← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 175

Sashe 39

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiga ta gaida Antyn nasu bata da yadda zatayi hakanan ta Hakura ni suka bari da kwashe takalma da jakunkunar su da suka watsar a tsakar Falon. Anum dakina ta Shige Saboda na maidata da ita da kayanta tare dani,ina shigowa na iske ta watso kayanta kan gado da karfi nace"Anum ba na hanaki watso kaya ba..? Cikin rigima tace"To umma ban ga wanda zan saka ba ne" Riga da sikat na Dauko mata na bata ina Fadin"Duk na goge fa kayan nan ammh ji yadda kika wargazasu Anum" Ganin ban ji dadi ba yasa tace"Kiyi hakuri Umma" Kanta na shafa ina fadin"Bakomai yar Umma muje aci abinnci" Musty kuma Amir ya cire mai kayan makarantar ya sakamai, na gida suka fito falo na zubo musu abinci Farar shinkafa da miya,Sa'adatu ta aiko min da Kayan Miya itama daga gidansu aka aiko mata dashi kamar babanta aikin gwari yake yi. Dukkansu waje daya na Hada musu kamar yadda na saba sun fara ci,Anum da Musty suka fara rigima kamar kullum nace su bari suka ki sai na kalle su ina fadin"Anum zan mai da ke cin abinci ke kad'ai tunda bakya jin mgana" Jin haka yasa Da sauri Amir yace"Umma ki yi hakuri Musty ke Tsokananrta ki barta mu rika ci tare" Sai na gyada kai ina fadin"Musty kana son Bulala ne..? Na fada ina nuna masa hannun alamun duka kafada ya makale dariya nayi kafin nace"To ka daina tsonakar Yaya Anum in baka son duka" Da sauri ya gyada min kai Lokaci daya yana fadin"To umma" Cikin Salom mganarsa ,cin abinci suka cigaba da yi a natse ni kuma Farhan dake baya na ne ya motsa sai na mike ina Jijjigasa Daidai da Bude kofar falo da Shigowar Yaya Ishaq bayansa Jamal ne da manyan Ledoji,Nasan har ga Allah bai kalleni ba,ballatana ma yasan wanda na Goya Sannu da zuwan ma da nayi mai ban ji ya amsa ba Jamal ne yake kokarin Sauke Lodijin hannunsa a falon da Sauri ya Juyo yana fadin"Jamal bani Lodojin Hannunka" Yafada daidai da yaran zasu tashi suna kiran Daada da karfi nace su koma su gama cin abincin su duk da ban kallesa ba nasan sai alokacin ya bini da kallo ni kuma sai na Dauke kaina ba domin ina jin Haushin sa ba sai domin nasan ba ni da wata Daraja a wajensa shiyasa nima na koyi kama kaina. Jin abunda nace ne yasa ya kalli yaran yana fadin"Ku gama cin abincin ok.? Atare suka gyada mai kai Jamal ya mika masa ledojin hannunsa ya shige Bangaransa sai da ya shige na Dawo da kallona wajen Jamal wanda ya zauna saman kujera su Amir na gaishesa ya amsa yana fadin"My Childreen how far" Amir ne ya amsa mai da We are fine Uncle"Dariya yayi yana fadin"Daddy na ya fi kowa gane karatu a makaranta ko Amir..? Anum ta tura baki tana fadin"Nifa Uncle" Kallonta yayi kafin yace"Mommy nama tana ganewa itama" Jin haka yasa ta washe baki Musty kuma ya tayata,Sai alokacin ya Dago muka gaisa,cikin yanayin mganata nace"Ya su Mama..?Daga ina haka da yammah nan..? Yana sauke ajiyar zuciya na gajiya yace"Wlh Dad din Anty Zainab muka kai Masauki sannan muka je Restaurant muka yi oder abinci muka Biya gidan Mama muka kai mata kinsan Mom din Anty Zainab din wajen