← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 175

Sashe 172

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin kayan akwatin daya dinkamin ne Tunda anan Abujan Maa ta bada aka dimkamin bayan na fad'a mata Measurement dina. Kayan sun karbeni Saboda Daidai jikina ne Badariya tamin Saukakkiyar kwalliya hade da Daurin maryam babbangida sai nayi kyau dani kamar a Sureni a gudu.. Ai ko Engr cak ya sureni haka ya Dagani Sama bai ji nauyi na ba,ya rika zagayen falo dani ni kunya duk kunya ya kamani ganin Badariya na wajen ashe tun Rumgumar Farko ta komaa ciki ta bamu waje. Dakyar na iya lallabasa ya yi wanka ammh sai da ya yi kara'in nasa dai ta bakinsa dai ba yayan ya yi ba kanin ne duk ya batamin kwalliya yasa sai da na gyara Daurin d'ankwalin Tunda har kan sai da ya sha Jagwagwala. Sai bayan ya yi wanka ya yi sallar mangariba da aka kira Isha'i sai ya jamu jam'i ni da shi bayan mun Idar ne muka fita falo na gabatar mai da abinci sai yace na kira Badariya su gaisa na leka na sameta itama ta Idar da sallar Dariya naga tana yi min sanin Dariyan da ma'ananta yasa ban tanka mata ba ammh ina ce mata Engr na mgana afalo ta mike tana Fadin"An gama yar shillan dake..? Sai na juya baya ban kara yarda mun hada ido ba na fice ina mirmishi. In na zauna ina kod'a Engr sai aka ga kamar ina zugasa ne ammh mganar gaskiya Engr shi ya kaini duniyar ma'auratan da bansan ma akwaita ba. Shi ya jiyar dani irin Dadin da mata suke ji a tare da mazajen su. Shi ya kara fahimtar dani aure da zamantakewa ashe ni a baya wahala kawai nayi,ban taba Dauka haka Aure ke cike da Ni'ima ba sai da na Samu Engr. Duk da kowani aure yana da nashi kalubalen,zo mu zauna a kace zo mu sab'a,ammh ni ta bangare na cika da Hamdala na kuma kara da Alhamdulillah. Tunanin da ya cika raina kenan ina zaune gefensa yana cin abinci sama sama yake mgana saboda bai cika son mgana in yana cin abinci ba. sallamar Badariya da shigowarta falon yasa ya Dakata ya dago yana amsawa Nesa dani ta zauna tana gaisheshi ya amsa cikin fara'a kafin yace"Matata zubo muku abincin mana tunda na lura yau wareni akayi tunda naga an zubamin nawa ni kad'ai" Mirmushi nayi kafin nace"Ni bana jin yunwa ne shiyasa sai dai in Badariya" Da sauri tace"Anty Fa'iza ki gayamasa mun ci da muka gama girkawa tun a bakin Tukunya" Hararanta nayi shi kuma sai ya kada kai yana fadin"Fa'izaa na yafe miki ba ma sai kin nemi gafarata ba" Dagani har Badariya muka yi Dariya matsamim ya yi sai da muka saka abincin muka ci kad'an tunda gaskiyanta ne tun a kitchen muka koshi sai dai an dauki Lokaci cikin ya Zazzage. Saboda gajiyan dake jikinsa yasa yace sai da safe zasu tattauna da Badariya da wuri muka shige ciki,saboda yana ta fad'amin ya yi kewata in zai koma kafata kafarsa bazai iya ba. Ai ko naga kewa haka ya rika min rawan jiki da Sambatu ni kaina na karbesa dakyau tunda nima nayi kewarsa sosai Rayuwa juyi juyi sai ga shi ni Fa'iza ke son al'amarin a baya Wlh tallahi al'amarin bai taba dad'ani da kasa ba. Da Asubaa yana kwance ni na tsokane sa muka buga kafi siga