Sashe 107
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
harareni yana fadin"Tambayeta ita ai tasan komai" Sai ta juya tana kallona kafin tayi mgana na tare ta da fadin"Kada ki biye masa bansan abunda yake mgana ba"Saboda kada ya kara mgana na yi wuf na fice ina sauke Numfashi,shikenan ma'auratan suka Daidaita kansu,Sati daya tayi mana sannan ta koma ta kuma ta tabbatar min zata yi kokarin ta ijiye aiki sannan ta Lallabi Daddy ko gida ya siya mata a nan ni ko araina nasan Yaya Ishaq bazai yarda ba. kuma Tsakani ga Allah wannan gidan yayi mana kad'an ace mata Biyu da yara ga Mama shima ai sai ya Duba ammh yadda bai sakoni aciki ba nima ban Tusa kaina ba.. Maganar auran Halisa ya taso Anty Binta ana ta shirye shirye ni dai nace zan gyara amarya ta bangaran jiki da kamshi,kuma Anty binta na fad'amawa sai gashi tana min godiya sannan tamin mganar zatayi Zobo da kunin aya ranar walima tana so nayi mata,girki ma in ba damuwa na shige gaba ban nuna mata komai nace duk zan yi,mun yi waya da Badariya tace bazata dawo ba,ni na bata baki tace zata dawo ana gobe Daurin aure tunda kano za'a kawo amarya sai ta biyo su ta dawo abunta nace shikenan kuwa. Da kudina na siyo kayan hadin Turaruka na had'ama Halisa da na Rushi da Humra da kwallacha sun kai na Dubu ashirin,sannan ga na gyaran jiki tun ana saura sati daya biki take zuwa kullum da yammah ina mata Gyaran jikin. Ranar da muka kwana uku muna yi sai dare na gama mata,ita da wata kawarta suka zo,kuma tare suka tafi a dakin Mama nake yi mata ita tunda ta gidace,Mama sai mamaki take yi tana fadin"Ikon Allah.." Ranar na gaji,ko zobon yammah ban Dafa ba Hafsah na makaranta,bata dawo da wuri ba,Ban iya ko yin abincin Dare ba saboda bayana ya rike sai nayi wanka na gasa jikina da Ruwan zafi nayi sallar mangariba ina zaune ina lazumi Hafsah ta shigo ina ta mata fadan ina ta Tsaya sai tace min bata samu abun hawa ba ne da wuri, sai na Sassauta nace in ta huta ta Dafamana ko Cousscouss ne. Tace to bari tayi sallah Yaran kuma suna Falo Yaya Amir na biya musu karatu ina jin tashin muryoyin su daga Falo,Chan sai ga Hafsah da wayarta ta kawo min Abba ke son mgana dani bayan na dauka mun gaisa yacee"Kuna lafiya ina matata da megidan naki..? Nace"Duk suna lafiya Abba" Sai yace"To madallah kan mganar Binciken da nace za'ayi kan Case din mijinki ne,Engr ya dawo nayi mgana da shi yace ba matsala sai dai zamu kara jira Tunda mahaifin nasa yana London Mahaifiyarsa ke chan za'ayi mata Dashen koda. hankalinsu duk ba'a kwance yake ba shiyasa har yanzu bai yi masa mgana ba" Sai nace"Ayya Allah ya bata lafiya Abba"Sai ya amsamin mud'an taba Hira har ya bama Ammi muka gaisa tana min Tsiya"Hajiya Fa'i mai turaran kamshi" Dariya nayi ina fad'in"Kai Ammi" sai kawai tace"Abban ki ma yace y'ata ta iya had'a Turaren kamshi" Kunya suka bani su ko ba ruwan su Abba da Ammi sai su,mun gama wayar kenan naga mutum tsaye a kaina ina dagowa cikin mamaki nace"Sannu da zuwa" Sai kawai yace"ina son mgana dake. ki sameni a dakina" Daga haka ya fice mamaki ya kamani na rike haba a fili nace"Topha..! Ina shirin tashi aka fara kiran