← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 175

Sashe 174

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana min tsiya ina Dariya. Ranar da Ishaq yaji ina da ciki sannan ga yara sun dawo da labaran mu ni da Engr sai kishinsa ya kasa boyuwa har ya bayyana ma zainab tunda kamar fada ba gaira ba dalili ya rufeta. Sai da Mama ta shiga mganar tace ya rika addu'a Allah ya yaye masa jarabawa ce da sakamako Oho ni bansan yana yi ba ina nan cikin jin dadi da kwanciyar Hankali. Sai da cikina ya yi wata biyar na bi Engr zuwa Edo muka shimfid'a wata Sabuwar rayuwa komai kuma na shirin haihuwa tun muna Edo muka gama shi chan na fara awo na kafin cikina ya kai wata Takwas na koma Abuja yace anan zan haihu kusa da iyayensa. Na sauka lafiya haihuwar asibiti ce Ammh ban jima ba na haifi ya' mace mai kama da Engr har gashin idon su tun a ranar ya yi mata Huduba da Hafsat zamu rika kiranta Tamadina sunan mahaifiyata nayi kuka nayi Dariya na karan da Engr ya yi min,Abba ma ya taka rawan gani Tunda sunan yar'uwansa ne,an yi suna na gani na fad'a na masu kuma da shi duka Ahalina sun zo har da Zainab da Mama da yara,Anty Binta da Ahalimta tare da Halisa da komai da ya Daidaita,Badariya ma tazo da jegonta tunda itama ta haifi diyarta mace taci sunan Hajiyar Yusuf itama suna zaune lafiya tunda sun daina shiga harkanta. Hajiyar Dala ma da ya'yanta sun min kara sun zo,na shiga na fita sannan na samu kyattuka Papa mota ya bani Kirar Honda karama mai kyau na mata Maa kuma ta siyamin Zinare mai Tsada Dangin su ma na Benue kuwa naga karan yarbawa zannuwa ashebe babu abunda basu taramin ba,ba ni kadai ba hatta dangina da abun arziki aka salleme su kowacce da Turmi da kudi a hannunta. Sai bayan suna ne Goggo karofi tazo ta zauma dani har nayi arba'in Allah Sarki goggo na,Ita ce uwa ta tun Tamadina na raye har kuma gobe ita ce. itama haka Direba ya maidata gida da kayan arziki daga gareni da mijina da Danginsa, na zama Topic of Diccussion a family din mu kowa sai dai kaji yana Fadin Faa'iza haka Faa'iza kaza. Bayan tafiyar Goggo na cigaba da renon Tamadina a gida bayan Engr ya bani Direba ya kaini garuruwan yan'uwana na yi musu barkan arba'in sannan na sauka a kaduna agidan mu nan na kwana Biyu sai da Engr yazo muka koma Edo tare da shi da D'iyarmu. *BAYAN SHEKARA BIYAR..* Bayan shekaru Biyar da suka gabata,Duk inda ake neman cigaban Rayuwa ni kam na gama samu ni Fa'iza sidi karofi ashekarun biyar din baya. Mun rasa Hajiya Kudirat,Shekaru biyu baya,Inno da Baba Ati suna nan a raye cikin koshin lafiya da kwanciyar Hankali. A bangaran rashi kenan bangaran Karuwa kuma bayan Tamadina na kara haihuwan ya'ya biyu Namiji da mace,mai sunan Papa muna kiransa Paa da mai sunan Maa Shukra muna kiranta Tauhidat,Bangaran ya'yana kuma Amir ya gama secondary school dinsa Da taimakon Engr ya samu gurbin karatu a Universty of Washington yana karantar Medicine,shekara uku da suka gabata,sai Anum dake karatu a Lagos States University lasu,tana karanta harkan mganguna phamacry. a shekara ta Biyu sai Mutsy dake University of Lagos yana shekarar farko ya na kuma karanta harkan