Mama ta sauka" Na jinjina kai ban yi mgana ba ya cigaba da fadin"Shine duk najini a gajiye me kuka dafa ne..? Kai tsaye nace"Farar shinkafa da miya ne a zubo maka ne..? Kai ya girgizamin kafin yace"Bari mu yi sallah naji an fara kira ma" Ina shirin mgana Yaya Ishaq ya fito Daga bangaransa, da Sauri bayan sa Zainab ne da kanwarta,Wacce ke jan Hannun yarinyar da suka zo da ita baiwar Allah tana ta kuka. Ganin su hankali tashe yasa Jamal ya mike cikin wani yanayi yana fadin"Me ke faruwa ne..? Zainab ne cikin rawar murya tace"Farhan..Ba mu ga farhan ba" Sai abun ya bani mamaki suna nufin basu ga Farhan goye a bayana ba..? Kafin na iya mgana Zuzu ta mari yarinyar nan Lokaci d'aya tana Hankadeta cikin fada tace"Ina Farhan.?wa kika bama shi..? Yarinyar sai ta kasa mgana sai kuka Ya Ishaq ya fara fadin"To ku ina kuka shige ku bar ta dashi..? Zainab ta fara fadin"Muna ciki ni da zuzu muna mgana mu ka bar Farhan hannun Shema'u" Ganin abun nasu ya koma kan yarinyar har Ya Ishaq ya fara fada ita kuma sai ta kasa mgana ta Dago tana kallona kafin nayi mgana da Sauri Anum tace"Jaririn Anty..?ga shi nan Umma ta goyasa" Sai kallo ya koma kaina ni kuma sai na juya bayana suka ga Farhan goye a bayana,yana barcinsa cikin kwanciyar Hankali ina jin su suka Sauke ajiyar rai a tare Zainab tace"Thank god.." Cikin yanayin mganata nace"Na shiga ne na iske yana ta kuka na karbesa ashe cibiyarsa ke ciwo shiyasa yake Rigima" Kamar kiftawan ido nagansu a gabana,suna rige rigen kwancen goyen bayana ba Ya Ishaq ba,sannan ba Zainab ba kanwarta ba,zuzu ce ta kalleni tana fadin"So kike ya karye kafarsa..?ba'a fara goyasa ba" Ni dai ban damu ba da Sauri na Sauko shi Tare suka karbesa ita da Zainab din Mamaki ya rufeni Lokacin da Ya Ishaq ya faramin fad'a meyasa ban yi mgana ba ina ji ana neman Farhan. Na kallesa cikin yanayina Kafin nace"kayi hakuri na zata ka gansa a bayana" Cikin Fusata yace"In da na gansa zaki ji muna neman sa..? Kuma kada ki kara goyasa tunda bai saba ba,Ba irin yaran ki ba ne da kika Saba goyasu ba" Kamar wata wawiya haka na bisa da kallon Zainab ta kara fadin"Honey kafarsa bata samu matsala ba ko..? Tafada tana nuna masa suka Taru suna kallon kafarsa yaron suna Tattabasa kamar na shafamai mugun abu,Cibiyar Ta bude tana kallo Zuzu ta leka tana fadin"What is this..? Wannan kayan fa..? Tafad'a a wulakance,karbansa tayi Tun anan ta cire mai kayan da na sakamai,Ita da kanwarta suka koma ciki Shi kuma ya bisu,kamar wani bita zai zai,ni dai da kallo na bisu Jamal ne, ya koma zauna yana fadin Allah ya kyauta. Yaran kuma duk sun yi wani iri,ganin abunda ya faru ni Dariya ma suka bani wai kafarsa zata samu matsala Saboda goye,Allah sarki rayuwa da goye na illa da tuni mu kan mu mun samu illah Tunda a baya kafin zamani ya zo da sauye sauye goyen aka sani ba wani gayu da feleke feleke irin na yan zamani masu nasaba da boko ya gama ratsasu ammh irin mu yan gargajiya ai goyen muka sani. Daganan dakina na koma Dauke da Ahmad araina nace in na goya nawa ai ba mai cewa zan karya masa kafa,Amir da Musty tare da Babansu da Uncle suka tafi