sallar Isha'i sai na mike nayi salla na idar kenan na mike ina ninke Darduma Anum ta leko tana fadin"Umma Daada na kira" Sai na gyada mata kai ban ko cire Hijabin jikina na fita zuwa Dakinsa ina Shiga sai faman safa da marwa yake yi har sai da nace"Lafiya..? Kai tsaye yace"Ina jin yunwa ina abincina.." Kai Tsaye nace"Aiki nayi nagaji sai da Hafsah ta shgo nace ta dafa mana ko Taliya" Sai kawai naga ya karisa ya rufo kofa da Sauri nace"Ya da rufe kofa..? Yana juyowa yace"Yau zamu yi ta kare Fa'iza hakki na zaki bani nagaji" Gabana ya fadi na kwalolo ido waje hakkina..? Na maimaita a raina. na shige su ga shi in nayi wani ihu yara na falo suna jin mu. bakina yayi nauyi ina ji ya ja har hannuna bakin katifarsa ya cire min Hijabin jikina cikin rawan murya nace"Abincin fa..? Kai Tsaye yace"Zamu ci in mun gama. Fa'iza bazan iya jira ba" Bakina naji yayi wani Dif. Jikina kuma Kamar mara Lakka, kamar rakuma da akala haka yafara bi da ni a gaggauce kamar daman ni yake jira. *Janafty* [7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2017* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* Saboda yanayin da zuciyata take ciki yasa kwata kwata gangan jikina bai karb'i sakonnin dayake aika min da shi cikin zafin nama ba,Doguwar riga ce a jikina har ya samu nasaran Rabani da ita,ammh na kasa wani motsi na riga na Sadakar bani da wani Tsumi ballatana Dubara a lokacin. Bakina ne yayi min wani irin nauyi, ina ji kamar ya kumbura saboda irin yadda Yaya Ishaq ya rika sumbatata a raina sai cewa nake yi daman haka Sumbarta take..? Sharaf nayi masa ko hannuna ban yarda na motsa ba,kwance nayi masa kamar ruwa ya cinye ni,Ina jinsa yana gwama Numfashi,sama sama sannan Lokaci d'aya yana sauke ajiyar rai chan naji yana kiran sunana fad'i yake yi"Fa'iza ki rikeni. Ki rumgume ni don Allah"Ya fad'a cikin wani irin yanayin da ba kowa zai iya sanin yanayin ba. Nayi masa banza kamar ban ji ba, kuka ne ya taho min daga karkashin Zuciyata sai hawaye sharr sannan na saki Shesshekan har yana jina. Sai naji kamar an zare masa lakkar jiki ya koma ya kwanta a gefe yana maida numfashi. ni kuma ina ta kukana sai ya mike zaune cikin yanayin Sarkewar murya yace"Yanzu Saboda zan karbi Hakkina ne yasa kike wannan kukan Fa'iza.? Shuru nayi masa ban yi mgana ba sai dai ina cigaba da kukana kamar karamar yarinya sai kawai ya mike Kaina na juya gefe har ya gama Suturtata jikinsa,ina daga kwance kawai naji ya yi wuf ya tadani zaune yana fadin"Tashi ki saka kayan ki" Sai na bisa da kallo ina Tunanin ko ya fara samun matsala ne ganin yana komai a gaggauce. Mikar dani Tsaye ya yi ya na kokarin sakamin rigar na rike hannunsa muryata a shake nace"Bari zan saka da kaina"Kamar wacce zan gudu ina gama sakawa ya jawo hijabi ya zuramin Saboda Sauri kamar zai ciremin kai, nayi baya ina kallonsa da Tarin mamakinsa Maikon hawaye sun cikamin ido ban samu damar mgana ba. kawai ya finciki hannuna ya isa ga kofa ya Bude yana jana muka fito Falo yaran duk suna falon suna ganinmu suka bimu da ido ganin yana kokarin Fita daga Dakin yasa na Turje ina fadin"ina zaka kai ni..?. Bai ko Saurareni