Sashe 88
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kowannen mu ya bada kinsan ba ni da shi Mama bata da shi ko da ta na nan Yaya ne kuma kina gani kece komai nasa yanzu,Anty Binta kuma bata ta kaina da na fara mata mganar kudi zata fara masifan itama bata da shi ke kad'ai gareni Anty Fa'iza don Allah ko rabi kika ragemin bakomai nagode".Sai ta bani Tausayi wane ni na manta da Badariya da Sanadinta na samu Rufin asiri, batare da sanin kowa ba na bata Dubu goma nace zan cika mata in na samu shima Dubun goma Sa'adatu ce chan inda muka taso ta samo min wata mata mai son Turare Humra,to da yake ina da Sauran kayan amfani sai nayi mata amfani da shi na samu ba laifi,Sai na koma ina Fafutukar yadda zan sama mata cikon sauran ga shi kuma salla ya matso,Allah ya taimakeni na samu aikin zobo da kunin aya na masu son da yawa da sallah dakyar na had'a mata dubu biyar na kara mata godiya har da kuka ta Rumgumeni tana fadin"Nagode miki Anty Fa'iza yadda kike jin kanmu Allah ya baki wanda zai ji kank'i watarana Allah ya Dauwamar da farinciki da arziki da wadata acikin rayuwarki gabad'aya" Na amsa mata cikin fara'a ina Fadin"ke meye na kuka share hawayen ki ko sai na kira miki Ya'yan ki ne..?jin haka yasa ta goge Hawayenta,ni na hanata nace ko yayanta kada ta fad'amawa ana saura kwana Hudu sallah tazo da murna tana Fad'amin Hajiyar su Raliya ta biya mata kudin sannan ta bata dubu goma tayi dinkuna sai tace zata maidamin da kudina na riga nayi niyya sai na karbi biyar din da na bata Daga baya na barta mata goman nace tana da bukatu tayi amfani da shi,Badariya ta yi murna tayi murna kamar bakinta zai yage addu'a kam na shata ni ko tana da Muhimmancin da bazan manta da alherinta gareni ba. Atamfa taje ta siyo da less sai mayafi da takalmi da jaka,Sai kayan shafa ina D'aga kayan ina fadin"Ehee! kaga yan mata." Tana Dariya tace"To Anty Fa'iza mace sai da kwalliya mazan nan, kuma suma kyale kyalen suka fi so" Na aminta da mganarta yasa nace"Hakane Allah ya kawo miji nagari"ta amsa tana rufe fuska ni kuma ina binta da Dariya sai da Yaya Ishaq yaga kayan ne ya tsareta sai ta fad'amai gaskiya kallo na yayi yana fadin"Lalle kina da d'aure ma karya gindi ke baki bukatar kayan kwalliyan sai ita..? Ina dariya nace"Me Fa'iza zata yi da kayan kwalliya ai wannan sai irin su Badar mata masu kyau da nasaba" Ita Badariya bata gane mganata ba sai ta karb'e da fadin"Kai Anty Fa'iza wlh kwalliya bata zaba bace.Mu mata kowa yasan yan ado ne da kwalliya" Shi kuma da yasan kan mganata sai yayi gum ya koma yana kallona ni ko na basar da shi,Daga ni har shi bamu san Zainab da yara zasu zo mana sallah ba,Mun samu tallafi shinkafa da naman sallah Daga gidan Hajiya Daga Korofi kuma Goggo ta aiko mana da kaji da kayan miya mangyada su maggi da sauran Cefane,an yi idi lafiya an sauko ranar nayi mana shinkafa da miya sai nayi mana cowslow,Sai zobo da kunin Aya Saboda Sallah Jamal ma ya dawo da da bai da kudin mota, yayan yace ya zauna chan yayi sallah nace hakan bai