← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 175

Sashe 64

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainab sannan ga Farhan, da zasu tafi Yara har da kuka shima yaro ai yafi son inda yara yan'uwansa suke. shima Rigiman ya saka Uban ya lallashesa Dakyar,Anum kuka Musty kuka suma sai sunje sai Zainab tace na had'a musu kayan su ta tafi da su kamar zan ce a'a sai kuma naga bani da wannan Hurumin balle da naga Uban gayyar bai ce komai ba., sai na shiga Daki na Hada musu kayansu a jaka,ba masu yawa ba saboda bana so su rasa din Tahfiz din su,Allah ya taimakeni Ahmad na barci da shima za'a sha Rigima da shi. Ji na yayi ina fad'a ma Zainab kada su Anum su jima saboda hadda Karaf ko sai a kunnensa cikin Kaushinsa ya kalleni kafin yace"Kada ki kara nuna min iko akan ya'yana Fa'iza, ki kiyaye ni Wlh" Har yana nuna min hannu a raina nace shi kuma wannan me akayi masa..?sai nayi kamar ban jisa ba. Saboda Zainab da ya'yana yasa nayi musu Rakiya daganan gidan Mama suka biya suka musu sallama sai gida ya zama Dagani sai Amir sai Ahmad. Sun tafi ko sati ba su yi ba Yaya Isa ya kawomin Dankareren Fridge dina da Starplayzer,murna ta kamani sai da nayi kwallah na Shafa na taba nayi addu'an da Fatan nasara da Yaya isa zai tafi nace yace ma Goggo Hafsatu tazo ina nemanta haka ko akayi washegari sai gata ita nasaka ta zauna ta Rubutamin duka abunda zan bukata, ina so mu shiga kasuwa na siyo kayayyakin mahad'in sana'ar mai yawa yadda zai jima bai kare ba. Kamar Badariya tasan ina nemanta sai gata tana ganin Fridge din tace"Allahu akbar Anty Fa'iza wannan abun arzikin haka.? Ni dai sai Dariya nake yi,Farinciki ya kasa boyuwa a saman fuska ta, albarka tayi ta sakawa itama, sai bayan ta zauna nayi mata bayanin kudin da aka had'anin Daga Korafi taji dadi tace"Allah yasa a mizani"Zuwanta yasa sai ita da Hafsatu suka dinga tsara yadda komai zai fara sun yi mganar goruna, nace ina da wasu da na tara Badariya tace duk da haka za'a karo Saboda abun fa so suke ya habaka kuma ya shahara. Hafsatu tace"Kuma nan gaba kad'an har da Sticker zata buga a saka sunanta ajiki" Badariya tace"in sha Allahu muna fatan ya zagaya nageria gabad'aya wannan kunin ayan da zobon namu ai ba irin nasu ba ne" Dariya nake ta yi musu naga sun fi ni zagewa,Ranar bamu je kasuwan ba sai Washegari Badariya ta dawo muka tafi mu uku dayake nasan abubuwan hadawar shiyasa sai siyayyan bata Dauki Lokaci ba kudi basu fi dubu Goma ba suka Rage bayan mun Dawo gida mun siyo sabbin Goruna,na wajena wanda na Tara Hafsatu ta wankemin su tas a daran na Dafa ganyen zobon da Safe kuma na Had'a shi ni da Hafsat muka dura su a gorinaa muka saka su acikin Fridge dayake ba waje a kitchen falo na ijiyesa, kunin aya kuma nace sai naga yadda wannan ya fara karbuwa Ruwa daman Tun jiya Hafsatu ta saka aka siya aka Dura aciki. Bayan yayi sanyi na Dauka na aika ma Sa'adatu da Habiba guda uku uku, Dayake Hamsin hamsin nayi saboda Farkon Farawa ne,Shi lamarin Ubangiji daman haka yake ballatana ga wanda yasan Allah ke yi sannan ya maida lamarinsa a wajen sa, cikin Sati uku da fara sana'ata sanu