zane zane,Ahmed sune bana zasu zana jarabawar Fita Su farhan na matakin SS1,Jamal ya yi aure zuwa Lokacin na riga na zama Babban Mace na taka duka matakin nasara a rayuwata Dalilin Engr yasa na zama wata macen da ban taba mafarki ba,Jamal ya yi aure anan kano kuma Engr ya yi masa hanya ya samu aiki da NITDA information Tecnology Development agency. Dake reshen jahar kano yana nan zaune a gidan kansa da Matarsa Abida. Engr kuma ya zama Chairman a ma'aikansu sannan ya zama d'an kwangila Papa ya gama Lokacinsa a EFFCC yanzu haka ya yi Ritaya yana gida yana Hutawa,Su kafaya sun yi aure kuma dukkansu auren gida suka yi ya'yan kannen papa suka aura Kafaya na Abuja Sharifatu na Oyo inda Mijinta ke aiki Hafsatu ma da Khadija sun yi aure rana daya ita Khadija V.c din Kasu take aure ita kuma Hafsah tana aure a zaria tana auren wani likita dake aiki a ABU chika. Shekara biyu da suka gabata gida ya Rage daga Ammi sai Abba,sai ta Dauko ya'yan kannenta guda biyu tana rike da su saboda zaman kadaici,yanzu zamana ya fi yawa a Abuja tunda ga yara bazamu ta tsallake tsallake ba Sai dai ina bin mijina Edo ina dawowa kaduna kuma muna zuwa sai muke sauka a gidan mu bamu da matsala. Engr ya yi min Tsari mai kyau game da kasuwancina ya Budemin katon shago mai kama da plaza inda aka sama wajen sunan SAFMA TURAREN WUTA AND KWALLACHA. ni kuma nake had'a turuka na da kaina sai dai ina da yara masu taimakamin,Turarukan wuta ne masu kamshi da nagarta kaf fadin Nageria ba wanda baisan Safma turaren wuta ba, ko Hajiya Fa'iza mai Turaren wuta da gyaran jiki ba. Tunda Engr yace duka kasuwanci ne na had'a na rika yi daga gari gari ina aika turarena sannan ina hadama amare kuma ina yin gyaran amare,na koyama mata dadama sana'ata a kyauta kuma suma suna chan suna cin gajiyan sa. Sannan na had'e da kungiyar Women charity Faudation da suka taba tallafamin nima ma zama acikin su ina kuma bada taimako daidai gwargwado. Yaya Abdul'ahad da Raliya suna chan Tunda bayan ya gama karatunsa sun rikesa achan itama bayan Walid ta kara Haihuwan mata biyu sai da muka gansu a hoto,sau daya suka zo gida suka yi wata daya suka koma. A mataki na rayuwan da nake ciki yanzu Allah ya gama cikamin duka Burika na,Ban yi ilimin zamani ba amnh ba inda zan shiga a raina ni sannan ban zama mai ji ba,ina nan da raunin ji na Engr bai taba kyamatata ba. Ni da kaina nayi tunanin naje Ear center a dubani duk da an haifeni da laluran ne, tunda na tab'a ji an ce masu irin laluran mu ma ana saka musu wata yar Na'ura domin karfin jin su ya karu. Ammah sai Engr ya hanani yace shi fa ni yake so,saboda haka na zauna ahaka baya son wata Fa'iza bayan bakar daya sani mai raunin ji. Shiyasa sai na bar mganar na kuma Rumgumi kaddara ta nagodema Allah,Yan'uwana duka na tallfesu,Ina da kudi ina da dukiya,da bansan iyaka ba Kuna Engr bai taba sama ma Nemana ido ba kudin da nake samu ta bangaransa bai taba fasa bani ba,Koda yaushe supporting dina yake yi yana karamin karfin gwiwa na zama giwar mata a dangi kowa ya taso da matsalansa waje na kuma zan mangance masa. ban taba duba baya ba komai ina yi ne sannan ina Duba zumunci