Sashe 87
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
murya yana fadin"Fa'ii...ki zo ki tayani barciii..'" Lokaci da'ya yana matseni a jikinsa inaji ta baya abu na dukan bayana na rikice iya rikcewa kamar wata gaula,Yana shirin ya kai hannunsa akasan zanina na shammacesa nayi kasa bai zata ba sai ya koma kan gado ya zauna Dabas ni kuma kamar wata yarinya sai na saka gudu na fice Daga Dakin, Allah yasa masu siyan zobon suna tsakar gida da sun sha kallon yadda na fito a razane,Kitchen na shiga ina Sauke numfashi har Lokacin Salon sa da Sautin muryansa basu bar jikina ba sai da na Huta sannan na samu ledan Aya na juye cikin wani Bokiti na zuba musu zobon na fita na mika musu shima ganin na gudu sai bai biyoni ba,Ranar wasan buya na rika yi masa bana son ma mu had'u,Da daddare dukkanmu muna falo shi yake koyama Amir lissafi ni kuma ina Rubuta ma Ahmad Huruful Hija'iya a wani Takarda inda zai ta maimaitawa Saboda ya iya rubutawa da karantawa,Dagowa goma sai naga idonsa kaina Lokaci da'ya yana dagamin gira da na Fahimci haka sai na daina yarda ina dagowa na yi kamar bashi ma afalon da zamu kwanta yayi ta tsiro da sani aiki ni kuma sai na saka ya'yansa daga karshe sai ya kalleni yana fadin"Fa'iza ina jin zafi ina so nayi wanka" Ban kallesa ba nace"Amir tashi kaje famfo ka tarar ma baban ka ruwa in ya cika Hafsah sai ta Dauko" Sai ya bata rai har Amir ya mike sai yace"Kai koma ka zauna. ke na saka in kuma baki yi shikenan" Ina kallon rubutun gabana nace"To Abban Anum baka ga aiki nake yi ma yara ba..? Amir ko sai ya mike yana fadin"Daada bari na cika maka" A chunkushe ya mike yana fadin"yi zaman ka zan yi da kaina" Dariya ta kusa kamani sai na Danne da kansa ya fita ya Debi ruwan yazo ya kai tiolet din Dakinsa, chan kuma ina Murnan na rabu da k'aya sai ga shi ya leko yana fadin"Baki shimfid'a zanin gadon da kika wanke ba ne Fa'iza..?daman yasan nayi wanki jiya kuma har da kayansa na wanke da zannuwan gado saboda bana so na shiga Dakin ya Ritsani ne yasa naki shiga na maida zanin gadon, sai kawai na kalli Amir ina fadin"Yana nan saman Dirowa dauko ka kaje ka shimfid'a masa" Ai ban gama Rufe baki yace"Bar shi bana so' Daga haka ya koma Daki sai da nayi Dariyan data kawomin Amir ya kuramin ido ina Dagowa muka had'a ido sai na Dauke kai ammh yaron nan sai cewa yayi"Umma Daada ne ya saka ki aiki fa..? Sai na ware mai ido ina fadin"Eh Daadan fa sai akayi ya ya..? Sai ya kasa mgana araina nace ji yaro da iyayin tsiya to dai har muka shiga barcin ban kara ganinsa ba ni kadai in tuna yadda ya yi jiya sai naji Dariya tazo min,Washegari da safe da ya fito na gaishe sa a dake ya amsa kayan karyawansa kuwa yana fita rakasu makaranta na shiga na ijiye mai na fito. sai da ya dawo ya iskeni ina karyawa a falo yana ganina sai ko ya zo ya zauna karshe dai tare muka ci ni dai ban sake ba sai da muka gama ne ya kalleni yana fadin"Yanzu abunda kika yi jiya kin kyauta kenan..? Ido na waro kafin nace"Me nayi..? Sai ya yi wani kamar maraya kafin yace"Au baki ma sani ba ko..?jiya nace ki gyaramin shinfid'a kika saka Amir ko..? Sai na dukar da kaina ina fadin"Ai lokacin ina ma yara a karatu ne" Ban dire ba ya tareni da fadin"Ko kina menene in na kira ki na sakaki aiki zaki ijiye kizo ballatana gyaran Shimfidar miji. Kin ga jiya kin kwana mala'iku na fushi da ke" Mamaki ya bani na kallesa sai yace"Eh mana ai kin fini sanin haka tunda Lokacin kina gaban Mama a kwai ki da son zuwa islamiyan nan ta la'asar" Araina sai nace ashe ya sani ganin ya nace da mganar ne yasa nace"To kayi hakuri" Nan da nan yaji dad'i ya washe baki yana fadin"Yauwa ko kefa yar albarkata. Ina fatan in nakara kiran gyaran Shimfid'a baza'ayi min gaddama ba ko?.sai na gyada mai kai saboda ya kyaleni aiko bai barni ba. sai ya rika jana da Hira yana shigemin ni ko ina baya baya labarai har da wad'anda basu Shafeni ba abun mamaki har yana tambayata yaushe zamu je karofi mu gaida su Goggo..? Sai kawai nace ranar da ya shirya sai yace sai weekend saboda yara. Ban ko tsaya mamakin sa ba domin yanzu ya daina bani mamaki in dan yayi wata mganar ko ya yi wani abun. Jamal ya yi shirin komawa makaranta acikin kayan abincin mu na dibar mai Taliya da shinkafa da man girki sai na bashi Dubu goma, biyar yayi pocket money, biyar yayi na mota nace in na samu zan bama yayansa ya Tura masa ya karba yana ta godiya har yana fadin"Allah ya