← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 175

Sashe 139

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi Lokaci daya yana fadin"Nagode sosai Allah ya yi miki albarka yasa ya'yanki su rama miki. Ammi ta amsa da Ameen kafin tace"Ba ka ce Allah ya bata miji nagari ba..? Ina jin Haka na mike ina fadin"Abba mu kwana lafiya" Ammi ta bini da Dariya tana Fadin"Diyar taka Baban Nana sai kayi da gaske ko wani gwaskan muka samu sai ta bamu kunya na lura da take takenta" Abba ya murmusa kafin yace"kyaleta ba mai yi mata Dole. in ma bazata kara yin auren ba ina bayanta" Ammi ta karkace baki kafin tace"Haba da kuruciyarta Baban Nana..?Allah zai kawo mata wani wanda zai kaunace ta saboda Allah ya rud'ata ta zo da kanta tana fadin Abba na amince masa" Ta karishe fad'a tana Dariya Abba ya jinjina kai yana Fadin"Allah yasa ni dai a nawa shawaran ta daidaita da Baban yaran nan ishaq ya yi nadama sosai wlh in da zata koma da ni kaina naso hakan'" Yana mgana Ammi na tabe baki sai da ya gama sannan tace"Nafi yi ma Fa'iza sha'awar sabuwar rayuwa akan ta koma Rayuwarta ta baya kwata kwata ishaq bai chanchanci a basa wani Dama ba, gwara haka dai kowa da nashi Kaddaran" Kai kawai Abba ya kada kafin yace"Tunda baki son sa ai komai zaki ce, ammh duk in da zata je bai kai inda ta fara gina Zuru'arta ba azizat. da sabon yabe duk lalacewar tsoho wlh gwara tsohon yaben nan ni a ganina" Ammi ta kada kai kafin tace"Wlh wani Sabon Yaben yafi tsohon sau Duhu" Kyaleta yayi sanin Halinta ita ko taki Hakura tacigaba da fadin"kuma in kana mganar ya'ya ne ai sun saba da Rashinta,suna zaune gidan uban su in da ya dace da su ita kuma Allah ya bata wani mijin taje tayi auranta ta Huta taji dadinta" Abba ya gyara zama yana fadin"Allah ya bata Azizat" Dariya tayi kafin tace"Ameen Baban Nanas d'ina" Girgiza kai yayi yana mirmishi kafin yace"'Allah ya shirya Maman Abdul'ahad' Da Ameen ta amsa mai tana Dariya mganar Fa'iza suka rufe su ka kama na Raliya da mganar sai Walid ya yi kwari za'a shiryamata tafiya wajen mijinta. ****** Kamar yadda nayi alkwari ban sauya ba tunda ina nan ba ranar Tafiya. Goggo ma bata damu ba tasan daman Ammi nata korafin rashin zuwana,aranta daman tasan sai an ganni kawai,daman ni nake yin girkin Rana sai nake dib'arma Abba Ammi ta kirasa ya turo Direba ya Daukan masa ya kai masa watarana ma in ya makara sai dai a basket yake tafiya da abun karin nasa ya yi achan ba'a Rufe Sati ba Ranar Abba ya dawo yace yunwa yake ji sosai. Ammi ta kallesa yana ragema Tie din wuyansa tsukewa tace"a'ah ina abincin da direba yakai maka..? Kai ya girgiza kafin yace"Wani abinci..?ai ina gaya miki tun rana na biyu da Ashuru ya fara karbo'min abincin su Engr Bashir suka sakamin ido. wlh tun suna su biyu har sukamin gayya suna min tsiyan ina musu wayau ina barin su da abincin kedaran maza ga mai dadi da Dadin dand'ano,da nakan samu naci ko ba da yawa ba,ai yau ko a bakina ina gaya miki Engr ya ga Shigar Ashiru Office d'i na da kwandon abincin bai yi mgana ba