kamata ba na hada dubu hud 'u aka turamai nace ya taho gida yayi sallah cikin yan'uwansa. Ranar idi da yammah sai ga Direba ya kawo zainab da yara,Gida sai ya Rud'e da Murna su Anum nata tsalle da Murna ganin kannensu Farhan na ganina ya Nufeni bakinsa har kunne yana fadin"Umma.." Na daukesa na daga sama yaro kamar balarabe wajen kyau yana bangalamin Dariya nace"Farhan d'an Umma" Tazo da naman sa an soya tare da naman kaza anyi pepe dinsa ga su cake samosa da su sprill role, ta zo da kantan kantan na lemuka da biskit, ta ce min Saboda sallah ko kuma in mun yi baki,Nace mata"Angode. Sai dai gaskiya sai kunin aya da zobo ya kare tukunnah" Tana dariya tace"Ga abun arziki wazai bi ta na kwalayen bature masu shegen zaki" Ishaq basa gidan shi da jamal sai dai suka dawo suka ganta kuma daga alamu uban gayyar yaji dadin ganin matarsa, Dakin mijinta na Sauketa,Yaran kuma suna tare dani Direban daya kawo ta bai koma ba. tace zai tsaya sati d'aya zasu yi zai maida su sai aka sauke sa Dakin Jamal. Sosai wannan sallar tayi mana Dadi,babu abunda yafi kwanciyar Hankali Dadi ni nake hidiman abinci na gida da na yara, Zainab sai da tana tayani da Hiran duniya,Farko da na sauke Zainab a dakinsa samu na yayi yana min mgana wai meyasa sai Dakinsa na sauketa,dakina fa..? Na kallesa ina fadin"Saboda mene?sai mu gamutsu da ni da ita da Anum kamar ba bu wani da'kin..? Kuma nan din ta saba sauka in tazo a Dakin naka shi yasa na sauketa anan" Sai kawai ya juya yana fadin"Ki bude dakin Mama ki sauketa anan mana" Mamaki ya bani Namiji sai a barsa da gulma ya gama wannan borin kunyan, sai ga shi suna kulewa a daki bamai jin su ammh yazo zai min dad'in bakin su na maza. A gida muka cinye sallar mu sai ranar washegarin sallah da kwana uku Zainab ta matsa sai na shirya mun fita. da zamu tafi,na saka atamfata da Hajiyar su Raliya ta dinka min,Zainab tace ban isa ba ta dinka mana Less mai kyau iri d'aya,har dinki daga Abuja aka dinko ta matsamin sai na saka Saboda kada tace ko ban karb'i kyautar nata ba ne,yasa na saka Doguwar riga A shape dinkin ya fita haka ya fitar min da Shape dina in kika ganni a lokacin bazaki taba yarda na haifi Yaro dan shekara sha biyu kamar Amir ba. Ina nan da kuruciyata sai dai kowa yasan Fa'iza yar gargajiya ce,ammh zainab bata barni haka ba,Hijabi na saka tace ban isa ba Dole na Dauko mayafin data aikomin da shi da Takalmi da jakata na saka,sai gani na fito ras dani na yarda da Hausawa da sukace kowa ya gyara ya sani ni kaina sai nake ganin kamar bani ba. Zainab ta kalleni sama da kasa kafin tace"Komai yaji ban da abu d'aya" Ina dariya nace"Ban yi kyau ba ko..? Sai tace"Aa fa.Lalli ne yayi miki cikas" Sai kawai na wuceta ina fadin"Lalle ai naku ne na fararan mata yan gayu" Domin tayi nata Hannu da kafa, abun ka ga farar fatar kamar don ita aka fito da zanen jan kunshi tana bi na a baya muka fito daga daki Lokaci daya tana fadin"Wlh ko ke kika yi ba karamin kyau zai yi miki ba Maman Amir" Ina jinta ban ce mata komai ba, ina jan abu zai fito