Sashe 80
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Janafty* [7/12, 10:17 PM] +234 906 320 7298: *KNKB2006* *Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* Ba nufina in yi Mama rashin kunya ba ne, saboda a uwa na Dauketa sai na Sadda kaina kasa ina fadin"Naga fad'an bai shafeni ba ne Mama" Sai ta saki baki tana kallona lokaci daya tana fadin"Wato bai shafe ki ba? ko ni ki keso na kwashe kayan nasa na wanke mai ishashiya Dangin Jaraba? Sai na dago kai kamar zan yi mgana sai na fasa na kama Hanya na fita Tsaakar gida yana Zaune kan kujerata ta tsuggunon Tsakar gida, ga kaya a gabansa ya saka Hafsah ta taran masa ruwan famfo Har ga Allah Dariya sai da ta kusa kamani yadda yayi kamar mai ko wankin,Karisa fitowa nayi ina fadin"wanki da kanka ina Zainab din..? Ko kallo na bai yi ba nima sai na juya ina kallon Mama da ta zata da na fito zan karbesa ne, sai taga akasin haka kafin tayi mgana na tare ta da fadin"Mama kada kiga laifina ba ga Zainab ba, ai itama matarsa ce. kince tana da Hakki a kansa kamar yadda nake dashi daman kuma kin kirata tazo ta kula dashi tunda kin ce ni ba takansa nake bi ba,Ki kirata tana ciki ta fito ta karb'i kayansa ta wanke shima ai yana daga cikin Hakkokin da kika mgana" Ina gama fad'in haka na kama Hanyar Dakina Mama ta rakani da kallo cikin mamaki tace"Fa'iza yanzu ni kike fadama wannan mganar..? Kafin nayi mgana ya katseta da fadin"Don Allah kyaleta Mama tun jiya na roketa ta rantse bazatayi ba" Sai mama ta shiga tafa Hannu tana salallami ni ko nayi shigewata Dakina na kwanta a gado na,ban san ya suka kare ba sai wajen sha d'aya na Safe na tashi na iske Hafsah ta gama Had'a zobon tana jiran ya huce ni ita ke bani Labarin yadda suka kare Zainab din ta fito tana wani yamutsa fuska tace a kwashe kayan aka kai wanki da guga zata bada kudin wai har tana fadin"Honey sai da nace kayi zaman ka achan ka ki inda kana chan wani kuma wanki ne sai kayi da kanka..? Dariya ma abun ya bani Hafsah tace"Yaya fa'iza wlh kin burgeni gwara da kika fara nuna ma Mama abunda take yi bata kyautawa" Mirmishi kawai nayi ban ce komai ba,ni ba mgana na maida mata ba Abunda ta bukata nayi mata daman na rantse bazan kara yi masa komai ba indai matarsa na nan,ba ni sun raina nawa ba? to yar masu da shi tazo tayi musu su gani. Ashe mgana bata mutu ba mama ta rika yawo dani wai Ishaq bai da lafiya bani da Tausayi da Imani na barsa zai wanke kayansa da kansa, da Mama tamin mgana nayi mata rashin kunya da Yammah sai ga Anty Binta tare da Anty Mahma har Dakina Anty Binta ta biyoni tana gayamin duk mganar da tazo bakinta cin mutumci sai wanda ta manta,Kamar na sani nace Hafsah ta tafi da Anum da Amir gidan nik'an Aya Ahmad da Musty ne kuma suna Dakin Mama wajen Fadil. Ko daga kaina ban yi na kalleta ba,sai da naga ta Dage wai in nace zan cigaba da yi ma Mama rashin kunya zamana ne zai kare a inda aka rufamin asiri sai alokacin na Dago ina kallonta kafin nace"To ko a yanzu din ma me ya rage..? Adai yi sha'ani an cuci na kauye" Bata Fahimci mganata ba ta cigaba da fadin mganarta ta dauka irin da ne har tana kokarin kamamin kunni nako mike nayi baya ina kallonta cikin Hargowa tace"Zaki dake ni ne Tattaciya..?bar ganin kin fara wannan sana'ar ta biyar goma dama bamu san asalin balbela ba ne sai ta gaya ma da ga kasar masar ta fito.." Na lura suna adawa da samun Cigaba na, a raina ko nace sai dai ku mutu sana'a yanzu na fara shi wlh. Ganin ta fara isata da mgana ga Musty ya shigo ya tsaya yana kallon mu yasa nace"kiyi hakuri Anty Binta ni fa ba rashin kunya nayi ma mama ba. Cewa tayi ta kira zainab ne saboda tazo ta kula da shi,Tunda ni ba na kula dashi. nayi laifi domin na sakar mata komai tunda gata tazo.? ai acikin kula dashi har da yi masa wankin kayansa.." Kawai sai ta kalleni bataji kunya ba tace"Lalle kin cika mara kunya Zainab din sa'arki ce ko Matsayin ku da'ya da zaki rika had'a kanki da ita..? Sai na dago ina mirmishi kafin nace'Tabbas ba matsayin mu d'aya ba, nasan wannan tun kafin ya aurota ya raba mana matsayi kuma kuka rabamananwannan matsayin. sannan ni nasan ba sa'ata bace saboda ni marainiya ce ban aje ba sannan ban ba wani ajiya ba, sannan ni ba yar gata bace kuma ba yar boko irinta ba, ni yar gargajiya ce da wahala da komai na ke rayuwata kin ga ni kaina nasan tazaran dake tsakani da ita kamar tazaran sama da kasa ne ku yi hakuri na manta