sai da aka tashi sallah da cin abinci yaga mun zame jiki mun shige Office dina ya Rutsamu Maman nana" Ammi ta zaro ido tana Fadin"Allah yasa ba laifi kuka yi ba? Abba yace"Wani laifi..?ai shima cewa yayi an munafuncensa barin ma ni ban taba gayyatansa shima yazo aci abincin da shi ba,karshen ta dai wanda zan ci na bar mai ni da yunwa na yini wlh sai santi suke suna fadin muna jiran na gobe Engr Usman" Ammi na Dariya tace"To sai kace musu me..? Abba yace"Nace ba mai gajiyarmin da D'iya kunyar Engr naji domin da kansa yace a fada miki a sawo da nashi Gobe ba Baban Nana kadai ke kaduna ba" Ya karishe fada yana Dariya Ammi ma Mirmishinta take yi kafin tace"Allah Sarki kada ya damu zan fad'ama Fa'i ta kara sanwa Hannunta ya yi albarka" Abba yace"Ban so a rika wahalar da ita ba domin Engr ya yi mgana ba, har ni hakura zan yi mu rika cin wanda ma'aikata ta bamu" Ammi tace"A'a bazai ayi haka ba. bazai gagara ba in sha Allahu" Da farko Abba bai amimce ba Darajan Engr da ba abunda bazai iya masa ba yasa ya amince,ammh sai da ya kirani yamin mgana har da bani Hakuri ina Son Halin Abba mutum nagari mai sanin Darajan dan Adam Ni ko nace masa bakomai na saba ba aikin da zai gagareni nan duniya. Abba nata min godiya kamar bai isa dani ba. Tunda ga ranar na kara sanwa a babban Tukunya nake yin girkin,a cika manyan kololi direba ya kai musu bayan abinci kullum da kalan lenukan da nake hada musu kala kala wadanda muka koya a katsina da kuma daman wadanda na iya tun a baya abinci ko kala kala nau'ika Dabam Dabam,ko wata rana da kalan Godiyan da Abba zai ce sun ce ayi min in ya dawo da farko sun zata Ammi ce ke yin girki daga baya ya fada musu Diyarsa ce to sun zata ko cikin ma yaran da ya Haifa ne. Abba da kansa ya fad'amin wani cikin abokan aikinsa yace a jinjina min tabbas a gaisheni bai taba cin girki mai Dadin girki ma ba har ko na matarsa Ranar ma Dubu Ashirin Abba ya kawo min Sabbin yan Dubu Dubu yace gashi in ji Engr yace a kai ma yar Baiwa. Ammi nata Dariya da naki karban Abba ya min tsawa yace maza na karba ai kyauta suka bani na wahalan da nake yi sai na karba,Itama Ammi da nace ta ciri wani abu ki tayi haka takemin ko Aikin Hada Turare na samu in na bata wani abu bata karba,Sai dai na bama su Hafsah kowacce dubu uku suna ta Murna. Inno ma na bata Dubu ukun ta karba tana ta saka albarka tana nan idonta ya tashi tana ta fama da shi Baba Ati na Korafi bata dawo ba. Yau da gobe bata bar komai ba,Har ga shi su Abba sun kamallah warkshop din su cikin nasara,Ranar da suka gama washegari bayan Abba ya fita ya kira Ammi a waya yace ayi girki na Mutum goma haka su Engr sun ce zasu zo godiya anjuma da Daddare. Bana gida ma Lokacin ina gidan Raliya ni da su Hafsah Ammi tamin waya,daga gidan Raliya Ashiru Direba ya wuce damu kasuwa nayo cefane,a hanya ma muna ta waya da su Anum sun samu wayar Mama,Amir ne kadai bamu yi mgana ba shi bai cika karamniya ba. sai mu yi waya da sauran yaran sau nawa shi bamu yi ba ko yana daki ko yana karatu baya son damuwa sai dai