dad'i,Da safe ma kafin mu tashi yace zai kara na bata fuska ina Fadin"Baka gajiya ne..? Duk sai ka tsotseni ko..? Yana dariya ya kamoni yana Fadin"Bamu gajiya zaki ce. kema ai ba gajiyan kike yi ba in fa kika ji ni nayi kamar zan sauka sai ki yi saurin rikeni kina Uhm uhm" Ya karishe fad'a yana kwaikwayon yadda nake yi ga kunya ga Dariya Engr halinsa sai shi bakina ya Mutu murus na kasa mgana ya sumbaceni kafin ya Dagoni yana Fadin"Bafa tsotseki zan yi ba. Yarinya ina da Fertilerzer mai kyau kinga yadda kika koma..?Tife din gaske kenan ke da zaki bani dama nayi ta damawa ina cigaba da kara'i na" Ai ko na basa dama kamar yadda ya bukata. sai ya koma bayan mun natsa fad'i yake yi"Kamar ma ban yi ba. Wlh komai ya sauya ya kara sugar" Kansa na dungure ina Fadin"Kuma sai akace komai kaji sai ka fad'a..? Bakinsa ya kama yana fadin"To in kama bakina kenan..? Harda wani ladabin Dole Mirmishi nayi kawai ban yi mgana shi kuma sai ya kamani ya Rumgumeni yana Fadin"Allah ya yi miki albarka. Allah yasa ki haifo kannen su Ahmad dozin Biyu haka" Mukamikinsa na Tokare ya yi gefe yana wash,Sosa wajen ya fara yana Fadin"Yaushe kika zama Muguwa Faa'izaa..? Ya ja sunan kamar wani abu,Hararansa nayi sai ya gane laifinsa da Sauri yace"To na rage Dozin Daya" Tiolet na shige na barsa ina ji yana Fadin"To naji rabin Dozin ga su Amir goma kenan ina laifi Father of 10" Sai dai na bige da mirmishi ina wanka Soyayya da kaunar Engr sun taru sun cikamin kirji sun hanani sukuni yadda yake kaunar ya'yana wlh ko Ishaq albarka shiyasa nake yi masa kara in muna mganar su sai dai nace ya'yan ka. Yaran nan suna da lambarsa barin ma Anum uwar karambani sai dai yace min sun kira shi da wayar Mama Amir ma suna mgana da shi,Zumunci dai ne kila bazai Dore ba tsakanin Engr Da Ishaq kowa na ganin zumunci da wani matsala ne shi Engr haka nan baya so ya shigo masa shima Ishaq din har gobe yana kaunar Fa'iza shiyasa baya son Doguwar mu'alama da wanda ya hanasa mallakar Fa'iza a karo na biyu. sai dai yaran bai isa ya raba su da mahaifiyasu ba yasan Fa'iza ta shanye abubuwa dadama Saboda yaran nan suna mata kauna ta sosai kuma shima Engr yasan yana kaunar su Darajan yana Son Fa'iza yana jin kishin yadda yaran ke kiran Engr Baba sai dai ba shi da yadda zai yi yasan ni ko ya fad'a ko kada ya fada Engr mutum ne nagartattacen kuma Kishinsa duk akan Fa'iza ta auri wanda ya fisa ne yana ganin ta cigaba fiye da in da ta dawo ma auransa. Da safe bayan mun gama karyawa Engr ya zauna da Badariya suka Tattauna ta fad'amai komai kuma ya gamsu a wajenta ya karbi lambar Yusuf ya kirasa suka gaisa ya fad'amasa sunansa Engr Abdulbasit Mijin Fa'iza yar'uwan Matarsa Badariya daman don ya shaida masa ne matarsa na wajen su da sauran bayanai yusuf ya rude Engr yace zai bashi address yazo nan Abuja yana son ganinsa. Abun mamaki da Sassafe sai ga shi jiyan ma bai samu jirgi ba ne da Shigar dare zai yi irin yadda Hankalinsa ya tashi yana son Badariya kuma bazai iya Rabuwa da ita ba. Engr bai bari yaga Badariya ba sai da suka tattauna na tsawon awa Biyu sannan