya tace"Allah ya saka ma Hajiya da Alheri" Suka yi dariya a tare ban shirya ba kawai naji bakina ya furta"Zan yi..Badariya zan yi dom Allah" Gabadaya suka Dago suna kallona Badariya ta kalli Raliya itama ta kalleta suka kuma dawo da kallon su kaina cikin Sauri nace"In ba damuwa ni ina so zan yi" Raliya tace"Da gaske Anty Fa'iza..? Ciki jin dadi kamar an ce ma an Daukeni nace"In sha Allahu. Badariya tace"To ke kin ji Raly maza ki samo ma Matar bro di'na Form dim ta cike kuma ki fad'ama Hajiya" Raliya tace"In sha Allahu kuwa ai tashi zaki yi muje gidan tare ki mata bayani mu karb'o tare kada tace shiririta na ne" Da Sauri ko Badariya ta mike tana Fadin"Yauwa muje..Anty Fa"iza bari muje gidan su Raly din na yi mgana da Hajiya insha Allahu zaki samu" Kai na gyada musu ina ma Raliya godiya tace"Bakomai Anty Fa"iza ni dai don Allah ki dauki bangaran girke girke yadda zaki kara zama top a harkan sai mu bud'e gidan abinci watarana" Sai ta bani dariya ammh a raina na amsa da Ameen haka suka fita suia barni kamar an sakani a aljannah haka kurum nake jin farinciki acikin raina na fara Hango mafitar da na Dade ina rokon Allah akanta,sai dai jikina yayi sanyi ganin har kwana biyu Badariya bata dawo ba ballatana naji yadda suka yi,Sai da Satin ya shige wani ya shigo sannan tazo da Form din tana fadin ba kowa a gida ne shiyasa najita shuru cikin mamaki nace"Ina mama taje..? Badariya tace"Abuja suka je ita da Anty Binta" Na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Me ya faru..? Badariya ta tabe baki kafin tace"Farhan ne ba lafiya mura yake ta fama dashi har ta na hanashi Numfashi sai da aka kwantar dashi a asibiti Ya Ishaq duk ya Rud'e ya Rudar da su Mama sai da sukaje suka gansa Hankalinsu ya kwanta" Cikin jimami nace"Wayyo ya jikin nasa..? Cikin basar da zencen tace"Yaji sauki sun koma gida ammh naji su mama na fadin baban zainab din yace zasu fita da shi kasar waje a kara Duba Lafiyarsa Nimonia ce ke damunsa" Na nuna jimami na sosai ina ta addu'an Allah ya basa lafiya Badariya ta fito da Jakarta ta Dauko Farar Takarda Doguwa tana fadin"Kin ji Anty Fa'iza matso mu cike wannan Form" Cikin Farinciki nace"ashe kin karbo min? Badariya tace"Eh ai tun ranar mukaje nayi ma Hajiya bayani bata da matsala tana jin ma matar Yayana ce tace bakomai basai mun biya kudin Form d'in ba tace ki cike a maida mata in sha Allahu zata sanar in Lokacin Traning din yayi ammh akwai pasport guda uku kina da shi..? Na kalleta saboda ban gane me take nufi ba da Sauri tace"Hoto karami nake mgana wanda za'a lika acikin Form din sauran kuma za'a kai musu" Ta fada tana nuna min inda za'a saka Hoton sai na gane nace mata bani da shi sai tace"Bakomai in mun gama zan Dauke ki Hoto a wayata in na fita sai na Biya shagon Hoto a Wanke min a maida shi karami yau nake so naje na kai ma Hajiyar, Mama ma karya nayi mata da zan yi subbmitting wani aiki a makaranta" Kusa da ita na matsa ta sauka kasa saboda yadda zataji dadin Rubutu ta dago tana fadin"da Farko a jikin Form d'in sunanki ake tambaya" Kai tsaye nace"Fa'iza Sidi karofi" Ina kallo ta Rubuta sannan tace shekaru na gayamata sai kuma ina da aure..?ta saka eh ya'yana na wa..? Ta saka,sannan yaushe Mahaifina ya rasu na ce ta saka shekaru goma sha da Rasuwarsa ta saka,sai ina da Mahaifiya..? Nace ta saka eh,Sai ina da Sana'a ?in akwai wata sana'a nake yi acikin gida? nace ta saka Babu,Sannan matakin karatuna nace itama ta sani ko Takardan gama primary ai ban da ita Saboda ban gama ba sai Badariya ta saka matakin karatu na addini Saukakkiya a Qur'ani da Sauran Littafai. Na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Kada su k'i daukata Badariya kila sun fi son masu takardan ko Sakandiri ne ko Hafsatu zan bar mawa..? Badariya tace"Zasu Dauke ki in sha Allahu ai ba da Takarda zasu amfani ba, da Kwarewa ce ke kuma ai bana jin ki ta wannan bangaran" Ni dai duk sai naji jikina yayi sanyi ta cigaba da karantomin ko'ina tana Fassaramim yadda zan gane tace ance in da wata matsala ta fanni hallita ko wani ciwo..? Nace ta saka ina da matsalan ji,ta saka Hearing problem,Sai adireshin gida nace ta saka na gidan yayanta Daga karshe sai jerin abubuwan da zasu koyar akwai girken girken zamani da na gargajiya nace ta cike min shi saboda na kara kwarewa, sai Gyaran jiki dilka da Halawa nace shima ta Cikemin,sai kuma koyan yadda ake had'a lemuka kala kala nace shima ta cikemin akwai koyar da Kunshi Fulawa,koyar da manshafawa da su sabulan wanka da na kamahi sai koyar da su yaji kori da kayan kamshin Girki sai koyar da Turaran kamshi na Itace da kwallacha suma nace ta cikemin duk zan koya Badariya na Dariya tace"Anty Fa"iza duk ke kad'ai an ya zaki iya..?. Ina da yakini acikin raina nace"In sha Allahu ai basu da wahalan dauk'a zan iya da amincewar Allah" Ta amsa min da in Allah ya yarda sannan daga karshe akace in mutum nason a bashi tallafi yace eh ta sakamin eh sannan da kuma abunda zakayi da tallafin in an baka Na kalli Badariya ina fadin"Kice ina son a bani tallafi nan saboda na kama sana'a daga cikin sana'o'in da suka koyar damu..Sannan saboda na rike kaina na kuma tallafama rayuwar ya'yana saboda inganta goben su watarana" Haka kuma ta rubuta sai lambar waya nace ta saka min nata tunda ni bani da waya sai ko ta saka lambar wayarta. Daga karshen karshen sai saka hannuna ta bani na jagwalgwala hakanan,Kafin ta tafi sai da ta D'auki Hotona a wayarta bayan na saka Hijabi tace zataje a fito mata dashi a gyara muka yi sallama zuciyata ta cika da murna ammh ban daina saka Allah cikin lamarina ba adaran nayi salla sannan nayi addu'an Allah yasa mafitan nan ta zame min mafitan alheri a rayuwata gabad'aya. Ni dai ina ta addu'a ko da naji shuru ban damu ba daman nace in mafitan ta alheri ne Allah ya tabbatar