mun yi waya da shi ta wayar Jamal in yana gari zai saki jiki mu sha Hira da shi na lura Shirgin yaran ne baya son shiga gudun reni. Tare da su Hafsah muka yi aikin Tuwon Shinkafa mukayi da miyar Allayahu wacce taji kashin Rago da manshanu sai Ferfesun kayan ciki da priderice,sai Fruit salat sai nayi musu kunin Aya ga zobo,sai lemun kankana,sai yammah muka gama muna gamawa ana kiran sallar mangariba Ammi bata da ko yar aiki komai ita ke yi da kanta,su hafsah na bar ma gyaran kitchen din ni kuma na tafi yin wanka nayi sallah ba Karya nagaji sosai shiyasa ina fitowa daga wanka nayi sallah na kishigida ina azkar barci barawo nata son sace ni karar wayata yasa na zabura Jummala ce ta kirani kan mganar gidan Alhaji Bukar na cikin gari sun turo da kaji talatin za'ayi musu Dambun kaji na girgiza kai ina fadin"Kai aikin ya yi yawa jummala..?zaku iya kuwa..? Jummala tace"Zamu iya maman Amir ga Zainabu ta dawo ma, sai nayi ma su laure mgana su Auwalu sai su tayamu Matsewa" Kai na jinjina kafin nace"Sun hado da kayan yi ne..? Kai tsaye tace"Ban duba ba tukunna" Ban damu ba nace"Duba bari na kira Goggo mu yi mgana" Goggo na kira bayan mun gaisa na fadamata yadda muka yi da jummala Goggo tace"Sai su yi ga su Auwalu ba komai zasu iya, da kina nan ai kun sha yin masu yawan su" Jin haka yasa sai nace to shikenan bayam gama wayarmu da Goggo ashe ma matan gidan Alhaji Bukar ta kirani sai na kirata daga baya mukayi mgana tace an ce bana nan,ammh sun kai ma Jummala nace ta fadamin kada su damu za'ayi ammh sai nan da kwana Biyar zasu samu tace bakomai sun san ka'ida na ko wacce kaza daya Dari takwas ce nake yi tace zasu hada su Turomin kudin aikina ta banki da haka muka rabu cikin Karrama juna. Sai daga baya na kira jummala na fad'amata yadda zasu yi tunda tace sun kawo komai da komai harda kayan kamshi,wayar ne ta Daukemin Hankali har akayi isha'i na tashi nayi salla barci ne malale a idona shiyasa na koma na kwanta saman gado sama sama naji mganar su Hafsah kamar wacce ta sha wani abu na kasa tashi,sai asuba shima sai da Ammi ta shigo ta tasheni na tashi ina jin kaina yamin nauyi. Ban ko san yadda bakin Abba suka kare ba sai da safe na shiga gaishesa ya Turomin tulin kudi gabana na kallesa da mamaki ina fadin"Kudin miye wannan Abba..? Kai Tsaye Ammi dake kusa tace"Kudin ki ne jiya bakin Abban ku suka ce a baki Tukwici da godiya" Ido na kwalalo,cikin mamaki kafin na samu bakin mgana Abba ya yi dariya yace"To rufe bakin mana Fa'i" Ganin yadda na bude baki cike da mamaki,da sauri na rufe bakin ina fadin"Abba naga kudin ne da yawa..?ni fa yarsu ce Abba don ma nayi ma abokan aikin ka girki bai kamata su biyani ba wannan kudin ai kamar biyana suka yi" Abba yace"Wlh haka na fad'a musu suki jin mganata sun so ma kizo ku gaisa akaje kin riga kin yi barci. nace a kyaleki sunce kema yarsu ce ba Kyauta ba ne Tukwaici ne" Sai naji na kasa mgana Ammi tace"Dubu Dari ce cif Fa'iza sai a kara jarin Turaruka.." Ina mirmishi nace"Allah ya biya su
Chapter 139 · 0% Book details