ba ya fincikeni zuwa waje sai kawai naga mun shiga Dakin Mama Lokaci d'aya yana fadin"Mama kin kwanta ne..? Mama na zaune saman kujera da waya a hannunta kamar ta ma gama wayar ne muka fad'o dakin yadda ta ganmu ne yasa ta mike a firgice tana Fadin"Kai lafiyan ku kuwa..? Gabanta ya zaunar dani yana Fadin"Mama gata nan ta fad'a miki meyasa take hanani Hakkina..? Ki tambayeta meyasa take guduna bata kaunar na rabeta. Mama Fa'iza na gudu na a Shimfid'a" Shi yake mganar nan ammh ni kunya da bakinciki sun rufemin ji na da ganina na wani Lokaci,Tsabar yadda na kad'u na girgiza da wannan wulakancin na Ishaq .ashe shi yana da bakin mgana ban sani ba..?ni shekarun da ya kwashe a jingine da aurene wajen wa na taba kai karansa.?sai shi ne yake da bakin mgana." Kaina na dunkule a kasa ina kuka kamar na mutu haka nake ji Saboda kunya ita kanta da Mama sai da ta kasa zama kunya duk ya Rufeta ta kasa mgana tana mamakin d'an yau. Kallonta yayi a rikice yana fadin"Baki ce komai ba Mama..? Sai Mama ta juya baya tana fadin"Fa'iza ki yi hakuri don Allah.Kada ki kara gudun mijinki a shimfid'a. kai kuma ka bita a hankali kada ka matsa mata." Wannan mganar ku ce Tsakaninku ne, don Allah kada ku kara sakani" Daga haka ta shige uwar Dakin ta tabar mu nan zaune,shi yana Tsaye ne kamar wani Saraki. Kafafuwana sun yi min zafin da na kasa tashi sai da na ganshi Durkushe a gabana yana fadin"Kin ji dai abunda Mama tace ko..?kada ki karamin Gaddama in dai na kira ki a Shimfid'ata" Sai kawai na Dago Rinannun Idanuwana na sauke a kansa cikin wata irin murya mai cike da Takaici nace"Meyasa ka kawo k'ara na wajen Mama..? Sai hawaye ganin kukana sai kuma ya Rud'eni ya fara kokarin son rikoni yana fadin"To ke ne Fa'iza duk yadda zan yi dake kin ki ganewa shiyasa na kawo kararki wajen Mama" Ture hannunsa nayi dake kokarin rikeni na mike Dakyar ina fadin"n ban taba kawo kararka ba. Ban taba fad'ama kowa halin da nake ciki ba,ko da yan'uwana ne. sai kai ne da bakin ka yafi nawa Tsini..?. Na karishe fad'a a Fusace cikin kuka Sai shima ya mike yana kallon Dakin da Mama ta shige Lokaci daya yana Fadin"haba mana.." Kuma wai yana kokarin rikoni Saboda bai da kunya a fusace na make Hannunsa ina fadin"Tunda kaso a fasa komai za'a fasa kowa yaji" Ganin ina nufar dakin da Mama ta shige yasa ya rikoni da karfi yana Fadin"Don Allah a'a Fa'iza don Allah" Daman ba fad'a zan yi ba sai na Turesa na kama Hanya na fita Daga Dakin mama,zan shiga Dakina ya Taremin Hanya yana faman marairaicemin sai kawai na juya da gudu nayi hanyar waje saboda naji hayaniyar yara har lokacin suna falo kamar abinci suke ci bana so su Fahimci abunda ke faruwa. Shima da gudun yabi bayana yana kiran sunana gaba na ya sha yana Haki yace"Ke ke ina zaki..? Cikin duhun Korodin dakin Jamal na balla masa Harara ina fadin"Tafiya zan yi..Zan tafi ne wlh bazan zauna dakai ba" Na fad'a masa cikin Tabbacin mganata sai ya Rude ya fara fadin"Ban gane ba. Wani irin tafiya kije ina kuma..?. Kai Tsaye nace"In da baza'a takurani ba sannan inda nima zan kai kararka.Nima ai ka jingine shekaru ina maka gadin ya'yan ja wa na taba