ne ammh daga yau zan kiyaye zan kuma tsaya a iya matsayina" Sai ta kad'a kai tana fadin"Da kin ma kanki kiyamullaili" Ta juya ta fita Musty ya rugo da gudu ya rikeni yana fadin"Umma zagin ki take yi..?. Da sauri nace"A"a hira muke yi Musty" Yaro da Fahimtar abu sai yace"Umma naga fa fada take miki" Nasan sa da surutu su Amir na Dawowa zai gaya musu sai nace"Waya fad'a maka..? Hira muke yi baka gani ba.? Sai yayi shuru ya kasa mgana ni kuma sai na daga sa sama ina juyi da shi sai ya fara bangalan dariya. Har Anty Mahma sai da suka kitso mata zencen ta shigo Dakina tana fadin"Gaskiya Fa'iza baki kyauta ba,ban san ki da haka ba,Bai kamata bai da lafiya ki barsa da wanki ba. kuma ina ruwanki da Zainab ita da ba mazauniya ba, dubiya tazo yi zata koma inda ta fito ke dai kiyi aikin ladanki kada ki manta duk abunda kika yi na lada agidan mijinki za'a ninka miki ne kin karanta na kuma san kin san haka" Gani nayi in na tsaya mata bayani ma bata Lokaci sai kawai nace"In sha Allahu baza'a kara ba" Sai taji dadi ta dafani tana fadin"Yauwa ko ke fa Fa'iza in anjuma ki shiga ki bama Mama Hakuri shima ki basa Hakuri" Sai na gyad'a mata kai araina ina jinjina al'amarin wannan rayuwar. Sai ta gyara zama tana fadin"Hajiya Fa'iza mai zobo da kunin aya naga fa alaman kin fara samun kasa da wannan sana'ar kin zama big madam" Sai ta bani dariya na dara ina fadin"Kai Anty mahma da zoyala" Agabanta Hafsah ta had'a kunin Ayan da zasu tafi na bata harda zobo ta karba tana fadin"Kada mu zama karya Jali fa..?. Sai nace"Kada ki damu bazaku karya ba" Sai tamin godiya ta fice zuwa Dakin Mama ina jin tafiyar su ita da Anty Binta Gogan daman dakin Mama ya yini shiyasa Tun safe bamu hadu da Zainab ba sai da Daddare muna falo ina ma yara karatun Hadisi suka shigo ita da shi,Yaran sun riga sun sani in suna karatu ba na barinsu su tashi sai ba su tashi ba Ahmad ne ya mike da gudu ya nufesa sai ya Dagasa sama yana fadin"Kai ma fa ka fara zama Lukuti irin musty" Saukesa yayi ko sauraran gaurancin da Ahmad ke masa bai yi ba Zainab kuwa kala batace min ba,gani nayi kamar ranta yana bace ne sai nima na kame kaina haka suka shige ko sannu Daga shi har ita ba wanda yace min. nima ban damu ba na cigaba da yi ma yara karatu bayan mun gama nayi musu Tarihi sannan nace su je su kwanta. Ni da Anum da Hafsah muke kwana adakina Hatta Ahmad na maida shi tare da su Amir da Safiyar asabar suna da Tahfezz karfe Takwas na tafi kaisu da kaina Saboda Amir ya shiga ajin yan Hadda akwai littafan da zai siya sannan ina son naji karin bayani,na jima a makarantan suna ta gayamin kokarin yarana musamman Anum da Amir malamin Qur'anin su Anum yake min godiya lokaci d'aya yana Fadin"Saudatu ta fadamin Ummansu ke musu karatu agida sosai na yaba miki kin yi kokari kuma hakan da kike yi ya kara taimakon yara wajen hazaka da maida Hankali da ace iyaye mata da maza zasu san amfanin koyar da yaro kad'an daga abunda ka sani agida da yara da yawa sun zarce Tunanin iyayansu" Na jinjina kai ina yarda da mganarsa Saboda ban zauna ba ko na bangaran Bokon da ban iya ba ina sawa su koyama junansu na addinin kuma da na kwarewa ban ta gajiyawa ba domin shi kadai gareni da zan basu su godemin watarana. Sai wajen Tara na Dawo gidan na iske Rigima acikin gidan Tsakanin Zainab da Yaya Ishaq,Allah ya taimaka Hafsah bata nan na aiketa kasuwa ammh Badariya na gidan,Suna Dakinsa ne ammh fad'an nasu yayi kamarin da gabadayansu suke daga muryoyin su,da na dawo na kasa karisawa Dakina kamar zan shiga na gani wata zuciyar ta kwabeni tana fadin"Ke fa'iza ina ruwanki.? Aiko sai na kama kaina na kama Sabgan gabana dakin yaran na fara gyarawa na fito falo kenan Sai ga shi ya fito har yana Tureni bai sani ba nayi Saurin yin gefe kamar kububuwa haka ya shige Dakin Mama itama sai gashi ta fito tabi bayansa tana fadin"Wlh baka isa ba Ishaq" Itama tabi bayansa Fuu kamar zata tashi sama,sai gani rike da baki ina binsu da kallo ina nanata sunan Ishaq din da naji ta ambata, tunda nake ban taba jin ta kira sunansa gatsal ba sai dai Honey, ashe su Honey an jiki yau din nan. Domin duk rashin karfin jina haka na rika jiyo tashin muryoyin su Mama nayi suna yi kamar ta kasa tsawarta musu ne sai ga Badariya ta shigo da Fadil tana Lallashinsa yana ta kuka na ijiye tsintsiyan Hannuna na karbesa ina fadin"Me ya same shi? Badariya sai ta koma ta zauna tana fadin"Rudewa