Ban taba shafa man da zai sakani Haske ba,sai dai jin dadi da hutu da shafa mayuka masu tsada yasa fata ta sauya na zama yar lukwai lukwai dani,a yanzu haka ina da Shekara arba'in ammh in ba fad'a nayi ba bazaka taba ganewa ba tunda ina nan yar Caras dani daga ni har Engr kamar alokacin muke cin zamanin mu. Engr ya tallafa min na kai Goggo da Mallam Hajji sun sauke Farali sannan na gyara gidan da Tamadina tayi aure na kuma bama maman isuhu jari Sa'adatu da Habiba ko ba bu abunda bana yi musu,jari na basu dukkansu suka kama sana'a Yaya Asiya itama ta fara harkan Saida zannuwa,Yaya Mariya kuma ta koma makaranta ta hada Degrre dinta hafsah ma tana zaria tana aikinta tana cin moriyar karatunta. Bangaran zainab da Ishaq kuma sai hamdala kowa ya rumgumi kaddaransa tunda yasan har Abada Fa'iza tayi masa nisa,sai dai yayi namijin kokarin rike kan ya'yansa Engr ma yaso ko Ahmad ya bar mana mu rike yace bazai bani ba ai bai gaza ba nima ban damu ba tunda na Haifi wasu ya'yan haka na gayama Engr ya kyale masa ya'yansa tunda muma mun haifi namu. Ni da Zainab zumuncin mu har a gidan Aljannah,ta daukeni kamar yar'uwanta haka nima muna gayama juna sirruka sannan muna bama juna shawara tana zuwa gidana in ta shigo Abuja nima ina zuwa wajenta in na Shiga Lagos ammh gidan Anty Fadila nakan sauka sai dai naje mu ga juna mu yi zumumci. Daga yaran har Zainab har su Mama ba wanda ba na yi ma alheri sai dai su ji kunyata ammh ni,ko ajikina saboda zumunci sannan kuma na manta baya ni gaba nake dubawa saboda da ban yi hakuri ba da ban kawo matakin Rayuwa mai ingancin da ni ke ciki ba yanzu. Yanzu haka da bikin Anum ya taso zata auri yaron gwamnan Jahar katsina abikin wata course mate dinta Aisha Kabir Mahuta ya ganta yace yana so,dayake har katsinan ta biyo Aisha shi kuma wanda Aishan ta aura babansa yayi mataimakin gwamna itama Aishan babanta sanata ne. Ban taba tunanin ko a mafarki zan zama surukar gwamna ba sai ga shi Allah mai Daukaka ya Daukakani. Ishaq ya yi mana kara ya nemi Engr da shi akayi mganan aure su kuma suka yanke sadaki da komai. Wata Biyar suka saka,kuma ba'a kasar nan zasu zauna shi a babbar Birnin U.S amarecia yake aiki da wata ma'aikata mganguna. Ban saka bakina akan harkan bikin ba na barma Zainab komai itace uwar amarya ko abu ne sai dai nace tayi ma su Anty fadila mgana ko su Yaya Mariya mganar kayan gyara ne kad'ai nace zan yi ma Surayya dee marubuciyar Halin yau mgana na gyaran amare na kuma gayamata tace ba damuwa mun gama mganan zata had'ama Anum mganganun gyara da Saiwar kazan Gudiyo. Tunda taji ma y'ata ce shikenan tace ai itama uwa ce,kada na damu zata gyara Anum,saboda tun bayan kayan da na siya a wajenta lokacin bikina da Engr muka saba muke zumunci da ita. Sannan sai Turaruka da nace zan yi mata da Hannuna. Mganar kayan daki kuma Engr da Ishaq suka ce zasu gyara mata kayattaccen gidanta mai sama da kasa dake katsina jamal kuma zai yi kayan gara a matsayinsa na Uba. Su yaya Mariya da su Anty Fadila kayan kitchen da su labulayya,Abba kuma yace tunda an waresa shikenan zai d'inkama Amarya kayan fitar Biki.
Chapter 174 · 0% Book details