Sashe 71
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da na yara sai kujeruna sai kayan sana'ata da kayan amfanina na Kitchen, sauran kuma aka kira Dilallai suka yi musu kudi hakama gidan Mama kusan rabin kayan duk sai da su akayi abun akwai tausayi sosai Yan'uwa ma sun mana kokari Goggo ashe bata zauna ba ta saka ya'yanta suka hada kudi Dubu dari ta kawo tace a kara ita Hajiyar Dalan ma ba wanda ya kara jinta Ina gani Yaya Ishaq nata sunne kai kunya duk ta kamasa. Da kudin da Anty Binta ta hada da wanda mijinta ya taimaka harta Dangin mama suma sun taimaka aka Hada Miliyan Daya da rabi da su,aka samu gida acikin gari sai kuma Allah ya saukaka mana abun kusa da makarantan yara ne, ko ba abun hawa zasu taka da Kafarsu,Gida ne flat na daidai misali,Shashen Farko falo da Bedroom guda uku sai Kichen sannan kowani Daki akwai tiolet sai dayan Shashen Bedroom biyu da falo ba kitchen sai tsakar gida sai daga wajen Koridon kofar waje akwai wani Daki sai akace Jamal zai zauna anan. Tun kwana Biyu kafin Wa'adin ya cika kayan mu suka fara yin gaba mu zamu zauna a mai Dakuna uku, mama kuma da Badariya zasu zauna a dayan Shashen,Allah sarki Rayuwa Daman KANA NAKA ne shima Allah ya riga ya gamasa nasa,ranar da zamu tashi yara nata murna zamu tashi,har gwara Amir shi ya fi so wayau. Ni kaina sai da nayi hawaye inda ka saba da kewar yanayin rayuwa su Sa'adatu duk da su muka kwashe sauran kayana sannan nace don Allah ta gwada sana'ar zobo saboda mutanen dake barayin kada ciniki ya Gudu bayan na tashi,tace in sha Allahu zata jaraba. Su Mama su ma a ranar sukayi parking din komai,Goggo bata zo ba ammh Anty Nasara tazo ita da Yaya Asiya muna tare da su da Hafsat da makota na bangaran su mama kuma yan'uwanta da su Anty Binta. Yaya Ishaq da jamal su suka samo motocin da suka kwashe kayan suma sai da suka Chaji kudad'e masu yawa. *Janafty* [7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2003* *Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* Kafin mu karisa chan gidan sai ga Matar Yaya isa tare da kanwarta,Yaya mariyasa nasan bazata zo ba.duk da ta bada uzurin bata jin dadin jikinta,ammh ni nasan dalilin ta. tare da su da makotana su Sa'adatu muka tare a daidaita zuwa anguwar Ajiwa,koda mukaje mun iske su Mama achan,Gidan mai kyau ne saboda sabon gida ne sannan wanda ya zauna agidan bai dade ba ya tashi. kuma basu lalata gidan ba,ammh dai yaya Ishaq ya sake fenti ya gyara bayika sannan an gyara glop din wuta in da suka samu matsala shi kan shi da'n wannan gyaran sai da ya ci kudad:e sosai. Mun iske su Anty Mahma har sun gyara barayin da mama zata zauna,bata dawo da wasu kaya ba Falon kujeru biyu aka saka sai cafet. sai Dakin Badariya katifa da Wardrope sai kayanta, Dakin mama ne aka jera mata gadonta da wadrope dinta,Da muka zo sai da muka shiga Shashen Mama muka ga waje muka saka albarka yara daman tuni Jamal ya taho da su nan muka iske su sun warware suna ta murna abun ka ga yaro Amir ne kadai muka zo tare da shi. Da taimakon Anty Mahma da su Yaya Asiya suka share bangaren da zan zauna suka gyaramin, sun maidamin kujeruna a falo da Cafet sai tibi. wanda naso a had'a a saida Yaya ishaq yace a barta tunda an saida na bangaransa,Duka kayan kitchen dina sun koma Saboda yana da girma har babban Freezerna,na kasuwanci ya samu waje da Buhu buhun robobina da sauran aya da ta ragemin sai Ganyen zobo da sauran kayan abincin da muka dawo da su, suka jeramin a Store din kitchen sannan suka gyara Dakin Yaya ishaq kusa da Dakin yaran ne da aka jerama gadajen su da wadrope din su,Shima katifa ce kadai sai akwatin kayansa sai Cafet karami na tsakar daki ni kuma suka maidamin gado na da sauran kayyakina kafin yammah waje ya fito ya yi kyau suka wanke tsakar gidan tas ya bushe gwanin ban sha'awa abun da yafi burgeni ta bangaran shashena akwai Daga gefe wani karamin Rumfa kamar na shan iska inda a raina nace zan rika hada hadar da sana'ata a wajen. Hafsatu ta yi abinci na saka aka dibar ma su mama,aka akai musu da shi,Saboda Dare dukkan nan suka kwana Anty Mahma ce ta koma gidanta har Anty Binta nan ta kwana Yaya ishaq kuma suka kwana Dakin korido shi da Jamal, sai da safe bayan an karya suka fara shirin tafiya. Yaya Asiya da Anty Nasara suna min fada da nasihan kan sai na ninka Hakura na wajen iya zama da mama, in a baya zama bai had'amu ba yanzu kuma ya had'amu sai na zama mai Taka tsantsan da kiyayewa. Ban ce musu komai