a wannan bakar fatar tawa ina fitowa yaran na Falo suka dago suna kallon mu sai kawai Anum da Amir suka hada baki wajen fadin"Laa! Umma kin yi kyau wlh.." Musty da Ahmad ma suka karb'a Farhan na jin haka shima yace"Umma jin yi kyau" Fadil na gauranci yace"Chauu.." Gabadaya muka saka Dariya,Ni na sabe Fadil na rike yaran duk sun ci yan kanti mazan kaf iri d'aya Zainab tayi musu Anum kuma an cakare da Doguwar riga da takalmin yan gayu Badariya ta kaita akayi mata jan kunshi da kitso da yake bata dauko suma na ba,tana da gashi an yi kitson gaba yaji bit sai yanga take da farko ma kin saka Hijabi tayi sai da nayi mata jan ido,Zainab ta hana sai ta Dauko mata wani karamin mayafi ta nad'a mata, muka fita daman ta fad'ama megidan zamu fita gari gidan Anty Binta mu gaisheta yace to. Ban kulle dakin ba tunda suna waje da Jamal jakata na Hannun Amir na Zainab na hannun Anum ta kama ta rike in ka ganmu bazaka taba cewa muna cikin wani hali ba,ko mijin mu bai da aiki ba kila in an fad'a maka ma bazaka yarda ba. Suna tsaye suna mgana da Jamal yaran suka fara fitowa ganin su shar da su yasa yafara washe baki Jamal ne yace su jere a dauki Hoton Tarihi ko da muka fito har Baban duk suna ta Hotuna Zainab ce a gaba sai ni a baya ina rike da Fadil zainab nata min Tsiyan na nad'a mayafi a kaina,nace mata ban iya saka shi a saman kafad'a ba ne. Tunda muka fito idonsa ke kaina kallo kamar zai fad'i,har yana wani bude ido sai ji nayi kawai ya kira sunana"FAA'IZAAA...! na dago ina kallonsa Fadil dake ta mika masa hannu alamun ya Daukesa bai ma gansa ba ya saki baki da hanci yana kallona Ya nuna ni yana fadin"Fa'iza ke ce.? Sai dariya ta kamani nace"Ba Fa'iza ba ce Wannan Uwar Fadil ce" Sai nan ya gano abun da yayi sai ya fara sosa keya Jamal yayi dariya yana fadin"Matar bro ba bro ba,koni ban gane ki ba da farko". Hararansa nayi ina fadin"Uhm ka manta ne" Karaf ko Anum tace"Daada yaga Umma tayi kyau ya saki baki yana kallonta"Zainab ta kwashe da Dariya tana fadin"Yes my Daugther" Sai kunya ta kamani na sadda kaina ya matso ya karbi fadil daga hannuna ammh sai da ya gogi jikina Lokaci daya yana fadin"kin yi kyau,Sannan kamshin yayi dad'i" Sauran Humran da nake hadawa ce in ta ragu sai na ijiye ban ma cika shafawa ba yau ma Zainab ce ta matsamin sai da na shafa,da sauri nayi baya ina yake sai ya basar ganin Zainab kusa dani sai ya kalleta yana fadin"Matan Abuja sun yi kyau" Hararan soyayya tayi masa tana fadin"Ai yanzu ta zama matar katsinawa" Dariya mukayi gabad'aya Fadil ne ya fara kuka yana mika hannu muna juyawa muka ga yara har sun rigamu shigewa mota nayi dariya ina fadin"Dole fadil yayi kuka yaga za'ayi masa kan ta waye" Mikamin shi yayi yana fadin"Sai kun dawo, kada kuyi dare jamal fita zai yi ni kad'ai ne agidan" Zainab ta wuce tana fadin"Honey sai fa mun zaga gari ka ma yi hakuri kawai" Ni dai ban ce komai ba muka shige mota wata bakar Jeep ce kaf ta Daukemu su Anum an kame agaba kamar motar gidan su dariya ma tabani,Gidan Anty Binta muka fara zuwa