a anguwanrmu,balle su Sa'adatu sun ta min tallah,Da D'aya d'aya Biyu biyu aka fara zuwa siya sai gashi an gane ni, da ina yin na mudu da rabi na zobo sai na Dawo na Tiya har da rabi,Ni kad'ai nake abuna Hafsatu ta koma gida Karofi Satin su Anum hud'u babansu ya Dawo da su kwana D'aya yayi ya koma kuma yaga komai tunda yana gidan masu siye siye suke shiga suna fita yadda bai min mgana ba nima ban damu da yasan komai ba,To ina ruwan kaska da kifi..? ni alokacin ma Sabgan gabana ta isheni. Ko wata biyu ban rufe da farayin zobo ba na fara had:awa da kunin aya, Ruwa kuwa Mota ke saukemin Haruna yayi min Hanyar motar ruwa take kawomin har Kofar gida tana Saukemin.Saboda Hidiman yara sun koma makaranta yasa sa'adatu takan shigo ta tayani Wani Lokacin kuma Badariya na lekoni,Itama ta bangaranta ba abunda zan ce mata sai godiya tunda taje da shi makaranta kawayenta suka sha suka fara santi, Tundaga b'atagwara suke zuwa siyan zobo na da kunin Aya na, Har kuma Lokacin Mama ko Anty Binta basu san halin da ake ciki ba. Ban rufe wata shidda da fara wannan sana'ar ba,na sanu sosai a rana na kanyin zobo fin ma Tiya hud'u kuma ya kare,Sannan na chaba Lokacin azumi nayi ciniki,sai na Dafa zobo sau biyu arana kunin aya kuwa na Tiya Biyar shidda duk yana karewa Musamman daga gidansu Raliya Direban su ke zuwa ya siya fin na Dubu uku in ji Hajiya balle da yake sanyi ga Dad'i ga gard'i sannan cikin Tsafta ba kazanta. Na aika da shi har Karofi Goggo da su Yaya mariya sun sha sun kuma saka albarka,Yaya Asiya ce kadai bata sha ba tayi nisa,na yarda da mutane da suke fadin in kana da abun yi na sana'a damuwa ma bata da wani muhalli a wajenka,to hakan ne ya faru dani ne, ni mantawa ma nake yi da ina da wata matsala tunda nasan dadin Goma Biyar shikenan Rayuwata ta sauya Daga duhu zuwa haske cikin Lokaci kalilan Allah ya Daukakani,Sannan nayi amfani da Damar haka na tallata ma mutane na ina had'a Turaren wuta humra da na Kamshin Daki, da kwallacha sannan ina yin Dikar Amare da Halawa. Duk da Ribar zobo da kunin aya na siya kayan amfanin wannan bangaran,Aiki na farko da na fara na Hajiyar su Raliya ce diyar kanwarta zatayi aure ta bani kwangilan had'a Turaren wuta na Rushi da na Humra,Sannan ni nayi ma Amarya Gyaran jiki,kuma ta bani kwangilar abinci,Kafin na rufe shekara na yi suna ta wannan bangaran Domin ina yin Girki a gida in dai bai wuce Takeway ashirin ba ko Hamsin,in ya wuce haka sai dai naje gidan masu sha'anin sai dai bana kwana wasu ni nake siyan komai na girki sai dai su bani kudin a Dungule in kuma yana da yawa sai dai na amshi kudin sallama. Taimakona D'aya da Hafsatu ta gama jarabawarta ta Dawo wajena ta na taimakamin,Su Mama sun ji na fara sana'ar kunin aya da zobo, to azaton su Sana'ar bata D'ore ba shiyasa basu damu ba.shi kuma Yaya Ishaq yana ganin komai ammh kamar an Daure masa baki bai taba min mgana ba, nimana zama Busy women ban da Lokacinsa balle na tsaya masa bayani. Sai dai na gayamai sana'ata ta jama'a ne,sannan ina zuwa kasuwa kuma in fita ta kamani ta bangaran kwangilan girki zan fita,sai yace min ai na zab'i Rayuwata sama da aure nayi duk abunda naga Dama babu ruwansa dani,tunda yace haka na fita Sabgan sa,to ni zai gayama aure..? Auran da a D'ofane ya ke..? Daganan ban kara bi ta kansa ba harkan Gabana nake yi,Ya'yana kuwa ba na yarda na shiga Lokacin su ko ya yane ina basu Lokaci na domin sune dukkan karfin gwiwata. ******* *BAYAN SHEKARU BIYU..