ba. ammh ina ji a raina zan iya zama da mama a kowani Hali ai ni ba bakuwar cin mutumcinta ba ne na riga na saba da Hallayarta na zauna da ita tsawon shekaru fin biyar naci wahalarta bayan kuma na auri Dan'ta ban tsira ba, to ban ga abunda zai bani tsoro akan hallayar Mama ba. Kafin azahar suka koma karofi narakasu har bangaran Mama suka mata sallama bamu fahimci yanayinta ba,sama sama ta amsa tare da yi musu godiya,sai da suka tafi naji wajen yayi min bambarakwai irin baka Saba ba Hafsah dai tana ta kara gyara dakunan,su Anum kuma suna ta Murna Musty har ce min yayi"Umma ina son sabon gidanmu' Nayi mai mirmishi kawai ban ce komai ba araina ina jinjina yarinta Amir ne kadai yasan halin da ake ciki Anum kuma uwar Shiriritace Dadi suke ji ganin har da Mama ta Dawo gidanmu da zama basu Dakinta basu Shashen da muke basu tsakar gida suna murna,Abu daya yasa gidan ya sakeni Burgeni akwai ruwa sosai domin akwai Famfo a tsakar gida, sannan suna da wuta kamar anguwan da muka taso,sai dai ita wannan anguwan tafi cika da mutane daidai misali ba kamar na masu hali da dukiya ba. kwanan mu biyu a gidan sauran kud'aden da suka rage Hannun Yaya Ishaq ya yi mana siyayyan kayan abinci da su, da suka dawo siyo cefanen kayan abincin.Dakin Mama suka sauke komai ina cikin Dakin yaran ina gyara musu kayan da yake duk an hada kayan ne waje da'ya basu raba musu ba, ni kuma da na samu natsuwa sai na zauna ina ware ma kowa nashi ina saka musu a inda ya dace. Sai ga Anum tazo kirana in ji Daada na kalleta cikin mamaki sanin baya nan tun safe ya fita cikin yanayin mgana nace"Ina Daadan yake..? Kokarin hawa kan kayan da nake kan gyarawa tayi na hanata ina Hararanta sai ta juya tana Tura baki kafin tace"Yana Dakin Mama" Jin haka yasa na tsaida abun da nake yi na fita falo na Dauki Hijabina Hafsah na zaune a kasan cafet tana Duba Littafinta Amir na gefenta kamar yana gane me take rubutawa na Fice ina fadin"ina dakin Mama" Suka bini da toh da sallama na shiga,Na iske Mama zaune kan kujera jamal na gefenta yana danna waya Yaya Ishaq na nesa da ita ga kayan abincin nan a falon ta Badariya bata nan taje gidan Anty Binta da Safanan. Har kasa na duka na gaida Mama da gida ta amsa a Dake kafin ta kalleni tana fadin"Kayan abinci ne ya rikita da Sauran kudin da suka rage a hannunsa ya siyo.Shine yayi mganan za'a sauke a bangaran ki zaki rika Dafawa kina bamu nace ya kiraki gaki ga shi ga ni,ki fad'a da bakin ki in zaki iya dafa mana abinci kina bamu bana son abunda raina zai rika baci Daga baya" Kalamanta sai suka bani mamaki na Dago ina kallonta shima na juya muka Hada ido sai ya Dauke kansa nima sai na maida kaina kasa cikin Ladabi nace"Ai mama ko ba na auran Yaya Ishaq kina da hakkin da zan dafa abinci na baki indai muna zaune waje d'aya bakomai bazai gagara ba, da yardan Allah" Kai ta daga sama kafin ta karkace kai tace"Shikenan a kwasa a kai dakin ki" Har na mike zan fice tace"Sai a bi a hankali kin dai gani ba irin baya ba ne lokacin da akwai, yanzu babu. sai kiyaye da barna Ahto" Ban ce komai ba na fice a raina ina mamakin Mama yadda bata kaunar taga na zauna lafiya cikin Aminci sai ta Kirkire wata mgana da zata zama cin Fuska a gareni. Jamal ya shigo da kayan ina Dakina Hafsah ta leko tamin mgana nace ta gwadamai inda zai saka su,Ita ta nuna mai Store ya shiga ya jera komai ba wani abun sakawa a fridge sai kayan miya,sai kayan lambu da suka siyo ba su da yawa,Tun daga ranar ni nake abinci Safe da rana da yammah har Dakina nake kai ma su Mama cikin wata Cooler mai girma yadda zai ishe su ita da jamal da Badariya,Ni kuma na ji da Yara sannan da Babansu kamar yadda wahalan komai nasa ya dawo wuyana yanzu tunda yana gida bai fara fita ko'ina neman aiki ba, kamar yadda yace zai fara fita ya gani ko za'a dace. Da kaina na shiga makotan mu gidajen da ke kusa damu muka gaisa na gabatar da kaina a matsayin makotan da muka dawo anguwan cikin Satin da ya gabata, na daina barin kaina Cikin Duhu tunda na san shiga mutane nada Dadi ban kara yarda na zauna agida ba. Duk kuma inda na shiga sai yi musu tallar ina Saida zobo da kunin aya, sannan ina hada Turarukan wuta na Daki da Humra da kwallacha sannan ina Dilkar Amare na gyaran jiki,Sai girke girken suna biki ko walima na kuma ce su min tallah wasu har suna tambayata ko akwai zobon nace ban fara ba tukunnah,sai mun natsa agidan, sannan sun tabbatar min da zasu siya Insha Allahu sai naji dadi kwarin