masallaci ni kuma muka yi namu ni da Anum. Daganan ta tafi bangaran Baban nasu,Ta damu sai taje sai nace ta tafi,Su Amir kuma sai da suka yi Isha'i suka dawo suma ban kara ganin su ba Bangaran suka shige Jamal kadai ne afalo na zubo mai abinci yaci muna dan Taba Hira sama sama bai jima ba yayi min sallama ya tafi. Daki na koma nayi wanka nayi ma Ahmad,na shiryasa nan da nan sai barci yau bai yi rigima ba sosai su Anum sai goma saura suka Dawo Daki suna bani labarin sun ci nama da Ice Cream,Amir dai bana jin bakinsa sai bakin Anum da baya gajiya da mgana. Washegari ba makarantar Boko sai Tahfeez tun safe nayi musu shiri suka wuce,Shinkafar jiya data rage na Dumama ma yara sukaci suka tafi,Sai Sauran Taliyan data rage na Dafa musu da miyar suka tafi da shi ni kaina Sauran Shinkafar naci bamu da dankali ba kwai ba komai na Kayan breakfast ballatana nayi musu sai na kama kaina,ina gama abunda zan yi na koma daki bayan na tattara kayan yara da suka zubar afalo. Dakin su na shiga nayi musu kaye kayen kayan da suka watsar sannan na koma nayi wanka na yi ma Ahmad daman na Dama mai kunninsa na dura masa yasha sai ya cigaba da Wasan sa,Ganin ban da wani abu da zan yi sai na dauko Qur'ani na fara karantawa ina cikin karatun ne naji Muryan Yaya Ishaq na kiran sunana sai da na kai karshen Ayan sannan na Tsaya Daga bakin kofa ya tsaya Ahmad na ganinsa ya fara tafiya wajensa yana Washe mai baki ya Dauke sa ya daga sama yana fadin"Ahmad ka zama kato yanzu" Shi ko sai bangala Dariya yake yi. Hijabin jikina na gyara sannan na kallesa ina fadin"Ina kwana.." Ya amsa ba tare da ya kalleni ba ya cigaba da fadin"Ba abun karyawa ne..? Kai tsaye nace"Babu komai na cefane shinkafar jiya ce da nadafa ta rage muka dumama muka ci ni da yara" Shuru yayi bai kara mgana ba daganan ya fice Dauke da Ahmad ashe kasuwa ya tafi yayo mana Cefane duk da bamai yawa ba ne zai iya isa har bayan sun tafi muma yayi mana Saura. Na rana kadai yace nayi Inaga a waje ya siya musu wanda zasu karya da shi,couscouss nayi musu da rana mai Hanta da kayan lambu,basu fito ba nima ban bisu ba sai bayan La'asar na shiga muka gaisa sama sama Farhan na Hannun kanwar ta kamkamesa sai ban zura kaina wajen karbansa ba,na fito na koma Daki Ahmad kamar ya sani yaki ko sauka yaje wajen zainab din data ke kiransa ya lafe ajikina. Tunda suka zo suna bangaransa komai sai dai na shigar musu da shi ban damu ba domin nasan lada zan samu ciyar da su din da nake yi sannan Gidana suka zo akwai hakkin abinci su a wuyana. Kwanansu uku da zuwa Ya Ishaq yace na shirya zamu je gidan Mama na gaida iyayan zainab,Da daddare mukaje dukkanmu har da yara da ita Zainab din sai da naga mahaifiyarta da mahaifinta naga inda suka Dauko Kyan Fuska Mahaifiyarsu Hajiya Halima mun gaisa cikin Sakin Fuska Mahaifin su Dr.Lawal ya amsa min a Wani karkace ya kalli yarsa yana fadin"My dota wannan ce abokiyar zaman taki..? Ta dagamai kai tana fadin"Yes Daddy" Ya kalleni ina Duke gabansa Ahmad na Hannuna kafin yace"Sannu" Nayi shuru domin ban jisa ba Itace tace"Daddy ta na da problem din
Chapter 39 · 0% Book details