ya kira wayata yace na Turo Badariya,mu dai tare muka bar su biyu su fahimci juna bayan Engr yace mata ta saki ranta in sha Allahu wannan matsalan angama da ita. Bai yi wani bayani ba sai chan ba jimawa Badariya tazo tace min yusuf yace tare zasu koma naji Dadi na yi ta mata Fatan alheri ina kara jadaddamata ta yi hakuri ta kuma kara Hakuri. Badariya tayi mirmishi kafin tace"Nagode Anty Fa'iza ke da Mijin ki kin yi min dukkan gatan da Dangina zasu yi min Allah ya saka da alheri. Yusuf yace an daidaita bayan tafiyata Yayansu ya shiga mganar Hajiyarsu ta amince ya sauyamin gida sannan an yi min iyaka da matarsa kuma ya fadamin megidan ki ya yi masa Fad'a sosai ya kara nuna masa tunda yana sona to yasan Darajata" Nasan halin Engr daman bazai yi wasa ba muka rumgume juna,muka fita tare har Falo Yusuf nata godiyan Hidima itama Badariya nayi Direban gidan su Papa ya kira shi yazo ya kaisu Filin jirgi Yusuf bakin nan kamar Gonar auduga tsakanin miji da mata sai Allah har ta fad'a masa tana da ciki. Nima ranar tukwaici na musamman na bama Engr saboda jin dadin yadda ya maida matsalan Badariya kamar tawa muna kwance kaina na saman kirjinsa bayan ya gama shagalinsa yace"Ki daina min godiya duk mai kaunarki nima ina kaunarsa kin fad'amin yadda Badariya ta kaunace ki saboda Allah nima sai naji ina Kaunarta Saboda wanda ta kaunace ki domin sa" Kuma fa ba wani labari na bashi ba nadai fad'amasa Badariya mai kaunatace shima yace tunda tana kaunarki nima ina kaunarta,Washegari gidan su Papa muka yini ni da shi muna ta Hidimanta ma Hajiya Kudurta da Burinta ya gama cika Tunda Oluwatosin ya yi aure kuma daga gani yana cikin kwanciyar Hankali ita da Maa suna ta godiyar Abinci har Papa sai da ya yi min mganar ina ta Dawaniya da su bana gajiya..? Kaina na kasa ina mirmishi nace ba wani Dawaniya aciki suna ta min godiya da zamu tafi Maa ta bani Mayafai da Turarukan wuta sai ban ce mata ina hadawa ba na bari sai naje kaduna na hado mai kyau da kanshi na kawo mata. Da muka dawo gida nayi ma Engr mganar turaruka sai yace na bari akwai tsarin da yake so ya yi min yadda Sana'ata zata tafi tare da zamani daman na fad'amasa ina so maje kaduna ko nayi sako,asiyo min kayan hadin na hada a gida saboda Maa,kuma tunda naji yace haka sai ban kara mgana ba, nasan tunda yace yana da Tsari to ina tabbatar ma kaina Tsarinsa a kaina mai kyau ne. Ban sani ba ko Badariya ta kira chan Lagos ta fad'ama su Mama komai,?ni dai sai kiranta nagani tana ta min godiya har Anty Binta ma ta Kirani sai gashi da bakinta take fad'amin Halin da Halisa ke ciki da mashayin mijinta kuma an yi an yi yaki sakinta. Tana kuka tana fad'amin ko zan fad'ama Engr in zai iya wani abu nace mata zan fada masa in sha Allahu. Ni kuma ganin taimako ne sai nake gayamasa,nima sai alokacin yake fadamin Yaya Ishaq ya kirasa yana ta Godiyan abunda muka yi ma Badariya kamar mun yi mata wani Hidima,mganar Halisa kuma yace sai ya shiga kano zai ga mijin Halisan da kansa ko jari ne bai da shi a bashi ammh sai in har zai daina shan
Chapter 172 · 0% Book details