kawo babban Shago Matar bro.' Ina yar dariya na amsa mai da Ameen haka ya tattara ya tafi to yayan bai da ko sisi yana nema nema. itama kanta Maman bata da shi kawayenta duk sun gajeta ba wacce tafi bani mamaki sai Hajiya Barira bata zo ba tun bayan da Yaya Ishaq ya fito Sannan Mama ta shirya taje gidanta bata sameta ba,Kuma bata biyo sahu ba kuma bata Hakura da binsu ba shine da yagaji ya yi mata mgana fadi yake yi"Mama yanzu rayuwar nan ba irin da ba ne. In kana da shi ayi dakai daga Lokacin daka rasa bamai son rabarka ka zame masa wahala Mama.ni kaina alokacin da nake dashi abokai har da na banza kuma ai mun taimaka musu ammh yanzu ko kare bana gani ballatana kira an san bani da shi kowa Tsoron haduwa dani yake yi kada na gayamasa matsalata" Ko nace ya taimakeni" Mama ta gyada kai tana fadin"Uhm nagani,ammh na Dauka ko kowa zai gujeni ban Dauka harda Hajiya barira ba, ta bani mamaki kamar mafa blooking dina tayi fa"Dariya yayi yana fadin"Shi yafi komai sauki Mama bazata yarda ku hadu ba, tasan baki da shi yanzu zaki yi Tunanin samun wani abu daga barayinta, a baya kina da shi kuna nima ina dashi kinga dole ta rab'eki ki kama kanki da kowa kawai ki Rumgumi kaddaranki Mama kina gani ko a yan'uwa sai wanda yaga Allah ne yake tunawa dakai in ka shiga Halin babu, sai kuma wanda ma kake tsammanin zai tsaya maka ranar da baka da shi, sai kiga shine ke baya baya dakai. wanda ka gujema Lokacin da kake da shi shine in ka shiga Halin Rayuwa zai taimake ka" Mama na hawaye tace"Hakane wlh nagani Ishaq" Tana tuna Hajiyar Dala ko wayarta bata son dauka yanzu. Ammh Goggo ko bata zo ba zata aiko da Sakonta tabbas Lokacin da suke da shi basu mu'amalance ta da kyakyawan mu'amala ba,ammh ita bata rike su ba ta Duba zumunci ta kuma bi Umarnin Ubangijinta.. Nan ya fice yana fadin"to haka halin mutanen duniya yake Mama Lokacin da kake da shi ayi da kai, in kuma baka dashi ayi da wanin ka" *Janafty* *KNKB2009* *Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* Haka muka cigaba da lallab'a Rayuwarmu yau fari gobe Tsumma. abunda aka samu aci agode ma Allah ba domin ina samun,masu son Turaruka ba,da tuni jarin Zobo da kunin aya sun Dargane da Hidiman gida na yau da kullum,To riban da nake samu na turarukan,sun fi na su auki. da shi nake had'awa muna rufa ma juna asiri sannan Allah ya sanya ma kasuwancina Nasibi komai na yi sa sai ya kare kuma ana nema,Shi kan shi Yace min ya gaji da zaman gida ba abunda yake yi ranar har ce min ya yi ko zan fara doramai zobon da kunin Aya ne yana zuwa tasha ya zauna min..? Sai da naji kwallar Tausayinsa na kallesa yana bakin kofa zaune duk ya rame ya lallace ba wannan farin ba kyau ba fafa ba,kwanbo rayuwa kenaan. A lokacin ban ce mai komai ba sai da ya karamin mgana sannan nace mai"Ko fita da shi baka ga inayi ba, a gida ake siye shi. Kai ma da wata mgana ka ke" Cikin bayyana yanayin dayake ciki yace"Bazaki gane ba ne Fa'iza wlh na gaji ne ko Dako zan je na fara ne..? Na kallesa ina maimaita"Dako..? Sai ya gyad'amin kai yana fadin"Shima sana'a ne kuma akallah zan rika samun wani abun da zan rika taimaka miki da shi" Da sauri nace"Aa ka bari dai mu yi Tunanin wata sana'ar tukunnah" Da haka ya bar mganar tunda muka yi wannan mganar sai ta Dameni sai naga yana da gaskiya shi magidanci ne,zama agida kad'ai ya isa yasa bawa Damuwa na yi ta tunanin sana'ar da zai fara ban samu mafita ba, yanzu fa ko wata sana'a ta kudi ce sai kana da shi,ni kuma d'an jarin nawa kad'an ne Riba kuma agida muke cinye su don ma yan'uwa suna ta tallafawa. Babban sallah tazo tana matsowa bani da matsala tuni na wanke ma yara kayan su na goge ga kuma na wajen Zainab, daman basu saka ba,ni daman bani da matsala in dai ya'yana zasu saka su fita cikin tsara Allah ya gama min komai Mama bata nan ta tafi Yamai da Hure zata koma sai ta bita,tafi wata achan ina jin Yaya Ishaq na fadi'n kila chan zatayi sallah Sai kuma naji gidan ba Dadi ba Mama ko yaya mutum yake Rahma ne haka ma yaran su yi ta fadin"Daada yaushe Mama zata dawo..?sai yace"Zata dawo in sha Allahu" Ga Hafsah ma sun yi Hutu ta koma korafi tayi ma su Goggo Hutu, Badar kuma tana gidan Anty Binta suna ma Jarabawar Fita ne bayan sallah zasu gama makarantar gabada'ya ita da Raliya tun nesa da kofa tazo ta sameni tace min"Anty Fa'iza zamu gama makaranta akwai kudin riga da zamu yi na graduation din mu, wajen dubu ashirin ake so