* Katsina. *Layout* 8:12pm. Zaune nake saman sabon gadona da ban jima da sauyasa ba,ina ta had'a kayana da kwanakin nan nq maida Hankalina wajen hadasu waje daya. Duk wani abu daya Danganceni in dai nawa ne,wanda kuma bai da alaqa da ni,na bar shi,ina cikin zakulo kayan Wardrope dina na chan kasa kasa da na jima ban saka su ba, naci karo da ledan kayan da Anty Binta ta taba bani na Fadar kishiya auran Zainab. Wanda Yaya ishaq ya yi min kusan shekaru Biyar da wani abu ko Kallon su ban karayi ba,Bayan su ma akwai wasu na sallah da Mama ta tab'a aikomin sau d'aya,suma din banta Amfani dasu ba,na rika ware su agefe nawa wanda na d'inka da gumina da wanda yan'uwana suka Dinkamin ina ware su a gefe daya. Kamar wani abu ya shiga kaina sai na Dakata na koma nayi Tagumi da Hannuuwana Bibbiyu.shin hukuncin da nake shirin Dauka bazai shafi rayuwata da na ya'ya na nan gaba ba..? Sai wata zuciyar tace"Ko ban zabi hakan ba.Hakan ya dace domin babu amfani cigaba da zaman". Da haka na kara samun yakinin cigaba da aikin gabana,Ban ji shigowarta ba sai ji nayi an fad'omin a saman kaina har sai da na Tsorata Ina Dagowa naga Anum sai na bata rai ina Fadin"Bansan sangarta ke har gobe baki girma Anum..? Baki ta tura kafin tace"Umma yaya yace ki zo lokacin karatu ya kusa" Agogon dake dakina na Daga na kallah, karfe takwas da rabi ya wuce da sauri na Dafe kaina kafin nace"Ban san lokaci ya tafi ba,muje kada Mallam Amir yamin Bulala" Dariya Anun ta farayi lokaci d'aya tana fadin"Umma sai Yaya ya dake ki..? Ina Dariya nace"Sosai malami na ne fa, in na makara zai min Bulala" Itako abun ya bata dariya ina rike da Hannunta har tsakiyar falona,Wanda ya sauya yanayi a baya kujerun duk sun mutu da Cafet d'in ammh yanzu na Sauya sabbin kujeru da Italian Cafet sannan na sauya ma falon da Dakunan Sabon Fenti na siya ma yaran Sabon Tibi,Ko a yanzu ma Mbc3 ke aiki shi kad'ai ,Ahmad ne ke saka rigiman sai an kunna masa. Kanwata Hafsatu na kalla dake kan kujera ta kishigid'a da katon katakon ta na yanka salatif, Anum nace ta yanka ta yi mawa da Daddare nagaji da ganinta da Farar kafa,Musty na zaune a kasa inda Karamin allo yake kafe a Tsakiyar falon,Amir na kallah dake tsaye yana faman rubutu da Alli. Hafsatu ta Dago tana fadin"Umma ta makara yau" Ina yar Dariya cikin yanayina nace"laifin ki ne.da baki ankar dani akan Lokaci ba" Zama nayi a kasa kusa da Musty,ina leka abunda yake rubutawa a littafinsa cikin dariya yace"Umma zane nake yi" Fuska na gyara kafin nace"Sarkin zane fa to me ake zanawa yaron Umma? Da Sauri Anum ta leka sai ya Boye yana bata rai,ta na kokarin kwacewa ganin sun fara kokawa sai na Raba fadan ina fadin"Anun koma ki zauna yaron Umma nuna min abunda ka ke zanawa.? Sai da ya boye kada Anum ta gani
Chapter 64 · 0% Book details